Showing 48001 words to 51000 words out of 70101 words

Chapter 17 - Angon Mata Biyu Book Complete By Maryam M Hashim

likita watana uku bana ganin al'adana"

"Baki da ciki"

"Wallahi karya kake yi ina da ciki"

Taja tsaki cikin fushi ta fice ya bita da kallo


Haseena wani asibitin ta kara zuwa amma abu daya aka sake fada mata bata da ciki,
karyatawa ta yi sai tafi wani asibityn daban amma duk zancen daya, daga karshe ta wuce gidan
Feedo ta same ta

Feedo ta ce yana ganki haka kamar akwai damuwa

Haseena tai wani ajiyar zuciya "Feedo wai banda ciki"

"Waya fada miki baki da ciki?"

"Yanzu haka daga asibity nake, na je asibity ba daya ba ba biyu ba sun tabbatar min da single
nake"

"Taya haka zai kasance"

Feedo ni abinma da yafi damuna wata uku fa bana ganin al'adata taya za'a ce banda ciki

Feedo ta ce to abinda zai faru yanzu muje wurin Likitan da ya yi miki aiki ya sai ya bincika ya ga
meke faruwa

Feedo ta tashi suka fita, Asibitin da aka yiwa Haseena aiki suka tafi, tun a hanya Feedo ta
rubuta text message ta turawa likita abinda zai fada idan sun karaso

Suna isowa Asibityn suka wuce office din likita direct suka sameshi zauns, suma suka zauna

Feedo ta shiga magana cikin zafi zafi "Haba Doctor ya zamu biyaka milliyoyin kudi akan ta
samu ciki kuma har yanzu shuru, kuma wata uku bata ga al'adanta ba"

Likita ya ce ai haka na faruwa kuma alamun nasara ne, ya kalli Haseena "muje na kara duba ki

Haseena ta tashi suka shiga wani daki bada dadewa ba suka fito suka zauna

Feedo ta ce ya ake ciki

Likita ya ce Haseena tana dauke da ciki har na tsawan wata uku sai yasa bata ganin al'adanta

Haseena ta ce meyasa sauran Asibitin da naje suke fada min banda ciki

"Haj Haseena binciken su daban nawa daban, kuma ba zasu gani ba saboda cikin yazo da
matsala"

Feedo ta ce wani irin matsala kenan?

"Abin dake cikinta baya girma yana nan har yanxu a gudan jini but zan bata wani magani da
zata rika amfani dashi nan da wata uku cikin zai yi girma"

Wani farin ciki ya baiyana a fuskar Haseena, Feedo tai ajiyar zuciya ta kalli Haseena

"To saiki kwantar da hankalinki, tunda bincike ya nuna kina da ciki"

Haseena ta rungume Feedo tana fadin thank you my Feedo, you are so sweet

Feedo ta ce kema haka Haseena

Daga asibity gidan Feedo suka dawo cikin farin ciki, suka kunna shisharsu daya sha mix da
tabar wiwi, suna sha suna hira

Haseena ta ce ina ganin yadda Aisha zata ganni da ciki, wow nasan zata kusa mutuwa

Feedo ta ce kuma gashi dakyar ta kara samun wani cikin, kinga kenan yanzu ke zaki yi ta tara
yara a gidan

Haseena ta ji wani farin ciki a ranta sai ta ce wallahi har na kosa wata ukun nan ya cika cikina
ya fito, kawata akwai feelings fa

"Nasan zaki aikata"

Suka fashe da dariya gami da tafawa


Aisha Don kwance kan gado a bedroom din Ammi, Don sai shafa cikin Aisha yake yi yana jin
yadda Bebinshi ke motsawa

"Kamar na taba kai"

Aisha tai smile "kodai bayansa ka taba"

"A'a kaine, na gane shape din daga gani ma irin kaina ne"

Aisha tai dariya kamar cikinta zai fashe "mijina kenan mai abin dariya"

Don ya sauka daga kan gadon "to ni na gama miki sallama, zan wuce ki kulan min da Kanki da
kuma Baby"

Aisha ta marairaice tai dai dai da ido kamar za tai kuka "uhm uhm ni nafara gajiya da tafiyar da
kake yi gaskiya"

Don ya ce wannan tafiyar da nake yi don ke da Baby nakeyi kuma ya fi zaman da nake yi a
baya babu aikin yi, kinga yanxu ai nafi mutunci kuma abin ki yi alfahari ne

Sauka tai daga kan gado ta je ta rungume shi "a kullum ina alfahari da kai mijina, Allah ya tsare
min kai ya kuma daukaka min kai, ya kareka daga sharrin makiya"

Yai murmushi yana dan jan hancinta "ameen my love"

Ta kai bakinta kan bakinsa suka shiga tsotsar miyaun junansu sun kai kusan minti Bihar suna
kissing sannan suka fita

Ammi da Abba zaune a falo suna hira Haseena ta shigo cikin sallama suka amsa fuskarsu
dauke da annuri, ta zo gabansu ta durkusa "sannunku Ammi ina wuni"

"Lafiya lau Haseena"

Ammi ta ce ya kwana biyu?

"Lafiya lau wallahi Ammi"

Abba ya ce Haseena babu dai wani abu ko?

Haseena ta girgiza kai alamun a'a "Abba babu komai wallahi, muna zaune lafiya"

"To dakyau haka ake so"

Tun daga nesa Haseena ta hango Don da Aisha suna takowa daga matakan bene zasu shigo
falo, wani bakin ciki ta ji ya ziyarci zuciyarta amma ta jure ta mike ta tana fadin Oyoyo sister na
ina kewanki

Cikin Aisha bai fito ba saboda tana sanye da wani doguwar riga, dinki buba, kuma dama cikin
nata girmarsa a marane bai fitowa

Haseena ta zo ta rungumeta "sister ki dawo gida mana"

Aisha ta ce nan kusa insha Allah

Haseena ta ce yar uwa ki tayani murna fa ina da juna biyu wata uku

Aisha cikin farin ciki ta ce wow yar uwa gaskiya na tayaki murna

Aisha ta je wurinsu Ammi da sauri tana fadin Ammi yar uwata Haseena tana da ciki wata uku

Farin ciki ya baiyana a fuskar Ammi da Abba

Ammi ta ce masha Allah ina farin ciki sosai

Abba ya ce wallahi baki kaini farin ciki ba

Don kallan Haseena ya tsaya yi cikin mamaki fadi yake a zuciyarsa "me wannan kuma take nufi
da tazo tana wani karyar tana da ciki, taya zata yi ta dauki ciki, ko zata dauki ciki ai ba yanzun
ba, saita kai shekarun da zata dauka"

Ya gaji da jin shirme ya ce Ammi abba ni zan wuce

Aisha ta ce Ya Umar a cikin wannan halin zaka wace, Aunty Haseena na bukatar kulawarka,
tana dauke da Baby

Smile din karfin hali yai ya ce ga amanarta na baki saiki kula da ita, ni sai na dawo

Bai jira ya ji me za'a kara fada ba ya fice Haseena ta bishi da kallo tana murmushi

Abba ya ce Babana ya dage sosai, ya maida hankali a harkar kasuwanci

Ammi ta ce baka dan yadda nake jin dadi ba a raina

Iyayi Haseena take ta yi, mini mini ta ce tana son cin wannan, anjima ta ce wancan, haka ta
wuni ranar a gidan tana iyayi wai ita a lallai mai ciki zata haifi dan masu gida, haka ta wuni a
gidan sai wurin karfe takwas da rabi ta wuce gida

Aisha kwance kan gadon tana rike da cikinta tana tuno mijinta tana murmushi, Ammi ce ta shigo
da waya ta mika mata

"Gashi Inji Umar"

Da sauri Aisha ta tashi zaune ta amsa wayar ta manna a kunne, jin muryar Don tai ya ce Hello
wifey, wani farin ciki ta ji a ranta kuma ya baiyana a fuskarta

Ammi fita tai don su samu suyi wayarsu

Aisha ta ce Habibaty ina missing dinka sosai

Don ya ce tun dana sauka na kasa tabuka komai kawai tunaninki nake ta yi

Ta marairaice kamar za tai kuka "yaushe zaka dawo?"

"Jibi insha Allah"

"To Allah ya dawo min da kai lafiya"

"Ya Baby na?"

"Ga Bebinka yana ta tokari na"

Yai yar dariya "Dakyau Babyna, samin wayar a kan ciki naji Baby na"

Aisha ta dora wayar a kan cikinta na wani lokaci kamin ta mayar ta manna kunnanta

"Kaji ko?"

"Eh naji"

"Amma ka kira Aunty Haseena kuwa ka ji ya take ya Baby?"

Bata rai ya yi sannan ya ce ke wai waya fada miki tana da ciki, karya fa take yi

"Ya aka yi kasan bata da ciki"

Shuru Don ya yi na wani lokaci sannan ya ce ai nine mijinta banyi mata ciki ba gaskiya

Aisha ta ce Habibaty ya kake hakane, Aunty Haseena fa tana da ciki ka kula da ita

Don ya ce to shikenan na ji tana da ciki zan kira ta na duba Baby

"Yauwa Habibaty"

Haka suka cigaba da hirarsu cikin soyayya

Haseena kuwa an kasa bachci me kyau, wai imagine take yi wai ita ce take da ciki, farin ciki ya
hanata bachci, washegari kuwa tunda sassafe ta shiga kiran yan uwa da abokan arziki tana
fada musu Allah ya kawo ciki, sai fatan alkairi suke mata suna tayata farin ciki

Wizzy ya fito harabar gidansa ya je zai shiga motarsa sai ga Bilkeesu ta shigo gidan, ya dakata
yana kallanta, ta karaso har gabanshi ta tsaya, yar madaidaiciya fara, tai kyau, budan bakin
Wizzy ya ce Baiwar Allah ni yanzu na daina neman mata, ki fita kawai

Bilkisu ta dan murmusa sannan ta ce nima ba wai nazo nemanka bane domin muyi iskanci,
nazo ne domin na fada maka wani magana

Ya gyara tsayuwarsa "to ina jinki"

"Inata neman hanyar da zan hadu da abokinka Don ban samu ba, sai na samu labari kaine na
kusa dashi sosai dalilin dayasa nazo wurinka kenan"

"Menene hadinki da abokina Don?"

Ta dan murmusa "taimakonsa nake son yi, ana son halaka shi ni kuma ina son tsamo shi"

"Halaka kuma ban fahimce ki ba?"

"Matarsa Haseena tana dauke da cutar HIV"

Wizzy ya zaro ido cikin tsoro ya nunata da yatsa "ke karki kawo min rainin hankali mana, ya zaki
ce matar abokina tana dauke da HIV"

"Mijinta abokinka ne, ni kuma kawarta ce tun kafin tayi aure, nasan sirrinta da dama, da ita
muke zuwa club, nasan mazan da take hulda dasu kuma ni nake rakata wurin malamai domin
fitar da kishiyarta Aisha"

Wizzy ya rikice gabadaya, hankalinshi ya tashi, cikin kankanin lokaci kuma ya nemi Bilkisu ya
rasa, bai san yaushe ma tabar gabansa ba, fita yai yana dubata a layin, babu ita babu

kamanninta, ya dawo ya tsaya yana tunani da sake sake a zuciyarsa

"Na shiga uku, idan har yarinyarnan gaskiya take fada rayuwar Don ya kare, HIV, anya Haseena
za tai haka, yanzu na fadawa Don ne ko kuma nai shuru da bakina, gwara dai na fada masa
yasan matsayin da ake ciki"

Kiran Numban Don yake ta yi amma ba'a dauka sai can zuwa anjima da Yamma Don ya kirashi
ya fada masa aiyuka ya yi masa yawa a can inda yaje, idan ya dawo gobe zai zo su yi magana

Ta bangaran Bilkisu gidan Feedo ta wuce direct tai smile tana fadin "I know you can do it"

Bilkisu ta ce tun yaushe ai nan da kwana biyu labari zai isoki Don ya saki Haseena

Feedo ta fashe da dariya sannan ta ce kinga daga Haseena sai Aisha

Bilkisu ta ce a zuciyarta sai kuma ke shashasha karuwar mijinsu

Feedo ta hada musu shisha suka fara sha suna busar da hayaki, jin karan mota suka yi Feedo
ta kalli Bilkisu

"Kamar motan Haseena, shige uwar daka ki kulle Kanki a ciki"

Bilkisu ta tashi ta shige bedroom din Feedo ta kulle kanta a ciki dai dai da shugowar Haseena ta
karaso ta rungume Feedo

"My sweety ya kike?"

"Oyoyo my Haseena"

Haseena ta ce tun a hanya nake jin fitsari bari na shiga na yi

Feedo zaro ido tai cikin tsoro ta shiga fadi a zuciyarta "ohni Feedo ya zanyi idan Haseena ta ga
Bilkisu, nasan ma me zance mata"

"Ke kawata ban fada miki ba"

"Ina jinki"

"Bilkisu ta shigo hannu, yanzu hakama tana Bedroom dina

Haseena ta ce dakyau Feedo, sai yasa nake yinki over

Haseena ta tunkari Bedroom din, ta murda kofar ta jishi a kulle ta juyo ta kalli Feedo

"matsiyaciyar ta kulle ta ciki kamar tasan zata sha bakar azaba dani"

Feedo ta turawa Bilkisu text message akan karta taba bide kofar, ta tashi tazo bakin kofar suna
ta bibbigawa

"Dan ubanki ba zaki bude ba"

Bilkisu ta ce ba zan bude ba

Haseena ta ce kinji matsiyaciya ko to yau ina gidan nan sai kin bude, saina miki rashin mutunci

Bilkisu ta murmusa ta ce a zuciyarta "Haseena kenan ai da Feedo ta bani damar bude kofar nan
wallahi budewa zan yi nafi karfin ki duke ni, sai dai ni na yi miki shegen duka

Feedo ta ce muje musha shisharmu kafin zuwa anjima ta gaji ta bude kofar

Suka je suka zauna suna shan shishansu, Feedo ta turawa Bilkisu text message akan idan tana
jin yunwa ko kishin ruwa ta bude fridge din dakin akwai shawarma da lemu da ruwa

Ta turo mata da reply "ok"

Haseena ta zauna a gidan har dare Bilkisu bata bude kofar ta fito ba, ta kalli Feedo

"Tsinanniyar matan nan ba zata bude bafa"

Feedo ta ce idan yunwa da kishir ruwa suka addabeta dole zata fito

Haseena ta ce nidai tafiya gida zanyi, gobe da sassafe ina nan shugowa

Feedo ta mike tai mata rakiya har harabar gida, bayan Haseena ta ja motar ta ta wuce Feedo ta
dawo ciki ta tarar da Bilkisu zaune, Feedo ta fashe da dariya

"Kin zaunu yau gaskiya"

Bilkisu ta ce wallahi don dai kece kawai kika ce kada na bude amma ba don haka ba wallahi
saina fito nayi mata tsinannan duka

Feedo ta ce ai akwai lokaci yana zuwa da zaki yi mata dukan, amma ki bari sai kin gama min
aiki na sallameki, kin ga saiki yi mata duk abinda kika ga dama

Bilkisu ta watsa masa wani kallan kiyayya sannan ta mike "ni zan tafi gida"

Feedo ta ce to sai gobe, Bilkisu ta fice


Washegari Haseena tunda sassafe taje gidan Feedo amma ta tarar da babu Bilkisu, zaro ido tai
ta kalli Feedo "ina Bilkisu?"

Feedo ta ce jiya nasha Codine na yi makil, bachci ya debe ni, ban tashi bama sai yanzu da kika
shigo, bansan ya akayi ta gudu ba

Haseena ta zauna kan kujera cike da takaici "gaskiya na yi bakin ciki, wallahi naso na gurje
bakinta yai jini, na ja gashin kanta har saiya tsinke"

Feedo ta ce ai bai baci ba, zan sa akara kawo min ita, sai ki yi mata duk abinda kika ga dama

Haseena tai wani ajiyar zuciyata "ai kuwa dai kisa akara kamo mim ita, don ba zan barta ta ci
banza ba"

Feedo ta ce maman Baby kenan dafatan dai ana shan magani?

Haseena ta ce ina sha sosai, ai bana wasa, kinma san miye kuwa?

"A'a sai kin fada

"Ina son zan baki wasu kudi kije Italy ki sayo kayan Baby"

Feedo ta ce dakyau Haseena kinyi shawara me kyau, yanzu yaushe ne tafiyar?

Haseena ta ce ni ba zai yu naje ba, ke kadai zaki je, nan da wata daya insha Allah

"To Allah ya kaimu"

"Amin"

Suka kawo wani hirar daban suka fara yi

Aisha ta fito ta sami Ammi zaune a falo "Ammi sannu da kokari"

"Yauwa Aisha, ya nauyi?"

"Alhamdulillah, Ammi ni zan shiga kitchen"

Ammi ta kalleta "me zaki je kiyi a kitchen, komai kike so ki fadawa ma'aikata su kawo miki"

Aisha ta marairaice "Ni Ammi fa Ya Umar yau zai dawo, ni nake so nayi mishi abin tarba"

Ammi ta danyi smile sannan ta ce to me dadi miji kafin ki yi min kuka saiki shiga ki yi masa

Aisha ta ji wani farin ciki saita wuce kitchen ta shiga hada nau'ikan abinci da abin sha, bayan ta
gama ta kai komai Dining ta aje sannan ta wuce daki tai wanka ta yi kwalliyarta cikin wani
shadda mai uban tsada da kyalli, dinki riga da siket ne, ta rangada daurin dan kwali, ta feshe
jikinta da turaruka, ta yi matukar haduwa, ta tsaya tana kallan kanta a madubi, ta ce a zuciyarta
"na yi kiba ba laifi" saita shafa cikinta tana murmushi

"Baby ka yi missing Daddy ko? yana kan hanya yau tare zaku kwana ko?"

Ta cigaba da magana da Bebinta cikin shauki da tsananin soyayya


Wizzy shi ya je ya dakko Don daga Airport suka zo gidanshi domin tattauna maganar da Wizzy
da matsu yai dashi, Don ya kalli Wizzy

"Ina jinka Wizzy"

Wizzy ya ce a zamanka da Haseena me ka taba experience na rayuwarta, ya halinta yake
karka boye min pls

Don ya ce meya kawo maganar nan, miye dalilin wannan tambayar

Wizzy ya ce nine babban abokinka, ba zan ga abinda zai cutar da kai ba na bari, a jiya wata
Yarinya ko mata zan ce maka tazo ta same ta fada min maganganu marasa dadi akan Haseena
kuma wani abin daya bani mamaki na nemeta sama da kasa ban ganta ba kamar aljanah

Don da sauri ya ce me ta fada maka akan Haseena

Wizzy ya ce ta nuna min Haseena mutumiyar banza ne amma ni duk bai dameni ba, abin daya
fi damuna cutar da ta ce tana dauke dashi

Don ya zaro ido cikin tsoro "wani cuta kenan?"

Wizzy shuru yai yana fargaban fada masa, Don ya ce ka fada min Wizzy wani cuta ne?

"HIV"

A sittin Don ya mike yana fadin "na shiga uku"

Wizzy ya ce karka tayar da hankalinka don Allah

Don ya ce Wizzy na ga ta kaina,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0