Showing 21001 words to 24000 words out of 35990 words
ba wani abu sabo, insha Allah zata
daina ".
Murmushin takaici Jannat tayi tace "karki damu, tana da gaskiya da gidan Ubansu suke wazai
goranta masu, gara ta rika tunasarmun da inda nake kona san abunyi, ni ban riketa a raiba".
Da gudu Mahmoud ya shigo dakin ya fada a bayan Amira ya rungumeta "Aunty Momy na
dawo"abunda ya fada kenan.
Share hawayenta tayi kafin ta juyo don tasan halin Mahmoud da shegen wayau ga surutu,
"Oyoyo yaron Aunty sannu da zuwa, ya School din? ".
Hannuwansa duk biyu yasa ya tallafi fuskarta "Aunty waya Saki kuka na halbeshi da bindigar
Daddy ?".kamar daga sama taji tambayar tasa.
"Habibi Idona yakemun ciwo nefa"ta basa amsa.
Da gudu ya fita a dakin, part din Faruq ya shiga yana hak'i baya parlo Kai tsaye Bedroom ya
fada yana maida numfashi.
Juyowa Faruq yayi ya jingina da mirrow yana kallon Mahmoud yace "ba sallah yaron Aunty? ".
"Oh am sorry Abban twins, Aunty na tana ciwan idone fa, sai ruwa yakeyi ".Mahmoud ya basa
amsa ,be jira me Faruq zece ba ya Kama hannunsa suka fito, har dakin Jannat ya kaisa lokacin
Iftihal ta fita, zaunar dashi yayi a bed yace "Daddy ka tambayeta ka bata magani, bara naje na
canza kaya kafin Ammi na ta fito da gudu yabar masu dakin.
"me yake damun ki ne ?".
Kamar daga Sama taji tambayar tasa.
Basarwa tayi tace "ba wannan yaran bane sai wahala suke bani ba "ta kare maganar yata
kwabe fuska.
murmushi kawai yayi don tsab ya gane ba abunda yasa ta kuka kenan ba, sharewa kawai
yayi yace "to Maman biyu ae sai hakuri,kuma kinga Anif ae baya da rigima, rigima saidai
takwara na ".
Murmushin ta mai kyau tayi har hakoranta suka bayyana "kilama gado yayi, kaima kawa Ammi
rigima ".
Sosai ta birgesa da irin farin cikin da yaga tana yi, yunkurawa yayi zai mata dundu.
"Allah Yaya na daina fad'a, bakayi rigima ba "ta kare maganar tare da rumtse idanuwanta
sosai ta soma kyarma.
"matsoraciya "ya fada ya kwashe yaran yabar mata dakin.
*********
Shirin biki ya kankama babu abunda Ummu da Mama (Maman Hanan) basu gama ba, amarya
sai shan gyara takeyi, har wani Shek'i takeyi,lefe na gani na fad'a Umma ta hadawa y'ar tata
akwati goma.
B'angaren Ango suma babu abunda basayi harta kayan sakawa komai iri d'aya Sadeeq da
Ahmad sukayi, saidai a bikin ya hana hidimar komai daurin aure kawai za'ayi sai walima, Umma
ce ta had'a walima daren aure,yaune ya kama ranar walima, an shirya komai tsab, Manya
manyan Malamai Umma ta gayyata, amarya tasha kyau cikin purple lifaya da wani d'anyan leshi
shima purple ga zanan lalle ansha ga kitso tayi matukar kyau sosai, Wa'azi sosai Malamai
sukayi akan aure da biyayyah ga miji, Amarya tasha kuka sosai Wa'azi ya ratsata, tasha
kyaututuka daga y'an uwa.
Ranar daurin aure
yaune ya kama ranar daure, kofar gidan Alhaji Aliyu ya cika d'an kam da d'an Adam abokai na
kusa dana nesa, sai kayi da gaske kake gane wanda kake nema, maroka sai aekinsu sukeyi.
Can kusa da liman na hango taurarun wato Ahmad da Sadeeq komai nasu iri daya harta
agogo sunsha kwalliya cikin wata d'anyar shadda Ash colour sai Hula da takalma bakake sai
fitar da wani sihirtaccen kamshi sukeyi suna kyalli.
shelar dana jiyo ne ta tashi hankali, yasa na kara kutsawa don tabbatar da abunda kunne na
yaji mun, tabbas haka ne An daura auran Zainab Kabir (Hanan) da Sadeeq Nasir akan sadaki
naira dubu d'ari.
mikewa sukayi fara'a fal fuskar su, suna gaisawa da jama'a,ana masu murna, bani kadai na
shiga rudani ba har mutane da yawa a wurin.
Tofa Reader's kunji wata sabuwa.
Majidad'iâœ�í ¼í¿»
مسب* الله Ù†Ù…ØØ±Ù„ا *Ù…ÙŠØØ±Ù„ا
*____________________________________*
*í ¼í¼ˆí ¼í·°AINUWA í ¼í·¼RITER'Sâœ�í ¼í¿¼*
*í ¼í·¦SSOCIATIONí ¾í´�í ¼í¿»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡
*DAFIN SO*
í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡
Story and writing by
*Maryam Ismail*
*MAJI DAD'IN KAINUWA CE* âœ�í ¼í¿»
facebook
Maryam ismail(maji dadi)
Inster
maryam maji dad'i
Page 99 to 100
Radau haka taji shelar daurin auran ta, a kunnen ta, wasu hawaye suka wanke Fuskar ta, ta
rasa gane shin na farin ciki ne ko kuwa aka sin haka?, tabbas tasan tayi rashin wanda take so
har abada, amman tasan Sadeeq ma ba daga baya ba, tashin hankalin ta shine idan Umma taji
ya zata dauki abun, sai dai kuma tana farin ciki donta auri wanda yake matuk'ar son ta.
Umma kam mutuwar tsaye tayi, ko dai Kunnen ta ne beji mata daidai ba?, Auran Ahmad akeyi
yau ba na Sadeeq ba, rud'ani ta shiga sosai, waya ta dauko ta soma kiran layin Daddy, baya
amsawa ,haushi taji ta yi jifa da wayan,safa da marwa kawai takeyi duk ta rasa meke mata
dad'i.
Bayan lafawar mutane, Daddy suka tara meeting din gaggawa wanda kowa ya halar ta, tun
daga y'an gidan su Ahmad, Sadeeq kai harda na su Hanan.
Cikin nutsuwa take shigo wa, babbar lufaya ta yafa sai zuba kamshi take yi,gefan Umma ta
zauna kanta na kallon k'asa ta gaishe su, amsa sukayi tare da saka mata albarka.
Sai lokacin Daddy yayi gyaran murya, aka bud'e taro da addu'a sannan yace "Nasan da yawa
cikin ku, kuna dauke da tarin tambayoyi akan sabon Al'amarin da kuke ji yanzu, amman idan
kuma kuka tuna komai Allah yana iyawa, to ba zai zama abun mamaki ba, kamar yacce kowa
ya sani ansa aure da niyar Ahmad amman kuma Allah da ikon sa sai ya koma akan Sadeeq, ina
so ku sani dama Allah ya nufa Hanan matar Sadeeq ce ba Ahmad ba, hakan ya faru ne ta
dalilai, da azo a samu matsala gara kar a fara".
Nan Daddy ya fad'a masu komai ya faru da yacce akai auran ya koma kan Sadeeq, Alhmdllh
kowa ya gamsu da baya nan sa.
"Ae ba wata matsala indai Hanan ta amince, don ni ita nafi ji, duka da Ahmad da Sadeeq duk
yara na ne ,fata na Allah ya basu zaman lafiya "Umma ta fad'a.
Sosai Hajiya taji dad'in karar da Umma tawa yaron ta, wanda bata yi tunani ba, albarka tasa
masu tare da yiwa Umma godiya.
"To Alhmdllh tun da kun fahimta, sai dai ina rokon ka Ahmad daka fitar da Mata, zaman ka haka
nan bazai yiwu ba, karka bani kunya "Abbu ya fad'a (baban Sadeeq).
Sosai sukayi godiya, sannan aka tashi taron cike da so da kaunar juna, kamar Family d'aya, da
yamma aka kai amarya dakin ta, washe gari akayi walima, Ahmad yasa Umma zata masa
magana amman sai ta share shi,shima haka yaci gaba da rayuwarsa cikin jin dad'i .
B'angaren Amarya da Ango kuwa hankali kwance suke zaman lafiya, Sun fahimci juna, suna
rayuwa cike da girmama juna.
A gurguje pls
After 6 year's
Yara ne maza masu matuk'ar kama da juna, ga shegen wayau, kamar yaran larabawa, komai
nasu iri d'aya, ball suke halbawa a cikin makeken Gate din gidan, karar motar da suka ji ne yasa
sukayi wurin motar da gudu suna "Appie oyoyo ",cikin sauri Faruq ya fita a motar ya rungumi
yaran tare da d'agasu Sama yace "Oyoyo my twin's "kallonsu yayi sosai sannan yace "Anif
waya saka ball?"
Kyakyawan yaron da aka Kira Anif wanda daka gansa kasan be cika hayaniya ba yace "Just ina
gwadawa ne ".
Jansu yayi zuwa cikin gida, anan suka samu Mahmoud yana ta aekin game a system yanzu ya
zama saurayi yana JS 2.
da gaggawa ta safko daga stairs tace "Mahmoud maza dakko mun Anif, Ball fa yake yi, yasan
baya da lafiya kuma "
Sai lokacin ta lura da Faruq dake dauke da yaran, murmushi tayi tace "Appie sannu da zuwa,
harka dawo? ".
kallonta kawai yake yi, tayi masa matuk'ar kyau, sanye take cikin dogon riga na material Pink
colour Sosai kayan suka Karb'i jikinta ga daurin zara buhari datayi, sosai ta kara fari da kyau
tayi d'as abun ta ga kibarta daidai kwanin sha'awa.
Sauke yaran yayi yace "eh Aunty na dawo ".
kama kunnen Anif tayi "Ahmad bana Hana ka Ball ba? "
"aushhh Aunty kad'an nayi, banyi gudu ba, am sorry to "Anif ya fad'a.
Janye yaron yayi yace "Amira aeko mutuwa tana kunyar idon mahaifi, karki cirewa yaro na
kunne ".
Dariya Mahmud yayi yace "Aunty muyi tafiyar mu, idan Appie yaga twin's ko kulamu baya
sonyi".
Haka dai suke ta fira gwanin burgewa, kafin kowa ya kama gabansa.
******
da gudu ya fad'o masa ya fige tab din dake hannunsa, shiru yayi idonsa k'asa can kuma yace
"Stop disturbing me pls, i hate that nonsense "
Zaro ido Arif yayi a fusa ce yace "u call me nonsense,am not i think u are "
wani uban naushi Anif yawa Arif a baya,yana d'agowa ya rama shima, jin hayaniyarsu yasa
Jannat shigowa d'akin ,da sauri ta rike hannun Anif tace "what's that, bana hanaka dukan sa ba
"
"Aunty he call me nonsense "Arif ya fad'a.
Cikin tsawa Anif yace "u did First, who ask u to come here"
"stop that, bana son wannan fad'an ranku zai b'aci yanzu kam ".
naushi Anif ya kaiwa chair din dake gabansa sai hawaye shar shar, bakin ciki ya dame sa an
hanashi ya rama, barin d'akin kawai yayi don tsabar takaici.
ji tayi har cikin ranta bata ji dad'i ba, don gaskiya tana matukar son Anif kuma tasan baya da
rigima zaku iya wuni a wuri be tanka kaba tasan Arif ya tsoka nesa, to amman bata da yarda
zata yi.
"Arif ka daina tsoka nan sa, bana son kuna rigima ".
Bude baki yayi zaiyi magana da tsawa tace "keep quite boy".
Ta fita tabar masa dakin.
Majidad'iâœ�í ¼í¿»
stylish Star ✨
مسب* الله Ù†Ù…ØØ±Ù„ا *Ù…ÙŠØØ±Ù„ا
*____________________________________*
*í ¼í¼ˆí ¼í·°AINUWA í ¼í·¼RITER'Sâœ�í ¼í¿¼*
*í ¼í·¦SSOCIATIONí ¾í´�í ¼í¿»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡
*DAFIN SO*
í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡
Story and writing by
*Maryam Ismail*
*MAJI DAD'IN KAINUWA CE* âœ�í ¼í¿»
facebook
Maryam ismail(maji dadi)
Inster
maryam maji dad'i
Page 101 to 102
Tun da ya dawo gidan bega Anif ba, tun daga dakinsu yake kwallah masa Kira "Anif, Anif, my
Son Why are you "shiru beji motsin kowa ba, da Jannat yaci karo, "ina Anif? "tambayar daya
jefa mata kenan, kauda idonta tayi "bansan ina yake ba "ta bashi amsa a takaice, wani wawan
kallo ya jefa mata "amman ae kinsan ba lafiya ne dashi ba, kuma kika barsa, bazaki iya neman
sa ba "kwafa yayi, ya wuce bayan gidan, enterance na lambun gidan ya shiga, can ya hangosa
mak'ale bayan flowers sai gyarman sanyi yake numfashinsa na fita a sassarke, da gudu ya isa
Wurin sa yana jijigasa, idanuwansa harsun canza kala, daukarsa yayi da sauri ya fito zuwa
compound na gidan driver din Ammi yake kwallahwa Kira, har riga rigan fitowa Ammi da Jannat,
"lafiya Kake kwallah wannan kiran haka? ",turus tayi ganin Anif a Hannun sa "subuhanallah
meya samu Ahmad din ","ki tambaye ta Ammi "ya kare maganar yana jefar Jannat da harare,
Key ya fizge daga hannun Bala ya fad'a motar ya fizgeta da uban gudu, cikin gaggawa Gate
man ya bude masa, shikam yayi gaba, "wai me yake faruwa ne Maryama?, meya samu yaron
ne? "
Shiru tayi tana raba ido, "Ammi nima ban gansa tun dazu bafa "ta bata amsa.
"maza dauko mayafin ki da Key din mota ,mu bisa ",da gudu tayi daki ta dauko hijab, dakin
Ammi ta shiga, Ibtisam ce kawai a dakin bata kulata dame take fad'a ba ta zari Key tayo waje,
ita ke driving din kai tsaye asibitin su Dr Salim suka nufa, mintuna kad'an suka kaisu, a
reception sukayi tambaya, aka basu amsa yana Emergency, tun daga nesa suka hango Faruq
yana ta safa da marwa da sassarfa suka isa, "ya jikin sa? "Ammi ta tambaya, goge zufar kansa
yayi "abunda nake jira kenan "ya bata amsa.
Ta glass din wurin Jannat ta hango yaron ta likitoci a kansa harda abun tai makon numfashi
,tuni hawaye suka wanke mata fuska yaron da take masifar so kamar ranta, shine yake wahala
haka saboda saka cin ta, tuni ta rude tana karanto ko wacce irin addu'a tazo mata, ganin ya
yunkuro kamar zai dai na numfashi, bata san ta Saki kara ba, tana bubbuga Glass din kofar
shiga take nema, da sauri Faruq ya rike ta "oya keep quite, bana son shirme anan ","Appie kaga
yana wahala fa, mutuwa zaiyi ya barni, idan ya mutu zan bisa Allah, kace ya tsaya don Allah
karya barni bazan kuma bari a b'ata masa rai ba ".
"shhhhhii nace kiyi shiru ba, kina mayar dake gida ",shiru ta hadiye kukan dake taho mata
zaunar da Ita yayi, Ammi tazo tana bata baki da hakuri, Dr Salim na fitowa duka Suka mike
suna jiran mezai fad'a, "karku damu Asthma dinsa ce ta tashi, da alama ya zauna wuri me
sanyi, ko kuma an bata masa rai, dole sai kun kiyaye wannan fa, yanzu komai yayi daidai zaku
iya tafiya "takarda yaba Faruq "a nemi wannan drugs din friend ".
"OK insha Allah, thank u, sai mun hadu "
Ammi ta karbi driving motar ta tayi gaba, shikam yana front site, sai Jannat a baya ga Anif a
cinyar ta Yana bacci, shafa kansa take tana hawaye da tunanuka iri iri har Suka iso gida, da
gudu Arif ya fito yana kallon Anif dake hannun Faruq har dakinsu aka kwantar dashi a bed,
kansa Arif ya shafa Yana kallon Faruq "Appie meya same sa please"ya kare maganar yana
marairaice fuska kamar zaiyi kuka, "Asthma dinsa ya tashi, but he is getting better karka damu
".gyada kai yayi yace "Allah ya basa lafiya ",duk wunin ranar Arif anan ya wuni sai da Faruq yayi
da gaske sannan yaci abinci kadan, beyi daidai ba har sai da yaga Anif ya tashi, kuma Alhmdllh
ya tashi da sauki, bude idon sa na farko shima Arif ya tambaya a tare sukaci abinci sannan
yasha Drugs dinsa suka fara kallo. Sosai Jannat tayi farin ciki da ganinsu haka, taji dadi sosai
tana godewa Allah.
7days latter
Kowa gidan sai shirin tafiya biki akeyi Abuja, sosai hankalin ta yake tashe, dondai bata son yiwa
Ammi Gardama da bata je ba, duka Sun gama shirya komai a mota, sai tafiya motan farko
Ammi, Ibtisam da Mahmoud, sai Arif wanda duk inda Ammi tasa kafan ta yana biye da ita, Bala
driver ya dukasu sukayi gaba, sai dayan Motan Ibtihal da Anif a baya, ganin harsu Ammi Sun
tafi Jannat bata fito ba yasa Faruq komawa don dubo ta, tsaye ya ganta tayi shiru, "Amira ya
kira sunan ta "dagowa tayi tana raurau da idon ta, juya mata kai yayi ya kama duka hannu
wanta biyu suna fuskantar juna "bana hanaki tunani ba, Amira ki yarda dani babu abunda zai
sameki ina tare da ke, ki tsai da hankalinki zuwa Abuja bashi zaisa ki rika tuna baya ba, ki
fuskanci gaba yaci ace yanzu farin ciki zakiyi kodon rayuwar yaranki kinsan suna bukatarki, ki
daure kinji, insha Allah komai zaiyi daidai ".
Gyada masa kai tayi tana share hawaye, mikewa tayi, batace komai ba tabi bayansa, front sit ta
shiga nan Suka dauki hanyar Abuja.
Majidad'iâœ�í ¼í¿»
stylish star✨
مسب* الله Ù†Ù…ØØ±Ù„ا *Ù…ÙŠØØ±Ù„ا
*____________________________________*
*í ¼í¼ˆí ¼í·°AINUWA í ¼í·¼RITER'Sâœ�í ¼í¿¼*
*í ¼í·¦SSOCIATIONí ¾í´�í ¼í¿»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡
*DAFIN SO*
í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡
Story and writing by
*Maryam Ismail*
*MAJI DAD'IN KAINUWA CE* âœ�í ¼í¿»
facebook
Maryam ismail(maji dadi)
Inster
maryam maji dad'i
Page 103 to 104
Sadaukarwa ga Real majidadi fan's group
Tunda Suka doshi hanya ta kasa sukuni, hankalin ta duk inda yake ya gama tashi, rayuwar da
tayi baya ne kawai ke dawo mata, fad'uwar gaba kam ba'a maganan sa, duk wannan abun da
takeyi Faruq yana lura da ita, ya rasa me yasa ta tayar da hankalin har haka, juyowan da zaiyi
ne suka had'a Ido, hawayen da yaga suna shirin safkowa ne yasa ya girgiza mata kai, itakam
batayi aune ba taji hawayen na gangarowa akan kyakyawar fuskar ta.
"oh no, meye na kukan kuma?, please kiyi hakuri ".
Runtse idanuwan ta tayi da karfi, gaban ta na tsananin fad'uwa "Yaya inajin kamar zan mutu da
tsoro, gaba na yana faduwa".
Kallon Jannat ya Kama yi, a karo na barka tai"ki fara karan ta addu'a, bana son wannan
damuwar ".
A hankali ta soma Karan ta duk addu'ar da yazo gaban ta, ba wani jimawa bacci ya dauke ta,
ajiyar zuciya ya sauke, zuciyar sa cike da tunani iri iri. Sai da ya rage a motar shi kadai ke bayi
bacci ba, tunda suka fara tafiya sallah kawai ke tsayar dasu ,cikin dare suka iso Abuja, firgigit ta
bude idanuwan ta, jin sanyayyar iskar dake ratsa ta,tun da tabar garin su yaune