Showing 3001 words to 6000 words out of 37771 words

Chapter 2 - Rana Daya Book 1 Hausa Novels By Halima Abdullahi Mashi

ba kiyi aure ba?” Ta sauke ajiyar zusiya,
sannan ta sunkuyar da kai
“Ina yini?” Ta gaida shi. “Lafiya lau.” Ya amsa.
Kaka ta ce. “A tsaye za ku gaisa?” Ya kalli Kaka, sannan ya kalli Aliya. “Zo mu zauna can
kujerar kada Kaka taji abin
da zamu fada.” Aliya taja mayafinta ta rufe gefen
fuskarta alamun kunya, zuciyarta kuwa fal murna.
Gani take yi ma kamar ba gaske ba ne, wai
Shatimanta ne a gabanta. Sai da suka zauna ta sake gaida shi. Ya ce, “Ya ya ki ka ji da ki ka
ganni?” Ta ce, “Har yanzun bangama yarda cewa ba mafarki nake yi ba.”
Yayi murmushi, “Ni mamakina ashe ba kiyi auran ba?” Ta ce, “Duk wanda suke son in aura ni
kuma bana sonsu, sai wan Babanmu na Katsina ya ce su bar ni in zabi miji da kaina.To sai
Yayanmu Aliyu ya kawo min form din School of Nursing, shi ne ma na maida hankalina a kan
karatu.Ya ce, “Yanzun kin gama kenan?” Ta ce, “Eh, har na gama Practical dina, kuma na fara aiki a
wani asibitin kudi da ke nan unguwar.
Ya ce, “Shekarunmu nawa da rabuwa ne har da ki ka yi karatu ki ka gama?” Ta ce, “Shekaru
uku fa da watanni kenan.”.
“Hmm! Haka ne. Za ki iya tuna rabuwarmu ta
karshe?” Ta daga kai kamar mai son tayi tunani. Ta ce, “Mun rabu ne wata ranar Asabar wadda
ba zan taɓa mancewa da ita ba.Mun rabu kafin Asabar din a kan magabatanka

zasu zo, amma maimakon haka sai na ganka da
labarin wai Mahaifanka sun ce za ka tafi Dubai don kayo Degree na biyu. Ta lumshe ido kafin ta
ci gaba da magana. “Ba zan iya misalta bakin cikin da na tsinci kaina a wannan ranar ba, domin
a cikin gida ina fuskantar
matsin lamba a kan in fitar da mijin aure. Na ce to, ka sa a zo a fadawa iyayena ko za su
amince in jira ka. Washegari Lahadi ku ka zo kai da abokinka Munnir don neman yardar iyayena
su bar ni in jira ka dawo, sai Mahaifana suka ce sam! Ba zan jira ka ba, aure za su yi min.” Ta
sake yin shiru tare da sauke ajiyar zuciya, sannan ta kalle shi. “Haka ne?” Ya ce, “Ashe dai ba ki manta ba. Ni Yayanku Aliyu ma ce min yayi
dama wani abokinsa yana sonki, shi yasa na yanke
hukunci cewa yanzun kin yi ‘ya’ya biyu.”
Tayi ‘yar dariya, “Duk sun zo na ce ban son Ya ce, “Ashe rabona ce, amma kina da su. kishiyoyi
fa!”
Ta zaro ido, sannan ta dube shi “Kayi aure ne?”
Ya ce “Rana daya za a sa ku a lalle.” Ta ce, “Nasan kana zolayata ne.” “Zancen gaskiya kenan
Aliya, ku uku ne. Bayan na tafi Makaranta cike da bakin cikin
rabuwa da ke, sai Allah Ya hadamu da Amna, ‘yar
asalin jihar Kano ce, tana da dangantaka da
Masarautar Kano., Babanta mai kudi ne sosai.
Amna ta birge ni da halayanta na kamun kai, da nutsuwa, haka yasa wasu dalibai ke surutun
tana da girman kai. Gidan da take kusa da namu ne mu kan hadu lokuta da dama in Makaranta,
ko in mun je sallah. zamu shiga
Ni dai tana birge ni, kuma ina son mu ke magana. Sai wata rana nayi mata sallama ta amsa
muka gaisa, na ce ita ‘yar Nijeriya ce a wacce jihar? Ta ce Kuno. Tun daga lokacin muka soma
magana har
soyayya ta shiga tsakaninmu, sai ma na gane son
da take min ko kwatanshi bana yi mata. Har mun
shirya batun aure da ita.
Kasancewar zan rigata dawowa sai muka shirya zan jirata. Na rasa sadarwa tsakaninmu da ita
sakamakon wayoyina da Laptop da barayi suka sace. Yau din nan ta kira ni ta ke sanar min
dawowarta kasar.”
Aliya ta danne kishinta ta ce, “To ka ce mu uku ne dayar fa?” Ya ce, “Nafisa jikar Kaka ce, ina ce
kin santa ma?”
Aliya ta ce “Dama kuna soyayya da Nafisa ne? nasan ta mana.” Ya ce, “Kafin in dawo iyaye
suka kulla, yanzun su ba su san ma da batun Amna ba bare naki. Yanzu dai za mu gyarota da
Kaka, saboda in ta yarda dole Baba ya yarda, shi kuma in ya cije dole Hajiya ta saki.”
Aliya ta ce, “Tab!” Ya ce “Ba za ki iya ba ko?” Ta ce “A’a in ana auren mata dari Shatima ka aura
ba zan ki ba, na dai tausaya maka ne.” “In kuma na samu ta hudu sai in cike kawai.”
Ya fada cik zolaya. Aliya ta ce, “Ni dai yanzun
ka fada min wa ka fi so?””Wadda ta fi sona.” Ya bata amsa a takaice tare da mikewa. “Bari in tafi
ko, amma kafin nan ki tashi kije gida zamu yi magana da Kaka.” Ya mika mata wayarshi
karama.”Sa min lambarki, ki ajiye da sunan da ki ka ga
ya dace.” Ta saka lambar tayi shiru tana tunanin

sunan da zai dace.
Ya ce, “Ki zabi duk sunan da ki ka sa shi ne sunanki a bakina.” Cikin sauri ta rubuta (My Love)
ta mika mishi. Ya amsa ya kalleta.My love?”
Tasa hannu ta rufe fuska cikin jin kunya. Ya ce, “Zan kira ki da wannan sunan a gaban kowa
ma, kuma ina son ke ma ki kira ni da shi a gaban kowa.
Ya nuna mata hanya da hannunshi, “Je ki
sallami Kaka.” Ta tsugunna a gaban Kaka ta ce,
“Zan tafi gida.” Kaka ta ce, “Har kun gama hirar?
To Allah Ya tabbatar muku da alkairi.” Har bakin falo ya rakata, sannan ya dawo gurin Kaka. Ya
ce, “Kin ga abin Allah ko Kaka!”
Ta ce, “Ai ni na zaci ita ce ta biyun.” Nan ya bata labarin Amna. Ya ce, “Goyon bayankı kawai ni
ke nema.” Ta ce, “Shatima nemi komai gurin Allah. ni ai in hudu za ka yi ina murna, don bana
son ragon namiji.



*Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan
account number👇🏻*

```ACT<<0700549935
Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925```

*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427*_____
*🏚️RANA DAYA 🏚️*

CHAPTER 3

*BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*

*Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan
account number👇🏻*

```ACT<<0700549935
Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925```

*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427*

*Masu bukatar a tallata masu hajar su ko link din group din su na kasuwanci suyi magana ta
wannan number 09068032427 zamuyi maku akan farashi me sauki*


Mun tsaya

Ya nuna mata hanya da hannunshi, “Je ki
sallami Kaka.” Ta tsugunna a gaban Kaka ta ce,
“Zan tafi gida.” Kaka ta ce, “Har kun gama hirar?
To Allah Ya tabbatar muku da alkairi.” Har bakin falo ya rakata, sannan ya dawo gurin Kaka. Ya
ce, “Kin ga abin Allah ko Kaka!”
Ta ce, “Ai ni na zaci ita ce ta biyun.” Nan ya bata labarin Amna. Ya ce, “Goyon bayankı kawai ni
ke nema.” Ta ce, “Shatima nemi komai gurin Allah. ni ai in hudu za ka yi ina murna, don bana
son ragon namiji.

Shatima mai sunanka gwarzo ne, mu hudu ya aje, ba dai rana daya ba. Amma tsakaninmu
babu nisa. Duk ciki ni ce kararmu, yau ina abokan zaman nawa? Ina shi Maigidan namu? Duk
sun amsa kiran Ubangijinmu.
Mun zauna da dadi-ba-dadi, kuma an yi zaman mutunci, kullum ina yi musu addu’ar samun
rahamar Allah, kuma. Allah Yasa tawa tayi kyau irin tasu. The de jah manch slara ar Tilb 2
Ya ce, “Amin Kaka.” Ta ci gaba da fadin, “Mata hudu ba matsala ba ne matsalar tana tasowa ne
daga gurin namiji in ya kasa adalci a gidansa.”
Ya ce, “Kaka ni ai renonki ne ko? In sha Allah zan yi ba zata.” Ta ce, “In dai sunanka
Muhammad Ja’afar, kuma ka amsa lakabin ka na Shatima, to kuwa nasan kai gwarzo ne.”

*******
Tun da aka soma yi wa Malam Adamu gashin kashi sai jikin ya soma sauki. Dubu ishirin da
suka samu a gurin Alhajin nan ta taimaka musu sosai.
Ummu Salma ta sauka daga cikin Adaidaita dauke da kwanukan samira tuwo da miya. Ta shiga
cikin asıbitin da hanzarinta don kaiwa Mahaifanta tuwon da ta yo bayan ta gama suyar Wara, ta
samu riba tayo cefane ta girko.


Tana taka matakalar da zata hau sama in da dakin maza yake, sai ko kafarta ta zame, takalmin
kafarta silifa mai soso ya taimaka gurin zamar da
ita har ta kai kasa.
Ba damuwarta faduwar da zata yi ba, damuwarta kawai kar abincin Mahaifanta ya zube. Sai dai
ta makaro, domin tuni abincin ya tarwatse a kan siminti.
Wata ma aikaciyar gurin ta soma yi wa Salma fada. “Ke da Allah can! Kin zo kin bata wa
mutane guri da wannan kazamin tuwon naku, da Allah zo ki share shi.”
Ta mike tana kukan bakin cikin asarar abincin
iyayenta. Daidai lokacin da wata mai sharar asibiti
ta iso. Wannan ma’aikaciyar tana ci gaba da yi wa
Salma sababi. Mai sharar ta ce, “Irin kazantar da ku ke yi a gidanku shi ne kin zo kina yi mana a
nan guri din?” Ta tambayi Salma cikin hausarta mara dadi.
Salma dai sai kallon su take yi. Ma’aikaciyar ta ce, “Ba za ki kwashe mana warman kazantar a
nan gurin ba? kalli wai wannan ne abincin da za’a ba mara lafiya. Ta ya ya zai warke yana cin
irin wannan kazanta?”Cikin mutanen da suka taru a gurin suna kallo sai wata daga ciki ta ce,
“Gaskiya bai kamata ku saka yarinya karama a gaba kuna mata ihu ba, ita ma ai ba za ta so ba

tayi asarar abincin da Allah ne kadai yasan yanda suka samo shi
Nan suka dawo kan matar, hayaniya ta soma yin sama. Tasa hannu zata dauki tuwo, sai ta ji an
ce”Bari kar ki taba.” Tana dagowa sai taga Alhajin nan shi da wani a cikin jerin mutanan da suka
taru a gurin.
Ya ce, “Ina ma su yin sharar asibitin?” Matar ta ce, “Mu ne muke shara, amma ita ne ta kwashe
wannan din da ta zubar.”
Ya ce, “Zo ki wuce, ku ku bar shi in ba za ku
kwashe ba.” har ta nufi sama ya ce, “Zo nan.” Ta
nufo gurinshi, ya ce “Bimu daina kukan.” Ta ce,”To.”
Tasa kasan hijabinta tana share hawaye. Ya ce.. “Kin gane ni kuwa?” Bayan sun je gurin mota.
Ta ce, “Eh, na gane ka. Kai ne wanda ka taimake mu shekaranjiya.”
Ya ce. “Sunana fa?” Ta sake kallonshi, sannan ta girgiza kai “Ban san sunanka ba.” Yayi
murmushi, sannan ya ciro kudi a aljihunshi ya nuna mata wata hanya.”Ki bi nan ki dan mike za
ki ga shagunan saida abinci, su wanke miki kwanukan sai ki sai musu abinci.”
Hannu biyu tasa ta amshi kudin, tana ta godiya. Shima abokin yana cikin mota lokacin, ya ciro
dubu daya ya ce, “Kara mata.”
Salma tayi godiya, sannan ta mike hanyar da ya
nuna mata cikin murna tana kirga kudin, dubu
hudu ne cas! Duk da dubun abokin.
Sakwara ta sai musu da miyar agushi, ta sai musu lemon roba da ruwan sanyi. Tana isa Innarsu
ta idar da sallar La’asar. Ta ce, “Yau ba kasuwa ne hala muka ji ki shiru
Ummu Salma?” Ta ce, “Ai nazo tun dazu ɓarewa
ya yi. Nan ta basu labarin komai, sannan ta kawo
sauran kudin ta ba Innarsu. Inna ta ce, “Ba na amsa duka ba Salma, bani dai dubu guda sai ki
rike dubu biyun, ke da ki ke dawainiya da mu. Shi kuma Allah Ya shi masa albarka, ya saka
mishi da alheri, ya biya masa bukatunsa shima.” Salma ta ce, “Amin Inna.
Sai bayan Isha’i sannan Innarsu ta ce, “Maza ki zo Salma ki wuce dare yana yi.” Ta ce, “To
Innarmu, bari in zo in je.”
A bakin titi tana jiran mota, wata ma’aikaciyar jinya ta fito itama tana jiran mota. Salma ta dube
ta cikin faduwar gaba, don tana zaton matar dazu ce da ta yi mata cin mutunci.
Ta saci kallon matar duk da akwai duhu ta gane ba fuskar waccan ba ce. Dan Adaidaita ya zo
wucewa, tare suka hada baki gurin fadin. “Tudun Wada.”
Ya tsaya ya dauke su, ma’aikaciyar ta ce, “Ashe unguwa daya za mu?” Salma ta ce, “Eh, nan za
ni.” Ta sake cewa, “Kin zo duba mara lafiya ne?”
Salma ta ce, “Eh, Babana aka kwantar.”
Ma’aikaciyar ta ce, “Allah Ya ba shi lafiya.”
Salma ta ce, “Amin.” A zuciyarta ta ce, ‘Ashe dai
ba duka Nurses din nan ba ne suke da wulakanci, da ko har na tsane su.” Alhaji Isa Shatima
yana zaune a falonsa da
misalin karfe tara da rabi, labaran kasa suke kallo
tare da matarsa Hajiya Halima.
Dukkansu Tea suke sha wanda suka maida shi al’adarsu duk dare Daidai wannan lokacin ya
kalli wani daurin auran da aka gama nunawa na ‘yar. wani Minister daga cikin Ministoci.

Ya ce, “Au! Hajiya Halima har na tuna.” Ta ce, “Ka tuna me?” Ya ce, “Da na je duba Hajiya yau
da safe take fada min wata magana da na kasa ce mata komai.” Ta maido da hankalinta kanshi
sosai. “Meta ce?” Ya ce, “Shatima wai mata uku zai aura…”
Kofin hannunta ya kusan faduwa, sannan ta kware da ruwan zafin da ta kurba. Dan tari ta shiga
yi har ta yi zaton asmarta ce zata tashi, sai sannu Alhaji ya ke yi mata.
Kusan minti biyar sannan ta dawo hayyacinta. Idanunta jajir ta ce, “Amma dai wasa ya ke yi
ko?” Alhajin ya ce, “Babu alamun wasa a fuskar Hajiya lokacin da take yin maganar.”
Hajiya ta ce, “Hmm! Wannan hira ce ya ke yi. Ban da Shatima ina zai kai mata uku?” Ya ce, “Na
fadi hakan sai Hajiya ta min gorin da na gwammace ban yi magana ba sannan ta saki zancen
alamun an wuce gurin.
Hajiya Halima tayi shiru tana tunani. Badi’a ta shigo falon zata dauki takardarta wadda tayi
home work da rana. Hajiyar ta ce, “Badi’a zo nan, kira min Yayanku a samansa.
Kammala aikinsa ke da wuya ya rufe Laptop din yana hamma, ya sani ba bacci ba ne yunwa ce
ke damunsa, don bai ci komai da rana ba.Ya ji an kwankwasa kofa. Ya ce, “Shigo.” Tayi sallama
ya amsa, ta ce “Hajiya tana kiranka Yaya.” Ya ce, “To ina zuwa Badi’atu.”
Gabansu ya zauna ya gaishe su, sannan ya ce, “Gani Hajiya.” Ta gyara zama ta hanyar dora
kafarta daya a kan daya, duk lokacin da tayi hakan ya san umarni zata ba da na dole, don haka
sai ya sake nutsuwa don jin abin da zata zo da shi.
Koda yake tuni ya soma hasashen abin da zata yi magana a kai, zancen auransu da Nafisa…
Ta katse tunanin shi da cewa, “Yanzun Mahaifinku ya ke bani labarin wai za ka auri mata uku
rana daya?”
Ya sunkuyar da kai cikin mamakin har zancen
ya riske su da sauri haka! Yana tunanin lallai da
gaggawa lamuran za su ke zuwa masa. Ta ce. “Kayi shiru Shatima?” Ya sake sunkuyar da kai.
Ya ce, “Haka ne Hajiya.” Ta ce, “Amma ka fita a tunaninka ko? Ya ya za ka yi da mata uku rana
daya? Yaron ka da kai Shatima za ka dora ma kanka matsalar iyali da yawa furfura ta fito maka
ko? To ka sani ban amince ba sam-sam!” ya dan gyara zama. “Hajiya duk al’amarin ya zo ne ba da shirina ba, sai da shirin Ubangiji.
Kuma Hajiya shekaruna talatin da shida, ai ko na girmi yaro.Sannan addinina bai hana ni ba,
Allah a cikin Alkur’ani mai tsarki ya fada mana cewa, mu auri mata biyu, ko uku, ko hudu. In ba
za mu iya adalci ba sai mu auri daya. To ni kuma ina da tabbacin zan iya adalci, don ina alfahari da irin tarbiyyar da ki ka bani, adalcin
da ki ka tsaya a kai ki ke yi ma kowa da shi muka dogara.
Kuma shi ni ke kwatantawa a ko’ina, da shi
kuma zan zauna da mata ko nawa ne. Ina son ki sa albarka a cikin wannan auran, albarkarki ita
ce ginshiki Hajiya.” Ta ce, “Ai kai Shatima ko dan siyasa ya fi ka iya zance kuwa? Ni dai kaje
kayi tunani a kai, rike
mace ko guda daya ce sai jan namiji. Amma kai ka
ce rana daya guda uku!” Ya ce, “Hajiya ki sa albarka.” Ta ce, “Yanzu dai ba zan saka ba, in kana
son in saka sai dai ka duba a cikin ukun ka dauki guda daya, ka zaɓa in ma ba Nafisar ba ce dai
wadda kafi so.
Don ka san an ce so daya ne tak! Kuma mace daya ka ke wa a cikin ukun, don haka sai ka cire
ta.”

Ya kalli Mahaifin nashi wanda bai ce kala ba tun da suka soma magana. Ya ce, “Alhaji ba ka ce
komai ba?” Ya ce, “Ba ni da ta cewa Shatima, duk abin da yafi alkhairi Allah Ya zaba, tunda ka
samu daurin gindin Tsohuwa a ta gefena ka kai makura.
Shatima ya yi murmushin nasara a ta wannan gefen. Hajiyar ta ce, “Ka je kayi tunani nan da
jibi.” Shatima ya mike cikin rangaji tare da fadin “Badi atu ta kawo min abinci Hajiya.”

**
Tunda Kaka taji sallama tare da kamshin kalolin abinci ta tabbatar cewa Hajiya Halima ta diro
gidan, domin wannan ita ce shaidar farko da take fara alamta mata cewa Surukar arziki ta shigo
gidan.
Ta fito daga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0