Showing 24001 words to 27000 words out of 29251 words
school ```
*RØØKÏÊY D BEST*
[14:56, 02/12/2017] +234 703 786 0131: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO*
*GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED
ON FICTION & CONCOCTION_*
® REAL PURE
MOMENT
OF LIFE WRITER'S
*MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_*
*BY*
*_ROOKIEY KAXS_*
*DEDICATED 2*
*_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_*
*_Assalamu Alaikum Masoya na nayi farin ciki sosai da na dinga cin karo da sak'wanninku
tabbas idan ba makaranta barubuta, amma ina so ku fahimci wani abu guda d'aya idan muka ce
a rayuwa duk abin da muke so sai mun samu to muna tare da wahala sannan akwai matsala
babba domin wani abun ba alheri bane idan mun k'wallafa rai mun same shi daga baya za
muzo muna da nasani dan haka dan Allah 'yan-uwana mu kiyaye mu rungumi duk k'addarar da
ta zo mana hannu bibbiyu, saboda haka ina so duk abin da ya faru a littafin nan ku d'aukeshi a
matsayin K'ADDARA da JARABAWA, Muje Zuwa. sannan wannan Shafin na sadaukar dashi
ga duk wani masoyin ALLURA TA TONO GARMA����_*
91-95
Washe gari da safe bayan sun kammala komai na aikin gidan suka yi shirin school sannan
suka had'u a dinning dan yin breakfast, Favorite food d'in Ayusha Mummy ta dafa wato D'an
wake amma abin mamaki shine kowa yana cin abincin banda ita ta tsaya sai jujjuya fork take.
Dad ya dube ta da kyau yace "Auta lafiya bakya cin abincin, tunanin me kikeyi haka?" "ba
komai" "da komai mana Auta,tunda kin kasa kai koda gudan d'anwake d'aya ne bakin ki, while
kin san cewa saboda ke nayi d'an waken nan" "wallahi Mummy bana jin zan iya cin d'anwaken
nan saboda gaba d'aya nayi loosing appetite d'ina, baki na ba taste wallah" Dad yace "Look
Auta!!! har yanzu akwai sauran damuwa a tattare da ke so say out your mind ni kuma nayi miki
alk'awari zan zame miki garkuwa na miki abinda kike so idan bai fi k'arfina ba"
Kallaman Dad sun matuk'ar kashe mata jiki har take jin ba zata iya gabatar musu da
buk'arta ba amma wata zuciyar tace da ita "haba Ayusha this is the only opportunity left!!!
wallahi idan kikayi wasa da wannan damar shike nan kin rasa Dream Guy d'inki har abada, you
better do something to save your love, ki zab'i inda zaki samu farincikin rayuwar ki, me zakiyi da
tsoho ai yaro sai yarinya "
D'aya zuciyar kuma tace "a gaskiya Ayusha idan kikayi haka baki kyautawa iyayen ki ba ki
duba kiga irin damuwar da suka shiga yanzu sakamakon rashin cin abincin ki, har suna ikirarin
komai kike buk'ata zasu miki, to idan ki sanar musu canjin ra'ayin da kikayi ya zasuyi feeling and
da wani ido zasu kalli su Anty Zee while in public kika furta cewa kin amince da auren Alhaji
Umar, ya kamata ki dawo hayyacin ki kisan me kikeyi domin dream guy d'in naki ma bai san da
existence naki ba balle ya damu dake"
Bata gama deciding wace zuciya zata bi ba taji Mummy ta jefo mata tambaya a k'ufule "wai
ke ba magana ake miki bane kikai banza da mutane Ayusha bana son sakarcin banza da wofi
fa". wasu hot-hot tears ne suka fara gangarowa daga idon ta a hankali ta bud'i baki zatayi
magana sai ta tsinci kanta a mai jin kunyar iyayen ta.
Dad yace "kinga Auta idan baza kiyi magana ba shikenan, amma ki sani barin damuwar taki
a ciki ba shi zai magance miki ita ba. "Dad dama ba komai bane fa, tun jiya da muka baro asibiti
nake ta tunanin halin da Uncle Umar yake ciki shine nake so idan mun tashi daga school mu
biya mu duba shi"
A take Mum ta fara washe baki "dama wannan ne damuwarki kika tsaya kina wani
kwane-kwane, ba komai idan kun tashi daga school d'in sai ku je" nazarin ta sosao Dad yayi
sanna yace "kin tabbata abin da kika fad'a mana haka ne?" "Eh haka ne" "to shike nan Allah ya
miki albarka ya baki ladan biyayyan da kika mana, shima Alhajin idan yaji sauk'i sai a fara
zancen biki dan ba wani dogon lokaci za'a d'auka ba saboda yanayin da ake ciki"
Da k'yar da lallami suka shawo kanta taci abincin, bayan sun gama Dad ya basu kud'i yace
su Siya fruits da drinks su kai asibitin.
Suna fita ta fashe da kuka Aneeserh tace "dan Allah K'awata ki kwantar da hankalin ki
mana, naga alama kin kasa karb'ar k'addarar da ta zo miki, saboda haka ni zan koma ciki na
sanar da Mum &Dad cewa kin janye maganar auren Alhaji Umar ai abin is understandable "
tana gama fad'an haka ta juya da niyyar komawa gida da sauri Ayusha tasha gabanta "dan
Allah kiyi hak'uri K'awata wallahi na kasa amincewa zuciyata ta so shi amma daga yanzu na
miki alk'awarin zan amince dashi zan karb'e shi a matsayin hannu bibbiyu koda kuwa hakan na
shirin barazana ga rayuwata ne saboda haka daga yanzu na sadaukar da soyayya Dream guy
zuwa gare shi"
Rungumota Aneeserh tayi sukayi ta kuka san ransu sannan suka k'arasa car park Ayusha ta
bata key ba musu ta karb'a da yake itama ta iya motan suka nufi boko, da yamma liss suka je
asibiti, abubuwa da dama sun faru tsakani Ayusha da A. Umar tayi k'ok'arin danne tsanar sa a
fili ta bashi kulawa ta musamman, ita ko Anty Zee sai nan-nan take da Ayusha kar abu kad'an
ya faru tace ta faso domin tayi observing cewa dauriya kawai takeyi ba son shi takeyi ba, Allah
ya taimaka Muneerah bata nan tun jiya da ta fice bata sake lek'ewo ba, Rahma ma tunda ta tafi
da azahar bata dawo ba so abin ya zo da sauk'i, sai da sukayi Magrib sannan suka koma gida.
Kusan kullum Ayusha sai taje duba Alhaji Umar amma fa kullum da daddare bata bacci
dream guy d'in ta ne ke zuwa mata a mafarki da kalamai masu rikitarwa tun tana damuwa har
ya zama jiki.
Bayan sati d'aya aka sallami Alhaji Umar daga asibiti Alhamdulillah an samu improvement
sosai domin ya dawo normal sai d'an abinda ba'a rasa ba, kwanan shi uku da sallama ya fara
zuwa Zance, Ayusha in taje banda Uhm.. da ummm-ummm babu abinda take cewa har a tashi
daga hiran idan ta dawo tayi ta kuka domin yanzu Aneeserh mai d'ebe mata kewar ma bata nan
ta tattara ta koma school.
A kwana a tashi ba wuya har sun fara exams a lokacin ne aka. tsaida lokacin auren ta da
Alhaji bayan ta gama exam's da two weeks, ba k'aramin tashin hankali Ayusha ta shiga ba da
jin labarin auren, amma saboda tsananin tawakkali irin nata bata tab'a yarda Mum &Dad ko
Aneeserh sun gane hakan ba, sannan bata da aikin yi cikin dare sai ibada, (karatun Al-Qur'ani
mai girma, Nafilfili da Nagartattun addu'oi) tana sanar da ubangiji damuwar ta.
Ranar last paper sukayi sharing IV k'awayen ta mamaki suke domin sun san Ayusha bata
son aure yanzu ita da take ikirarin sai tayi Masters da PHD sai gashi 300level d'in ma bata
gama ba zata shiga daga ciki, da suka isheta da zolaye tace "kai ku k'yaleni lokaci na ne yayi,
daa d'in ma yarinta ne ke damuna, yanzu da na girma ba gashi na rigaku kawo miji ba "
Sai suka kwashe da dariya suna tambayar ta event nawa za'ayi a bikin Sai tace dasu "ku
kwantar da hankalinku 'yammata, bawani bidia zamuyi a bikin ba domin mijina Ustazu ne,
walima ce ran Friday sai yini ran Saturday that's all, batun anko kuma ba siya zakuyi ba Daddy
ya mana odar dogayen rugunan da zamu sa a walima shi kuma ango ya siyo mana atamfar da
zaku sa ranar d'aurin aure abinda zakuyi kawai d'inki ne fak'at!!!"
Nan fa 'yammata suka kacame da hayaniya kowa na tofa albarkacin bakinshi daga masu
cewa"gaskiya Dad da Ango sunyi sun rage mana wahala" "gaskiya an kwafsa mana da baza'ayi
chasu ba" sai masu cewa "hakan ma yayi dai-dai ai, albarkar aure ake nema ba komai ba"
Bayan sun gama exam's da kwana biyu suka shiga raba anko daya yake friends d'in nasu
basu da yawa basu wuce 20-25 ba a kwana 3 suka kammala komai domin AYUSHA ba wani
gayya tayi niyyar yi ba suma wad'annan d'in dalilin da yasa ta basu I.V ba komai bane illa
course mates nata ne da kunya suna tare ba'ayi grads ba suji labarin tayi aure ba invitation, da
baza tayi inviting nasu ba.
Sun gama rabiya da kwana d'aya suka tattara suka nufi D'angyatin garin su Aneeserh tare
da Mum & Dad, iyayen Ayusha sun sha wahala sosai wajen shawo kan iyayen Aneeserh akan
abin da suke aikata mata, da farko iyayen ta rufa ido sukayi suka fara rashin mutunci "wai su
babu wanda ya isa ya koya musu yadda zasu tafi da rayuwar iyalinsu, wato ma dan rashin
mutunci ma k'ararsu ta kai ko? to daga yanzu sun soke university d'in ma zaman gida za tayi
tunda bata san ciwon kanta ba" da yake Mum &Dad mutane ne wayayyu sun san yadda zasu bi
da mutum duk irin bak'aken maganganun da suke fad'a musu bai sa sunyi fushi dasu ba, sai ma
gyara zama da sukayi saka fara sanar da su illar abin da girman hak'k'in d'a akan iyayen sa.
Jikinsu yayi sanyi sosai sukayi ta kuka suna neman gafarar Aneeserh sannan suka ce ta
sanar da Mujaheed idan ya shirya ya turo magabatan sa a d'aura musu aure rana d'aya da
Ayusha, nan dai farin ciki ya dawo sabo"
Nan fa Dad ya nemi alfarma cewa idan iyayen Mujaheed sun amince da auren yana so a
d'aura a katsina tunda can Aneeserh zata zauna, sannan batun kayan d'aki shi zai musu,
Abban Aneeserh yace ya amince a d'aura auren a can amma shi zai musu komai da komai
domin a karo ma farko ya faranta ran d'iyar sa.
Kowa ya amince da hakan domin Wannan alamu ne na cewa ya zubda makaman shi,
Ayusha ce tayi wa Mujaheed waya ta sanar dashi abin farin cikin da ya faru, yayi murna sosai
da daddare ya k'ira ta ya tabbatar mata da cewa gobe iyayen shi zasu zo, a daren suka sanar
da iyayensu.
Kamar yadda Mujaheed ya fad'a hakan kuwa akayi domin iyayensa sun zo an tsaida
maganar aure, washe gari Mum & Dad suka koma Katsina suka bar su Ayusha a D'angyatin
domin Maman Aneeserh tace itama baza a barta a baya ba ita zata gyara 'yammatan ta in yaso
ana sauran two days to bikin sai suje gaba d'ayan su.
Duk abinda aka sa masa rana sai yazo yau ta kasance ranar walimar Auren Ayusha da
Aneeserh inda Angwaye da Amare da sauran 'yan uwa da abokan arziki suke farin cikin
wannan ranar banda Ayusha domin ta so ace da dream guy d'in ta akeyi amma haka tayi ta
managing rayuwar ta har zuwa ranar d'aurin Auren.
Ranar Saturday da misalin 10: 30 am aka shaida d'aurin auren ANEESERH da MUJAHEED,
AYUSHA da ALHAJI UMAR muna musu fatan zaman lafiya da farin ciki mai d'orewa.
Lokacin da Ayusha taji an d'aura aure haukacewa ne kawai batayi ba domin dak'yar
Aneeserh dak'awayen su suka shawo kanta domin tirewa tayi sai an warware auren Allah yaso
duk Dramar da akeyi iyayen su basu sani ba so sunyi nasaran shawo kanta amma fa wunin
ranar da ba a dad'in rai tayi ba.
Da dare yayi su Anty Zee 'yan d'aukar Amarya suka zo nan ma Ayusha tace bata san zance
ba da yake normally amare nayin haka sai mutane basu fahimci komai ba, ana cikin show d'in
dangin Mujaheed suka zo nan fa aiki ya dawo sabo da k'yar aka raba Ayusha da Aneeserh
domin kowa cewa take ba zata tafi ba sai ta raka 'yar-uwarta sai da aka musu da gaske kafin
suka rabu.
SARDAUNA ESTATE aka kai ANEESERH ita kuma AYUSHA G.R.A daren ranar da
zazzab'i ta kwana duk wanda suka kwana a gidan ta basuyi baccin kirki ba domin ta matuk'ar
tada musu hankali. Nidai RØØKÌÊY KÆXS nace Allah ya bada zaman Lafiya AYUSHMAR, ya
kawo Zuria d'ayyaba.
Kuma ANEESMU ban barku a baya ba duk da cewa kuna k'aunar junanku hakan ba shi zai
sa na kasa yi muku addu'a da fatan alkhairi ba.
*_#TEAM FAHAD kuyi hak'uri da abinda ya faru nima ba da son raina Alhaji ya auri Ayusha ba
amma ku sani mutum bai isa ya wuce k'addarar sa ba, kuyi duba ga Aneeserh a lokacin da
batayi zato ba rayuwarta ta canza ta dawo dai-dai domin ta tsaya ta jajirce ta mik'a lamuran ta
ga Allah. Dan haka kuyi hak'uri kuci gaba da bibiyata domin tsugunno bata k'are ba dan har
yanzu ALLURA bata TONO GARMA ba._*
*RØØKÎËY D BEST*
[14:56, 02/12/2017] +234 703 786 0131: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO*
*GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED
ON FICTION & CONCOCTION_*
® REAL PURE
MOMENT
OF LIFE WRITER'S
*MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_*
*BY*
*_ROOKIEY KAXS_*
*DEDICATED 2*
*_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_*
96-100
Washe gari da safe jikin Ayusha ya tsanan ta sosai dan haka ba'ayi wata-wata ba su Aunty
Fareeda suka kaita ALHERI SPECIALIST HOSPITAL wani private hospital da ke nan G.R.A.
suna zuwa basu tarar da mutane ba kasancewar asibitin private ne dan haka babu b'ata lokaci
Doctor yayi diagnosing nata, bayan yayi wasu 'yan rubuce-rubuce ya d'ago ya kalle ta da kyau
sannan yace "ke ko 'yammata tunanin mai kike haka kina nema ki illata rayuwar ki,gaskiya
tunani bai kamace ki ba at your young age" .
Duk da azababben ciwon kan da ke damun ta hakan bai hanata d'agowa ta galla mishi
harare ba a zuciyar ta tana fad'in (lalle Doctor d'in nan ya raina min wayo, ina ruwan sa da
shekaru na da zaina min kallon yarin ta, yana wani iyayi sai kace shi d'in wani babba ne
Mtwss!!!" taja tsaki ashe ya fito fili bata sani ba.
Da sauri yace "sorry 'yammata na miki shishigi a lamarin ki ko" kafin tace wani abu Aunty
Khadija ta shigo hannu ta rik'e da waya "Doctor sannu da aiki, Ayusha ga Mummy nan zakuyi
magana a waya" bayan Ayusha ta karb'i wayan Doctor yace "Bismillah Anty ga waje ki zauna za
muyi magana da ke,ku ne kuka kawo wannan patient d'in ko,dan naga kuna kama sosai hala
SISTER d'inki ce ko dama ba wani abu bane illa ina so ku mata fad'a ta rage yawan tunani
domin yana gab da ya mata mummunan illah" hospital card ya mik'a mata "ga wannan kuje
pharmacy ku siyo Magani,Allura da Drip ne aka rubuta zamu bata gado domin za'a d'aura mata
drip kuma condition d'in nata is not stable tana buk'atar hutu"
"Doctor bazai yiwu mu tafi da ita gida a sa mata a can bane,saboda Amarya ce jiya aka
d'aura auren ta, kaga hankalin mutane zai tashi sosai idan suka ji an kwantar da ita anan" "eh to
za'a iya sa mata a gidan ma amma dan Allah a keb'eta daga cikin mutane domin hayaniyar su
na iya coursing wani ciwon, sannan tana buk'atar kulawar ku domin jinin ta ne ya hau sosai
sakamakon wani b'accin rai ko damuwa da tasa a ranta so you need to counsel her because
she is in risk at her young age"
"Innalilahi wa'ina ilaihi raji'un yaushe Ayusha ta kamu da hawan jini dama ni nasan ba son
mijin nan take