Showing 27001 words to 29251 words out of 29251 words
Chapter 10 - Allura Ta Tono Garma Book Compelet By Rookiey
ba, tunda haka ne wallahi sai an raba auren nan" ta fad'a tana kuka a lokacin ne
Aunty Fareeda ta shigo da Ayusha tace "Doctor ga patient d'in ka na dawo maka da ita wai
hajijiya take ji sosai" kafin Doctor yayi magana Aunty Khadeeja tace "Ayusha yaushe kika fita
bamu sani ba" "ai kina mik'a mata wayar ta fice ina kallon ta, dama zata ji hajijiya mana tana
tattare da yunwa cikin ta ba komai ga zazzab'i da sauran su" cewar Doctor kenan.
Aunty Fareeda ta kuma cewa "Khadeeja mai ya same ki naga kamar kina kuka" "ba kama
bane Aunty kuka nake Ayusha na d'auke da hawan jini saboda rashin adalcin da aka mata na
aura mata wanda bata so, wallahi zanyi iya kacin bakin k'ok'ari na naga an raba auren nan" sai
ta kuma fashewa da kuka.
"Yi shiru Khadeeja wannan ba maganar da zamu tattauna a nan bane saboda haka kiyi
hak'uri yanzu ta lafiyar ta muke tukun idan mu koma gida zamu san me zamuyi a kai" Doctor ya
tambaye su ko suna da wanda zai mata allura ya sa mata drip ne a gidan Anty Fareeda tace
"muna dashi Doctor wannan da kake ganin ta ma Nurse ce so zatayi duk abin da ya dace"
"OK!!! tunda haka ne ba damuwa kuje ku siyo sai tai mata abin da ya dace Allah ya bata lafiya"
"Ameen Doc." suka fad'a a tare sannan suka fita da ita.
Suna fitowa daga office d'in Doctor suka nufi pharmacy, bayan sun gama da komai suka
koma gidan Amarya suna isa suka ga gidan ya sake cika da mutane sai faman sannu ake
musu, d'akin Ango aka kaita domin nan ne ba hayaniya.
Aunty Zara'u Cousin sister d'in su ce ta shigo musu da breakfast tana fad'in "sannun ku da
dawowa, ga breakfast nan Aunty Zee ta aiko tun d'azu" "OK sannu da k'ok'ari K'awas had'awa
Ayusha tea tasha, sai tasha magani a sa mata drip" cewar Anty Fareeda kenan.
"Ok to ba matsala Allah dai ya baki lafiya Amarsu ta Alhaji, wallahi yarinya ki kwantar da
hankalin ki ki zauna da mijin ki lafiya" Aunty Zara'u gidan surutu kenan tana had'a tea tana
suburbud'a zance bayan ta gama suka sa Ayusha a gaba sai da ta kusan shanye one cup
sannan tasha magani Aunty Khady ta d'aura mata drip,a hankali ta samu bacci ya d'auke ta
sannan suma suka samu sukayi breakfast.
Sun kai kusan minti talatin suna hirar duniya sannan Aunty Khadeeja tace "Sister har yanzu
baki ce komai ba game da issue d'in Ayusha da na miki magana d'azu a asibiti ba, nifa gaskiya
zan je gida na samu Daddy na mishi bayanin abin da ke faruwa domin wallahi ni bazan iya barin
ta cikin halin nan ba"
"Matsala ta da ke gajen hak'uri wallahi, yaushe ma muka dawo gidan balle mu tattauna
batun, maganar ki akan hanya take amma yanzu mu bari idan Ayusha ta tashi daga baccin sai
muji labarin komai kafin musan matakin da zamu d'auka, kar muje mu yanke hukunci kuma ya
zama tana son kayan ta" "haba Sister wani irin so kuma wallahi tallahi Ayusha ba Son shi take
ba kawai dai an tursasata ne amma in banda k'addara me zatayi da tsoho sa'an baban ta ko ni
da nake da 26yrs yamin tsufa balle Ayusha Sweet 18"
Murmushi Aunty Zara'u tayi tace "Deeja k'aya baki san na gida ba, idan banda abin ki akwai
wanda ya isa ya wuce k'addarar sa ne? Allah ne kad'ai yasan dalilin had'a auren nan ki duba fa
kiga yadda Mum suke da Aunty Zee amma gaba d'ayan su suka iya amincewa had'in nan cikin
sauk'i ai wannan ma kad'ai ya ishe mu muyi accepting fact d'in dan haka ni a ganina raba auren
nan ba shine mafita ba addu'a ya kamata mu bisu dashi dan bamu san me zai faru a gaba ba"
"yawwa K'awas fad'a mata dai ko zata gane" cewar Aunty Fareeda kenan "babu abin da zan
gane wallahi!!! baza ku gane rad'ad'in da take ji ba tunda ku ba auren dole aka muku ba ni dai
gaskiya bazan..."
Bata k'arasa maganar ba Ayusha tayi saurin cewa "Dan Allah Aunty Khadija kiyi hak'uri kar a
ra ba auren nan wallahi ina son shi na amin ce zan zauna dashi" kawai sai ta fashe da kuka.
Da sauri suka koma wajen ta suna lallashin ta "Ayusha karki yaudari kanki da wad'an nan
kalaman da baza su miki amfanin komai ba, ni da ke da su duk mun san bakya son shi, to why
not mu samo mafitar da zata sama mana kwanciyar hankali baki d'aya, dalilin da yasa kika ga
na dage da hakan shine ni auren soyayya nayi nasan dad'in ta na san d'acin ta, idan kana son
mutum no matter how hurting d'in ka da zai yi zaka iya resisting kayi controlling kanka
albarkacin SO sai kiga zama yayi lasting forever, but idan baka son mutum baza ka iya jure
komai ba no matter how little it is baza a je ko ina ba za'a fara facing problems, kin sani mijina
barrister ne nasha ganin cases d'in aure k'iyaya a wajen shi and abin ba dad'in ji that's why
bana so kema ki shiga irin wannan halin gashi matsalar kina da kishiyoyi ba d'aya ba ba biyu ba
har uku, idan ita Anty Zee mun san tana da pure mind are we sure of the rest? dan haka
maganin kar ayi ma kar a fara ne just accept the fact that bakya son shi wallahi you will see
wonders" duk wannan bayanin Aunty Khady ke zizaro su.
Wasu Zafafan hawaye ne suka zubo daga idanun Ayusha tabbas tasan maganganun da
Aunty Khady take fad'a gaskiya ne amma baza ta tab'a accepting ba tunda har yanzu bata san
matsayin ta a wajen Dream guy ba,da ace ta san inda yake to wallahi babu abin da zai hanata
d'aukan shawarar 'yar-uwar ta, kai!!! koda tasan inda yake ma baza ta kashe auren ta ba dan
tayi alk'awarin sadaukar da farin cikin ta ga iyayen ta, "kinyi shiru Ayusha baki ce komai ba ko
har yanzu kina kan bakan ki ne?"
"Tabbas Aunty maganar ki akan hanya take amma bazan iya rabuwa da Uncle Umar ba
though ban tab'a jin ko da d'igon son shi a raina ba, nayi alk'awarin sadaukar da soyayyata
gareshi domin farantawa iyaye na, nasan duk kan ku baku gane inda zance na ya dosa ba
amma Yanzu zan warware muku zare da abawa"
Ido suka zuba mata suna kallon ta nan dai ta kwashe musu labarin abinda ya faru from A-Z
hatta labarin Dream Guy bata b'oye musu ba, sannan ta k'ara da cewa "Dan Allah Sisters kuyi
hak'uri mu yarda da k'addarar da ta same mu sannan kuyi min wata alfarma ko da wasa kar ku
bari wani yasan ina da hawan jini nayi alk'awarin kula da kai na zan koma Ayushar da kuka sani
, Mum & Dad idan suka san ina da hawan jini zasu shiga damuwa zasuyi zaton na kasa musu
biyayya ne"
Maganganun Ayusha ya tsuma su sannan ta basu tausayi sosai kaf cikin su babu wacca
bata zubar da hawaye ba amma basu da yadda suka iya da ita domin matacciyar soyayya
takeyi ,wanda take so d'in ma bata san shi bata san komai game dashi ba kuma bata da
tabbacin cewa yana son ta itama ko sun kashe auren ma a banzan domin Allah yafi mu sanin
dalilin faruwar hakan.
Anty Khady tace "Allahu Akbar Kabeeran!!!,Alhamdulillah Allah shine abin godiya, na gode
Allah da bai bari shed'an yayi tasiri a zuciya ta na aikata babban laifi ba Alhamdulillahi ala
ni'imatullah" gaba d'ayan su suka amsa da "Allah shine abin godiya" nan da suka din ga jan
Ayusha da labaran da zasu sakata nishad'i da walwala, sannu a hankali ta fara warewa kamar
ba ita ba.
*_10:00am_*
K'arfe goma dai-dai taje tayi wanka ta can cad'a kwaliya ta sa kaya ta fito fes a Amaryar ta
sak, san nan taje ta gaisa da mutane ta dawo d'akin Oga wajen Anties sunyi ta bata shawarwari
masu inganci game da yadda zata tafi da rayuwar auren ta tun da ma gidan su ba d'aya da
kishiyoyin ba.
*_Bari mu lek'a rayuwar FAHAD (Dream Guy)_*
Kamar yadda na fad'a muku a baya ya hak'ura ya fauwalawa Allah komai dangane da pretty
yaci gaba da tafi da harkokokin shi dai-dai gwargwado amma a duk lokacin da ya keb'e shi
kad'ai bashi da wani aiki sai tunanin ta da imagining irin rayuwar da za suyi da ita idan sunyi
aure.
Wani abin mamaki shine a 'yan kwanakin nan yana yawan mafarki da ita tazo ta durk'u sa a
gaban shi tana kuka tana fad'in "dan Allah dan annabi mijina ka taimakeni rayuwata tana cikin
hatsari kai ne zab'i na kai ne farin ciki na,kai kad'ai ne zaka iya taimaka min a halin da nake ciki
yanzu" shi kuma sai yaja mata dogon tsaki yana fad'in "tafi can malama ki nemi mijin ki bani ba,
ni ba sa'anki bane na miki nisa neman da nake miki ma dan in baki hak'uri ne dan gane da buga
miki motor da nayi yanzu da ki hak'ura da kar ki hak'ura duk d'aya a waje na" sai ya tafi ya bar
ta a wajen .
Da zaran ya farka daga mafarkin sai ya tashi ya d'auro alwala ya gabatar da sallah yana
kuka yana rok'on Allah ya masa zab'in da ya dace, idan gari ya waye kuma ya k'ira Mummy ya
fad'a mata labarin da mafarki da yayi sai tayi ta mishi nasiha da addu'a wani sa'in har kuka yake
mata a wayan.
Ana cikin haka ranar Sunday da yamma bayan sallar la'asar yana zaune a kan sallaya yana
tilawar Al-Qur'ani mai girma, Suratul Maryam yake karantawa,sai yaji wayar sa tayi ringing bai
d'aga ba sai da ya k'arasar da Ayar da yake.
Abokin sa Shareeef ne ya k'ira "Assalamu Alaikum warahmatullahi ta'ala wabarakatuhu"
shine abin da yace da yake gaskiya shi ba kasafai zai d'aga waya yace "Hello" ba tare da ya
fara sallama ba.
*_(Yana da kyau yan uwa musulmai idan zamu amsa waya mu fara da sallama domin wani
lokacin bamu san wane ne zai k'ira mu ba,bamu san dame yazo ba, yazo da mugun nufi ne ko
sab'anin haka wannan sallamar da zamu fara gabatarwa kafin Hello na iya zame mana garkuwa
da kariya a garemu ALLAH YASA MU DACE)_*
"Wa'alaikumussalam,Aboki na ina ka shiga haka ina ta kira bakayi picking da wuri ba,to ka
fito ka bud'e min k'ofa gani a k'ofar gidan ka dan nasan kana gida ba inda kake zuwa kamar
matar kulle" "to gani nan zuwa Suda sarkin magana idan ka fara magana no comma no full
stop"
Yana gama fad'an haka ya kashe wayan dan yasan halin Shareef da surutu ba k'aramin
aikin sa bane ya rike shi da magana a wayar ya hana shi bud'e k'ofar da wuri.
*_Kafin ya k'arasa bakin k'ofa naji an k'ira sallan magrib a 9ja shine na barsu na taho nayi
sallah so ku jira in na idar sai naci gaba da d'ebo muku rahoto da fatan masu karatu kuma idan
lokacin da kuke karantawa yayi dai-dai da na sallah zaku ajiye kuje kuyi domin sallah gaba take
komai, labarin yana nan a inda yake babu inda zai je amma Sallah idan ya wuce ya wuce kenan
sai dai na gobe ga me rabon gani daga ni har ku bamu da tabbacin cewa zamu samu na
Goben_.*
*_Allah ya bamu ikon kiyaye sallah a kan lokaci wannan itace tunatar wan da nake so na mana
ayau kuma Alhamdulillah nasan zai tunatar da wasu Allah ya bamu ikon tsira ranar
alk'iyama,Bissalam NICE DAI HAR KULLUM_*
*RØØKÍÊY D BÊST✍��*
*ROOKIEY D BEST*
Copied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
Cool novel, makeup and kitchen2⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen3⃣)
WHATSAPP NO:
+2349030159301