Showing 18001 words to 21000 words out of 35990 words
maki su, ni kuma nayi maki alkawari bazasu taba kukan rashin mahaifi ba indai
ina raye "
Da irin wannan maganganun ya kwantar mata da hankali, kwanansu d'aya aka sallamesu daga
asibiti suka koma gida, tasha mamaki babu abunda bata iske ba tun daga bed din yaran da
kayan sawa da duk wani abun da suke bukata, ita kanta saida ya cika mata akwati d'aya na
kaya, rasa bakin godiya tayi har kwallan dadi saida tayi, Sosai Ammi ke kula da ita da yaranta. Zaune take ta fito wanka, yaron na farko sai faman tsala kuka yakeyi, dayan kam ko yayi kuka
muryarsa bata fita sosai beda kuzari sosai, kallonsu kawai takeyi tama rasa me zatayi masu,
turo dakin yayi ya shigo da sauri ya tureta ya dauki yaran ya soma jijigasu, kafin ya fara basu
fida, nono baya isarsu, saida sukayi shiru ya kalleta yace"yara da haihuwa kwana hudu shine
zaki rika sakasu gaba suna kuka ko?, ki daina tun kafin mu bata ,wanne suna kikeso a masu
huduba dashi? "ya jefo mata tambaya.
Dukar da kai k'asa tayi tana k'ara gyara towel din data rufe kanta dashi, sannan tace "Yaya ka
zab'a masu duk d'aya ne. "
"no ki fad'a sunan da kike so, yanzu ke keda wannan hakkin".
Shiru tayi kamar tana nazari ,sannan tace "asawa Babban Umar Faruq(ARIF) karamin kuma
Ahmad (ANIF).
Murmushi ne ya subuce masa yace "First Father and Second Father kenan, Allah ya raya su ".
Huduba ya masu sannan yace "Amira ina ganin kamar Anif baya da cikakkiyar lafiya, bayan
suna zan kaisa a dubasa, Arif ya fishi kuzari da komai ma ".
Kai kawai ta gyada yayi murmushi ya mike yabar d'akin, kai tsaye d'akin Ammi yaje ya fad'a
mata sunan da aka sakawa yara, tayi murna sosai sannan tayi masu addu'a.
Ranar suna ansha shagali, anyi komai cikin wadata da kwanciyar hankali, naira a aljihun Faruq
kam ta koka, dan taro sosai Ammi tayi saidai muyi addu'ar Allah ya raya mata yaranta. Sosai ta
murmuje tayi kyau abunta, bama zaka tab'a cewa ta haihu ba, duk rabin rainon yaran yana
hannun Ibtihal ne da mai aekin daya samo mata,suna zamansu cikin jin dad'i,har gida Dr Salim
ya turo Dr ya duba Anif nan yake fad'a masu Asthma ce yaron ke garesa da ciwon zuciya dole a
kula dashi sosai, kada ana takura masa da kuma barinsa yana yawan kuka .
Tunda Faruq ya fad'a wa Amira hankalinta yayi mugun tashi, rungume yaron tayi ta fashe da
kuka tace "kaci sunanka Ahmad Anif babu abunda ka baro na mahaifinka, ina fatan Allah ya
tsare man Kai ya baka lafiya ".
Da kyar Faruq ya lallasheta yace zai nema masa magani ko a inane kada ta damu ciwo ba
mutuwa bane,haka dai Sukaci gaba da rayuwa duk kularta ta maidata akan Anif sukayi
shak'uwa sosai ko kad'an bataso yayi nisa da ita.
*ABUJA*
sukuku ta shigo gidan da k'atuwar jakkar kayanta fuska a kunbure, "yau na shiga ukku ni Goggo
meya sameki Madina ?",ta karashe maganar tana sakin roban Hannunta garin tuwon da zasu
tuk'a ya b'are a k'asa.
kuka ta fashe dashi tazo ta rungumeta, sai lokacin Malam dake alwala ya juyo ya kallesu takaici
ne ya kamasa ya girgiza kai yana k'ara godewa Allah daya natsar masa da Faty harya aurar da
ita, itama Madina a kullun fatan shiriya yake mata, mikewa yayi yabar gidan dama masallaci zai
tafi.
zaunar da ita Goggo tayi ta bata ruwa a randa, saida tasha sosai sannan ta soma ajiyar zuciya,
"ke bansan iskanci tunda kin huta sai ki fad'amun meke faruwa kuma"Goggo ta fad'a a masife.
"Goggo Ashman aure zaiyi, Alhaji Mado ya koreni, Goggo na shiga ukku duk wasu wanda suke
tare dani yau Sun gujeni Sun juyamun baya ya zanyi da raina ".
Salati Goggo ta Saki tana tafa hannu "shi Atman yake ko ubanwa dan yana kwallon shege
tantiri shine zaice aure zaiyi, to wallahi be isa ba, duka zanyi maganinsu y'an iska kawai ki
share hawayenki, ina nan baki ba kuka".haka taita sababinta, ita dai Madinat wanka tayi ta
hadiyi magani donduk dukan da Ashman ya mata yasa jikinta yayi tsami, baccin wahala ta
farayi.
*******
sanye yake cikin Farin Kaya yadi yayi matukar kyau ga Hula dara ya murza a kansa ga agogon
Gucci daure a tsintsiyar Hannunsa, takalmi yan soke ne kafarsa sai fitar da sihirtaccen kamshi
yakeyi, parlo ya fito beko tanka kowa ba ya zura kai zai fice, muryar Umma yaji tace "kai zo nan
ka duba wannan kayan ".ji yayi zuciyarsa na neman fashewa badon yaso ba haka yazo yana
bin tarin kayan su biscuits da alawa da kallo an cika wuri dasu, "kayan saka bikinka da Hanan
ne, kuma baza'a saka da nisa ba,saika fara shiri ".
Kai Kawai ya gyad'a bece komai ba ya tashi ya fita, gidan gonar Sadiq yaje yana neman hutawa
da zafin da zuciyarsa ke masa anan ya samu Sadiq ,shima be kulasa ba yaci gaba da harkar
gabansa, Sadiq kam be wani ji babu dadi ba,don yanzu mishkilancin Ahmad yafi na ko yaushe
baya magana ko kad'an aeki ma sai yaga dama yake zuwa.
******
A yaune duban al-umma suka shaida auran Ashman da Mubaraka akan sadaki nera dubu
hamsin, ango yasha wanka saidai yak'en dole yakeyi ji yakeyi kamar a mafarki, be bari anyi
shagali ba haka akayi bikin shalin alin gara amarya tayi Mothers day, da yamma haka aka kaita
gidan auranta wanda iyayenta suka narka dukiya a ciki, amarya sai murna yau burinta ya cika ta
auri Ashman da take so tun yarinta, kuma tayi alkawarin zama dashi ta ko wanne hali.
*Maji Dad'i* âœ�í ¼í¿»
í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡
مسب* الله Ù†Ù…ØØ±Ù„ا *Ù…ÙŠØØ±Ù„ا
*____________________________________*
*í ¼í¼ˆí ¼í·°AINUWA í ¼í·¼RITER'Sâœ�í ¼í¿¼*
*í ¼í·¦SSOCIATIONí ¾í´�í ¼í¿»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡
*DAFIN SO*
í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡
Story and writing by
*Maryam Ismail*
*MAJI DAD'IN KAINUWA CE* âœ�í ¼í¿»
facebook
Maryam ismail(maji dadi)
Inster
maryam maji dad'i
Page 93 to 94
*ina bada hakuri da jina shiru, kunsan rayuwar abubuwa basu Karewa,a kara hakuri my real
fans*
Zaune yake ya rike babbar riga a hannu ya zame hularsa baya shiru kawai yayi yana jin fadan
da iyayen nasa ke masa,kwatakwata hankalinsa ba wurinsu yake ba, shidai kawai yaji Adnan ya
tab'ashi alamar ya tashi su tafi, murya ciki ciki ya musu sai da safe, Sannan Suka fita.
"Ango kasha kamshi, kaga Angon Mubaraka".abunda Adnan ke fad'a kenan.
"wallahi zanci Uwarka, Shege kawai, ae duk da Hannunka aka mun wannan iskancin".
"Munahiki kana so kana kaiwa kasuwa, aure dai dole kayi ".da dariya k'asa k'asa ya figi Mota
suka bar wurin.
Har cikin gida ya rakashi kafin ya baro gidan, Kai tsaye gidan ya shiga babu alamar akwai
mutum a gidan d'akinsa ya shiga yayi wanka, ya fito daure da towel, tsaye yayi cak yana
kallonta da mugun mamaki, a harzuk'e yace "Ubanwa ya kawoki d'akin nan? "
Kyarma ta somayi tana raba ido don ta tsorata sosai, "ina jin tsoro ne Yaya "ta k'are maganar
tana hawaye.
Dafe Kai yayi "dallah ki rufe mun baki malama, ansan kina tsoron aka maki auran? ".
Had'iye kukan tayi dana kyarma, don gani take kamar jibgarta zaiyi, k'asa ta zame tana raba
ido.
Banza yayi da ita ya karaso cikin d'akin ya shirya, kafin ya haye Bed ya bata baya. Itama anan
ta zame tana bacci sai da Asuba ya tasheta shikam ya wuce masallaci.
******
"kaji Iskanci zagayen uwar me kakewa mutane? ",Sadeeq ya tambayeshi.
"ka fiye damuna Sadeeq, don Allah ka rabu dani "yana fadin haka ya kuma juya kanshi dake
matuk'ar sara masa, duk abun duniya ya masa yawa akai.
"solution fa kake so Ahmad, in baka fad'amun damuwarka ba, wa zaka fad'a wa ".
"a Gida ne aka kawo kayan saka biki na da wannan Yarinyar ".
Jin wani abu Sadeeq yayi har cikin ransa, donko ya dad'e da soyayyar Hanan a zuciyarsa, ya
kasa furtawa ne don ganin wanda akeso a aura mata .
"kaga akwai mafita,matso kaji ".
A kunne ya masa rad'a,murmushi Ahmad yayi yana kallonsa tare da girgiza kai sannan yace
"shikenan bara mu gwada sa'a".
*******
"waini na rasa meke damunki, wanne irin ciwo ne haka Madinat, ina kika kwaso shi, alamu ya
nuna kamar kina da ciki, yaushe rabon da kiyi al'ada?".
"Goggo na dad'e "ta bata amsa tana goge baki dukta galabaita ta gama kwarara amai .
"amman akwai sakarar yarinya, shine kuma kikayi shiru, so kikeyi ki jawo mun sheri, aeko maza
ki shirya asibiti zamu yanzu ".
hijab kawai Goggo tasa ta, tasanya Madi gaba suka je Asibiti, gwajin farko aka gano tana da ciki
wata biyu, salati Goggo ta Saki cikin tashin hankali tace "likita a zubar dashi yanzu nan ".
"bazai yiwuba inko aka zubar dashi zata rasa ranta don bata da cikakkiyar lafiya, sai dai kuyi
hakuri kuga abunda Allah zaiyi ".
"na mutu wallahi bazan zubarba, haka kawai na kashe kaina, wallahi nafi son raina akan komai,
kinga tafiyata ni, yo kaina farau bare naji kunya " .da sababi Madinat tabar asibitin ba arzik'i
Goggo ta biyota sai fad'a sukeyi a hanya.
******
Da sallama ya shiga gidan ,cike da farin ciki Umma ta tarbeshi suna gaisawa sannan tace "ina
abokin naka, aeni yau nasan fushi yake dani "
Sallama Ahmad yayi beko kulasu ba ya wuce d'akin Granny.
Maji Dad'iâœ�í ¼í¿»
مسب* الله Ù†Ù…ØØ±Ù„ا *Ù…ÙŠØØ±Ù„ا
*____________________________________*
*í ¼í¼ˆí ¼í·°AINUWA í ¼í·¼RITER'Sâœ�í ¼í¿¼*
*í ¼í·¦SSOCIATIONí ¾í´�í ¼í¿»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡
*DAFIN SO*
í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡
Story and writing by
*Maryam Ismail*
*MAJI DAD'IN KAINUWA CE* âœ�í ¼í¿»
facebook
Maryam ismail(maji dadi)
Inster
maryam maji dad'i
Page 95 to 96
"ka gani ko, sai fushi yakeyi dani, bayan gata nake so na masa ".
"to Ummu sai hakuri ae, insha Allah zai daina"ya bata amsa.
"shidai ya sani amman dole yayi aure ae, kuma badai wannan me kama da aljannun ba Allah".
Murmushi kawai yayi, yana tunanin wacce irin kiyayyah ce tsakaninta da Jannat.
"bari na gaishe da Granny "ya fad'a tare da mikewa.
Da Sallama ya shiga dakin Granny "y'ar tsohuwa matsamun na zauna kusa da amaryata".
"haba rabani da yaudara irin taka, kazo yau kamun wayau".
"haba yaufa dake nake auren,har toshin kaza zan kawo maki na amarci "ya Kare maganar yana
zama kusa da ita.
Wani harara Ahmad ya jefa masa yace "dallah malam ka zauna kayi abunda ya kawo ka".
"D'an nema da yake ta ciyoka ko, taimakonka zanyi idan kuma ka matsamun wallahi zan
tafiyata"Sadeeq ya fada.
Magana sosai sukayi da Granny kuma Alhmdllh ta fahimcesu, sannan tace kada su damu zatayi
abunda ya dace insha Allah. Da farin ciki Ahmad yabar dakin, yaji dadi sosai hankalinsa kwance
a ranar,sosai ya sake ranar har mamaki Umma takeyi,a ranar aka saka bikin nan da sati ukku,
komai Umma ta soma shirin biki, ko wanne bangare na amarya da ango shirin biki sukeyi, cikin
ikon Allah Granny ta fahimtar da Daddy abunda suka tattauna da yaran kuma ya fahimta yayi
na'am dashi.
*********
Sosai tayi abinci ta gyara ko ina fes, wanka tayi tasha kwalliya cikin atamfarta mai calar Blue
sosai ta Karbi jikinta tayi masifar kyau, be dawo gidanba sai wurin 10 kai tsaye dakinsa ya shiga
yayi wanka, ya fito yana goge kai da karamin towel, knocking yakeji "come in"ya fada yana
murza mai a jikinsa.
Tun kafin ta shigo kamshin turarenta ya bide dakin, taku takeyi cikin nutsuwa harta iso kusa
dashi ta duka har k'asa tace "ina kwana ",gabanta na dukan ukku ukku tana Tsoron amsar da
zata samu dauriya kawai tayi ta shigo,ba kamar data ganshi da towel.
Tsab ya gama karantar yanayin da take ciki, kawar dakai gefe yayi yace "lafiya".
Murya na rawa ta kuma cewa "your break fast is ready Sir".
"nace kiyi girki da ni ne?, ko kuwa nace zan rika cin jagwalwalonki? ".
Tuni idonta ya kawo ruwa tace"kayi hakuri, gani nayi ya dace nayi, tunda zamanka nakeyi ".
"Owk kije ina zuwa naga ko zan iya daurewa naci ".
Murmushi tayi k'asa k'asa don harga Allah taji dadin amsawar da yayi, don ba haka tayi
tsammani ba,mikewa tayi tana tafiya, da kallo ya bita ko ina na jikinta rawa yakeyi, donko
mubaraka itama ba baya ba wurin kyau.
A gaggauce ya shirya cikin k'ananun kaya don fita zaiyi, sai zuba k'amshi yakeyi ya fito, zaune
take a parlo da sauri ta mike ta karbi wayoyinsa da Key din motarsa ta bisa baya zuwa dinning,
tunda ta bude girkin, kamshinsa ya bide wurin chips ne da farfesun y'an ciki sai ruwan lipton da
yaji kayan kamshi, yana yatsine fuska yake cin abincin kamar yana tauna magani(í ¾í´£í ¾í´£anji dadi
anata fuskewa kafin mubaraka ta halbo jirgin mutum).be wani ci sosai ba ya mike ya karbi
kayansa tana masa Allah ya tsare bece komai ba ya fice abunsa. Tashi tayi ta soma tattare
wurin.Haka rayuwa ta ci gaba da tafiyar masu, tun yana d'an shareta harya fara kulata wani
lokacin har fira suke d'anyi, don mubaraka ba daga baya ba.
**********
"me kake tunani Abban Sulaiman "Momy ta fada.
murmushi yayi yace "ina tunanin rayuwa ne, Momyn Jannat ".
da sauri Momy ta dago tana kallon Abba wanda rabon da taji ya Kira sunan Jannat tun ranar
daya koreta, wani sanyin dad'i taji a ranta ganin koya sauko ne.
janyota yayi zuwa jikinsa yace "kina mamaki ne Umman Jannat? "
gyad'a kai kawai tayi tana murmushin itama.
"ba abun mamaki bane, dama can sharrin zuciya ne, yanzu kam ina rokon Allah ya nuna mani
y'ata kodon na gyara kuskuren dana aekata".
Hawayen dad'i ne suka zubowa Momy ta d'aga hannu tana godewa Allah daya nuna mata
wannan rana, sosai suka sha soyayyah ranar ran Momy Fes.
"uban me kuma kake leke, shege me siffar aljannu "Inna ta fada tana fitowa daga part dinta.
"karki kuma cemun shege tunda kinsan Ubana, part dinki na lek'ane ne, wallahi zamu koma
da"Sulaiman ya bata amsa.
Harara Inna ta watsa masa tace "wallahi Sulaimanu ina raga maka ne saboda wancan matar
daka dake dauke da tsohon ciki da tuni nasa anyi waje da kai kaima ".
"aeko ke da kinga inda zaki, donni kinsan ba'a wannan dani, tsohuwa kin kusa mutuwa amman
ki hayyaci kowa wallahi nayi maganinki"barin wurin yayi yanajin in yana wurin ba hakuri zaiyi ba.
"kuma nace Shege, munahiki Allah wannan yaron indai yana gidannan wataran kasheni zaiyi
"tanayi tana matse kwallah.
dariya Sawam ya fashe dashi yace "dama shine maganinki ae, inkin raina kowa shi Zai saita
maki sahu ae, kema saiki tab'o wanda ya fiki ".
"kaini naga jaraba, shegun yara duk Sun gado bak'in hali irinna Uwarku, nidai banga ranarku
ba, Duka zansa ya koremun ku daga gidan ".
"kanki akeji dai, kinga tafiyata "nan ya barta tana sababi.
bari mu leka Adamawa
Majidad'iâœ�í ¼í¿»
مسب* الله Ù†Ù…ØØ±Ù„ا *Ù…ÙŠØØ±Ù„ا
*____________________________________*
*í ¼í¼ˆí ¼í·°AINUWA í ¼í·¼RITER'Sâœ�í ¼í¿¼*
*í ¼í·¦SSOCIATIONí ¾í´�í ¼í¿»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡
*DAFIN SO*
í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡í ¼í½‡
Story and writing by
*Maryam Ismail*
*MAJI DAD'IN KAINUWA CE* âœ�í ¼í¿»
facebook
Maryam ismail(maji dadi)
Inster
maryam maji dad'i
Page 97 to 98
"kinsan Allah zan Kira Yaya Faruq, ki tashi ki kama yara sai zuba kuka sukeyi, kin tsaya
kallonsu ".
"ni bansan me suke soba, nidai na gaji wallahi abada su "Jannat ta kare magabar tana raurau
da ido hawaye ya cika taf a idonta.
"mtswww aekin banza, ubanwa ya haifesu da za'a badasu, kin wani damu mutane, to ki
daukesu ku tafi gidan ubansu idan akwaishi "Ibtisam ta fad'a.
Uwar harare Ibtihal ta jefa mata tace "ke baki daina shiga abunda babu ruwanki ko?, wai harsai
yaushe zakiyi hankali ".
"dallah malama rufemun baki, ko ciwan kanki baki sani ba kawai kin zama y'ar raino ,to karya
nayi inda uban a tafi wurinsa mana, kuma wallahi idan kika kara cemun bana da hankali sai
munyi bala'i dake ",zura shoe dinta tayi tabar dakin tana sababi.
Itakam Jannat hawaye yaki k'afewa daga fuskarta, ashe bata huta da wahala ba, ashe gori
bazai kare mata ba, lallai Uba daraja ne ga yaransa sai yanzu take kara jin ciwan abunda
Ashman da Madinat suka mata, bata tabbatar Sun gama tarwatsa mata rayuwa ba sai
yanzu,dafa kan yaranta tayi hawayenta suka zuba akan fuskarsu tace "mahaifinku na sanku,
yana kuma kaunarku kaddara ce ta rabaku kuma ina fatan ko bayan raina ta sake had'aku ".
Zuru yaran sukayi mata, wanda sunyi wayau sosai gasu bulbul abunsu kwanin sha'awa, sai
halba kafafu suke suna gwaranci, jin tausayin yara na ratsata tayi, dafa kafad'arta Ibtihal tayi
tace "Aunty Amira don Allah kiyi hakuri, kinsan halin Ibtisam