Showing 9001 words to 12000 words out of 29251 words
shiga ciki ta tarar da Mum &,Dad a falo suna hira,da gudu ta fad'awa Dad tana
fad'in "Oyoyo Sweet Papa yau nayi missing naka sosai, i hope kai ma kayi missing" "nayi
missing naki sosai Auta, tun d'azu nake jin gidan some how saboda baki nan" "Allah sarki My
Love yanzu kam na dawo zaka ji ka normal" "tabbas Auta na naji normal yanzu" dariya tayi tace
"Alhamdulillah tunda kaji garau bara naje na kwashi gaisuwa wajen Sweet Momma na"
"Hmm....dama kin rik'e gaisuwar ki tun da Daddyn ki kad'ai kika sani kuma kike missing" "haba
Sweetheart baki gane bane shi fa Dad rabona dashi tun da na dawo daga school while ke kuma
bamu wani dad'e da rabuwa haba Habibty kar kiyi fushi da Autar ki mana" "to shike nan Auta na
karb'i uzurin ki, ya kika baro min Aminiyar tawa" lafiyan ta k'alau tana gaishe ki" nan dai Ayusha
tai ta basu labarin gidan tare da kud'in da Abba ya bata, su Mummy harda d'aukan ta k'ira Anty
Zee tai musu godiya.
10:00pm nayi Ayusha tai musu sallama ta haye d'akinta tana shiga ta rage kayan jikin ta ta
fad'a wanka tai shirin kwanciya, tun da ta kwanta ta nemi bacci sama da k'asa yak'i zuwa babu
abinda idanun ta ke hasko mata sai fuskarsa, kunnuwanta na d'auko mata sautin Zazzak'ar
muryar sa me kama da busar sarewa a yayin da yake fad'in..............
```To fah masu karatu nawa kunnen ya kasa jiyo mana sautin muryar tasa kuyi min afuwan haka
amma in shaa Allah zan ci gaba da bibbiyar Ayusha dan gano cewa wani me sa'an ne yayi
tattaki ya ziyarci zuciyar ta a wannan daren ```
*ROOKIEY D BEST*
[14:53, 02/12/2017] +234 703 786 0131: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO*
*GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED
ON FICTION & CONCOCTION_*
® REAL PURE
MOMENT
OF LIFE WRITER'S
*MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_*
*_This page is for you FATTY AXLAND (Mrs Lameed'o) Happy Birthday to you my special friend
WLLNP❤Hip��Hip��Hip��Hurray_*
*BY*
*_ROOKIEY KAXS_*
*DEDICATED 2*
*_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_*
41-45
Tunda suka shiga lecture ba abin da take ganewa, attention d'inta complete ya karkata ga
tunanin guy d'in da ya buga mata mota, burin ta shine ta ganshi ta bashi hak'uri ko ta samu
relief.
Kamar daga sama taji an tab'a ta ance "Baby in love tashi mu tafi kowa ya watse ya barmu"
a firgice ta juyo ta juyo da kallon ta ga Aneeserh sannan ta sauk'e wani zazzafan ajiyan zuciya
tace "wallahi har kin bani tsoro" ta kalli hall d'in wayam sannan ta sake cewa "yaushe aka watse
aka barmu mu kad'ai" " dama ina zaki sani kin tsunduma cikin kogin so" mik'ewa Ayusha tayi
tace "kin ga malama bana son sharri, kefa dama baki iya samun abu ba daga baki labari sai ki
canza akalar zancen, dan haka bana so zancen ya tsaya a haka" murmushi Aneeserh tayi tace
" 'yanmata stop deceiving your self frankly speaking you are in love dan haka zan taimaka miki
da addu'a Allah ya had'aki da lucky guy d'innan da ya sace miki zuciya " murmushi Ayusha tayi
tace "ni na dad'e da gano cewa kina da mental problem so na miki uzuri lets go "
Fitowa sukayi daga hall Aneeserh ta rakata bakin gate ta tari Napep bcoz na cikin school d'in
is occupied with people, sallama sukayi da junan su sannan suka rabu.
A b'angaren Fahad kuwa yana fitowa daga Fatie Shema estate ya karkata akallar motar shi
zuwa hanyar da zata kai shi main road na 'Yar_adua University, agogon hanunshi ya duba yaga
time 3: 45pm waje ya Samu yayi parking a kusa da wani masallaci, alwala yayi yai sallan
la'asar yana mai addu'an Allah ya had'ashi da pretty d'insa.
4:05pm sharp ya fito daga masallacin motarsa ya nufa gaggawa saboda kar ya makara wajen
neman pretty, tuk'i yake a nutse zuciyar sa na mararin kallon ta yana zuwa dai -dai da wajen
wani road division d'aga idon da zai yi ya kalli right caraf yayi arbada da side view d'in ta,
kokwanto yake kamar ita kamar ba ita ba, bai yi aune ba yaga ta karkato da fuskarta zuwa side
d'in da yake, ba shiri ya karkata akalar motarsa daga left zuwa right dan ya cimma su amma
unfortunately sun mishi nisa, wani wawan tsaki yaja yace "pretty me yasa zaki min haka, kin san
baza ki bari muyi magana ba me yasa zaki bayyana gare ni, dan Allah ki tausaya wa rayuwa ta,
ki tsamo zuciya ta daga kogin son ki " haka dai yayi ta sumbatun sa shi kadai kamar wani
tab'ab'b'e, da yaga babu sarki sai Allah sai ya hak'ura ya koma gida.
A b'angaren Ayusha kuwa tana zaune cikin Napep tana ta sak'a da warwara ta yadda za'ayi ta
had'u da wannan guy d'in, ji kamar wani abu ta mitsine ta, da sauri ta dawo daga duniyar tunani
juyawan da zata tayi arba da kyakkyawar fuskarsa yana k'ok'arin juya kan motar sa da sauri
tace da mai Napep d'in "Malam yi sauri ka k'ara speed uzurin gaggawa ya taso min" shi ko
kamar jira yake da sauri ya zaburi Napep a 90.
Yana sauk'e ta a k'ofar gida ta zaro 1K ta bashi ta nufi k'ofar shiga gida "Hajiya tsaya ga can
jinki " "No ma rik'e na barma" "Godiya nake ranki shi dad'e Allah ya saka miki da alkgairi"
"Ameen" tace sannan ta shige gida.
As usual Mum & Dad ta tarar a folo gaishe su tayi ta nufi upstairs Mum ce ta dakatar da ita
"Auta dawo nan, akwai maganar da muke son yi da ke yanzu" dawo wa tayi ta samu guri ta
zauna a k'asa.
Dad ne ya fara magana kamar haka "haba Autar Mum &Dad me ke damunki ne kwana biyu
naga kin canza, idan wani abu kike da buk'ata ai sai ki sanar mana ba kisa kanki a damuwa ba,
ke kanki kin sani farin cikin ki shine namu babu abin da zaki nema mu kasa miki face yafi k'arfin
mu, saboda haka feel free ki fad'i buk'atarki in shaa Allahu zamu miki gwargwadon iyakar mu"
k'ak'alo murmushin dole tayi tace " babu abunda nake buk'ata Dad, kawai dai boko ne ke gara
ni, assignment sun min yawa ga thesis dake gaban mu that's all" "Ayusha yaushe kika fara
b'oye mana damuwar ki, wannan maganar da kika fad'a ba gaskiya bace, ni na haifeki nafi kowa
sanin halinki saboda haka fito fili ki fad'i mana damuwar ki"cewar Mummy kenan.
Shiru tayi for some seconds sannan ta sauk'e ajiyar zuciya tace "Mum & Dad ina alfahari
daku kun kasance nagartattun iyaye masu kula da sauk'e nayin da Allah ya d'aura musu, na
gode sosai da kulawar ku gareni Allah ya barmin ku, ina so ku kwantar da hankalin ku, ku
yarda cewa babu abinda ke damuna face boko stress kun manta 300level nake yanzu komai
k'ara zafi yake"
To shi kenan "Auta Allah ya tabbatar mana da alkhairi" "Ameen thumma Ameen iyayen
k'warai " zama tayi suka sha hira da iyayen ta har dare suna tare, da lokacin bacci yayi tayi
sallama dasu ta nufi makwanci ta sai bacci ya gagara tunanin shi ya sake dawo mata, wani
zazzafan hawaye ne ya fara gangarowa daga idonta.
Zuciyar ta ce ta fara tariyo mata abinda ya faru d'azu take tace "Ayusha why!!! me yasa
zakiyi haka, ke da kike nemansa ruwa a jallo ki bashi hak'uri amma zaki guje masa, kina da
tabbacin zaki sake had'uwa dashi nan gaba!?" sai ta fashe da kuka "wayyo ni Shatu na cuci
kaina idan na mutu da hakkin mutumin nan me zan cewa mahalicci na, na tabbata cin mutuncin
da nai masa ne ke addabar zuciya ta da zaran na bashi hak'uri komai zaiyi normal.
```to masu karatu Ayusha dai ta kasa amincewa tana son Fahad all what she knows is that tana
bashi hak'uri shike nan zata ci gaba da normal life nata. Shin haka abin yake ko yaya ina,idan
kuma akwai wani solution da kuke gani Ayusha zata bi tunanin Fahad ya bar zuciyar ta ta ko da
basu had'u ba to sai ku bata ina jiran comments naku kafin nayi typing next page NA BARKU
LAFIYA taku har kullum```
*ROOKIEY D BEST*
[14:54, 02/12/2017] +234 703 786 0131: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO*
*GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED
ON FICTION & CONCOCTION_*
® REAL PURE
MOMENT
OF LIFE WRITER'S
*MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_*
*BY*
*_ROOKIEY KAXS_*
*DEDICATED 2*
*_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_*
*_Kindness Indeed Is Kindness I will never ever forget you in My life, you are more than a
friend to me, My love for you is parmanent no wala-wala no algus I really appreciate your
kindness, love,care and concern, you always put me in the right part when I'm wrong, you make
sure i succeed before we depart i really miss you My Mentor HANEEFAH USMAN the whole
page is your's������i heart you Beb❤ keep on rocking dear you rock even in the heart of
your enemies LONG LIVE MY HANNEE_*
36-40
Babu abin da kunnuwan ta ke d'auko mata sai sautin zazzak'ar muryar sa me kama da
busan sarewa a sa'ilin da yake ce mata "pretty wait!!!" a fili ta furta kalmar "OMG!!,wallahi ni d'in
nan banza ce me yasa na wulak'anta shi ban tsaya na saurare shi ba, to wai ma ina ruwa na
dashi ne da zan tsaya ina tunanin shi may be ma ya manta da existence d'ina yana can yana
harkokin gaban sa ya barni da tunani!" tana ta tunane-tunen sa har sarkin iya sata ya sace ta, a
b'angaren Fahad ma haka abin yake tunda ya shiga d'aki ya watsa ruwa ya haye gado bai sake
sanin halin da yake ciki ba dan ya tafi duniyar tunanin pretty bai samu ya rintsa ba har asuba.
Tunda bacci yayi awon gaba da ita bata farka ba sai 6:30 a firgice ta tashi tana salati, tana
ganin time tace "ya salaam!!!, yau nice na makara banyi sallar asuba a kan lokaci ba" da sauri
ta sauk'o ta nufi toilet ta d'auro alwala ta gabatar sallah da azkar sannan ta fad'a toilet tayi
wanka, a gaggauce ta shirya cikin wani material gown rose pink, light make up tayi sannan ta
d'auko milk veil tai rolling takalmi da jaka ma milk sannan ta feshe jikinta da designer perfume
na FARASHA ta fito daga d'akin ta nufi wajen Mummy.
Tana shiga d'akin Mummy taga wayam da alama bata ciki so direct kitchen ta nufa ta
taradda ita tana had'a musu breakfast, " Morning sweet Momma da fatan kin tashi lafiya!" "lafiya
lau Auta,har kin fito, to maza je ku gaisa da Daddyn ki a falo kiyi break" "Mum ni fa bana jin zan
ma iya cin abincin nan ba yau nayi latti sosai" tana gama fad'in haka tayi saurin ficewa daga
kitchen d'in dan tasan halin Mummy yanzu zata sata a gaba tace sai tace and ita kwata-kwata
ma bata buk'atar cin komai.
A falo ta iske Dad d'urk'usawa tayi har k'asa tace "Morning Dad da fatan ka tashi lafiya"
"lafiya na lau Auta an shirya boko kenan, yana da kyau a dinga bada himma, Allah ya miki
albarka, ya sanya albarka a rayuwar ki ya baki sa'an abinda kika je nema" "Ameen Thumma
Ameen Sweet Papa, ni zan wuce school" "ki tsaya muyi breakfast sai nayi dropping naki tun da
ba motor a hannunki" "A'a dadi ka bari zan tafi a NAPEP coz idan na tsaya break zanyi latti"
"ok ba damuwa ga 5k ki rik'e a hannunki ko zaki buk'aci wani abu" "No Dad ka bar shi akwai
kud'i a hannu na wanda mijin Anty Zee ya bani jiya" "to shi kenan Auta a dawo lafiya Allah ya
kare" " Ameen"
Tana fita k'ofar gida ta samu NAPEP ta shiga, a cikin gida kuwa Mum & Dad na breakfast
Daddy ya kalli Mummy yace "Fatima wai baki fahimci wani changes a tattare da Auta ba ne?,
naga yau d'in a bai-bai take" "wallahi Alhaji rigani furtawa kayi amma tun jiya da daddare na
fahimci hakan,amma koma miye ne anjima idan ta dawo sai mu tambaye ta" "to shi kenan Allah
ya kaimu anjiman dan ni sam bana son ganin Auta ta cikin damuwa" haka dai sukayi ta tattauna
wa game da batun Ayusha.
Tana shiga school ta k'ira Aneeserh a waya, ringing biyu yayi tayi picking "Hello K'awata wai
kina ina ne tun d'azu ina ta trying layinki ban samu ba yanzu har Mr Patrick yayi lecture baki
nan" "wallahi yau makara nayi ban tashi da wuri ba yanzu haka na shigo school d'in kina ina"
"ok ki zo ina zaune a bayan library" "ok to ganin nan zuwa"
Tana zuwa bayan Library ta hango Aneeserh a zaune waje ta samu kusa da ita ta zauna
sannan suka gaisa kallo d'aya Aneeserh tai mata ta gane tana cikin damuwa sassauta murya
k'asa tayi sannan tace "k'awata me ke damun ki dan naga damuwa k'arara a fuskar ki" "ba
komai kawai dai bana jin dad'i ne" " Hmm... K'awata kenan to ai baki san wani abu ba duk
wanda yasan ki a jiya ya ganki yau ya san kina cikin damuwa balle kuma ni da muke tare da ke
kullum ya za'ayi dan naga changes a tattare da ke na kasa fahimta kawai Malama ki fad'a min
matsalar idan da taumakon da zan iya sai nayi" shiru tayi na d'an wani lokaci sannan daga baya
ta sauk'e wani dogon ajiyan zuciya sannan tace "jiya bayan mun sauk'e a hostel mun juyo", nan
dai ta zayyane mata labarin Fahad hatta baccin da ta kasa saboda shi bata b'oye mata ba daga
bisani tace
"wallahi ni babban damuwa ta ma shine bai wuci ina zan ganshi na bashi hak'uri ba" Aneeserh
tayi shiru tace "ki kwantar da hankalin ki k'awata in sha Allahu Allah zai bayyana miki shi and
also na fahimci cewa zuciyar ki tana k'ok'arin fad'awa tarkon so ko ma in ce ta fad'a ciki
tsundum" "lalle yarinyar nan baki da hankali dan nace miki ina son ganin shi na bashi hak'uri sai
kice na kamu!!! ce miki akayi na shirya yin soyayya yanzu" " ko kuma kece babbar mara hankali
ba yaya kike k'ok'arin hana zuciyar ki a bin da take so, Ayusha ki saurare ni da kyau kin san dai
na girmeki a k'alla na baki shekara d'aya me kyau so wajen hankalin ma da bambanci,ke da
kanki kin san na fiki sanin me duniya take ciki must especially ma ta b'angaren soyayyah!!"
tana gama fad'in haka ta tuntsire da dariya dundu Ayusha ta d'aka mata sannan tace "shegiya
yar iska ai dama anan kika fi k'wari ko Romeo and Juliet haka suka ganki suka barki " sosa
wurin dundun tayi tace "Allah ya isa daga fad'an gaskiya sai ki dake ni" haka dai sukayi ta
shirmen su har next period yayi suka koma lecture hall.
A b'an garen Fahad kuwa tun bayan da ya idar da sallan asuba ya kwanta bai farka ba sai
12:pm shima da k'yar ya iya tashi yayi wanka yaje gaida Mum a falo ya sameta tana kallo
waje ya samu ya zauna sannan yace "ina kwana Mum, da fatan kina lafiya" tun da ya shigo
falon take kallon shi har zuwa lokacin da yake gaisheta bata sauk'e idonta a kan sa ba har ta
amsa masa da "lafiya My Son, sai yanzu ka tashi daga baccin Abban ku ya bar sallahu cewa
idan kayi ka biya office ka same shi " "ok" shine kad'ai abinda ya fad'a ya mik'e tsaye sannan
yace "Mum ni na tafi amma dan Allah kimin addu'a Allah ya had'ani da pretty na bata hak'uri"
murmushi tayi tace "dawo ka zauna My Son akwai wata muhimmiyar magana da zamuyi da kai"
Waje ya samu ya zauna yana kallon ta sai da ta tabbata yayi paying attention nashi sosai
sannan ta ce " yi maka addu'a ya zama wajibi a gareni My Son, amma dan Allah ina so ka nutsu
ka kwantar da hankalin ka idan Allah yayi zaka had'u da pretty ka bata hak'uri zaku had'u dan
haka ka cire damuwa a ranka ka dawo normal yadda kowa