Showing 15001 words to 18000 words out of 29251 words

Chapter 6 - Allura Ta Tono Garma Book Compelet By Rookiey

Rookiey   

16 Jul 2026

286

musamman,
lallab'asu ake kamar k'ananan yara, a guji duk wani abinda zai b'ata musu rai saboda lafiyan su
idan ba haka ba komai zai iya faruwa Allah ma ya rufa asiri" gaba d'ayansu suka amsa da
"Ameen" Doctor Ahmad yace "kuma dan Allah kar a taru a wajen shi dayawa idan da hali ma
mutum d'aya ya zauna a wajen shi" "shi kenan Doctor in shaa Allahu zamu kiyaye duk abinda
kuka ce bi'izinillahi rabbi zai samu abinda ya keso"




Tun da ta fara maganar Muneerah ta zuba mata eyes jira take takai aya ita kuma ta d'aura
daga inda ta tsaya, Anty Zee na rufe baki tace "Ai nasan ke abin bazai tab'a damunki ba, so
dole kice zai samu abinda yake so tunda ba ke za'ayi wa kishiyar ba" "to ke da kike tada jijiyoyin
wuyan ke za'a yiwa kishiyar?" cewar Rahma kenan.


Doctor Sa'ad yace "dan Allah Hajiya kuyi hak'uri ya isa haka, yanzu da lafiyar shi zaku ji ko
da batun kishiya" ya nuna Muneerah yace "ke d'in ba yanzu kika zo waje na kina kuka in
taimaka miki baki son Alhaji ya mutu ba?, amma gashi kece me tada zaune tsaye, abinda nake
so ki sani shine kiyaye lafiyar shi a hunnun ku take sai ki zab'a ko, ki barshi ya samu abinda
yake so ko kuma rayuwar shi ta k'are a haka, dan naga alama ke ce me matsalan" yana gama
fad'ar haka yayi ficewar sa suma fitowar sukayi daga office d'in suka nufi wajen Alhaji, bacci
yake sosai amma kana ganin shi kasan yana fama da jiki.




Misalin k'arfe biyar da rabi ya farka, Anty Zee da Rahma ne suka taimaka masa ya zauna,
"sannu Alhaji, ya jikin da fatan ka fara jin k'arfin jikin ka" atare suka fad'i hakan, shiru yayi yana
kallon su d'aya bayan d'aya "ina Muneerah take" ya fad'a a hankali bud'e k'ofar d'akin da akayi
ne yasa su yin shiru basu bashi amsa ba.



Da sauri ta k'araso wajen shi tana fad'in "ka kwantar da hankalin ka mijina in shaa Allahu
zaka samu abinda kake so dukanmu mun amince ka k auri wacca kake so, ko ba haka ba
Anty" da k'yar Anty Zee ta iya d'aga kai ta amsa mata alamar eh!!! haka dai sukayi ta kwantar

masa da hankali da kalamai masu sanyaya zuciya a haka dare tayi suka tattara suka koma gida
suka barshi da Anty Zee.







Washe gari y'an dubiya sukayi ta zuwa dubashi cikin su harda Mummyn Ayusha da Dad,
satin su d'aya a asibiti aka sallame su suka koma gida, kulawa sosai yake samu wajen matan
sa a haka har ya wartsake ya dawo normal kamar bashi ne yayi jinya ba.



*_BAYAN SATI BIYU_*


*_5: 00pm_*
Alhaji Umar na zaune a d'aki yana sana'ar tasa wato tunani, Hajia Zee ta shigo d'auke da
tea flask da fara'ar ta ta k'araso gurin shi ta ajiye flask d'in a kan center table,mug ta d'auko ta
tsiyaya mishi sannan tace "Alhaji ga ruwan zafin nan ka sha" shiru taji yayi bai amsa ba, ajiye
mug d'in tayi a gefe ta d'aura hannu ta a saman nashi tace "haba Abban Fahad, dan Allah
yaushe zaka daina tunanin nan haka tunda muka dawo daga asibiti nace zan je na sanar da
iyayen Ayusha abinda ake ciki ka hana, kuma kai banga kayi yink'urin yin wani abu a kai ba
gaskiya ni kam bazan iya jurar ganin ka a irin wannan halin ba saboda haka in shaa Allahu
gobe zanje gidansu na sanar da iyayenta halin da ake ciki"





"Kina da tabbacin cewa yarinyar da iyayenta zasu yarda? " shine tambayar da ya jefo mata
"kwarai kuwa tun da na amince in shaa Allahu suma baza su k'i amincewa ba dama abinda zai
hanasu amincewa saboda ni ne" "to naji, idan iyayen ta sun amince yarinyar kuma fa?" "kar ka
tada hankalin ka akan wannan Ayusha kamilar yarinya ce, mai tarbiyya da bin umarnin iyaye
matuk'ar iyayenta suka yarda da kai to itama zata yarda domin a duniya bata tab'a bijirewa
umarnin su, idan kana tunanin cewa ko tana da wani saurayi ne a'a mahaifiyar ta ta shaida min
har yanzu bata fara soyayyah ba"

"Madallah da matar k'warai irinki, Hajiya Zainab Allah ya saka miki da alkhairi yasa ki gama da
duniya lafiya, da ace duka mata zasuyi koyi da irin kyawawan halinki da mata dayawa baza su
shiga wuta ba"



```Masu karatu ku jimin Alhaji da sweet mouth... Lols

Sai mun had'u a next page dan gani badak'alar da za'a kwasa
Bissalam
Nice har kullum```




*ROOKIEY D BEST*
[14:54, 02/12/2017] +234 703 786 0131: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO*
*GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED
ON FICTION & CONCOCTION_*


® REAL PURE
MOMENT
OF LIFE WRITER'S
*MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_*





*BY*
*_ROOKIEY KAXS_*

*DEDICATED 2*
*_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_*





61-65

Haka dai Alhaji yayi ta kalallame Anty Zee da sweet mouth, ranar through out wuni yayi
yana farin ciki hatta 'yan office nasu sun fahimci hakan, ko ina sai side talks ake domin rabonsu
da suga farin ciki a fuskar sa tun lokacin da ya fara afkawa kogin so, kai hatta matan sa da
'yayan sa sai da abin ya dinga basu mamaki domin sun dad'e basu ga yana sakar musu fuska
haka ba yau har zama yayi a falo akayi hira dashi kamar da.

Masu karatu kuji Alhaji da zak'ewa sai kace wanda aka ce mishi Ayusha da iyayen ta sun
amince (Lols) .




Washe gari ya kama Sunday tun safe Anty Zee ta fara shirin tafiya misalin 10: 30am ta gama
komai nata d'akin Alhaji ta nufa domin yi masa sallama, tana shiga ta tarar shima ya shirya tsaf
cikin wani cuffee brown shaddar shi me d'aukan ido.




"Hajiya Hajjaju gidan sammako, wato fa ke da gaske kike sai kin nemowa angon naki mata ,
to masha Allahu haka ake so ke dai kici gaba da bada himma ladan ki na wajen Ubangiji"





Murmushi tayi sannan tace "Yaa Alhaj, sarkin dad'in baki, ni dai kabar fasa min kai na da
yawa, irin wannan kwalliya haka sai kace me zuwa zance" shima murmushin yayi sannan yace
"kai Hajjaju ta inda kika b'ullo kuma! to ni wajen d'aurin auren wani abokina ma zani, sai ma
muje na sauk'eki tunda naji kince motar ki na gareji ko?" "eh wallahi tun jiya Bala Driver ya kai
ta yanzu na k'irashi a waya yace ba'a gama gyaran ba so muje ka ajiye ni kawai sai yazo ya
d'aukeni" " ok haka za'ayi Uwargida sarautar mata" "Hmmm... kaji dashi dai"





Murmushi yayi yace "Hajiya Zainab ikon Allah muje kar na makara sha d'aya da rabi ne
d'aurin auren" fita sukayi daga d'akin suna fara'a, key d'in motar ya bata sannan yace "je ki jirani
a mota bari nayi sallama dasu Muneerah" "ok" shine abinda tace ta karb'i key d'in ta wuce.

Bayan yayi sallama da sauran matan ya dawo mota suka fice daga gidan, hira suke sosai
cikin ni shad'i kamar wasu saurayi da budurwa, suna cikin tafiya wayarsa tayi ringing, yace da
Anty Zee "Hajjaju angon ne ma yake k'ira sa min wayar a hands free, muji dame yazo" "to"



Tana sawa Alhaji yace "Ango kasha k'amshi! ka jini shiru ban iso ba ko wallahi uwargida ce
ta rik'e ni amma yanzun nan zan k'ara so" "aboki dama ka zauna a inda kake dan an ma fasa
d'aura auren" "what!!!why!!! ya akayi haka ta faru " "kai dai ka bari kawai yanzu haka ma bana
gari idan na dawo zamu tattauna batun" "to shikenan Allah ya dawo da kai lafiya yasa hakan
shine mafi alkhairi" "Ameen"




Bayan ya gama wayan ya kalli Anty Zee yace "uwargida kin ji abin bak'in cikin da ya faru da
abokina ko" "wallahi kuwa, Allah ya rufa asiri" "Ameen" haka dai suka ci gaba da hirar su har
suka isa k'ofar gidan.





"To Hajjaju Allah ya bada sa'an abinda aka zo nema ina nan ina jiran feedback Hajiya ta"
"Alhaji akwai wani hanzari ba gudu ba, me zai hana mu shiga tare, ina ganin abin zai fi zuwa
mana da sauk'i" "yanzu ke a ganin ki hakan yayi" sosai ma, bari na shiga na sanar dasu zuwan
ka " "your wish is my command ranki shidad'e" murmushi tayi ta sauk'a daga motar ta shiga
gidan.





Da sallama ta shiga gidan a falon k'asa tayi kicib'is da Mum & Dad na breakfast a falo, da
sauri Mum ta nufo ta tana fad'in "lalle yau munyi babbar bak'uwa gaskiya k'awata kin shammace
ni yanzu nan fa nake cewa Abban Ayusha ya kamata anjima naje na dubo ku tunda aka sallame
ku sau d'aya naje, ya me jikin to, ga waje ki zauna" "jiki Alhamdulillah, yanzu haka ma tare
muke dashi yana waje" "Haba Abuwa ya zaki baro min aboki a waje sai kace wani bak'o, bari
naje na taho dashi" cewar Daddy kenan, yana gama fad'an haka yayi waje.

Murmushi Anty Zee tayi tace wato mijin ki bazai daina cemin Abuwa ba ko? ko da yake nasan
maganin sa" Mum tace "kun fi kusa me shiga zancen ku shi zai ji kunya"



Dad ne suka shuga tare da Alhaji Umar, zama sukayi a kan kujera bayan nan gaisuwa ya
biyo baya, bayan an gama gaisawa Mummy ta kawo musu kayan motsa baki, sun kai 30
minutes suna hirar duniya domin sun dad'e basu had'u dukansu a waje d'aya ba.





Daga bisani Anty Zee tace "wai ni ina d'iyata ne tunda nazo fa ban ganta ba, kuma ko motsin
ta banji ba" "laa Ayusha ai baza ki ganta yanzu tana can tana sana'ar baccin nata da yake jiya
munyi dogon hira sosai Aneeserh ce ma ta iya fitowa ta had'a mana breakfast " cewar Mummy
kenan.



"Yauwa ni kam ina so naga Aneeserh nan da nake ta jin labarin ta rannan da nace Daughter
tazo min weekends ma cewa tayi inyi hak'uri sai Aneeserh ta tafi" Daddy yace "ai Aneeserh
yarinyar kirki ce sosai"




"Allah sarki, yauwa tun d'azu mun tsaya surutu bamu samu mun tattauna abinda ya kawo mu
ba" inji Anty Zee, Mummy tace "ai ni nasan ruwa baya tsamin banza yaushe rabon da kuzo
gidannan tare to Allah yasa dai lafiya" "Anty Zee ce tace "lafiya lau sai alkhairi, wata
muhimmiyar magana ce ta kawo mu, amma bamu san yadda zaku d'auki maganar ba"



Sannan taci gaba da cewa "Munzo neman wata alfarma ne a gurin ku da fatan baza ku kasa
yi mana wannan alfarman ba" "wallahi k'awata kin bani kunya, ke kanki kin sani tun muna yara
d'ayan mu baya tab'a neman abu wajen d'an uwansa ya rasa to me yasa yanzu zakiyi kokwanto
wajen tambayata abu har ma kike k'iranshi da alfarma" "ba haka bane k'awata wannan karon
abin yasha ban-ban, ni dai fatana ku amince da buk'atar mu"

"Kar ku ji komai Abuwa, tun kafin ki fad'i buk'atarki an amsa miki" inji Daddy, shi dai gogan
namu shiru yayi yana kallon ikon Allah zuciyan sa sai dukan tara-tara yake da ya tuno kalaman
uwargidan sa na jiya da daddare inda take cewa "ka kwantar da hankalin ka My Lurv nace
maka muddin na gabatar musu da buk'ata ta zasu amince" take sai yaji relief domin yaga
alamun nasara a tattare dasu.



Baiyi aune ba yaji tace "wato abin da yake tafe damu shine... " sai ta tsinci kanta da jin
nauyin maganar, hankalin Alhaji yayi k'ololuwar tashi take ya fara auro irin halin da zai shiga
idan ya rasa Ayusha.




"Ci gaba da magana mana Abuwa, lokaci na tafiya fa azahar ma ta gabato" cewar Daddy,
Mummy tace "k'yale yar rainin hakali idan taga dama kar ta fad'a d'in" "kwantar da hankalin ki
k'awata me kika ci na baka na zuba, yanzun nan zakiji komai , dama akan Ayusha ne tun ranar
da Alhaji ya d'aura idonsa a kanta yaji duk duniya babu wanda yake so ya aura sama da ita,
nasan zakuyi tunanin abubuwa da dama a kai na, to ni na yarda na amince da hakan shiyasa
ma nayi masa jagora zuwa gareku!!!?



Dakata Zainabu, kina nufin d'an wajen ki Fahad ne yaga Ayusha ko kuma wa? " tambayar
da Daddy ya jefo mata kenan, k'arfin hali tayi tace "ba Fahad nake nufi ba Alhaji Umar baban
Fahad ne yaga Ayusha yake so" "wallahi tallahi k'awata kinyi asarar rayuwar ki, sai kace kin
rako mata duniya yanzu ke tsabar dak'ik'anci ki rasa wa zaki zo nemawa aure sai mijin ki, auren
ma na Ayusha ina hankalin ki da tunanin ki suka je, to idan ma mafarki kike to kiyi saurin
farkawa dan wallahi tallahi bazan tab'a amincewa da wannan iskancin ba Mtwww!!! kai ma na
dawo gareka babban munafiki wato buduwar zuciyar taka bata tashi sauk'a a kan kowa ba sai a
kan d'iyata!!! to ka sani ko zaka mutu baza ka tab'a samun ta ba dan haka ka tashi ka tattare
'yanmatan k'afafun ka bar gidan nan tun kafin nayi maka rashin mutunci, tsohon najadu kawai"
duk wannan bala'in Mummy ce keyi.....






Ajiyar zuciya me k'arfi Anty Zee tayi sannan tace "dan Allah dan Annabi k'awata ki kwantar
da hankalin ki, ki saurari abinda zan fad'a miki" "baki da sauran kalaman da zan saurara daga

gareki, kunya dai kin riga kin bani dan haka ki tashi ki bishi kuje wani wajen neman matar ba
nan ba tunda de ke kare ya riga da ya lashe zuciyar ki"



Ba suyi aune ba sai ganin Alhaji Umar sukayi ya zube a k'asa yana fad'in "dan Allah dan
Annabi ku taimaka ku ceto rayuwata daga halin da take ciki wallahi tallahi bazan tab'a iya
rayuwa ba tare da Ayusha ba rasa Ayusha dai-dai yake da rasa rayuwata!!!" sai kawai ya fashe
da kuka.



Mummy tsabar tak'aici ma kasa magana tayi, Allah sarki Daddy da yake shi namiji ne yasan
ba k'aramin abu bane zai iya sa gawurtaccen namiji kaman wannan kuka, yace "tashi ka zauna
Alhaji muyi magana"



A dai-dai lokacin suka jiyo ihun Aneeserh na fad'in "wayyo Allah na shiga uku Mummy kuzo
ku taimakeni Ayusha ta.....!!!"




```Masu karatu kuyi manage da wannan sai mun had'u a next page dan ganin me ya samu
Ayusha. Bissalam nice dai har kullum```




*ROOKIEY D BEST*
[14:55, 02/12/2017] +234 703 786 0131: ❄❄❄❄ *ALLURA TA TONO*
*GARMA* ❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄❄ *_A STORY BASED
ON FICTION & CONCOCTION_*


® REAL PURE
MOMENT
OF LIFE WRITER'S
*MOTTO:* *_we don't just entertain and educate, we also touch the heart❤of Readers_*

*BY*
*_ROOKIEY KAXS_*

*DEDICATED 2*
*_Summy SKT & Ummi Idris Aleey_*







66-70



Da gudu suka hau sama dan ganin halin da Ayusha take ciki, sun sameta a kwance
shame-shame kamar gawa a take hankalin su yayi mugun tashi Dad yace "Aneeserh me ya
same ta?" cikin kuka tace "wallahi nima ban sani ba dan muna zaune da ita tace bari taje ta
gaishe ku, bayan ta fita ta dawo cikin wani yanayin da ban tab'a ganin ta ba fuskar ta d'auke da
hawaye sannan ta rik'e kanta da hannun ta da sauri na nufi inda take sai gani nayi ta fad'i k'asa
tana nishi numfashin ta na fita sama-sama lokaci d'aya ya d'auke" sai ta k'ara fashewa da kuka.



Dad yace "Tabbas taji maganar da muke tattaunawa da alama suma tayi" kafin ya rufe bakin
shi Aunty Zee tayi saurin shiga toilet ta d'ebo ruwa ta watsa mata,Mommy na rik'e da ita sai tofa
mata addu'a take, d'ago idon ta tayi sukayi four eyes da Alhaji dogon tsaki taja sannan ta
nunashi da yatsa tace "wallahi idan na rasa 'yata kotu ce kad'ai zata rabani da kai"



Shi bai ma san

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0