Showing 3001 words to 6000 words out of 35990 words
banason kina yawaita
tambaya akanshi"Jannat ta fad'a cike da k'osawa.
Keeeee haka ya taka burki dab dasu, sora kad'an ya tab'a jikinta,wata iriyar razanannar k'ara ta
saki tare da duk'ewa kasa ta rufe kunnuwanta da hannuwanta.
A gigice ya fito daga motar don gani yake kamar ya takata ne,daiadai gabanta ya rangwafa tare
da fad'in"hey Baby ,tashi mana ,motan bata tab'aki ba"Ahmad ya fad'a cikin tausasshiyar murya
mai dadi wacce inba kana dab dashi ba,bazakaji me yake cewa ba.
Jin motsin mutum kusa da ita yasa ta mike a razane tare da mak'alkaleshi tana fad'in"Uncle
please ka daukeni daga nan,babaso"Jannat ke fad'a a matukar razane da tsoro.
Baya da zab'in daya wuce rungumeta a lokacin don ganin bata cikin hankalinta dukta
rude,"shiiiii"abunda ya iya furtawa kenan tare da bubbuga mata bayanta,daskarewa Madinat
tayi tana kallonsu zuciya cunkushe da kuna.
A hankali ta soma d'ago daradaran idanuwanta Wanda suka cika tab da hawaye ga zuciyarta
dake dukan ukku ukku don tsoro,tun daga k'asa take kallonsa har sama bata ida sakewa ba
saida tayi tozali da kyakyawar fuskarsa mai dauke da idanuwa masu kashewa duk wata mace
jiki,iya had'uwa Ahmad ya gama had'uwa ko wacce mace zatayi burin kasancewa a matsayin
matarsa.
Iskan bakinshi ya hura mata a fuska tare da d'aga gira d'aya da kanne ido d'a,da murya mai
kama da rad'a yace"kallon fa".
Wata iriyar kunya ta kamata data gane ya kamata tana kallonshi,hakan yayi daidai da isowar
Yaya Sulaiman daukarta sanin halinshi yasa ta duk'a da sauri ta tattara books dinta da suka
watse, ta tafi wurin motar.
Tunda ta juya baya yake binta da kallo kai "masha Allah" shine abunda ya iya fad'a a zuciya iya
had'uwa lallai wannan yarinyar ta had'u dukda ba wata babba bace,saida yaga tafiyar motarsu
sannan yaja tashi motar yabar wurin,sai lokacinma Madinat tabar wurin da tunani barkatai.
Wacece Madinat
Madinat y'ace ga malam Habu,Malam Habu matarshi d'aya wacce yaransa suke kira da
Goggo(lami),Goggo lami masifaffiyar mata Ce ga kwad'ayi da son abun duniya ,yaransu ukku
biyu mata d'aya namiji,Fatima itace babba yarinya mai sanyi hali kamar na mahaifinta ko
magana ma bata dameta ba,Sai Madinat wacce halinsu ya sab'a ,Madinat babu abunda ta baro
na daga halin Goggo,ta dauki burukan duniya ta sanyawa ranta,gashi ta fito daga gida mai
tsantsar talauci wada cin yau ko gagararsu balle na gobe,ta daukawa ranta burin auran mai
kud'i ,a duk duniya ta tsani wani yaci gaba sab'anin ita ta kasance mai fuska biyu wanda tana
bak'in cikin a nuna gidasu ace wai ita Y'ar gidan don haka tayi burin auran hamshak'in mai
kudi,sai Auwal wanda yake karaminsu.
Dalilin had'uwarsu da Jannat.
Tafiya yake da wasu tsummakaran kaya a jikinshi yayi lakwas dakin gansa kinsan yunwa ta
gama yi masa illah Malam Habu kenan,wata katuwar Jakka ya hango ,cikin sassarfa ya isa
gareta tare da budewa,mamaki ne k'ara ya bayyana a fuskarshi tare da k'ara waro ido
sakamakon abunda ya gani ,dollars ne cike da jakkar da wata rantsetsiyar waya a ciki,ringing
din wayarne ya dawo dashi daga tunanin da yake,hannu na kyarma ya dauki wayar yana
jujutawa da neman taya zaiyi ya ansa wayar,sai a kira na biyu ya iya d'aga wayar sallama dauke
bakinsa.
Alhaji dake zaune kan kujera yasha shiga ta alfarma ga Jannat dake kwance akan cinyarsa
tana wasa da tedy lokacin zatakai kimanin shekara 10,ansa sallamar yayi tare da fad'in"don
Allah a tare da wayarnan ko antsinci jikka a tare da ita"?.
"Eh kwarai kuwa,na tsinta,amma meye a cikin jakkar?" Malam Habu ya tambaya.
Murmushi yayi tare da fad'in sunanshi ya kuma cewa"kud'ine a ciki kuma dollars ".
Zunbur Malam Habu ya mike donjin sunan Alhaji,tabbas a garin babu wanda besan Sunan
Alhaji Abdullahi Canji ba" Alhaji karka damu kud'inka sun fad'o hannu na gari ,zan kawo maka
kud'in ka har Gida yanzu ".
" tona gode sosai,Allah ya kawoka lafiya"sanna sukayi sallama.
Daukar jakar yayi nik'i nik'i da sallama ya shiga gida,amma ko arzik'in a ansa masa be
samuba,saima muguwar Harar daya samu,kujera ya samu tare da zama duka yaransa suka
masa sannu da zuwa,ya amsa cikin fara'a da sakin fuska.
"Gara da Allah yasa ka dawo,gasunan har yanzu basu karya ba ,balle kuma na rana"Goggo ta
fad'a cike da masifa.
" a'a lami ba nabar kayan tuwo ba?"ya jefa mata tambaya.
"Wallahi baka isaba,yarana ba kalar cin tuwo ba,waima meye ka taho dashi a jakarnan irin ta
arnaku a bude mu wawasa namu kason".
Girgiza kai yayi ,beyi mamaki ba don yasan dama halinta ne"dukiyar amanace na tsinta,kuma
yanzu zan kaiwa maisu" ya bata ansa yana mikewa.
Tsalle ta daka dashan gabanshi tana fad'in "inka isa Allah ya tsinan,dole ka ajesu muma mu
dama kamar kowa,in banda rashin sanin ciwan kai sai ka tsinci kud'i kuma kace mayarwa
zakayi,to ba'a yika ba.
" ke Fatima tashi maza ki tuka maku tuwo,nina fita saina dawo"yana zuwa nan be jira cewar
kowaba yayi gaba abunsa har wankanma ya fasa.
Tun daga wannan rana wahalar Alhaji Habu ta gushe,Abba ya bashi jari duk wata kuma yana
bawa iyalansa abincin wata day'an kudade kuma ya dauki nauyin karatun yaransa ya kuma
bashi gidan zama,tun daga nan Jannat ta kwallafa rai ga Madinat suka zama y'an uwa na sosai
har makaranta tasa aka hadasu .
Ci gaban labari
*Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karshe*
*ALKALAMIN MARYAMA* âœ�í ¼í¿»
Pls
Vote
Comment
And share
Luv u guys
مسب* الله Ù†Ù…ØØ±Ù„ا *Ù…ÙŠØØ±Ù„ا
___________________________________
*í ¼í¼ˆKAINUWA WRITERSâœ�í ¼í¿¼ ASSOCIATION*í ¾í´�í ¼í¿»
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________
í ½í²žâšœí ½í²žâšœí ½í²žâšœí ½í²žâšœí ½í²žâšœí ½í²žâšœí ½í²žâšœ
*DAFIN SO*
STORY AND WRITING BY
*MARYAM ISMAIL*
{MAJI DA'DIN KAINUWA}
MARUBUCIYAR
SANADIN GATA
DALILIN SO
HANAN
YAUDARA KO BUTULCI
ASALI NA
TABON 'DA NAMIJI
ADDINI NA
SO 'DAYA
Fitattu sha biyar (15) 2020
Follow me on Facebook at
Maryam Ismail(maji dadin Kainuwa).
*page* 11 to 15
Tun a mota ya fara balbaleta da bala'i,"uban waye na ganki dashi acan tsaye?"
Shiru tayi a matsukar tsorace don ita kanta tasan bala'in Yaya Sulaiman yafi karfinta,wata Uwar
tsawa daya daka mata saida tayi zumbur ta baro sit din motar tana kallonshi idanuwanata
harsun kawo ruwa "ya ....ya shid'in ya kusa bigeni da...da mota ne"ta karashe maganar a
matukar tsorace.
" shine kuma don tsabar iskanci zan tambayeki kimin banza,wallahi zan b'alb'allaki idan na
kuma yi maki magana kikamun shiru"ya fad'a a hassale.
Bata kuma cewa komai ba ,don tasan donya tsaya ya jibgeta ba abu mai wahala bane ,Yaya
Sulaiman beda hakuri ko kad'an shiyasa take matukar tsoranshi ,har Allah ,Allah take Yaya
Sawam ya dawo daga tafiya koya koma kaita school.
Cikin wani tankameman gida sukayi parking ,fita tayi da sauri gudun karta kara had'asu ashe
tabar Textbooks dinta a ciki.
"Ke ubanwa zai maki dakon wannan Yan iskan books din naki?" Ya jefo mata tambaya murya
cunkushe.
"Kayi hakuri na manta ne"hannu na kyarma ta kwashesu ganin hararar da yake jefa mata yasa
ta zunduma a guje cikin gida.
Kwafa yayi tare da Jan tsoki yayi waje abunsa.
(Nikam nace matar Sulaiman ta bani wallahi wannan jaraba haka).
Waro ido ta kumayi don ganin da gaske Yaya Sawam tage gani wani ihu ta saki ta ruga ta
rungumesa tana fadin" Oyoyo Yaya Sawam dina,shine ka dawo baka fad'amun bako?".
Lallai nan nake ganin tsantsar kama domin babu abunda ya raba kamar Jannat da Sawam
,dondai yana namiji ne kawai,murmushi yayi tare da fad'in"lill baki girma har yanzu ba zaki daina
rungumata ba,kinfa girma kuma kinsan ba kyau ko".
Turo d'an karamin bakinta tayi tana fad'in"to kaiba Yayana bane ba,kai komai baka so"
Shigowar Abba ya katse masu firan,ya shigo cikin Shiga ta alfarma murmushi bayyane akan
kyakyawar fuskarshi ,kai tsaye tsakiyar Sawam da Jannat ya zauna yana shafa kanta tare da
fad'in "a'a mutanan Lagos zuwa ba sanarwa sai kawai mu ganka"
"Abba sannu da fitowa,zuwan bazata ne kawai na gaji da hutun na dawo gida nima,nayi missing
rigimar Lill"ya karashe maganar yana lekenta,itako tayi lamo jikin Abba batashi takeyi bama.
" ke kullun son jiki kamar Mage ,Abban ma saikin kwanta a jikinshi duk girmanki tashi maza kije
ki cire Uniform dinki"Yaya Sagir ya fad'a dake zaune tun d'azu yana kallon yarintar da Janna ke
saki.
"Idan bata kwanta jikin Abbanta ba,jikin wa zata kwanta Sagir" Abba ya bashi amsa.
Wani tuk'uk'in bak'in cikine ya turnike zuciyar Sulaiman yana ganin duk sakalcin Jannat dasa
hannun Abba yarinya na SS3 bata daina kwanciya akanshi ba.mikewa yayi fuuuu hakan kuwa
yayi daidai da fitowar Innata "au don rashin Arziki Sule bigeni zakayi,yaro sai bak'ar zuciya
kamar ba misulmi ba ina dalilin wannan bak'in halin baka".
Wata Uwar harara ya watsa mata yace" inna tureki meye a ciki ni bani wuri Kafin kijiki a k'asa
kur'an"yana zuwa nan yayi gaba abunsa sai surhwa bala'i yake.
"Sai dai ka ture Ubanka Abdullahi gashinan,d'an banza marar mutunci dakai"
Dariya Sawam ke dannewa amma saida ta fito har dukewa yakeyi don tsabar dariya.
Take kam Inna ta juyo kanshi "kaji wani marar mutuncin ko,yaushe ma ka dawo d'an banza mai
Jan kunne d'aya bayan d'aya zanci mutuncinku nasan tsiyar dazan kulla maku Yan banza".
Tsalle Sawam ya daka tare da rungume Innata yace" I love u Innata".
"Kaga aekinku kenan,maza zauna Ku barta ta huta " Abba ya fad'a.
"A'a banni dasu duka zan iya dasu wallahi" Innata ta fad'a tana zama.
"Innata sannu da fitowa,bari na sauya kaya Nazo muci abinci kinji". Jannat ta fad'a tana
mikewa.
" to y'ar Albarka jeki kinji"
Maida kallonta tayi ga Sagir "tokai ina Uwar taku kuma,da baka iya tankawa mutane don bakin
hali".
Murmushi kawai yayi yace " tana d'aki innata".
************
Zaune yake daga shi sai 3 quarter da singlet cikin kayataccen parlonshi Wanda yaji kayan more
rayuwa ko d'akin wata macen Albarka ,laptop ce gabanshi sai danne danne yakeyi Dr
Ahmad(Sorry a baya nace Ahmad business ya karanta,mistake ne Dr ne ya karanci Medicine
da fatan zaku fahimcenu) kenan,hankalinshi kwance idanuwansa sanye da siririn farin gilashi
irinna likitoci.
Ko Sallama batayi ba haka ta banko d'akin ta shigo tana kare masa kallo dason ya tanka
mata,banza yayi da ita don haka tazo kusa dashi ta zauna tana fad'in "yo aekin banza,waikai
Amadu ubanmi ka dauki kanka,ko ubanka Dana haifa innazo wuri shi yake fara yimin magana".
Dafe kai yayi alamar y'ar tsohuwar nan ta fara takura mashi gaskiya,amma bece komai ba.
" au shirun zaka kuma yimin,nace ae maka aure duk wannan iskancin zaka barshi ne ae".
Hannu ta zura k'asan Table din da yake zaune ta janyo plate din abinci lafiyayye jolluf rice ne sai
rabin kaza da koslow amma duka lomanshi batafi biyu ba ya ajiye,"yauwa na samu abun
kamaka bari na kaiwa Hauwa'u(Ummi)wannan tasan wahakar banza takeyi bacin abincin kakeyi
ba"tana zuwa nan ta mike.
Saurin riko hannunta yayi cikin sanyayyar murya yace"Granny please mana".
"Ja iri,yo uban menene hilis(please)kuma kasan nace ka daina man wannan shegen yaranyen
da bana fahimtar komai a ciki,sakeni kuma dole nakai mata kamaji" tana zuwa nan ta fige
hanunta ta fice daga part din tana sababi ta nufi part finsu.
Yatsanshi biyu ya saka yana murza goshinshi kamar mai luliya wani abu,lips dinshi ya datsa
sosai kamar zai fasa,tare da furzar da iska daga bakinshi Wanda hakan ya zame masa
d'abi'a,mikewa yayi cike da kasaita ya nufi part din Ummi.
"Aeke wahala kawai kikeyi dama kin daina kaiwa wancan mishkilin banzan yaron abinci,dondai
zubarwa yake koya tusa gaba yaita kallo,yanzu kiji wannan don Allah don besan darajar abincin
ba" Granny ta karashe maganar tana zama.
Wata kyakyawar mata na gani zatakai kimanin shekara 45 amma jikinta be nunaba yacce
Kasan y'ar shekara 30,haka take tasha gayu da wani d'anyan less kwalakwalan dake jikinta da
yanayin ta zaisa ka gane cewa tabbas Hutu da dukiya sun jiku a jikinta,daka ganta zaka hango
tsantsar kamarta da Ahmad ,bako musu zaka gane ita ta haifeshi,Hajiya Hauwa'u kenan .
Sake da baki haka tabi plat din hannun Granny da kallo sannan ta maida kallonta ga Ahmad
dake shigo yanzu,"Mama kinyi kokari da kika gano haka ,Ahmad bayajin magana Mama bansan
meyasa bayacin abinci ba".
"Kema kinji ki da wani batu marar dalili ina yaro zai samu natsuwa bayan kinsan beda aure
gashi da shegiyar kwakwa duk yabi ya zuke sai bak'in rai,wallahi mata zan samo mashi kuma
dole ka aura " Granny ta karashe magnarta tana jefawa Ahmad mugun kallo.
Tsaki yaja "ke dallah bar wurinnan,anawa mutane magana kin zura idanu kamar na mayu"
Ahmad ya fad'awa Saratu da taketa faman matsawa Ummi k'afa.
"Mugun banza Amadu abunda ka iya kenan" cewar Granny.
"Wai ke ba Sunana Amadu ba,u have to stop calling with that nonsense name" ya karashe
maganar a has sale.
"To sannu Ubale,wato ubana kenan,ance Amadu kuma al-qur'an ka kuma zagina saina rama ni
kake cewa citap(Wai Stop hhhhh),ja'irin yaro da Hauwa kake, silili kasau din banza mai kama da
zabayyana mumunan banza" Ta karashe maganar tana nunashi da hannu tare da tab'e baki.
Wata uwar tsuka ya saki tare da zama kusa Ummi.
Karab Granny tace"tsaka ma da tayi Allah tsine mata yayi balle kai kayan banza".
Daukan plat din abincin Ummi tayi tana murmushi itakam tanason zaman Granny da Ahmad
diramarsu na birgeta saidai ba ikon dariya."oya maza ka bud'emin bakinka tunda haka ka
zab'a".
Kumbure fuska yayi tare da turo baki sannan ya bude kadan,Ummi ta saka masa spoon a
baki,tauna abincin yake kamar yanacin magani dakyar yake hadiyewa.
"Innalillahi wa'inna ilaihar raju'una ni Salame,wannan bankad'a har INA,ki tusa gardin Allah
ta'ala kina bashi abinci kai hauwa bakiji dadi ba wallahi,ni kunga tafiyata kada kusa zuciyata ta
fashe". Tana zuwa nan ta mike tare da wucewa hanyar d'akinta,da harara Ahmad ya rakata
harta b'acewa ganinsa.
Da k'ar yaci quarter din abincin shima saida yaga ran Ummi ya soma b'aci yanaci yana yarfa
hannu kamar wani Baby,shikam a duniya cin abinci shine babban abunda ke takura rayuwarsa.
*********
Bako Sallama ta banko kyauran gidansu ta shigo tana huci,saman katifar Goggo ta jefar da
Jakar makarantarta tana fad'in" aekin banza wai meyasa kullun itace sama dani,kullun saita
samu abu kafin ni"Madinat ta karashe maganarta tana huci.
"Saboda kinsa sanya,kin yarda kin zama y'ar kore kin nuna rashin wayo" Goggo ta fad'a Wanda
shigowarta d'akin kenan ta tsinkayi zancan Madinat.
Murmushi Faty tayi dake zaune gefansu tana duba littafi"Haba Goggo ba haka ya kamata ki
mata ba,kamata yayi ki nuna mata mahimmancin Jannat a wurinta tasan sun banbanta,ya
kamata ta mayar mata da alkhairi kamar yadda ta taimaketa lokacin da take bukatar taimako
,amma saiki biye mata".
"Ke dallah wawiya Samara marar ilimi wacce ta gado bak'in hali irinna ubanta,kai wannan
yarinya da asibiti na haifeki zance an canzamin ne,idan ba zaki bamu goyon baya ba kul na
kuma jin bakinki ,me mugun baki kawai.
*Allah ka gafartawa iyayenmu kayi mana kyakyawan karashe*
*ALKALAMIN MARYAMA* âœ�í ¼í¿»
Pls
Vote
Comment and
Share
í ¼í½‡í ¼í¼¹í ¼í½‡í ¼í¼¹í ¼í½‡í ¼í¼¹í ¼í½‡
í ¼í½‡í ¼í¼¹í ¼í½‡í ¼í¼¹í ¼í½‡í ¼í¼¹
í ¼í½‡í ¼í¼¹í ¼í½‡í ¼í¼¹í ¼í½‡
í ¼í½‡í ¼í¼¹í ¼í½‡í ¼í¼¹í ¼í½‡í ¼í¼¹í ¼í½‡í ¼í¼¹
*DAFIN SO*
Story and written by
MARYAM ISMA'IL
*MAJI DA'DIN KAINUWA CE* âœ�í ¼í¿»
*FITATTU SHA BIYAR (15) 2020*
*LITTAFAN MARUBUCIYAR*
SANADIN GATA
YAUDARA KO BUTULCI
HANAN
DALILIN SO
ASALI NA
TABON 'DA NAMIJI
ADDINI NA
SO 'DAYA
AND NOW
*DAFIN SO*
í ¼í½‡í ¼í¼¹í ¼í½‡í ¼í¼¹í ¼í½‡í ¼í¼¹í ¼í½‡í ¼í¼¹
مسب* الله Ù†Ù…ØØ±Ù„ا *Ù…ÙŠØØ±Ù„ا
___________________________________
*í ¼í¼ˆKAINUWA WRITERSâœ�í ¼í¿¼ ASSOCIATION*í ¾í´�í ¼í¿»
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________
Page 16 to 20
"Dama aeke kullun duk abunda zanyi banyi daidai ba,keda baki da zuciya da kishin y'an uwanki
haka zaki k'are cikin bak'in talauci,ni karki kuma shiga harkata wallahi" Madina ta fad'a tana
nunawa Fati yatsa.
Girgiza kai kawai Fatima tayi tare da fita daga cikin d'akin yayinda zuciyarta ke mata wani irin
kuna bawai kuma don kalaman da Madinat ta fad'a mata ba a'a ta sabayin fiye da hakan
ma,kawai sai don tana guje masu dana sani da zasu iyayi ko wanne lokaci.
"Mtswww wannan yarinya da