Showing 27001 words to 30000 words out of 70101 words

Chapter 10 - Angon Mata Biyu Book Complete By Maryam M Hashim

tsoronsa ma nake yi tunda ya nuna bai son haihuwa,
hankalina ya tashi

"Yadda hankalina ya tashi naki bai tashi haka ba, ni da nake bukatar jikoki yaron nan nason
tozartani"

"Alhaji sai addu'ar, Addu'ar kawai zamu dinga yiwa yaron nan"

"Allah ya shirye sa"

"Amin"

Aisha kuwa tashi ta yi zaune tana kirjinta na dukan uku uku, ta ji kunya sosai, mayar da kayanta
ta yi ta koma ta kwanta, rungumar filo ta yi sosai tana tuna irin soyayyar da Don ya gwada mata,
sai ta fara jin haushin Ammi da tazo ta katse ta daga jin dadi, habadai ta cigaba da rungumar
filonta har bachci ya sace ta
Don bai tafi gida ba, wajen Wizzy ya nufa suka je suka cake abinsu da lokacin zuwa club ya yi
suka shirya suka tafi can

Washegari Aisha ta farka da asuba ta yi sallah ta roki Allah ya kare mata Baby, sannan ta koma
bachci, da gari ya fara wayrwa sai ta tashi ta je ta shiga wanka, ta fito ta shirya cikin sutura me
kyau, ai kuwa ta yi kyau sosai, ta kasa fitowa don bata son haduwa da Ammi, kawai sai ta yi
zananta bakin gado, tana jin motsin alamun za'a shugo sai ta kwanta da dauri ta rufe ido, Ammi
ce ta shugo ganin Aisha na bachci yasa ta fita, da fitarta Aisha ta tashi zaune

Haseena da tashinta ko wanka ta ga bata mata lokaci zai yi yasa bata iya jira ta yi ba, mayafi
kawai ta yafa ta fito harabar gida ta dauki motanta ta ja ta wuce gidansu Ammi

Da shugowarta falo ta ga Ammi zaune "ina kwana Ammi"

"Haseena an tashi lafiya"

"Lafiya lau Ammi, ya jikin Aisha?"

"Jikin Aisha Alhamdulillah, garau take"

Haseena jin wani abu ta yi ya tokare ta a zuciya, wani bakin ciki ya dabaibaye ta, ta jure ta ce to
bari na shiga na duba ta

Haseena ta kasa yarda da lafiyar Aisha kalau, hakan yasa zata je dubata da kanta

Aisha zaune bakin gado, tana jin motsin za'a shugo ta kwanta da sauri, Haseena ta shugo ta
tsaya tana kallan Aisha, ta shiga tashinta

"Ke tashi"

Aisha na jin muryar Haseena ta tashi zaune tana kallanta cike da tsoron karta cutar da abinda
yake cikinta

Haseena harararta ta shiga yi sannan ta ce lallai yarinya wato lafiyarki kalau, tabdijam akwai
aiki gabana

Haseena ta juya ta fita Aisha ta bita da kallo

"Oh ni Aisha, Allah ka kare ni nida abinda ke cikin cikina, Allah karka bawa wani damar cutar
dani"

Ta rungume cikinta tana jin wani farin ciki

Ammi ta ga Haseena ta fito "har zaki tafi kenan?"

"Eh Ammi zan je gida, akwai ayyukan da zanyi"

"To ya yi, sai anjima"

Haseena ta fuce, bata tsaya ko'ina ba sai kofar gidansu Bilkisu, ta yi parking ta fito ta shiga
gidan, samun Bilkisu ta yi a tsakar gida tana breakfast

"Ke wurin wani matsiyacin boka kika kaini na bashi har naira million uku bukata ta bata biya ba"

Bilkisu ta mike tana fadin ai tare dake muka je wurin malamin, wurinshi zaki je idan bukatarki bai
biya ba, ni babu ruwana

"Tabdi! Aiko baki isa ba wallahi, ko bukata ta ta biya ko nasa a kama yen gidanku"

Bilkisu ta fashe da dariya "ji karamar yer bariki, karkari idan kinsa an kama mu dole za'a so aji ta
bakina, me kike tunani idan na ce musu na rakaki wurin Boka domin kina so a kashe kishiyarki
bukatarki bai biya ba, shine kika sa a kama mu"

Haseena ta zaro ido ganin Bilkisu ta gano lagwanta, "ok ba kamaki zansa ayi ba amma ki jira ki
ga abinda zai faru"

"Haseena kenan aini duk wani iskancinki a tafin hannuna kike, kuma a bariki ma nasan inda
kika tsaya, idan naso tona miki asiri hatta mijinki sai ya rabu dake, don haka sai kija jikinki ki fitar
mana daga gida, kar kisa raina ya baci"

Cikin bacin rai Haseena ta fita, kaf duniyarnan ta rasa meke yi mata dadi, tsananin bacin rai
yasa ta biya ta je ta sayo codine ta wuce gida, ta dirka mai isanta ta kwanta tsakiyar falo bachci
ya dauke ta, cikin wannan yanayin Don ya shugo ya same ta, tsayawa ya yi yana kallanta sai
kallanshi ya kai kwalban codine, daukar kwalban ya yi ya shiga dubawa, zaro ido ya yi cikin
mamaki

"Codine ne fa"

Ya kara kallan Haseena dake kwance a kasa yana mamakin koshi bai taba shan codine ba
iyakacinsa tabar wiwi, wai matarsa ce ke shan codine, tsaki ya ja ya wuce dakin Aisha ya fada
kan gado ya kwanta yana tunanin Aisha, kewarta ce ke addabarsa, ya fara tuno irin ni'imarta, da
irin laushin fatan jikinta, ya shiga tuno yadda HQ dinta yake fitar da ruwan ni'ima, ya ji
bananarsa ta mike cak, tsintar kansa ya yi da son cin Aisha, kasa jurewa ya yi ya tashi ya fita

Ammi zaune a falo sai ga Don ya shugo idonsa ya yi ja ya tsaya yana gai da Ammi

"Ina kwana Ammi"

"Lafiya lau Umar"

Ya dan sosa keyarsa "na zo wurin Aisha ne, bari na je na ganta"

Ammi kallansa ta yi sama da kasa sannan ta ce "ba za ka ganta ba"

Ya zaro ido "meyasa?"

"Saboda baka son abin dake cikinta, ba zan bari ka cutar da abin dake cikinta ba"

Don shuru ya yi yana kallan Ammi sai kuma ya juya ya fice cikin tsananin bacin rai ta bishi da
harara "ya fi Nono fari"


Ammi yau sawa ta yi aka yi wa Aisha farar shinkafa da miyar shuwaka, ya ji kayan ciki da kayan
miya, ya yi kyau sosai, kuma an wanke shuwakar ya wanku sosai, babu daci, Ammi da kanta ta
kai mata abincin daki, ta tarar da ita tana bachci, Ammi ta ajje abincin "bachcin ya isa haka ki
tashi ki ci abinci"
Shuru Aisha ta yi tai kamar tana bachci, Ammi ta shiga tattabata "ki tashi ki ci abinci"

Tashi Aisha tai tana dan murza idanunta alamun bachci, Ammi ta shiga sa mata abinci a plate,
sai yanzu Ammi ta kula Aisha kunyarta take ji, ta kasa hada ido da ita, murmushi Ammi ta yi ta
fita ta barta, sai yanzu Aisha ta ji dai dai, sai ta gyara zamanta ta shiga cin abincin da Ammi ta
zuba mata a plate tana Santo
Haseena sai kusan karfe hudu na rana ta farka, tuni ta dauke kwalban codine ta je ta yardar
gudun kada Don ya shugo ya gani, ta shiga bayi tai wanka sannan ta fito tasa kaya ta shiga
kitchen ta hada shayi ta fito falo tana sha tana kallon talebijin

Don ne ya shugo babu sallama, ya tsaya yana kallanta, da sauri ta tashi zata je ta rungume sa,
sai ta dakata sanadiyar tsawan daya daka mata

"Baby meya faru?"

"Dama shaye shaye kike min a gida ban taba sani ba"

Ta yi shuru tana tunanin kenan Don ya shugo ya sameta cikin wannan yanayin

"Don Allah ka yi hakuri, ba halina bane, wani abu ne ya bata min rai kawai yasa na je na sayo
nasha domin samun sauki"

"Menene ya bata miki rai?"

Shuru Haseena ta yi tana rarraba ido "wani abu ne daban"

"Fada min"

"Ba wani abu bane, kawai ka manta"

"Kina so nafara zarginki, kwata kwata ban yarda dake ba, akwai abinda kike boye min"

Wucewarsa ya yi dskinta, ta tsaya tana tunanin me zata ce masa, sai ta tuna abinda zata fada
masa ta wuce dakinta da sauri

Zuwa dakinta ta yi ta ganshi yana tube kayansa alamun zai shiga wanka, sai ta je ta rungume
shi ta baya

"Zan fada maka abin daya bata min rai, kawai cikin da Aisha ta yi shi nake jin haushi, shike bata
min rai idan na tuna, banda burin daya wuce cikin ya zube"

Wani bakin ciki ya dabaibaye zuciyar Don, ya banbareta daga jikinsa ya juyo da sauri yana
kallanta

"Kina fada min cikina dake jikin Aisha shine bakya so? Ko kunyar idona baki ji ba"

Ware ido ta shiga yi "to ba kaima na ga baka son cikin ba, so fa kake a zubar"

Ya watsa mata wani mugun kallo "Nina fada miki bana son cikin?

"Ka fada a gabana naji"

"To ki sani ba wai cikin ne bana so ba, haihuwar ce ban shirya yi ba yanzu, kuma naga alamar
kamar akwai mugunta a zuciyar ki, karki kuskura na kamaki da laifin cutar da Aisha"

Ya shiga bayi bai jira ya ji me zata ce ba, ta bishi da kallo, idonta ya ciko da ruwa, zube
gwiwowinta ta yi a kasa tana mamakin yadda komai ya juye kanta, ta fara tunanin wani hanya
kuma zata bi yanzu don ganin burinta ya cika

Haka rayuwa ya kasance har tsawon wata uku, lokacin cikin Aisha na neman wata hudu, har
wannan lokacin Don bai kara zuwa gidansu Ammi ba, Aisha ta yi kyau sosai tsabar kulawar da
Ammi take bata amma fa tana kewar mijinta, tana son ganinshi, haka dai take zaman kadaici

Haseena kuwa yanzu ta canza takunta, zuwa tai ta yi odan kayan mata tana amfani dasu,
sannan ta koyo wasu salo da dibaru kala kala duk akan Don, hakan da ta yi a tunanin ta shine
mafita agareta, kuma hakan ya kasance don a kowani lokaci yana gindinta, ko'ina ya je zai
dawo ya nema ta bashi, yana yin yadda yake so, amma fa ya yi kewar Aisha, ya rasa dalilin

daya sa karamar yarinya take jagula masa lissafi, gashi yana son zuwa wurinta amma yana
tunanin Ammi, daga karshe dai ya yanke shawarar zai je kome zai faru ya faru

Ammi tana mamakin har tsawon wannan lokacin Haseena bata kara zuwa ganin jikin Aisha ba
kamar yadda a baya take nuna damuwa a kanta, kuma kota waya bata kira ba, har yanzu abin
na bawa Ammi mamaki

Ammi da Aisha zaune a falo suna hira sama sama, Ammi ta ce nafara odan kayan Baby fa'

"Me da me kika yi oda?"

"Durowa, keke, bath da sauransu" Ammi ta mike "bari naje na dakko dayar wayata na nuna
miki"

"Ok"
Ammi ta wuce Aisha zaune tabi Ammi da kallo tana murmushi tana yaba yadda sirikarta take
kulawa da ita, jin motsin an shugo yasa ta juya da sauri, Don ta gani, wani farin ciki ta ji a ranta,
ya karaso da sauri ya zauna gefenta ya rungumeta

"Haba matata meyasa zaki guje ni, ni ina can ina ta kewarki, ke kuma kina nan kina ta jin dadin
ki kin manta dani"

Marairaicewa ta yi ta yi dai dai da ido "ba kai ka ce baka son Babyna ba"

Yadda ta yi maganar ya bashi sha', awa, manna mata kiss ya yi a bakinta "taya zan ce bana son
Babynki, bayan Babyna ne nima, kawai dai ki fahimce ni ban shirya zuwan Baby ba yanzu, ki
bani hadin kai mu zubar dashi, kinga nan da shekara uku zuwa biyar saina kara yi miki wani
cikin
Da sauri Aisha ta janye jikinta daga nashi "ka wuce bana son ganinka, ni nafi son Babyna akan
kowa, ba zan taba baka hadin kai ba a kashe dana" hawaye ya ciko idanunta

"Yakamata ki fahimce ni, Aisha ke kadai ce macen da nake tunani a duniya kuma kona shirya
haihuwar Baby kece nake so ki zama mahaifiyarsa, ke nake sha'awar ki zama uwar yayana, na
yaba da tarbiyyar ki"

Ammi ce ta shugo rike da waya, tana ganin Don ta hada rai "Me kuma ya kawoka?"

"Haba Ammi bamu gaisa ba kuma naga nan ai gidanmu ne bai kamata ki tambayeni meya kawo
ni ba"

Ta galla masa harara "naji nan gidanku ne daga yau na koreka, karka kara zuwa"

Ya kalleta cike da mamaki "Ammi me na yi haka da zaki yanke min wannan hukuncin?"

"Au bakama san me ka yi ba, a gabana, a gaban Mahaifinka a gaban kowa ka ce baka son
jikana har kana fada mana a zubar, au kai bakama dauke shi wani abu ba, ya yi kyau, to sai ka
fita"

"Ammi naji zan fita amma da matata zan fita, gaskiya na gaji"

"Au jarabar taka ce ta motso ka shine ka lallabo ka zo, to babu inda zaka je da Aisha tana nan
gidan"

"Gaskiya ni dai a bani mata ta, kuma ni bada izinina aka dakko min mata ba, a karkashina take,
ni nake da iko da ita"

Ammi ta tsaya tana kallanshi cike da mamaki "to shikenan zan gani yau ni ce na haife ka ko
kaine ka haife ni"

Ta samu wuri ta zauna tana kallanshi, kallan Aisha ya yi "tashi mu tafi" Aisha ta kalleshi ta kalli
Ammi, Ammi dai nata faman kallan ikon Allah

"Ke na ce ki tashi mu tafi ko?"

Tashi Aisha tai da sauri ta koma wurin Ammi ta rungume ta

"Ammi ni bana so na tafi, zan zauna anan"

Ammi ta rungumeta tana shafar bayanta "kina nan gidan babu inda zaki je"

Cikin tsananin fushi Don ya tsaya yana kallan Aisha

Don ya kulu sosai, ganin rashin hakurinsa ba zai yi amfani ba yasa ya saukar da kai

"Ammi nifa danki ne, ki tausayawa min ki bani Aisha, ita ce kawai jin dadi na"

Ammi ta galla masa harara "me zaka yi da ita?"

Shuru ya yi yana dan sosa kai "nidai Ammi ki taimaka min, idan ba haka ba zan dawo gidan nan
na tare"

"Wallahi ka dame ni harka fara saukar min da ciwon kai, don Allah ka tafi"

Wani bakin ciki ya tsayawa Don a rai, ya fice bai ce komai ba, Aisha tabi Don da kallo,
tausayinsa ya dabaibaye mata Zuciya kamar ta tashi ta bishi amma babu dama, sai kuma ta

tuna yana son ya rabata da Bebinta ne, sai haushinsa ya kamata, Ammi ce ta kalli yanayin
fuskarta

"Ko so kike ki bishi"

Ta girgiza kai da sauri alamun a'a, nan take Ammi ta shiga nuna mata kayayyakin Baby da ta
fara oda, aikuwa kayan sunyi matukar kyau sosai, Aisha ta yi farin ciki da ganin kayan

Don wurin Wizzy ya biya yana masa complain akan abin daya faru

Wizzy ya ce haba Don miye wani abin bata rai anan, ga mata a gari, akwai fara, akwai baka,
akwai ja, akwai yaluwa, akwai wankar tarwada, akwai kore duk kallar da kake so babu wachca
ba za ka samu ba sai ka tsaya kana bata lokacinka a kan wata Aisha

Don ya girgiza kai "ba za ka gane ba Wizzy, nima narasa ya akayi, ban taba jin mace a zuciyata
ba kamar yadda nake jin Aisha, wallahi rashinta a tare dani damuwa ne, Ammi taki ta gane"

"Haba Don yawa ne wannan, da girmanka, ni Aishan nan ma fa ba wani kyau ne da ita ba
Haseena ma ta fita kyau"

Haushi Don ya ji a zuciyarsa "matar tawa ce bata da kyau?

Wizzy ya ce tooo Allah ya huci zuciyarka

"Kenan da kaje gidana kalle min mataye ka yi har ka gane daya tafi daya kyau"

"ba kalle su na yi ba da yawa, kawai a baiyana yake, kallo daya nayi musu na gane daya tafi
kyau"

Don karamar tsaki ya yi ya fice batare daya kara ce masa koma ba

Don tuka motarsa yake yana tafiya yana tunani "to wai ma meyasa zan batawa kaina lokaci
akan ta, duk zuciyata ta damu kamar ita kadai ce mace, to meyasa ta banbanta a cikin mata?
Ya tambayi kansa, sai wata zuciyarsa ta ce masa

"saboda ita ce mace na farko daka fara budewa sabuwa tal a leda, kai kadai kawai ka Santa"

Wani farin ciki ya ji ya ziyarce shi gami da yin wani ajiyar zuciya fadi yake a kasar zuciyarsa "ina
alfahari dake matata"

Hankalinsa ya kai kiran sallahn Azahar da ake yi, samun wuri ya yi yay parking sannan ya fito
ya shiga cikin masallaci

Yau Aisha dambun shinkafa tasa ayi mata, ya ji gyada da zogale, ai kuwa ta ci sosai har tai
gyatsa, can kuma ta cewa Ammi tana son shan chocolate, Ammi tasa aka kawo mata gari guda
ai kuwa Aisha tayi tasha tana jin dadi

Haseena kwance kan gadon ta tana tunanin meya faru ita har yanzu shuru babu labarin ciki,
harta fara tunanin ta je asibity ta bincike kanta ko kalau take, sai kuma ta basar da zancen data
tuna mijinta baya son haihuwa yanzu tana cikin wannan tunanin Don ya shugo, tashi ta yi ta je
ta rungumeshi
"Sannu da dawowa mijina"

"Tanx" kawai ya ce mata sannan ya banbareta daga jikinsa yaje ya zauna kan kujeran dake
dakin yana cire takalminsa, zuwa ta yi ta zauna gefensa

"Baka da lafiya ne?"

Ya juyo ya kalleta "me kika gani?"

"Na ga kamar baka cikin farin ciki, kamar akwai damuwar dake damunka"

Ya busar da wani iska daga bakinsa "babu komai"

Shafa shi ta shiga yi, ya rike hannunta "stop"

Ta tsaya tana kallansa cikin mamaki "na yi maka wani laifi ne?"

"Kawai I am not in d mood"

Ya jingina kansa da jikin kujerar kai hannu ta yi ta taba shi tana kokarin shafa shi

"Wai na tambayeki mana?"

"Ina jinka"

"Dani dake wa yafi wani jaraba?"

Shuru ta yi bata ce komai ba, sai ta janye hannunta daga jikinsa

"In kara tambayarki mana?"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0