Showing 21001 words to 24000 words out of 29251 words
Chapter 8 - Allura Ta Tono Garma Book Compelet By Rookiey
haka muna so ki taimaka wajen bata shawara ko Allah zai sa a dace, kin je
asibiti kinga halin da mutumin nan ke ciki amimcewar Ayusha ne kawai zai dawo dashi hayyacin
shi, kinga yana da kyau kema ki bada gudummawa wajen ceto rayuwar shi" ta k'arashe
maganar tana zubda hawaye.
"Ku kwantar da hankalinki Mum&Dad in shaa Allahu nayi alk'awarin shawo kan Ayusha ta
amince, zan jure duk wani wulak'anci da zata min dan na cimma buri na"
Dad yace "idan kikayi haka kin tabbatar mana da cewa ke 'yar halak ce, saboda haka daga
yanzu aikin ki zai fara Allah ya miki albarka ya baki nasara"
"Ameen thumma Ameen Dad, bari na shiga na sameta duk yadda mukayi da ita I will let you
know" "ok d'iyar albarka Allah ya bada sa'a" inji Mummy.
Aneeserh na shiga ta tarar da ita ta had'a kai da gwiwa sai kuka take, da sauri ta k'arasa
wajen ta tana fad'in "Subhanallah!!!, haba k'awata bai kamata ki tada hankalin ki akan k'addarar
da Allah ya sauk'ar miki ba, addu'a ya kamata kiyi Allah yasa hakan shine mafi alheri" "kar
kiyiwa k'addara sharri domin wannan ba k'addara bane son zuciya ne, me yasa Mum &Dad
suka canza sun kasa fahimtar halin da nake ciki, abin da ke damun Alhaji Umar shi ke damuna,
idan har bazai iya hak'ura da soyayyata ba nima bazan tab'a iya hak'ura da son wanda nake
k'auna ba amma gaba d'ayan ku daga ke har su kun kasa fahimtar hakan, to ki sani idan ma
aiko ki sukayi ki koma ki sanar dasu cewa nayi making decision ban amince da shi ba kuma
bazan tab'a amincewa da shi ba" tana gama fad'an haka ta fad'a kan gado ta fara wani irin kuka
mai tsuma zuciyar mai sauraro"
"Ayusha bazan tab'a mamakin fitowar wad'annan kalaman daga bakin ba, domin duk wanda
soyayya ta rufe masa ido babu abinda bazai iya aikatawa ba... amma ina so kiyi saurin dawowa
hayyacin ki k'awata ki sani fa shi bawan Allan da kike hauka a kanshi ma bai san kina yi ba,
baki da tabbacin zaki sake ganin shi a rayuwa idan har Allah ya k'addara had'uwar ku dashi ma
baki da tabbacin zai so ki ya aure ki"
"Ai dama banyi dan yasan inayi ba kuma da kike cewa bai zama lalle ya soni ba ban kai ya
soni ba? ko kina nufin bani da qualities d'in macen da ya dace a aura ne!!! wallahi Aneeserh kin
bani mamaki ban tab'a tsammanin haka daga gareki ba, Mum &Dad sun juya min baya kema
haka" sai ta k'ara fashewa da kuka.
Matsowa bakin gadon Aneeserh tayi sannan tace "k'awata ina so ki fahimci wani abu guda
d'aya idan kika ce mun juya miki baya sai Allah ma ya tambaya ki, muna k'ok'arin mu nuna miki
hanyar da ta dace ne, ki tuna fa tunda kike a rayuwarki baki tab'a neman wani abu wajen iyayen
ki kin rasa ba, duk wani abu da suka san zai saki farin ciki shi suke miki sannan suna gudun duk
wani abu da zai b'ata miki mai yasa a karo na farko baza ki faranta musu rai ba, kar ki manta
Ayusha Dad da bakin sa yace yana so ki mishi alfarma while kin san yana da right d'in da zai
iya d'aura miki aure da duk wanda yake so ko kina so ko ba kya so, and another thing da nake
so ki sani shine faranta musu rai dai-dai yake da faranta ran mahaliccin ki sannan b'ata musu
ma dai-dai yake da b'ata masa ki tuna da hadinsin manzon Allah ( S. A. W) da yake cewa
*_"Ridallahi fii Ridal Walidaini Wa Sukhd'ullahi fii Sukhd'ul walidaini "(Yarda Allah yana tare da
yardar iyaye kuma fushin Allah yana tare da fushin iyaye)_* saboda haka k'awata ina mai
shawartar ki da kiyi gaggawan dawowa hayyacin ki, ki farantawa iyayenki ko kya samu tabaraki
a rayuwa"
"Baza ki gane bane K'awata, wallahi dai-dai da na second d'aya ban jin zan iya k'aunar Alhaji
Umar, domin shi mutum ne mai son kansa da yawa, budurwar zuciya gareshi, kar ki manta Anty
Zee aminiyar Mummy ce tun yarinta tare suka tashi komai nasu tare sukeyi har sukayi aure
basu daina zumunci ba, Anty Zee ta kasance mace yar k'walisa da gayu ga addini da ibada uwa
uba ga san mutane d'anta d'aya a duniya Fahad daga shi bata sake haihuwan wani ba, Allah
yayi ta da son jama'a hakan yasa ta d'auko cousin sister nata Muneerah ta dawo wajen ta da
zama, Muneerah na primary 3 ta dawo wajen ta da zama tana gama secondary school tsabar
rashin adalci da son zuciya irin na Alhaji Umar ya aure ta, babu kunya kuma ya ajiyeta a gidan
take abin da ta ga dama domin Muneerah bata da kunya sannan bata da mutuci ko kad'an"
Daya ke Allah ba azzalumin nawansa bane shekarar Muneerah uku ya auro Rahma, Rahma
k'anwar kishiyar Maman Muneerah ce suna zuwa gidan tare da k'anne ta har Allah yasa ya
k'yallaro ta ya auro ta sannan ni ma yanzu yace zai aureni, inaa wallahi sai dai ya mutu ya bar
duniyar gaba d'aya amma bazan tab'a yarda na aure shi ba, mu uku Iyayen mu suka haifa,
Anty Khadeeja da Anty Fareedah sai ni Auta duk kansu auren soyayyah sukayi me yasa sai ni
da nake autar su za'a min auren dole a rasa ma wanda za'a aura min ma sai tsoho sa'an
Babana mai 55years a d'oron k'asa inaa wallahi da sake sai dai Mum & Dad su tsane ni su
daina sona kwata-kwata amma bazan tab'a yadda na aure sa ba" sai ta k'ara fashewa da sabon
kuka.
```Wasa Farin girki This is just the beginning of the story kuci gaba da bina dan ganin yadda
labarin zai kasance na barku lafiya masoyana ```
*RØØKÎÊY D BEST✍��*
[14:56, 02/12/2017] +234 703 786 0131: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO*
*GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED
ON FICTION & CONCOCTION_*
® REAL PURE
MOMENT
OF LIFE WRITER'S
*MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_*
*BY*
*_ROOKIEY KAXS_*
*DEDICATED 2*
*_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_*
81-85
Sake matsowa kusa da ita Ayusha tayi tace "ki kwantar da hankalin ki K'awata na fahimce ki
sosai da sosai amma ina so ki sani Mum & Dad baza su tab'a cutar dake ba a rayuwa wannan
zab'in da suka miki shine dai-dai a wajen su nasan zakiyi tunanin cewa dan ba ni ce cikin
wannan situation d'in ba yasa nake fad'in haka, to ki sani ko da nice iyayena suka nemin
alfarmar nan a guna zan musu duk da cewa they are not responsible parents basu yi deserving
a musu hakan ba amma domin samun rabauta wajen ubangiji zan amince musu" kuka ne yaci
k'arfin ta yasa ta yin shiru.
D'ago jajeyen idon ta Ayusha tayi sannan tace "what do you mean by they are not
responsible, Aneeserh iyayen naki kike fad'awa haka, bai kamata damuwa ta tasa ki fad'an
kalaman da basu dace dasu ba, ki tuna fa ke kike min nasiha akan iyaye no matter what they do
basu cancanci haka ba"
"Ayusha nasan abin da nake fad'a gaskiya ne so no need kiyi tunanin cewa ban kyauta
musu ba, idan kika ji labarina zaki san cewa eh lalle basu dace su zama iyaye na ba shiyasa a
ko da yaushe iyayenki suke birge ni rayuwar su tayi min A1".
"Ban fahimce ki ba k'awata" "yanzun nan zaki fahimce ni in shaa Allah, yaune rana ta farko
da zan fara baki labari na so tari ina attempting fad'a miki sai naji kunya ta dabaibaye ni amma
ya zama dole na sanar dake ko zaki d'auki darasi a ciki."
*_LABARIN ANEESERH_*
Da farko dai sunana Aneeserh Adam Muhammad, asalina yar jigawa ce a wani gari ana
k'iranshi D'angyatin, Mahaifina ya kansan ce yana kasuwancin fata kuma Alhamdulillah yana
samu sosai da sosai gidan mu babban gida ne me kyau da tsari, mahaifiyata Hajia Zainab ita
ce uwargida sai kishiyoyin ta Maryam da Halima, mu goma sha biyar ne a wajen mahaifin mu
kuma nice babba, mu bakwai wajen Mamar mu, sai biyar na Maryam uku na Halima"
Tun da na taso a rayuwata ban san menane parental love ba (soyayyar mahaifa) nayi
k'uruciya ta cikin wahala da tashin hankali, bani da ikon yi komai a gidan mu mahaifiyata bata
damu dani ba kamar ba ita ta haife ni ba, da nayi abun da bai kai ya kawo ba sai ta hau zagina
a gaban k'anne na da kishiyoyin ta kamar "shegiya, mahaukaciya, jaka dabba mara hankali
wacca bata san ciwon kanta ba, ke dai a haka zaki k'are".
Shiyasa daga kishiyoyin nata har k'annena basu ganin mutunci na yaro sai ya rufe ido ya
zage ni son ransa ban isa na tanka ba, shima mahaifin mu ba damuwa yayi da yaja mu a jiki ba,
abinci dai baya yanke mana a gidan nan sannan idan sallah ta zagayo zai mana d'inki amma fa
sauran responsibilities d'in sai a slow ko wace mata ita take yiwa 'yay'anta banda mahaifiyar
mu, gashi tana business sosai yadda bakya tsammani amma dai-dai da pant bata tab'a siya min
ba.
K'awata na taso cikin tashin hankali yadda bakya tsammani domin tsakanina da mahaifiyata
maganana mai dad'i baya shiga sannan kuma ta kafa min takun kumi ban isa na fita ko bakin
k'ofa ba ko k'awaye na ne suka zo ban isa na raka su ba, gashi ni kuma Allah ya halicceni me
farin jinin jama'a daga manya har yara idan na fita suna sona.
Bayan na gama primary school na tafi FGC Gwaram dake nan jigawa state, mahaifina yana
min shopping na provision dai-dai gwargwado ya bani pocket money da yasan bazan buk'aci
wani ba, to idan naje nakan siya inner waers da sauran necessary things d'in da bani dasu a
wajen metron namu.
Tunda na shiga secondary school rayuwata ta fara canzawa domin na had'u da friends da
yawa masu sona da k'aunata, idan mun zauna suna labari iyayen su sai dai nayi shiru domin
bani da abinda zance me dadi game da nawa iyayen idan lokacin visiting yayi sai dai amin aike
ko karen gidan mu bazan gani ba har visiting ya k'are.
A haka rayuwata taci gaba da tafiya har nakai SS1 a wannan lokacin na fara mallakan
hankalin kaina girma yazo, domin a lokacin na ma fara period, ranar da na fara period nayi kuka
sosai domin ban san wani abu game dashi ba wata k'awata mai suna Amma na samu na sanar
da ita abinda ke faruwa tace "ki kwantar da hankalin ki k'awata girma ne ya kamaki ai it's normal
a wajen ko wace mace, kinga ni a gida na fara so ban wani sha wahalan neman Pad ba
Mamana ce ta koya min komai sannan tamin nasiha sosai tace kar na kuskura na diga
mu'amala da maza ko da kuwa yayyena ne ko hanuna namiji ya rik'e zanyi ciki da zan dawo ta
had'oni da PAD shida dan haka muje na baki idan kin koma gida sai ki sanar da maman ki,
nasan zata ji dad'i sosai " muka je ta bani pad ta koya min komai.
Tun daga wannan lokacin na fara siyan PAD da kud'ina har na kammala secondary mahaifiya
ta bata tab'a attempting tambayana ko na fara period ko ban fara ba balle tayi k'ok'arin siyamin
pad, inada 16years na kammala secondary school Samari da dama sun na kawo min hari duk
wanda yace yana sona bana bashi fuska domin ina tsoron abinda zai je ya dawo, nayi applying
ABU &BUK ban samu ba ina ji ina gani na cinye wannan shekarar a gida.
The next year wani Uncle d'ina ya sake biya min kud'i nayi jamb shine na samu admission
anan 'YAR'ADUA UNIVERSITY KATSINA kafin na taho warning mai gamma iyayena suka min
akan soyayya musamman ma mahaifiyata da tayi ta jifana da kalamai marasa dad'in ji akan
maza wanda ko mak'iyinta akai wa baza taji dad'i ba.
A sheka da nazo Allah ya had'ani da ke da Mujaheed kun zamo wani babban jigo na
rayuwata wanda bazan tab'a iya rayuwa ba tare da ku ba, Mujaheed ya dad'e yana takura min
game da ya turo iyayen shi gidan mu nak'i amince mishi badan komai ba illah dan ban san ta
yadda zan shawo kan al'amarin ba,Ayusha iyayen ki sun min komai a rayuwa sun maye min
gurbin iyayena sun soni kamar d'iyar cikin su bani da abinda zan saka musu dashi sai addu'a
saboda haka dan Allah dan Annabi ki daure ki amince da buk'atarsu albarkacin kasancewar su
iyayen na gari"
Tana gama fad'in haka ta fashe da kuka Rungumota Ayusha tayi suka ci gaba da kukan su.
Sai da sukayi mai isarsu sannan Ayusha tace "lalle k'awata kinga jarabawar rayuwa Allah
yasa k'arshen wahalar kenan in shaa Allah zanyi k'ok'ari naga na dai-daita tsakanin ki da
iyayenki na dawo miki da farin cikin da kika rasa shekara da shekaru"
"K'awata na gode da kullawar ki gareni amma ki sani in da sabo na saba da halin iyayena
sannan shawo kansu ba abu bane mai sauk'i domin kaf family d'in mu babu wanda bai san halin
da nake ciki ba tun ina k'arama wasu ke k'ok'arin sulhuntamu amma abin yak'i so ni yanzu ba
wannan bane a gaba na fata na ki amin ce da buk'atun iyayen ki domin sun kai a sadaukar
musu"
"Aneeserh baza ki gane bane Mum &Dad are more than everything they deserve more than
sacrifice from me, the fact is that bazan iya amimcewa da soyayyar tsohon nan ba na tsane
yadda bakya tsammani"
"Ayusha me yasa kike da taurin kai ne, na san abin da ciwo amma yak'ar zuciyarki ya
kamata kiyi bawai kibi umarnin ta ba, ki zauna kiyi nazari sosai a kan batun idan kina da hankali
labari na da na baki ya isa ki k'ara tausayawa tare da k'aunar iyauenki" haka dai sukayi ta
tattauna batun sai wajen 2: 00am sukayi bacci.
*_WASHE GARI DA SAFE_*
Sai misalin 10: 00am suka tashi daga bacci already Mum ta had'a musu breakfast, so
had'uwa sukayi gaba d'ayan su sukayi break, ko a fuska Ayusha bata ga wani changes a wajen
iyayen ta ba, bayan sun gama break tace da Mum & Dad zata shiga ciki ta kwanta domin
baccin bai isheta ba.
Bayan ta shiga ciki Mum tace da Aneeserh "ya kuka k'are da ita jiya ne" "ke dai ki bari
kawai Mum, wallahi ban tab'a sanin Ayusha na da taurin kai haka ba sai jiya duk yadda nayi da
ita tak'i amincewa da batun yanzu haka ma bama magana na fita harkarta"
Dariya sosai ta basu sannan Dad yace "to in banda abinki d'iyata miye na gaba kuma keda
kika ce zaki jure duk wani wulak'anci da zata miki sai ki b'ige da gaba"
"Baza ka gane bane Dad gaban ma wani salo ne ai" "ok sai yanzu naje ghana"
A kwana a tashi ba wuya, yau ta kasance saura kwana d'aya ranar da Doctor yace Alhaji zai
farfad'o yayi, iyayen Ayusha sai zuba ido suke ko zata basu had'in kai zuwa wajen shi asibiti
amma shiru ko alamu babu a wajenta, Aneeserh ma da take jiyo musu information tayi shiru.
*_RANAR FARFAD'OWAR ALHAJU_*
6: 00am Ayusha da Aneeserh suka tashi suka shiga kitchen suka had'a breakfast sukayi
shirin zuwa school bayan sun gama suka zuba a flasks sukayi wa Mum & Dad sallama zasu tafi
school dashi domin yau suna da visiting lecturer kuma zasu iya kaiwa yamma lis a can, tsabar
takaici basu iya cewa dasu komai ba sai "Allah ya kiyaye hanya".
```To Masu karatu ku biyoni dan ganin me zai faru da Alhaji tunda Ayusha ta rufe ido ta kama
gabanta tayi