Showing 15001 words to 18000 words out of 37771 words
Chapter 6 - Rana Daya Book 1 Hausa Novels By Halima Abdullahi Mashi
“To zan daina cewa, kuma Allah Yaya duk nafi sonka.� Ya ce, “Gashi kin sake fada bayan
mun yi da ke sunan da zan kira ki da shi shi ne za ki kira ni.
Cikin shagwaɓa ta ce “To zan ce.� Ya ce, “To ce ina ji.� Tayi ‘yar dariyar kissa. Ta ce “Sweety.�
Ya ce, “Kai! Kin iya fada, dan kara in ji.� Ta sake fadi. Ya ce, “To na kashe Yaya din nan ko
matata?�
Ta cc, “Eh.� Ya ce, “Don Allah ki tashi daga ciwon nan kar ki zo ranar biki ba ki yi kyau ba. Ni fa
kin san bana son mace ramammiya.Ta ce, “To ai ba ka kirana ne kuma baka zuwa.� Ya ce
“Wannan ba shi ne yake nuna bana sonki ba, aikina yana da yawa, kullum fa Kaduna ni ke
zuwa ina dawowa, ga aiki a gida, ga ginin ku da za ku zauna. Abubuwa da yawa.� “To amma za ka ke kirana?�
“Duk lokacin da na dan samu sarari kamar haka zan kira ki, kuma zan zo yanzun dai kin
warke?� Ya tambayeta cikin nuna kulawa.
Ta ce, “Na warke.� Ya ce, “Yauwa sweety, duk lokacin da ki ka tuno ni kiji a ranki cewa ina tare
da ke dari-bisa-dari.�
Haka ya yi ta nuna mata sonsa har sai da ya
tabbatar ta gamsu, ta kuma yarda yana yinta sosai.
Tsawon awa daya kafin yayi sallama da ita.
Washegari misalin karfe takwas ya dawo daga Masallaci ya shiga motarsa ya zauna don ya yi
waya da Aliya.
Daidai lokacin da kiran ya shigo wayarta an dace da zata duba kudinta, ta gama saka lambobi
ta danna kenan kiran ya shigo, don haka ko ringing bata yi ba ya zama ta daga. Duk da taga
sunan Shatimanta ne bata so haka
ba, sai ka ce tana zaman jiranshi. Amma sai ta sa a kunne cikin kissa tayi sallama ya amsa, sai
ta ce, “Laa! Wai kai dinne da gaske?� “Kina zaman jirana ne?� Ya tambayeta.
“Ina yin mamaki ne a zuciyata ne naji cewa ina danna gurin amsa kira, nasa a kunne zan ji
muryarka, lallai sona da kai wani abu ne na musamman.�
Ya ce, “Nasan haka, ba ki bukatar sai kin tuna min shekaru uku kina jiran soyayya, ba abin
mamaki ba ne don kin ji a jikinki cewa kirana zai shigo.�
Ta ce, “To mu gaisa in ji lafiyarka.� Ya ce, “Ina cikin koshin lafiya, sai so da kaunarki da ke kara
samun mazauni a zuciyata.�
Ta lumshe ido. “Ni ko ina nan ina tunanin ya ya ka kare da ‘yar uwata, ko ta amince zata zauna,
da mu din?� Ya ce, “Ai tunda ki ka bani wannan shawarar naje na gwada. Tayi sosai, na kara
miki lambar yabo a cikin kaunarmu.� Ta ce, “Naji dadin haka.� Ya ce, “Ke kamar kya yin kishina,
wasu kuma suna cewa kishi yana daga cikin so, haka ne?�
Ta ce, “Ai kishin jahilci shi ke så wa ayi ta tashin hankali my love. Mu da muke Musulmi, gidan
Manzon tsira (S.A.W) shi ne fitilarmu, kalar kishin matanshi zamu yi, kishin faranta maka tare da
ba ka shawarwari nagari.
Kuma don ina kishinka ba zan kauda kai ga abin da ka ke so ba, zan danne in so abin da ka ke
so tsakani da Allah. Ina jin sauran matanka dani zamu zauna tamkar ‘yan’uwa.�
Ya ji dadin kalamanta, har yace�Ke ta daban ce a mata my love, haka a zuciyata.� Taji dadi
matuka. Suka ci gaba da hira har ta ke tambayar shi yana ganin auransu zai dauki tsawon wane
lokaci?
Ya ce, “Me yasa take tambaya?� Ta ce, “Ka san an ce me kwarmin ido da wuri yake soma
kuka.� Ya ce, “Haka ne. Ni dai a tsarina sai na gama muku wurin zama, sannan in zo kan batun
biki, don bana son a sa min rana mai tsawo. Komai-da-komai dai bana son ya wuce na da wata
tara.� Ta ce, “Allah Ya nuna mana lokacin. To ammal kafin lokacin za a sa manya a ciki ko?� Ya ce,
“Eh mana, da zarar sun gama bincike su za su zo ga manyanku, itama awa guda suka kwashe
kafin suka yi sallama,
Ita ko Amna yafi jin dadin yin waya da ita in yaje kwanciya, Don haka sai da ya gama komai na
al’adarshi kafin ya kwanta sannan ya kira ta.Yau ya ci sa’a a kiran farko ta daga, bai san ma ta
dagan ba sai da ya ji ‘yar muryarta ta ce, “Hello honey.� Ya ce “My honey kina lafiya?� Ta ce,
“Kamar yanda ka ke.� Suka yi hirarsu irin ta so da kauna, bata kawo mishi batun sauran ‘yan matan ba, shima bai
dauko mata ba. Tsawon awa daya yana yada manufarshi kafin suka yi bankwana.
Bayan duk bincike sai a ka tura neman aure, babu inda aka samu matsala sai gidan su Amna,
in da suka nuna a dan jira in sun gama bincike za su neme su. Bayan sati uku sannan suka ce
manyan su dawo.
Alhaji Musa Baban Nafisa shi ne zai amso auran Amna, ya zama ko ina an ba shi. – Gininshi
kuma ya kammala, amma fa asusun ya yi kat! Har sai da yayi aro gurin Babanshi. shi
Gida dai ba abin da yake jira sai masu gidan. Gurin tsara sadaki aka samu bambanci. Baban.
shi shi ne zai ba da Nafisa, ya murza gashin baki ya ce dubu dari ne sadakin ‘yarsa. Baban
Nafisa mai amsar ma Shatima aure ya ce “Haba Yaya, a dai rangwanta.�
Alhaji ya ce, “In suna so su bayar, ‘yarshi tana
da ilimi. Haka Baban Nafisa yayi masa transfer ta
dubu dari a nan take, abin gwanin sha’awa.Su ko gidan su Aliya hamsin suka saka mata, sai
kudin gaisuwa ashirin, saba’in kenan. Amna kuwa dukiyar aure dari, sadaki kuma hamsin. Duk
haka aka ba da, sannan aka tsaida lokacin aure wata sha biyu ishirin ga shi a lissafi sauran
wata hudu kenan. A son Shatima kar a kai wannan lokacin amma an duba lokacin da za’a samu hutu mai tsawo
kowane bangare suna cikin kasa kuma suna cikin jihar.
Kamar yanda ya tsara a wata daya yake kai musu ziyara, ran Juma’a yaje gurin Nafisa. Sati
yaje gurin Aliya Lahadi kuma yaje gurin Amna. Haka duk karshen sati yake tura musu kati na
dubu dai-dai. Haka kuma yake kiransu sau biyu a kwana goma,
Alhaji Musa Baban Nafisa shi ne ya biya
dukkannin sadakin. Anty Saude kanwar Baban Shatima ita ce ta dauki nauyin siyan takalman
da za’a zuba musu duka. Don haka ya amso lambobin takalmansu ya kai
mata, dama oder take yi.
Aliya ta kan tura masa da sakon Juma’a bata mantawa, Nafisa na tura masa da sakon barka da
safiya lokaci zuwa lokaci_____
*í ¼í¿šï¸�RANA DAYA í ¼í¿šï¸�*
CHAPTER 8
*BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*
*Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan
account numberí ½í±‡í ¼í¿»*
```ACT<<0700549935
Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925```
*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA
DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can
samaí ½í±†í ¼í¿»í ½í±†í ¼í¿»ko ku turo katin Mtn ta wannan number 09068032427*
*08146017245 hohoho wani Kaya Sai amale shin kunsan kayatattun magungunan Mata na
maman haidar*
*Kayan maman haidar basuda matsala domin traditional medicine ne Kuma anahadasu da
ingantattun itatuwa masu karfi da Basu da illah*
í ¼í½€í ¼í½€í ¼í½€í ¼í½€í ¼í½€í ¼í½€í ¼í½€
*1 Gumbar kankana da ayu* í ¼í½€í ¼í½€3 *Gumbar Madara da kwakwa*í ¼í½€í ¼í½€
4 *Kaza mekwai* í ¼í½€í ¼í½€
5 *Zabo me zuma*í ¼í½€í ¼í½€
6 *Kaza me alluraií ¼í½€í ¼í½€ sahihiyar mallaka ba boka ba malam*í ¼í½€í ¼í½€
7 *Kwallin idonka inadona*í ¼í½€í ¼í½€í ¼í½€
8 *Tauwadar mata*í ¼í½€í ¼í½€í ¼í½€
9 *ketar larabawa magani me kankarowa mace kima da daraja*
10 *Maganin sanyi me fatattakarsa duk kuwa nacinsa Koda bakya haihuwa indai matsalar
sanyice gwada wnnn*
11 *Maganin nono. Sahihi*
12 *Maganin hips and bobbs*
13 *hodar. Ni I'ma koramar mata*
14 *nakasan Mara babban sirri*
15 *kafi jijjibi*
16 *daga Sha Sai wanka kasaitacce magani*
17 *Dan kwankwalati namata da mazajensu Kevin Mata*
18 *matsin kinfi budurwa dubu ko haihuwa nawa kikai Babu magana*
í ¼í½€í ¼í½€í ¼í½€í ¼í½€í ¼í½€í ¼í½€í ¼í½€í ¼í½€í ¼í½€
*Maman haidar Bata tsaya anan ba*
*Tana Saida hijabai dayadikan su akan darashin sari yadika dila dilahijaban. Yan gayu sannan*
*takawomuku hadaddan sabulun gyaran jiki da hadin dilka Mesa sheki da laushin fata gaman
kitso Wanda laraba ke amfani dashi inkin gwada saikin dawo kudai kunemeni awannan
number* 08146017245
í ¼í½€í ¼í½€í ¼í½€í ¼í½€í ¼í½€
Mun tsaya
Alhaji Musa Baban Nafisa shi ne ya biya
dukkannin sadakin. Anty Saude kanwar Baban Shatima ita ce ta dauki nauyin siyan takalman
da za’a zuba musu duka. Don haka ya amso lambobin takalmansu ya kai
mata, dama oder take yi.
Aliya ta kan tura masa da sakon Juma’a bata mantawa, Nafisa na tura masa da sakon barka da
safiya lokaci zuwa lokaci.
Amna kuwa ba ta mantawa da tura masa sakon murna da shiga sabon wata a duk lokacin da
aka shiga. Tsarin kowaccensu ya birge shi
Shatima yana da kaifin basira, da hikimar zama
da jama’a, don haka yake ganin kamar cin tuwo ne
ko shan ruwa zama cikin mata hudu ma bare uku. Shagali ake shiryawa a kowane bangare
musamman gidan su Amna wadda ta kasance ita ce mace ta farko da za’a soma aurar wa a
gurin Mahaifinta.
Itama Nafisa ana ta shiri don ita ce ‘yar fari gurin Babanta, ga kuma dangi kowa na cin buri,
Aliya kuwa suma suna shiri daidai karfinsu, bata shagali suke yi ba su, suna ta kayan daki ne a
samu a yi mata gado seti biyu, ga kuma gara tunda sun san yana da hali da kyar in ba daki biyu
za’a kai ta ba. Sannan gefen kayan gyara jikin Amare ko ina suna ta yin daidai karfinsu. Alhaji Isa Baban Shatima cewa ya yi ba zai ba Shatima komai ba ‘yarshi zai wa kayan Gado da
kayan gara. Ya fadi haka ne lokacin da Shatima ya samu Babanshi da Hajiyar su a daki Baban
nashi yana tambayar wace gudunmawa zai ba shi?
Shatima ya ce, “Alhaji nima a dan duba min, Allah asusuna babu kudin kirki, gashi ko akwatuna
ban siya ba.�
Hajiya ta ce, “Amma jiya ka ce min Alhaji Murtala ya turo maka da dubu dari biyu ko? Yanzun
ma nike fadawa Babanku.�
Shatima ya ce, “To duk kowace ta min magana ashobe da za su fitar, Amna ce kawai bata min
ba, itama nasan zata yi, shi ne zan raba musu wannan dari biyun.�
Alhaji ya ce, “Ai kai dan dangi ne za ka samu gudunmawa, Murtala da duk cikin ‘ya’yan
Mahaifinmu yafi kowa mako, amma shi ya fara baka gudunmawa har dari biyu.�
Hajiya ta ce, “Ba dole kowa ya motsa ba tunda Babansu zai yi aure har mata uku rana daya.
Shatima ya ce, “Alhaji ka min daà wani abu koda canza min mota ne.�
Ya ce, “Au! Ka ma tuna min, Alhaji Nadabo ya
ce kaje gidan motocinsa ka zabi wadda ka ke so.�Murna ta cika Shatima. Ya ce, “Amma gaskiya
Baba Alhaji Nadabo ya yi min komai.� Hajiya ta ce, “Kuma fa ya ce duk ruwan da za a sha a
biki na gora aje kamfaninsa na ruwa a debo. Allah ya saka mishi da alkhairi.� Suka ce
“Ameen.�Shatima ya ce, “Allah Yasa mu ma abotarmu da Munir tayi kamar taku, shima yana da
irin halin Babanshi.� Ya cc, “To ke Hajiya har yau ba ki fadi naki ba.�
Ta ce, “Kai uban masu kudi da gata ka ke, nan da wata mai kamawa asusunka sai yayi kamar
zai fashe. Don haka ni yanzun ba zan yi alkawarin komai ba sai nan gaba tukunna.�
Ya mike “Shi kenan, bari in je in shirya yau Kano zani gurin Amna.� Hajiya ta ce, “Ka fa yi ma
Badi’atu alkawarin zuwa da ita tun shekaran jiya take min zancen.� Ya ce “To ta shirya har da
Munnir zamu je ni na ma manta da mun yi haka da ita.�
Karfe biyu sun isa birnin Kano sun samu tarba sosai musamman Badi’atu wadda tayi kyau cikin
riga da wando da mayafinsu ‘yan Dubai.
Amna tayi murna da zuwan Badi’atu, ta hada ta da kanwarta Sumy don za su yi sa’annin juna.
Tunda suka kebe ta shagulgulan da za su shirya. soma mishi zancen
Ta ce “Mu fa tun ranar Laraba zamu fara biki.� Ta tashi ta dauko mishi katin wanda aka tsara shi
da ruwan zaiba, jikinshi kuma ruwan jibi. Karamine kwarai katin sai shegen kyau kamar ka lika a
jiki kayi ado.
Ya karanta a ranshi ya ce tab! In ko shi zai ba da kudin shagalin nan za a samu matsala, don ba
shi da su, amma dai bari ya jira ya ji abin da zata ce. Ta dube shi.
“Katin yayi kyau kuwa?� Ya ce, “Sosai ma.� Ta ce, “Kamar guda nawa zan baka?� Ya ce “Tun da
yanzu saura kusan wata biyu har da kwanaki, ki bari sai abin ya kara matsowa, kar in zuba a
wani guri in manta.Kin san kaina kullum kara daukan hayaki yake yi, mata uku fa!�
Ta taba baki, “Ni ina mantawa da cewa bani daya ba ce, ko su Mom dina ba su fada ma kowa
ba sune kawai suka sani. Zan ajiye maka amma za ka zo min dai duka ko?�
Ya ce Zan dai zo amma ba duka ba, kuma mu da abokanmu zamu shirya Dinner wadda za ku
zo ku duka amma sai an kai ku.� Ta ce, “In lokacin mutane na sun watse zan je mana, amma in
suna nan sai dai kayi hakuri don ba su sani ba.�
To babu matsala, Allah Ya kai mu.� Munnir ma da ya ga katin sai ya ce, “Ni dai bari in rike
wannan yayi min kyau.�Sumayya da suka je dakin su da Badi’atu, ta nuna mata ashobensu kala
shida. Duk masu tsada ne kowane shagali da kalar da za a sa.
Badi’atu ta ce, “Lallai ku kam har kun fitar, mu dai sai cikin watan nan da zamu shiga sannan za
a
fitar, Kanwar Babanmu ce zata fitar da su.�
Sumayya ta ce “Mutum yaushe har ma an kusan gama bada wa. Yayar Babanmu tayo odar ba
saidawa ake yi ba, har kawayenta duk an basu ne tare da katin biki.�
Badi’atu ta ce “Tab! Duk wannan kuma za a ba mutum daya?� Sumayya ta ce, “Eh mana. Ita
kuwa Amarya kin ga kayan da zata sa da biki? Akwati uku ne aka je Dubai aka dinko su, na biki
ne kawai har ma da irin rigar aure dinnan zata sa.Tare aka siyo da kayan da shima ango zai sa
a ranar da takalmi da komai. Badi’atu ta saki baki,
har ta soma tunani tsarata kawai Summy ke yi
Har suka soma shirin tafiya Shatima bai ji tayi masa zancen kudin komai ba, kamar yanda Aliya
da Nafisa suka mishi da ya ziyarce su a ranakun Juma’a da Asabar.
Kowace ta tambayi kudin ashobe, da kuma sauran shagulgulan tata zata yi da kawayenta Ya
kalli Amna, “Ke ba za ki yi ashobe ba ne?�Ta lumishe ido, “Ai tuni sun cire abinsu, ni ai ba zan
sa ba, sun kusan gama raba shi ma.� Ya ce, “To yanzun me ki ke bukata daga gare ni don
shagali ko wani abu? Gara in sani tunda wuri kin san abin da yawa.� Ta ce “Ban gane ba.� Ya ce, “Kudin siyan ashobe da shagalin da zaku yi.� Ta girgiza kai tare da
tabe baki.
“Babu fa. Ni ban sani ba ko ana bada wani kudi
na shagali ba.� Ya ce, “Shi kenan, in dai da wani
abu sai muyi magana ko?� ta ce “To, babu matsala.� Ta ce, “Bari in je in kira Badi’atu din ko.� Ta
samu Mom dinsu ta hada ma Badi’atu sha tara ta arziki, irin su kayan kwalliya, da na ci, kayan
zaki, sai ko ashoben su kala shidan nan da
na kai, sannan Amna ta ba da turare a kai ma
Hajiya Hajiya kuwa tayi murma har taji cewa Amna ta kwanta mata a zuciya, a fili ta ce, “Harkar
arziki da me arziki ake yin shi.� Badi’atu kuwa sai labari a ke baiwa Hajiya na abubuwan da ta
gano, da kuma wanda taji. Hajiya ta ce, “Ai familyn Baita Nasiri sun fi da haka, masu kudi ne na
wuce tunani.�Kamar yanda iyayen Shatima suka ce, hakan ce ta kasance. Ana shiga watan sha daya, iyayensa maza da mata wadanda suke uba daya da
wadanda suke da dangantaka ta dan nesa. Sai kira suke Shatima ya turo da lambarshi ta
account.
Bayan haka suna kaiwa Kaka tata. Shatima ranar yaje gurin Kaka yana alfahari da sunan da
suka sa masa. Ya ce “Kaka ‘ya’yanki sun yi mini komai, sun cika asusuna da kudi gaskiya na
yarda da kalmar Hajiya ni ne dan masu kudi, kuma uban masu kudi.�
Kaka tayi dariya, “Tun daga haihuwarka goshinka kazo, uwarka bata baka labari ba? Ran da
aka haife ka Kakanka ya samu Sarauta, kuma ranar ne Sarkin Zazzau na wancan lokacin ya bai
wa Kakan naka kujerun Makka har uku.
Dama shi da matarshi ta fari sun je, don hakan sai ya bar mana muka je mu uku.�
Shatima ya yi dariya, “Ki ce da arzikina aka haife ni?� Ta ce, “Sha Allahu…� wayarshi tayi kira,
da ya duba Munnir ne. Ya ce, “Aboki ya ya ne?� Ya ce, “Na zo gida ba ka nan, gani tare da
Telan da muka yi magana da kai.� Ya ce, “To ku jira ni gani nan gidan Kaka nazo yanzu zan
fito.�Ta ce, “In kuma kuna sauri ka shiga ciki, Badi’atu ta dauko maka kaya a cikin Ghana most
go a kusa da