Showing 18001 words to 21000 words out of 70101 words

Chapter 7 - Angon Mata Biyu Book Complete By Maryam M Hashim

da ban kwana ba zaki ganni, shashasha kawai, kinje kin
dafawa mijina abinci kin cika uban gishiri kina son kashe mu, kinsa mijina yaki dawowa gida, to
wallahi idan bai dawo ba yau sai kin gane kuranki dani"

Tunda Haseena tazo ta fara magana Aisha ta dukar da kai hawaye na fita daga idanunta,
Haseena ta ja tsaki ta fita, dakyar Aisha ta karasa girki ta wuce dakinta ta fada kan gado tana
kuka, ta kasa cin komai

Don da Wizzy kuwa sun dade a lagos don jirgin farko suka biyo, Naira marley mawakin kudu da
ya yi suna a duniya da kanshi yazo ya dauke su daga Airport ya kawo su gidanshi dake Victoria
island, ya yi farin cikin ganinsu, musamman Don da childhood freind dinshi ne kuma abokin cin
mushensa ne, yasa aka kawo musu haddan Wiwi da aka nade su da dala, da kuma nau'o'in
abinci da tarin wine da drinks

Bayan sun gama shan Wiwi ya rarike musu ciki suka fara cin abinci, sun ci sun koshi sosai

sannan Naira Marley ya dauke su ya kaisu wani sabon wurin hutawa da aka bude, kamar ba a
Nigeria ba ga tarin yen mata da suke kaiwa da dawowa

Aisha wuni ta yi a daki sai wurin la'asar da ta ji yunwa na neman ya yi mata illa, ta tashi ta je
kitchen ta debo breakfast din data yi da safe ta ci ta koshi sannan ta yi sallah ta kai wa Allah
kukan damuwarta

Da daddare Aisha ta fito wanka kenan Haseena ta shugo cikin fushi ta shiga masifa

"Ba zai yuhu ba ki yi laifi ya shafe ni, dole ki je ki nemo min mijina, maza fita kije ki nemo shi"

Aisha ta shiga yin kuka "ni bansan inda yake ba"

"Babu ruwana da baki san inda yake ba fita zaki yi kuma karki dawo sai da mijina"

Hankalin Haseena ya kai kan sallamar da ake yi a falo, "karki fito bari naje na duba wake
sallama na dawo"

Haseena da fitanta ta ga Prof Attahir da Mum, bata gane Iyayen Aisha bane

"Sannunku"

"Yauwa sannunki"

Duk suka zauna a kujeran falo tana musu kallan rashin sani

Mum ta ce kai ke kadai ce, ina yer uwar taki?

"Babu kowa a gidan, ni kadai ce"

Prof Attahir ya ce to ina suka je?

Da gudu Aisha ta shugo falon saboda jin muryar iyayenta, sai fadawa ta yi jikin Mum tana kuka,
Haseena ta zaro ido, Mum ta dago Aisha tana kallanta

"Yata meya faru?"

Hankalin Prof Attahir yana kan Aisha "mamana meke damunki'

Aisha ta kalli Haseena dake tsaye tasha jinin jikinta, Haseena ta yi saurin karbar bakinta

"Tunda me gidanmu ya yi tafiya jiya take ta kuka, tun dazu nake dakinta ina rarrashinta,
zuwanku ne ma yasa na fito"

Mum ta tsurawa Haseena ido "amma ai kin ce babu kowa a gidan"

Haseena ta ce na fada muku babu kowa ne saboda bana son ku ga halin da take ciki ku daga
hankalinku

Prof Attahir ya ce taya kika yi kikasan mu iyayenta ne?

Haseena ta yi murmushi "Habadai ya ba zan sanku ba kuna Iyayen mijina, Mijina ya nuna min
hotunan danginsa gabadaya"

Prof Attahir ya kalli Aisha da idanunta suka yi ja "mamana hakane duk abinda ta fada?"

Aisha ta kalli Haseena sannan ta kalli prof Attahir ta gyada kai alamun Eh

"To mamana ai hakuri ake yi, baki ga yer uwarki ta yi hakuri ba, kuma ai zai dawo, uncle dinki
yau yake fada min ya tafi lagos kulla wani kasuwanci, ki yi masa addu'ar kin ji"

Aisha bata ce komai ba, Haseena ta shiga kitchen ta kawo musu kayan marmari da drinks da
sauransu sannan ta zauna ta sake jiki suna hira sosai, sun kai wurin karfe goma sannan suka yi
shirin tafiya, Aisha ta hau yin kuka sai dai su tafi da ita, suka yi ta rarrashin ta sannan suka kara
damkawa Haseena amanarta, dakyar dai ta barsu suka wuce
Haseena wani rankwashi ta yi wa Aisha a kai, sannan ta ja kunnanta daya da karfi, Aisha sai
ihu take yi

"Idan har kika kuskura kika fadawa wani wani abu dake faruwa sai na miki tsinannan duka,
shashasha kawai"

Haseena ta ja tsaki ta wuce dakinta, Aisha rusune a falo tasa kanta a tsakankanin gwiwowinta
tana ta faman kuka

Haseena ta tsaya a tsakiyar dakinta tana tunani "au ashe tafiya ya yi, kuma ya je kulla wani
kasuwanci, to yaushe zai dawo kenan" sai ta shiga gwada numbobinsa amma basa shiga, ta
shiga safa da marwa

Aisha daga karshe ta tashi ta koma dakinta, ta kwanta tana tunanin iyayenta

Don da Wizzy, Naira Marley ya kaisu wani club da mata tsirara suke rawa, eh lallai iskancin
Lagos ya fi na Abuja, Don ya zabi lafiyayyun yen mata da zasu tayashi kwana

Haka rayuwa ya cigaba da tafiya har tsawan kwana goma, Aisha ta rame, ta yi wani fari,
zazzabi ya tasa ta a gaba, Haseena kuwa kullum saita kira Don amma har yanzu bai cire ta a

blacklist ba, ga tsinannan azaban da take bawa Aisha, Aisha tsoron Haseena take kamar ita ce
zata zare mata rai

Don da Wizzy suna ta rayuwarsu a Lagos, Wizzy ya yi mamakin ganin Sallahn jam'i baya wuce
Don, kullum sallahnsa sau biyar a masallaci yake yi, hakan yasa jefi jefi yana binshi masallac,
kusan kullum sai ya yi tunanin Aisha, amma yana mantawa da Haseena Matarsa ce, Sannan
iskancin Don ya karu, shan Wiwi da zuwa club, wasa da yen mata duk sun karu, kuma akidarsa
na rashin son haihuwa ya karu, a ganinshi duniya yanzu aka fara, yana da sauran lokaci, gwara
ya ci karanshi ba babbaka bayan wasu shekaru sai ya haihu

Haseena tasa Aisha ta yi mata sinasir da miyan gyada, Aisha na cikin yin aikin, zuciyarta ya rika
tashi, ta kasa control din kanta, sai ta barke da amai, tun daga falo Haseena take juyo karan
aman, da sauri ta tashi ta shiga kitchen din ta tsaya tana kallan Aisha cikin mamaki dake amai
kamar zata fito da kayan cikinta
"Ke kada dai ace ciki kika yi?"

Haseena ta karasa wurin Aisha bayan aman ya yi sauki, ta shiga kallan kwayar idonta tana
kallan tafin hannunta, Haseena fita ta yi tabar kitchen, Aisha ta cigaba da aikinta jikinta na rawa,
can sai ga Haseena ta dawo da abin gwajin fitsari na ciki, ta mikawa Aisha wani karamin roba

"amsa roban nan ki tsugunna ki yi fitsari a ciki"

"Aunty bana jin fitsari"

"Don uwarki ina wasa dake ne, amsa ki yi, kwakulowa zaki yi"

Hannun Aisha na rawa ta amshi roban

Aisha ta tsugunna ta rufe jikinta da zanin jikinta, ta yi fitsari a roban, bayan ta gama ta tashi

"Aunty na gama" Haseena ta galla mata harara ta je wurin fitsarin ta duka sannan ta tsoma abin
gwajin cikin a cikin fitsarin sannan ta fito dashi ta tsaya tana kallo, ta dade tana kallo amma
shuru babu amsa, fita ta yi ta dawo falo ta je wurin AC ta tsaya saboda result ya fito amma
shuru, gabadaya babu wani layi daya fito, wurin na nan yadda yake, hankalinta ya kasa
kwanciya

Aisha bata san me Haseena take nufi ba data sata ta yi fitsari ba, kawai ta cigaba da aikinta, sai
ga Haseena ta shugo a fusace

"Bar aikin nan, zo mu je asibity"
Babu musu Aisha ta ajje aikin tabi Haseena har harabar gida, Haseena da kanta ta jasu a mota
har zuwa asibity

Da isarsu asibity Haseena ta yiwa likita magana akan su bincika mata Aisha ko tana da ciki

Nan aka shigar da Aisha dakin gwaji, aka shiga bincikata

Haseena ta shugo cikin Office din Likita jikinta na rawa ta zauna tana son sanin sakamako,
Likita ya mika mata result ta amsa, cikin sauri ta shiga dubawa, Haseena ta mike a rikice

"Na shiga uku na lalace, tawa ta kare, Don Allah Doctor ka taimake ni a cire cikin nan, wallahi
zan biya ko nawa ake bukata"

Likita ya girgiza kai, "ki yi hakuri bana abortion"

"Doctor zan biyaka daga million daya zuwa sama ka taimaka min a zubar da cikin nan"

"Zaki iya fitar min daga office, na fada miki bana zubar da ciki"

Ta watsa masa kallon banza sannan ta ja tsaki, ta fita ta samu Aisha tsaye a harabar asibitin

"Yau sai kin ci ubanki dani, wato ciki kika yi Aisha"

Aisha ta zaro ido "Aunty ina da ciki ne?" Sai kuma ta yi mrmushi

Haseena ta ce au murmushi ma kike yi

"Aunty ina son baby sosai"

"To dan ubanki baki isa ki haifi wannan cikin ba da raina a duniya, da kaina zan zubar dashi"

Haseena ta ja hannun Aisha da karfi suka fuce, gida suka dawo, Haseena ta yi parking a
harabar gida, ta fito a fusace, Aisha na fitowa Haseena ta kai mata wani wawan mari da da ya yi
sanadiyar ta fadi kasa, ta fara kuka

"Aunty ki yi hakuri"

"Don ubanki waya ce ki yi ciki a gidan nan?"

Cikin muryar kuka Aisha ta ce Aunty ba laifina bane Ya Umar shiya biyoni daki ya yi min ciki

Haseena ta kara kai mata wani duka

"Wallahi sai cikin nan ya bare yau"

Aisha tasa hannu ta kare cikinta tana kuka "Aunty ki barni da cikina, ki yi min komai amma karki
taba min cikina"

Haseena ta daga kafarta zata bigawa cikin sai ta dakata sanadiyar bude Gate da Security suka
yi alamun mota zai shugo, Haseena ta yi sauri ta daga Aisha

"Yer uwata yi hakuri kin ji, kar ki yi fushi"

Mota kirar Land cruised prado ya shugo harabar gidan, Haseena ta rungume Aisha tana
rarrashinta

"Zaki sanu lafiya, kin ji yer uwata"

Aisha ta shiga manajin munafurci irin na Haseena


Abba da Ammi ne suka fito daga motar, Aisha na ganinsu ta janye jikinta daga na Haseena ta je
rungume Ammi tana kuka

Ammi da Abba suka rikice gabadaya, Haseena ta shiga gaida su, basu bi ta kan gaisuwarsu ba
suka fara tambayar meke faruwa

"Bata da lafiya yanzu muka dawo daga asibity"

Ammi da Abba suka zaro ido "meke damunta" suka fada a tare

Haseena shuru ta yi wani bakin ciki na cinta a rai, ganin bata basu amsa ba yasa Ammi ta fara
duba Aisha, ta duba idanunta da tafin hannunta, ta kalli Abba, gaban Haseena sai faduwa yake
yi

"Kamar Aisha nada ciki"

Wani farin ciki ya baiyana a fuskar Abba, Haseena ji ta yi kamar ta kwarmatsa ihu, Aisha ta rike
cikinta kam kam kamar za'a kwace mata ta kara fashewa da kuka

Ammi ta Jawota jikinta "yata yanzu cikin kikewa kuka?"

"Ammi don Allah kar a rabani da Baby na, ina son Baby na sosai"

Ammi tai murmushi "wa zai rabaki da Bebinki, wani ya fada miki za'a rabaki da Bebinki, duk
wanda ya taba Bebinki ya taba mu ne, ba za mu kyale mutum ba

Haseena ta hadiye miyau dakyar ta ce muje ciki ku zauna ko?

Abba ya ce ai ba sai mun shiga ciki ba, tunda komai lafiya kawai zamu wuce

Aisha ta kankame Ammi tana kara kuka, Ammi ta kalli Abba

"Ina ga mu tafi da Aisha gida, Jikina bai bani lafiya ba"

Haseena ta yi sauri ta ce "yanzu in kun tafi da ita, ai ni ba zan iya zama a gidan ba ni kadai,
tunda shi baya nan"

Aisha ta kara kankame Ammi, Ammi ta yi wa Haseena wani kallo "Aisha ba za ta zauna a gidan
nan ba, idan ba za ki iya zama ba, zaki iya binmu"

Haseena zuciyarta ta yi wani suya kamar ta je ta shake wuyar Ammi amma ta jure "to bari naje
na hada kayana mu tafi"

Ammi ta kalli Aisha "to kema muje ki hada kayanki mu tafi"

Duk suka shiga ciki suka bar Abba tsaye a harabar gida


Haseena data shugo dakinta, safa da marwa ta shiga yi, gumi na keto mata

"Ba zaiyuhuba dole na dauki mataki, ba zan taba yarda a haife wannan cikin ba, da naga ranar
haihuwar cikin nan gwara naga ranar mutuwata, zan bi kowani hanya koda kuwa na halaka ne
na hana haihuwarsa"

Ta janyo akwatinta ta shiga jera kayanta

Aisha da Ammi a dakin Aisha, Aisha jikinta na rawa tana hada kayanta a akwati

Ammi ta kira sunanta, ta waigo ta kalli Ammin "naam"

"Me ke faruwa a gidan nan? Alamu sun nuna akwai matsala"

Aisha ta tuno fuskar Haseena, ta girgiza kai da sauri "A'a Ammi babu abinda ke faruwa"

"Karki boye min komai, tabbas akwai matsala"

"Babu komai Ammi"

"Waya ce zai rabaki da Bebinki"

Aisha ta yi tsuru tana kallan Ammi

"Aisha daure ki fada min komai, Aisha ta kara ganin fuskar Haseena tana harararta

"Ammi babu komai, kawai ina jin tsoro ne kada a raba ni da Bebinki"

Ammi ta yi shuru tana kallanta "to shikenan gama hada kayan mu wuce, Aisha ta cigaba da
hada kaya jiki na rawa Ammi na taya ta

Bayan duk sun gama suka fito suka samu Abba tsaye yana jiransu, ma'aikatan gidan suka
shigar da akwatunan bayan mota sannan duk suka shiga motan, Direba ya jasu suka bar gidan,

Da isowansu Ammi ta nunawa Haseena dakin da zata sauka, ita kuwa Aisha dakin Ammi Ammi
ta sauke ta, ai kuwa ta yi farin ciki sosai,

Abba ya kira likita domin tabbatar da cikin Aisha, a gwaje gwajen likitan ya tabbatar da tana
dauke da juna biyu, amma bata samun isashshen abinci kuma jininta ya yi kasa sosai

Hankalin Ammi da Abba duk ya tashi, nan take Ammi tasa ma'aikatan gidan su shiga girka
nau'ikan abinci masu Karin jini duk saboda Aisha, Aisha ta fara ganin wani irin gata kamar za'a
cinye ta

Don ya sakko daga fushin da ya yi, tunanin Aisha da kewarta su suka cika masa zuciya, har ya
fara jin ba zai iya kara kwana daya ba batare da ya ji dumin jikinta ba, dakyar dai Wizzy ya
shawo kansa akan ya bari gobe sai su taho

Haseena tsaye a can saman bene, wani wurin shakatawa ne a wurin, har Swimming pool, ta yi
nisa tana tunanin yadda zata warware matsalarta, can ta tuno wata hatsabibiyar kawarta,

"Yes, Bilki ke ce zaki iya warware min matsala ta"

wayarta ta shiga lallatsawa ta kira Bilki, bugawa daya Bilkisu ta amsa

Haseena ta zaiyanowa Bilkisu damuwarta, Bilkisu ta bata shawara akan akwai wani hatsabibin
boka shine zai iya lallata cikin Aisha kuma ya mallaka mata Don, suka ajje magana akan gobe
zasu hadu su tafi wurin bokan

Bilkisu tana katse wayan ta yi dariya "ji shashasha mara hankali"

Aisha kwance kan gadon Ammi sai murmushi take yi tana shafa karamin cikinta

"Nakosa Abbanka ya dawo, ina kewarsa, ina kallan farin cikin da zai yi idan ya dawo"

Ta cigaba da shafar cikinta tana yer murmushi Ammi ta shugo da shayi a hannun ta, ta zauna
gefen gado, Aisha ta tashi zaune tanawa Ammi murmushi

"Ga shayi kisha"

Aisha ta amsa "nagode" sannan ta fara sha a hankali, Ammi na kallanta cikin farin ciki

Washegari da sassafe su Don suka biyo jirgi suka dawo Abuja, Don gidanshi ya taho direct
burinsa kawai ya yi gamo da Aisha, ya shiga falo yana kiran sunanta amma shuru, dakin Aisha
ya shiga ya tsaya yana kallan dakin, ya je ya bude durowanta ya ga babu kayan ta, hankalinsa
ya yi mugun tashi, ya fita da sauri ya je dakin Haseena, nanma shuru, itama ya bude durowanta
amma babu kaya

"To meya faru bayan tafiyata"

Wayarsa ya shiga lallatsawa ya kira Haseena

Ta bangaran Haseena tana zaune bakin gado tana shirye shiryen haduwa da Haseena sai
wayanta ya hau ringing, ganin Don yake kiranta yasa da sauri ta mike ta amsa jikinta na rawa


"Hello mijina"

"Ina kuka je?"

"Ka dawo ne?"

"Ba wannan na tambayeki ba"

"Ina kike kuma ina Aisha?"

"Muna family house, Abba da Ammi suka zo suka dauke mu jiya"

Sai ya yi wani ajiyar zuciya, ya yanke wayan "Allah nagode maka, amma meyasa su Abba suka
dauke su, bari dai naje can gidan na ji kome ya faru"

Aisha zaune ita kadai a falo tana shan ice cream, Haseena ta shugo, Aisha tana ganin Haseena
sai tsoro ya kamata, Haseena ta hango Ammi na sakkowa daga matakalan bene, sai ta yi
kamar bata ganta ba, ta fara yiwa Aisha fada

"Haba sister, ya zaki dinga shan ice cream a halin da kike ciki, so kike ki haifa mana yaro da
mura, daga yau kada na kara ganinki kina shan abu me sanyi"

Ta amshe robar Ice cream din daga hannun Aisha, dai dai da karasowar Ammi, Ammi sosai ta ji
dadi a zuciyarta, tai murmushi ta ce Aisha gaskiya Haseena take fada miki, shan abu me sanyi
ba naki bane Yanzu, Aisha bata ce komai ba, Haseena ta zauna gefen Aisha ta dan jawota
jikinta, Aisha jikinta sai rawa yake yi
"Ki kwantar da hankalinki, Oga zai dawo"

Ammi tai murmushi ta zauna tana kallansu, sai Yanzu zuciyar Ammi ta sake da Haseena, ta
kuma godewa Allah daya bawa danta mataye na gari

Duk kallansu ya koma wurin Don, da Yanzu ya shugo, Aisha ta mike da sauri wani farin ciki ya
baiyana a fuskarta, Haseena da sauri

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0