Showing 12001 words to 15000 words out of 29251 words

Chapter 5 - Allura Ta Tono Garma Book Compelet By Rookiey

Rookiey   

16 Jul 2026

81

ya sanka daga jiya zuwa yau duk
kabi ka susuce ka sukurkuce, ko breakfast bakayi ba ka kama hanya zaka fita kuma na tabbata
idan ka fita ma ba abincin zaka nema ba kuma kasan matsalar da kake fama da ita, dan haka
bari na d'auko maka d'umanen ka na jiya" shiru yayi yana kallonta dan yasan tunda ta zaunar
dashi to sai yaci abincin.




Tashi tayi ta shiga kitchen ta d'auko masa abincin ba tayi tsammanin zai ci na kirki ba saboda
yanayin damuwar da ke bayyane k'arara a fuskar shi amma ga mamakin ta sai taga ya cinye
tas.




"Yawwa ko kai fa da kaci abin cin ai zaka fi samun kuzari a jikin ka" "wallahi Mum yarinyar
nan A ce a girki Allah yasa pretty ma ta iya girki haka" "Ameen My Son, yanzu dai ka tashi ka
tafi wajen Abban naku" " ok Mum sai na dawo" "to a dawo lafiya Allah ya had'a ka da pretty"
"Ameen Sweetheart" ya fad'a yana dariya sannan ya fice.


Bin shi tayi da ido tana mamakin yadda akayi d'anta ya sukurkuce one time " ya Allah ka
bayyana mishi wannan yarinyar idan har alheri ce a rayuwarshi" ta fad'a a fili.




Yana fitowa daga gida ya shiga motor Mai gadi ya bud'e masa gate ya kama hanyar office
d'in Abba, a zuciyar sa sai sak'a da warwaran hanyar da zai bi yaga pretty yake, "ya zama dole
ina barin wajen Abba na shiga Yar-adua neman pretty na" wanna shine kalmar da yake ta

maimai tawa har ya isa office d'in.





Yana zuwa ya tarad da Abba da wasu bak'i seat ya samu ya zauna sannan ya gai da su a
ladabce da fara'arsu suka amsa mishi sannan Abba yace "Fahad har ka iso kenan, to ya ka
baro mutanen gidan" "lafiyan su lau Abba" d'aya daga cikin mutanen ne yace "au Alhaji Umar
kana nufin Fahad d'an wajen ka ne ya zama haka" Abba yace "k'warai kuwa" "ikon Allah
gaskiya girman d'an mutum ba wuya nifa rabona dashi ina jin tun yana secondary, Masha Allah"
Abba yace "lalle kun dad'e baku had'u ba, Fahad wannan fa Alhaji Nafi'u ne Abban Su
Muneer,wan can kuma baka san shi ba abokin mu ne Alhaji Hussain daga Niger yazo" Fahad
ya sunkuyar da kai k'asa "Allah Sarki Abba sannu da zuwa ya Niger d'in da fatan ka barota
lafiya, Abba ya gida ya su Muneer shima mun dad'e bamu had'u ba"




Alhaji Nafi'u yace "Muneer lafiyan shi lau yana India next month zai kammala masters
nashi ya dawo" "Masha Allah" cewar Fahad sannan Alhaji Hussain yace "Niger lafiya lau take,
yaushe zaka kawo mana ziyara" murmushi yayi yace "next week zan koma school amma in
shaa Allahu ida na dawo next year zan je, domin akwai friends d'ina da nake son kai wa ziyara
can" "Masha Allah ai ziyara na da kyau sosai" Abban Muneer yace "kai yanzu a ina kake karatu
ka kammala degree d'in ne ko yanzu kake yi" Murmushi Abba yayi yace "ai yaron naka da zafin
shi ya taho ya gama Degree &Masters nashi yanzu haka yana PHD a U.K next year in sha Allah
zai gama" "wow!!! lalle yaron nawa babba ne wani course yake studying" "International
relationship" cewar Abba gaba d'ayansu suka ce "gaskiya abu yayi kyau Allah yayi Albarka"
"Ameen" ya amsa musu dashi sannan Abba yace "dama ba komai bane yasa nai k'iranka,illa
ina so kaje ka gano min sabon gidan da na siya last week a FATI SHEMA ESTATE ka gano irin
gyara-gyaren da ya dace ayi sai ka sanar dani" " ok Abba in shaa Allahu yanzu zan je" "yayi
kyau Allah yayi albarka,yauwa ina fatan ka fara shirye-yen komawa school d'in dai ko?" "Ameen
Abba na gama komai" "yayi kyau" sallama ya musu ya bar office d'in.






Direct FATI SHEMA ESTATE ya wuce bayan ya duba yana yin gidan da komai da za'a
buk'ata sannan ya kama hanyar Umar Musa Yar'adua University.

```masu karatu kuci gaba da bibiyar yar Mutan yobe dan ganin me zai faru a gaba da fatan
Allura ta tono garma na baku feelings.
Na barku lafiya ni ce dai har kullum```
[14:53, 02/12/2017] +234 703 786 0131: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO*
*GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED
ON FICTION & CONCOCTION_*


® REAL PURE
MOMENT
OF LIFE WRITER'S
*MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_*





*BY*
*_ROOKIEY KAXS_*

*DEDICATED 2*
*_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_*




*_Wannan Shafin naki ne FEEDO DEEDO YAR-FICIKA My Aminiya A.K.A Mosoyiyar amma fa
a daa bcoz yanzu kin zama 'yar AIR (Lols)Allah ya barmu tare, Allah ya nuna mama ranar
Aurenku da Ahmadie muje KT mu kwashi shoki_*


51-55


Alhaji ne yayi ta maza ya fara magana kamar haka " dama ba komai ke damuna ba illa...."
sai kuma yayi shiru "illa me?, dan Allah ka daure kayi magana mana" "Hmm!!! bawai maganan
bane bana so abin da zai je ya dawo nake gudu" "kar ka damu in sha Allahu babu abinda zai
faru sai alkhairi, saboda haka feel free and say out your mind " "emm... to dama de tun ranar da
na fara kallon ta Allah ya dasa min k'aunar ta a raina, da tunanin ta nake kwana dashi nake
nake tashi, duk hanyar da zanbi naga na yak'i zuciya ta nayi amma abin ya gagara dan Allah
dan Annabi ki taimaka min na same ta wallahi idan ban mallake ta ba komai zai iya faruwa"

yana kai wa nan ya fashe da kuka.



Da sauri ta matsa kusa dashi sannan ta rungumo shi jikin ta tana bubbuga bayan shi kamar
wani k'aramin yaro sannan tace "ka kwantar da hankalin ka My Love kai kanka kasan bani da
wata matsala akan kishiya, fatana shine Allah yasa sauran matan naka su yarda" wani
sassanyan ajiyar zuciya ya saki sannan yace "Alhamdulillah! amincewar ki kawai nake nema
Hajjaju sauran nasu mai sauk'i ne"



"To amma me yasa kafi buk'atar amincewa ta fiye da na sauran matan?, ina so ka sani dukan
mu matan ka ne matsayin mu d'aya ne a wajen ka so suma suna da hak'k'in ka sanar dasu"
"haka ne amma kusancin da ke tsakanin ki da ita nake dubawa shi yasa nafi bid'ar taimakon ki"



"Hmm!!! kusanci ya wuce Wanda ke tsakani na da Muneerah amma ka rufe ido ka aureta to
yanzu me zai sa na tada hankali dan zaka auri wata" "Hajjaju kenan dan Allah ki daina tuna
abinda ya faru a baya"




"Abban Fahad kenan ai tuna baya ya zama dole, ehm! wai ni wace kake son aura ne haka da
kake cewa akwai kusanci tsakani na da ita?"



Take yaji wani wawan fad'uwan gaba saboda yasan yanzu game d'in zai fara" "kai fa nake
tambaya kamin shiru?" ta sake jefo masa wata tambayar unexpected , dakewa yayi yai ta maza
a zuciyar sa ya k'udirta cewa ya zama dole yayi jahadi ya fad'a mata ko ma wace ce !!! sai da
ya gama tattaro nutsuwar sa baki d'aya sannan yace "d'iyar ki AYUSHA 'yar Hajia Fateema
nake so,kin ga idan nayi haka na raya sunnar Manzon Allah Sallallahu Alaihi wasallam" ni
Rukayyatuwa nace "Sunnah me k'arfi ma kuwa"




"Innalillahi wa'inna ilaihi raj'un, Alhaji me kake so ka zama a duniya, yanzu budurwar zuciyar
taka har takai ka son d'iyar cikin ka, no wanda kake ta kwana-kwana ashe kasan me ka tab'uka
tsabar idon ka ya rufe zuciyar ka ta k'ek'ashe ka kasa tuna matsayin Ayusha a waje na, to idan

ka manta bari na tuna maka Ayusha 'ya ce wajen Aminiyata da muka tashi tun muna yara
saboda haka idan kai baka d'auke ta a matsayin 'ya ba ni 'ya take a guna kuma kai ma ya zama
dole ka yarda da hakan, ko da yake bazan yi mamaki ba tunda ka Auri Muneerah waye baza ka
aura ba, ina so kasan wani abu guda nasan tunda ka furta kana sonta ban isa na fidda maka ita
daga zuciyarka ba amma ka sani k'arshen zamana da kai yazo, saboda bazan tab'a iya had'a
shimfid'ar aure da d'iyar ciki na ba, ina!!! wallahi never,over my dead body" tana gama fad'in
haka ta fashe da kuka sannan ta mik'e ta nufi hanyar fita.




Tana zuwa bakin k'ofa yayi saurin zuwa ya sha gabanta, zuba gwiwowin sa yayi a k'asa ya
dafa k'afafun ta da hannayen sa sannan yace "Hajia dan girman Allah kiyi hak'uri ki fahimce ni,
wallahi banyi hakan da niyar CIN AMANA KO CIN ZARAFI a gareki ba illa dan zuciyata ta samu
sukuni daga tarkon da ta afka, nima ba yin kaina bane, kin san shi SO ba ruwansa da cancanta,
ba ruwansa da dangantaka,please kiyi hak'uri ki taimaka ki cetoni, ki fidda ni cikin halin da nake
ciki, wallahi tallahi ba yin kaina bane" sai ya fashe da kuka, bangaje shi tayi tace "dakata malam
ni fa ban hanaka auran abinda zuciyar ka ke so ba, idan ka ga dama ba Ayusha ba ka had'ada
Hafsat da Maryam ma ka auro ba damuwata bane amma ka sani ni Zainab bazan iya zama da
kai a matsayin miji ba, mai budurwar zuciya kawai mtswww...." ta fice ta barshi a d'akin.




Tunda ta shiga d'akin take ta faman Safah da Marwa, can ta tuna ashe fa ta manta wayan ta
a d'akin shi da sauri ta nufi hanyar d'akin nasa domin tana da buk'atar wayan a kusa da ita,
tana shiga d'akin ta tarar dashi kwance shame-shame a k'asa dak'yar yake numfashi, da sauri
ta nufi inda yake "na shiga uku Alhaji lafiya!!! , me ya sameka" a dai-dai lokacin ta k'arasa
wajen da yake kwance, wani nishi me k'arfi taji ya sake sai numfashin sa ya d'auke d'if!!! wani
mahaukacin k'ara ta saki "wayyo Allah jama'a kuzo ku taimakeni Alhaji ya mutu" da gudu
mutanen gidan suka hallara, basu tsaya wata -wata sukayi rushing nashi zuwa AUTOPEDIC
HOSPITAL dake nan katsina.


```TAKU HAR KULLUM```



*ROOKIEY D BEST*
[14:54, 02/12/2017] +234 703 786 0131: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO*
*GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED
ON FICTION & CONCOCTION_*

® REAL PURE
MOMENT
OF LIFE WRITER'S
*MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_*





*BY*
*_ROOKIEY KAXS_*

*DEDICATED 2*
*_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_*




*_Wannan Shafin naku ne_!!!*
*_AYUSHA ILIASU MUSA (the eloquent writer of 'YAR BOKO very Interested and Educative
Novel) & AMEERAH AMNOOR (Saraku for life)na gode sosai da gudunmawar da kuke bani
Allah ya bar zumunci (AMEEN) ina k'aunar ku har cikin raina irin SOSAI d'innan��_*



55-60



Suna zuwa asibiti aka shiga dashi emergency room, likitoci biyu ne a kanshi, take nan suka
shiga bashi taimakon gaggawa. Hajia Zee da sauran kishiyoyin ta na zaune a reception sun
shiga cikin matsanan cin tashin hakali, kallo d'aya zaka musu su baka tausayi most especially
ita da tafi kowa sanin mene ne musabbabin abin, tambayar ta suke me ya sameshi amma ta
kasa basu amsar komai saboda tasan zafin kishin Muneerah yanzu sai ta fara musu hauka a
asibiti shiyasa suna tambayar ma tace "yanzu bata wannan muke ba, fatan mu dai Allah ya
bashi lafiya sai muyi maganar daga baya".




*_BAYAN HOUR D'AYA_*

Dr' Sa'ad ne ya fito biye dashi wata nurse ce hannun ta d'auke da file, yana k'arasowa suka
nufi wajen shi at once suka jefo mishi tambaya "Likita ya jikin nashi, ya farfad'o ne?" "Ku biyo ni
office mayi magana can"



Suna shiga suka samu waje suka zauna, rubutu yayi a hospital card nashi sannan yace dasu
"Hajiya ku kwantar da hankalinku in shaa Allahu zai samu lafiya, dama yana da Asthma ne?"
"Eh! Doctor yana dashi " "ok, Allah ya basa lafiya, asthma d'insa ce ta tace due to wani abu na
b'acin rai da ya sameshi and bai samu yasha magani ba har k'arfin numfashins sa ya d'auke so
hakan yayi leading to doguwar suma, yanzu haka Dr. Ahmad na gudanar da wasu bincike a
kansa in shaa Allahu zai farfad'o any moment from now, so ga wannan kuje pharmacy ku siyo
da sauri magani ne da allurai, dan yana farkawa za'a mishi alluran "




Da sauri Anty ta k'arba tace mun gode Doctor, sannan suka fice daga office d'in zuwa siyan
magani, tana zuwa pharmacy aka duba bubu ko d'aya daga cikin so da sauri ta k'ira driver a
waya yazo ya sameta su shiga gari ne, ko minti uku batayi da k'iranshi ba ya zo suka tafi.Sun je
a k'allah chemist uku basu samu ba sai a na hud'un suka samu complete.



Ko 30 minutes basuyi da fita ba alhaji ya farfad'o a dai-dai lokacin Hajia Muneerah da Hajia
Rahma sun shigo, "Hajia dan Allah dan Annabi ki barni na aureta, wallahi nayi alk'awarin yin
adalci a tsakanin ku" kalmar da ta fara fitowa daga bakin shi kenan.



"Tabd'i jam!!! wallahi sai dai ka mutu baka aureta ba, wato dama ciwon SO ne ya kwantar da
kai anan duk muka bi muka tada hankalin mu to wallahi baka isa ba" "haba Muneera me yasa
sam baki da tausayi ne, ki dubi halin da bawan Allan nan yake ciki amma kizo ki titsiye shi da
masifa da wanne zai ji da ciwon da ke jikin shi ko da masifar ki"


"Ai dama ke ba hankali ne dake ba Rahma!!! ko da yake kin ci amanata kin aure min miji ai
baza ki damu ba dan yace zai k'ara aure" " dakata!!! malam kar ki nemi ki wuce gona da iri dan
na auri mijin ki sai me, ke d'in ba mijin wata kika aure ba, idan abin kunyar ne ma ai daga gindin
ku ya fara fitowa mtsww!!!"

Suna cikin hayaniyar Anty Zee ta shigo d'akin idonta bai sauk'a a ko ina ba sai kan Allahi da
yake ta fitar da wani irin numfashi yana kakarin amai, da sauri ta bankad'e su ta nufi wajen shi
tana "innalillahi wa'inna ilaihi raj'un!!!"a dai-dai lokacin ya fara amai, wani ihu Anty Zee ta saki
"wayyo Allah na shiga uku!!! shi kenan kun k'arasa shi aman jini fa ya keyi" wani mugun tsaki
Muneerah ta saki sannan tace "idan k'arasawan ne ma sai dai in ke zaki k'arashi tun da kin k'i
amince mishi ya aure wacca yake so, wallahi ki sani duk abinda ya samu mujina to kiyi kuka da
kanki" tana gama fad'in haka ta fita ta nufi office d'in Doctor Sa'ad da gudu.



Abin bai bawa Anty Zee mamaki ba saboda ta dad'e da fahimtar cewa Muneerah, jaka ce
bata hankali, a kan kishi babu abinda bazata iya yi ba.Ita ko Rahma nufowa tayi wurin Anty Zee
ta taimaka mata suka d'aga Alhaji dan har ya gangaro daga kan gadon.





Doctor Sa'ad ne zaune a office Muneerah ta shigo da gudu Doc!! Doc!! please we need
your help Alhaji zai mutu kazo da sauri ka taimake shi kar ya mutu" kawai sai ta fashe da kuka
"Sorry Madam,you don't need to cry addu'ar ki yafi buk'ata by now , so muje in ganshi"




Suna shiga suka tarar Doctor Ahmad yazo joining nashi Sa'ad yayi suka bashi duk wata
kulawa da ya dace, alluran da aka siyo Sa'ad ya mishi sannan ya umarce su da su biyo su
office d'in doctor Ahmad.



Suna shiga suka basu wajen zama, bayan sun zauna Doctor Ahmad ya fara magana kamar
haka "da farko ina so na sanar daku cutar da ke damun mijin ku tare da hanyoyin da za'a bi a
shawo kan matsalan, idan har kuna son lafiyar mijin ku ya inganta to sai kun taimaka masa, kun
k'arfafa masa gwiwa wajen ganin ya samu abin da yake so, mijin ku ya kamu da Heart Attack
wanda akafi sani da ciwon zuciya sakamakon mummunan b'acin rai da ya shiga game da wani
abu wanda mu nan bamu sani ba sai ku matansa, rashin wannan abin na iya zama barazana ga
rayuwarsa"

Doctor Sa'ad kuma ne yace "kamar yadda d'an uwana ya muku bayani zan d'aura nawa
akai, mutanen da suke d'auke da irin wannan cutar suna buk'atar kulawa ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login