Showing 12001 words to 15000 words out of 101327 words

Chapter 5 - Afiyya Book Compelet Novels By Aishatu

Aishatu   

08 Jul 2026

150

da alkhairi ya bar zumunci!"

Yayi murmushi jin Dadi yace

" Fanta dama Ina Neman ki, naso har karshen sati naje maiduguri na sameki"

Nanny ta gyara Zama tace

" Akan me fa?"

" Akan dukiyar Afiyya ne, bakya ganin ni ya kamata ace nake rike da dukiyar ta tunda ni ke rike
da ita?, Amma yaronnan Babawo sede kawai duk wata ya turo min kudi na kula da ita..."

Nanny mamaki ya karu Akan nada, dama tunda yace zai rikeni tasan tabbas dukiyar da Abbu
ya barmin yake yiwa, to Amma batai Yi tunanin zai iya fallasa abinda yake ji ba.

" Wai kana nufin shi Karamin Alhaji Bai baka komai ba?"

" Inafa ya bani Fanta? Maryam ce zata Bari ya bani. Tabi ta kankane komai, ni nake wahala da
yarinya Basu ba"

Nanny ta sauke ajiyar zuciya but ya kamata tasan me yake faruwa, hakan yasa tace

" Basu kyauta ba, ai tunda Kai ke rike da ita ya kamata komai nata ace a hannun ka yake, ya
kamata ace komai Kai kake kula dashi"

Yayi tsaki irin na bacin Rai dinnan yace

" Lokacin da akai rabon gado, akwai kadarori wajen uku da yace kada a taba ta Afiyya ce ta
makaranta, da wani gida da Kuma wata gona se gidan Mai a Kano, Babawo ko takaddu gurin
Bai zo dashi ba, ganin sun tubure ba zasu bani komai ba yasa nace musu kawai sede duk wata
su dinga aikon da kudin ciyar watta, shi ne nake tsira da wani abun fa!"
To bansan me Nanny ta yiwa kawu ba da har yayi trusting dinta yake bude Mata cikin shi bayan
Kuma daga Ummaan su matar shi Babu Wanda ya taba fadawa abinnan, Nanny ranta ya

mugun baci, ta rasa ya zata kwantata son zuciyar Kawu Sa'idu, ya takura se ya rike ni, hatta
kudin abincin da ba wani abincin arziki ake bani ba se an biya shi, wannan wanne irin rashin
zumunci ne, Bayan tasan lokacin da nawa uban nada Rai yayan shi da komai nasu shi ke
dawainiya dasu.
" Fanta so nake ki lallaba su ko gidan man ne a bani, nasan dukka kowa na ganin girman ki, ke
kika go kowa sanin abinda yake akwai, gidan Mai ya dawo hannuna, na Miki alkawarin Zan
dinga fitar Miki wani Abu a ciki"

Nanny tace

" Wannan ba matsala bane, Dana koma zanyi magana da karamin Alhaji"

Ya Mata godiya se tace Masa

" Me yasa Afiyya baka maida ta can makarantar ta Abuja ba? Bayan suna baka kudin
makarantar ta"

Yayi dariya yace

" Makaranta ai makaranta ce Fanta, ko Ina aka kaika zakai karatu, kinji tsadar makarantar ne ai
wannan almubazzaranci ne"

Hawaye Suka taru a idanun ta tayi saurin shanyewa ta koma aikin ta, shima ya Shiga ciki Yana
jin burin shi Yana daf da cika.


Kamar yadda teacher na zaure yayi ma su Junaidu alkawarin da zarar ya cika sharudda
ukunnan to kuwan zai ga aiki da cikawa, Yana gamawa ya fice zuwa inda yake koyar aiki, yayi
aikin shi se ya tafi majalissar su ya zauna, ya samu dukka suna gurin Dan kaida ce duk
yammaci se sun hadu a wañnan gurin. Suna ta Hira suna dariya Malam da Jarma na zuke
zuken abinda suka Saba, shi Junaidu ya rage sosae saboda dama influence din su ne, Amma
huzaifa Bai ma taba zuka ba shikam Malam he's always the lead. Bayan an gama maghrib
kowa ya Kama gaban shi. Fatima ce da girki tun karfe hudu ta kammalla haka take badai kaga
tayi Daren girki ba. Ruwa ta tafasa ta shiga wanka, tana watsa ruwan taji wani kaikayi a duk
inda ruwan ya sauka, ta dubi jikinta gurin yayi jawur tamkar ta kone, a gigice ta dubi ruwan tasa
hannunta Amma shima hannun tana fito dashi se kaikayi yayi jawur, zani ta daura ta fito a guje
tana kwalawa Hajja Huwaila Kira, kafin Hajja ta fito tuni Hasiya ta fito ta same ta tsakar gida
tana faman sose sosen jiki, Hasiya tace

" Fatima ya akai?"

Ta kasa magana se nuna Mata take da hannu, tana Susa, lokacin Hajja ta fito itada Amarya

suka samu Fatima tana Neman cire zanin jikin ta, ga yaran duk sun zagaye ta wasu a ciki na
kuka, hannunta Hajja ta kama Suka shiga daki, Suka fara duba jikinta, duk inda ta Sosa yayi
burdi yayi Kuma kwaf kwaf kamar konuwa. Hajja ta Yi shiru Dan ita ta rasa abinda zata ce tunda
take Bata taba ganin abin ba, ta dauka hijabi tace da Hasiya
" Ke ki zauna da Yara, ni Kuma da Amarya zamuje general, ki aika a fada ma Malam"

Da hakan Suka Taya Fatima ta shirya,suka samu Keke napep Suka tafi general, kowa idan aka
bude gurin gani suke allergy be hakan yasa focus din maaikatan asibitin, sede ana
administering drugs din kamar bama shiga suke ba, in fact tunda jikin ba bukatar su yake ba
kokarin reacting musu take. Anan Malam yazo ya same su, hankalin shi ya tashi ganin
maaikatan sun ce sede su turasu AKTH suga dermatologist kawai, Malam ya karba takardar, ga
Fatima ciwon se Kara Hawa take, se ihu take tana Kiran sunan Allah tana su taimaka Mata
kaikayi zai kasheta.



A wannan Daren da Junaidu ya dawo ya samu gidan tamkar gidan makokin, yaran na tsakar
gida sunyi jugum, Wanda sukai kuka zuwa lokacin sun hakura, Bai bi ta Kan kowa ba ya shige
dakin abin shi ya zauna Yana ayyana ya kamata ace zuwa yanzun aikin shi yaci Akan Fatima,
tunda kuwa Jarma yace Masa tamkar yankan wuka haka aikin malamin yake, Yana cikin zaune
Sega zainab ta leko, tunda sukai abin kudinnan yarinyar ke shishigge Masa tana son ganin ta
wanke laifin ta. Yana zaune ta shigo ya dago ya kalleta yace

" Meye?!"

Ta zauna tace

" Mama ce Bata da lafiya!"

Ya gyara Zama yace

" Me ya sameta?"

Ta zauna tana kuka ta fada mishi komai, maimaikon taga ya canja yanayin fuskar shi zuwa
tausayi, se taga Yana murmushi, yace

" Abin yazo kenan! Kije zata ji sauki"


Zainab jiki a sanyaye ta fito ta dawo tsakar gida tayi shiru tana tunanin halin da uwar ta ke ciki,
Bata Jima ba suka dawo da Fatima dan a wañnan Daren bazasu iya tafiya Kano ba sede zuwa
gobe. Ihun da take yasa Junaidu fitowa kofar daki ya zauna, Bai ce musu kala ba Amma se

smirking yake Yana kallon yadda Fatima ta Zama Yar bori, sight din kawai dariya yake bashi, ya
zauna yaki tafiya Yana hango duk abinda takeyi, gasu Hajja Huwaila nata karbar jike jiken
ayatul shifaa daga gurin Malam, Suka zaunar da ita suka Bata Tasha, Yana shiga cikin ta ta fara
amai bakikirin, Hajja ta Kira Malam yana zuwa yace wannan sihiri ne Kuma an karya shi, Hajja
ta rike kirji yayinda Hasiya da Amarya suka furta


"Sihiri malam!"

Ya gyada Kai yace

" Tabbas sihiri ne! Allah ya Bata lafiya"

Suka saka ta kuskure bakin ta, ta saki ajiyar zuciya ta lumshe idanu bacci ya dauke ta. Malam
ya gyada Kai ya juya zuwa dakin shi, daidai dakin Junaidu yaji Yana waya

" Man nake fada maka abin yaci fa, dukda dama ba wani tsawon lokaci zai dauka ba Amma
nasan ta karbi wahala"

Ya Jima Yana sauraron magamganun Junaidu Amma ya kasa gane inda zancen ya dosa, shi
yaron tsoro yake bashi tunda Suleiman yace ya ganshi tsakar dare Yana Kona wani Abu a
kasko shikenan ya koma jin tsoron shi. Shidai yasan kullum Yana adduar Allah ya shirya yaron
Amma Kuma har yanzun abubuwan Junaidu Kara gaba suke. Ranar baccin dadi Junaidu yayi,
Dan burin shi ya Gama cika. Da asuba kowa ya tashi yin sallah, seda ya Bari kowa ya fita
massalaci, masu Yi a gida sun tayar, ya fito Dan shi ba sallar yake ba se jefi jefi idan ya ga
dama. Dakin Fatima ya wuce ya sameta tana kan sallaya tana sallah, ya zauna Kan kujera har
ta idar Dan ita Bata lura da shigowar shi ba. Tana idar da sallar ya sakko ya nufo ta, da sauri ta
juyo zatayi ihu yace

" Junaidu ne!"

" Me kake min a daki? Fitar min daga daki nace"

Yayi dariya yace

" Ba wani Abu nazo nayi Miki ba, daki da kike cewa na fitar Miki daga shi, ai ni Banga daki anan
ba. Kinga sakamakon zagi da sharri da Kika min, ko Baki fahimci nine nasa aka Miki sihirin da
kikai kaikayin jiya, idan Baki fita harka ta ba Zan saka an Miki wanda Zaki rasa rayuwar ki gaba
daya, ko ki haukace, Kuma wallahi zakiyi kyau da hauka.."
Yayi dariya ita Kuma tuni jikinta ya fara rawa, tsabar yadda ta tsorata da maganar shi.

" Idan kinji shikenan kin tsira idan..."

Malam ya bude labulen dakin a zuciye ya Shigo, Fatima da Junaidu lokaci daya Suka Mike,
Fatima tayi saurin matsawa gefen Malam Neman kariya, yayinda Junaidu ya tsaya sokoko Yana
tunanin abinda zaiyi, Wani Mari Malam ya sauke Masa a saman kuncin sa, yayi baya kamar zai
fadi, ya cakumo wuyan shi ya tsayar dashi ya Kara Masa wani, cikin tsananin bacin Rai yace
" Ni Dana zaije gurin bokan! Malamin tsubbu! A gidana"

Junaidu yayi shiru yana kallon Malam dake janshi har ya kawo shi tsakar gida, dake fadan
malam yasa duk sun firfito Dan ganin meke faruwa, duk suna tsakar gidan yasa Sukai carko
carko suna kallon Malam da Junaidu a hannu, ga Fatima a gefe se hawaye ke bin fuskarta!





Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam First bank of Nigeria send
evidence to 09063467258.[15/12, 10:38] +227 98 36 59 34: Junaidu ya runtse idanun shi Yana
tuno kalaman malam daya bayan daya, yasa hannun shi ya hargitsa gashin da ya Tara a
kanshi, looking like the bad guy he always is, ya sakko da katon akwati ya fara life kayan shi a
ciki

" Malam kada kayi haka, kada ka yanke hukunci lokacin da ranka ya baci, yawanci idan akai
haka a gaba zaayi Dana sani, Kai me fada ne, Kai me bawa Yara tarbiyya ne kada kayi haka
Malam!"

Hasiya ta fada tana jin kamar ta kurma ihu, Hajja dama tunda taji abinda ya furta ta sulale a
gurin ta zauna, saboda tasan matsawar ta cigaba da tsayuwa jirin da take ji zai yadda ita ne a
gurin, Kuma ba lallai ta Kara taka kafafunta ba. Malam Bai ce ma Hasiya komai ba yaja hannun
Fatima ya maida ita daki sannan ya dawo tsakar gidan, Amarya ta dube shi tana kuka tace
" Malam ka sassauta zuciyar ka, ku kuke yiwa mutane waazi akan kada su Bari bacin Rai yayi
ruling din su se gashi Kai da bakin ka ka tsinewa Dan da ka Haifa ka Kuma Kore shi daga
gidan! Malam"

" Na fada Junaidu na fitar shi a cikin Yayana, kada ya Kara waiwayata sannan Kuma kada ya
Kara zuwa gidana"

Daga haka ya juya ya wuce dakin shi, Hajja ta fara kuka Hasiya na Taya ta, amarya ce me Dan
kwarin gwiwar Basu hakuri da lallashin su. Junaidu ya kammalla hada kayan shi tas, ya fara
kokarin Jan akwatin Sega Hasiya da Ummiey sun shigo, Ummiey kanwar shi ce,

" Yanzun Junaidu baka bawa mahaifin ka hakuri ba, me yasa kake haka?"

Ya kakkabe kanshi yace

" Ya Dade Bai hakura ba in har ni Zan bashi hakuri. Duniya da Fadi maye ba zaico Kan shi shi
kadai ba"

Ummiey ta rike hannun shi tace

" Dan Allah Junaidu karka tafi, Dan Allah kaje ka bashi hakuri, durkusawa wada ba gajiyawa
bane"

Ya doke hannunta yace

" Ni Zan durkusa na bashi hakuri, ni basamude ne Kinga yazan durkusawa wada kuwa?"

Ta share hawayenta tace

" Mahaifin ka ne fa, idan ka tafi Ina zakaje"

" Ke Wai Ina ruwanki, badai ya koreni ba yaje ai watarana zai neme ni, Baba Hasiya ki kula min
da Hajja nagode!"

Daga haka yaja kayan shi ya fita ko tsakar gidan Bai kalla ba balle yaje ya ma Hajja sallama,
Hasiya ta biyo shi ta rike rigar shi tace

" Tafiya zakai? Ba zaka bashi hakuri ba wai!"

" Ki Bari Dan Allah Baba Hasiya, kawai Zan wuce ne"

Daga haka Bai Kara waiwaye ba ya juya ya bar gidan, duk abin Junaidu da ya fita daga gidan
yaga Babu inda zau nufa, garin Babu mutane saboda safiya su Kuma ba Yan uwa ke gare su ba
se kawai yaji wani kunci da takaici ya lullube shi. Ya cigaba da tafiya Yana cin buri da alwashi a
cikin zuciyar shi, inda Suka Saba Zama yaje ya zauna, shi daya sannan ya fito da bankin shi ya
fasa, kudi sosae ya taru a ciki Dan shi mutum ne Mai adani bawai komai ya samu yakai ciki ba.
Kamar yasan irin wannan ranar zata zo masa ya dinga Tara kudi, mikewa yayi ya siyo abinci
yaci sannan ya dakko wayar shi ya Kira huzaifa yace Masa ya sameshi a gurin su, sannan ya
taho da sauran.


Nanny kwana biyu ta kara, ranar asabar da safe ta gama Shirin ta zata tafi, tun dare da Naga ta
na saka min komai yadda ya kamata kayan data siyo min na fara kuka, ko lallashin na Bata

Kara Yi ba ta kyalleni. Na kalleta idanuna sunyi jawur nace

" Nanny tafiya zakiyi? Ki tafi Dani Dan Allah Nanny, it's horrible living here"

Ta rike hannuna tace

" Ni awa Zan tafi dake Afiyya? Zan cigaba da zuwa Ina ganinki inshallah, duk abinda kike
bukata kimin waya zansan yadda zanyi a kawo Miki. Karki manta you've to live saboda iyayenki
su samu masu musu addua, karki manta da maraicin ki, a kullum ki tuna Allah shi ne gatanki
Kuma komai ya faru dake kaddara ce. Naga hisnul Muslim dinki a jaka, na Kara Miki wani kiyi ta
addua komai zai zo da sauki ko ba yau ba, akwai ranar da zakiji Dadi!"

Na saka kaina a hannunta na dinga kuka, zuciyata ciwo take min, a shekarun da nake dasu
kalilan na fuskanci abinda da yawa Basu San Yana wanzuwa ba.

" Idan naje maiduguri zanyi magana da dangin Maman ki muga ko zasu zo su dauke ki, sannan
zanyi magana da Alhaji karami naji ko akwai abinda zai iya Yi"

Nayi saurin girgiza Kai Ina jin bacin Rai Yana mamaye ni nace

" Nanny Dan Allah kada kiyiwa kowa magana, ki rabu dasu Dan Allah, a yanzun bana bukatar
su. Watarana Nima Zan fita daga halin da nake ciki"

Se tayi murmushi me ciwo tace

" AFIYYA kada kiyi fushi dasu, akwai abubuwan da a shekarun ki bazaki gane ba,nasan nan
gaba Zaki fahimci waye ainahin kawun ki Sa'idu. Kiyi addua sosae Allah zai kawo Miki dauki"

Kasa rakata nayi, na tsaya kofar daki nayi ta kuka, Mino da Siyama na tsaye suna kallona da
tausayi musamman Mino, Ummaan su dama Bata fito ba, daki sukai sallama, kawu ya leko yayi
Mata godiya yace Yaya ya kaita Tasha, ya koma ciki. Har ta Kai zaure se na nufe ta da gudu na
rungume ta, na rike hannun ta Ina fadin
" Nanny kin yi min alkawarin Zaki dinga zuwa akai akai ko?"

Ta gyada min Kai ta share min hawayen dake zarya a kumatuna tace

" Kiyi shiru kinji, karki Kara kuka komai zai wuce"

Ta dubi Yaya dake a hargitse, idanun shi sunyi ja tace

" Me sunan waziri amanar kanwar ka, ka kula da ita Dan Allah"

Daga haka ta fita, na Dade a zauren Ina kuka, Babu Wanda yazo ya lallashe ni seda nayi me
isata sannan na dawo ciki nayi shara na hada wuta. Nayi wanka na saka Kaya, Yan kayan Dana
cire naje na wanke su dukda ba iyawa nayi ba Amma wannan rayuwar da nake ciki ni ce uwata
ni ce ubana, Babu me cemin nayi wanki ko akasin haka, ita dai indai nayi Mata aikin ta to idan
naga dama ma kada nayi wanka. Inata sakin ajiyar zuciya naji an kwalla min Kira,na fito Amma
na kasa magana ta dubeni tace

" Bakin ki ciwo yake Miki da Zan kiraki ki ki amsawa?"

Nayi Mata shiru kawai, daka min duka tayi a cinya ta tareda dangwarar min da shayi tace

" Shegiyar yarinya kawai"

Bance komai ba na juya na bar tea din a gurin, ba abinda nake son Sha kenan ba, in fact abinci
a wañnan lokacin shi ne Abu na karshe a wanted list Dina, kawai space nake bukata. Na koma
daki nayi jugum se jin kawu Sa'idu nayi Yana kwalla min kira, na fito a hankali shima ban amsa
ba, Ina tsayawa kawia naji saukar Mari a kuncina, bana tunanin an taba Mari na, idanuna a
warwaje na rike gurin na dago na fara kallon shi, kallon da nake Masa na mamaki, tsoro, tsana
da Kuma warning, hakan yasa ya daka min tsawa yace

" Saukar da idon ki kasa shegiya kawai!"

Have you ever felt pain radiating daga zuciya zuwa kowanne sashe na jiki kuwa? Wannan
kalma ta shegiya na tsane ta, tafi Marin ciwo a gurina. Naki dauke idanuna yau taurin Kan ya
motsa , sede ya motsa inda bazan ci nasara ba. Waya ya dakko ya min duka da ita, na dinga
kuka Ina ihu Amma se zagina yake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login