Showing 12001 words to 15000 words out of 37771 words

Chapter 5 - Rana Daya Book 1 Hausa Novels By Halima Abdullahi Mashi

yaje gurin Kaka a can zai ji gaskiyar magana, to wai bai je ba ne?� Mama ta kalli yarta
cikin tausayi, “Bari
Babanku ya dawo sai kuje gurin Kaka tare don kiji da kunnenki.�
Ta ce, “Amma dai zance mafi inganci shi ne mu ukun kenan?� Ta ce, “A’a, ni na fada miki ban
san komai ba sam-sam!�
Ta ce, “Ai ko yau da dare zan je tare da Baba
din.� Ya zuba ido yana kallon gurin zaman Nafisa, “Ina me wannan kujerar?� Mama ta ce, “Tana
dakinta tana kunci.� Ya
tsura ma Mama ido.Wane kunci kuma?�
Ta ce, “Zancan auransu da Shatima mana, bad na fada maka tace ya fada mata su uku ne rana
daya ba, ka kira Alhaji ya ce maka kaje gurin Kaka ka ji cikakken zance.�
Ya aje cokalin hannunshi ya kurbi ruwa sannan ya mike. Dakin Nafisa ya nufa saboda duk cikin
‘ya’yansa babu kamar ta a zuciyarshi.
Kwance ya same ta tana wasa da rigar wayarta, amma ga dukkan alamu tunaninta ba ya tare
da rigar wayar, hankalinta yana can wani gurin.Ya tsaya a gabanta, sannan ya maida
hannuwansa baya. Ya ce, “Nafisa!� Ta dago ta dube shi. Ya ce, “Me yasa ba ki zo cin abinci
ba?� Ta ce, “Na koshi Babanmu.� Ya ce, “Ina son ki fada min damuwarki.� Ta dago ta kalle shi.

“Babanmu ina son ka binciko min gaske ne Yaya Shatima mu uku zai aura rana daya?� Ya kalli
‘yarshi cikin tausayi, duk da kunya irin ta Nafisa amma sai da ta iya yi masa wannan magana.
Ya ce, “Tashi muje gidan Hajiyar yanzun.
Cikin sauri ta saka hijabinta.
Kaka ta idar da sallar Isha’i tana jan carbi kafin tayi shafa’i da wutiri. Sallamar su ta jiyo, duk da
bata san ko wane ne ba, ta raya a ranta ba za ta fito ba sai dai in na gida ne su shigo cikin
dakin nata.
Maryama ta shigo ta ce, “Kaka ga Kawu Alhaji nan.� Ta ce, “Kamar murya biyu naji.� Ta ce, “Eh,
shi da Nafisa ne.� Ta ce, “Su shigo ciki.�
Gabanta suka zauna suka gaisheta. Ta kalli Nafisa, “Dama kina nan?� Ta sunkuyar da kai. Kaka
ta ci gaba da yuwa Nafisa fadan rashin son shiga jama’a, da rashin zumunci. Hakuri tayi ta
baiwa Kaka.Alhaji Musa ya ce, “Hajiya kiyi hakuri, wannan halinta ne rashin son shiga mutane,
kullum tana gida in dai ba Makaranta taje ba.� Kaka ta ce “Ita dai ta sani, ga shi nan za ki yi aure da kishiyoyi, zama ne za ku yi na wanda ya
iya allonsa ya wanke ya sha…�
Nafisa ta dafa kirji. “Dama gaske ne Kaka ba ni kadai Yaya Shatima zai aura ba?� Kaka ta ce,
“Au! Dama bai fada miki ba?�
Nafisa ta soma kuka. Alhaji ya ce, “Hajiya bai kamata a bar Shatima yana dan karamin shi ya
auri mace sama da daya ba, zai hada ma kanshi damuwar da zata sa shi yayi da na sani.�
Kaka ta ce, “Allah Ya raba shi da aikata da na sani, sunna fa zai yi, ibada ka ke fada min da na
sani? Yanzun dai a takaice ka taso ‘yarka ne ka fada min cewa ya fasa auran ‘ya’yan wasu ya
auri ‘yarka?�
Ya sunkuyar da kai, sannan ya shiga ba Hajiya hakuri don ba a son ɓacin ranta saboda tana da
hawan jini. Duk da haka Hajiya ba ta yi shiru ba sai da tayi masu tatas!
Ta ce, “Ku kun kasa zama jarumai, kun amince ku mutu da mata dai-dai shi yasa kowanne zai
zo yana fadin bai kamata ba, amma ba wanda ya kawo min aya ko hadisi da ta haramta masa
auran.Ke kuma ko da dayar zai zaba ai ba ki ciki, saboda akwai yarinya Aliya ‘yar makotanmu
ce, sama da shekaru uku tana jiransa. Don haka kin ga kema cikin ‘yan kari ki ke.Nafisa ta mike
fuuu! Cikin kuka ta ce, “Kaka
sai anjima.� Alhaji ya ce, “Bari mu tafi Hajiya.�Ta ce, “Ku gaida gida.�A mota yana ta lallashinta.
Ta ce, “Baba ni dai kawai na fasa, na hakura.� Ya ce, “A ‘a Nafisa, kar ki ce haka, ki bari dai
muje gida.
Iyayen sun tasa ta a dakin Maman suna lallashinta, kan cewa tayi hakuri kar ta ce ta fasa,
domin Kaka za ta yi fushi.
“Kin san dai fushinta zai janyo babbar matsala.� Mama ta ce, “Ke da yake dan uwanki, Hajiyarsu
ke tafi so, kuma kema kin san dole zai fi sonki saboda dangantaka.�
Haka dai suka yi ta lallashinta har taje ta kwanta, amma ba don ta gamsu da maganar
mahaifinta ba.
Tun da ya isa kofar gidan gabanshi ya fadi, duk yanda yake zaton kudin su Amna daga ka kalli
gidan kasan ya wüce yanda ya zata.
Dama tun da ya taso daga Zariya waya suke yi har ya iso tangamemiyar kofar gidan tasu mai
kama da kofar gari.
Maigadi ya bude masa ya shiga. ‘Yan matasan samari ne suka tare shi. Ya fito cikin shiga ta

alfarma, shadda ce gizna mai kalar kwai. Yayi matukar kyau da bakar hular da ya dora.Su ne
suka jagorance shi zuwa wani
kasaitaccen falo. Duk da suna da kudi ya tabbata
su Amna sun fi su nesa ba kusa ba.
Amna ta fito cikin doguwar riga English wears, sai dan mayafi karami da ta yafa. Tayi kyau
matuka. ‘Yan gidan suna ta zuwa suna gaishe shi (kannenta). Dama ta fada masa ita ce mace
babba a gidan,
sai wanta namiji babba yana zaune a Ingila da
matarshi da yara biyu. Amaryar Babansu ta zo
suka gaisa, itama yarinya ce danta daya.
Tayi masa jagora zuwa gurin Mahaifiyarta ya gaishe ta. An shirya mishi abubuwan ci da sha na
zamani. Sannan sun yi hira sosai irin ta masoya, amma ya matsu ya fada mata cewa su uku
ne.Ita ma a nata ran ta matsu ta san abin da zai zo mata da shi, wanda ya ce ta yi masa addu’a
a kai.Ya kalleta da niyar maganar, sai ta riga shi da cewa, “Ban ji kayi maganar da ka sani in yi
maka addu’a ba?�
Ya cire hula ya ajiye, yasa hankici ya share zufar da ta ratso goshinsa a nan take. Sannan ya
ce, “Ki min alkawari abin da zan fada ba zai raba mu ba?�
Ta lumshe ido, muryarta can kasa. Ta ce, “Nayi
maka alkawari ba zan barka ba.� Ya ce, “Na taba
baki labarin Aliya budurwar da na fara yi nace
ba za ta jira ni ba ko?�
Ta daga kai tare da fadin “Na tuna. Ya ce, “To ashe tana nan tana jirana.� Ya tsura mata ido
yaga yanda zata dauki maganar. Tabbas fuskarta ta canza, sannan tayi shiru ta
kasa magana. Ya ce, “Kin yi shiru honey.� Ta
dube shi “Me zan ce maka? Na fahimci ka sani in yi addu’a a kan cewa zaka min kishiya, haka
ne?� Ya ce, “Kishiyoyi za ki ce dai, domin gida sun cire min Nafisa baya-bayan nan. Yanzun dai
ku uku ne za a yi rana daya.�
Ta tura kanta cikin cinyarta. Ya tausasa murya.�Kar ki damu Amna, wallahi ina matukar sonki.�
Ta dago ta dube shi.�Nafisar ba ta dame ni ba amma na tuna yanda kayi ta bani labarin Aliya da
soyayyarku. Nasan kafi sonta.�
Ya ce, “Ni nafi sonki, saboda kin fi sona.� Haka ya yi ta lallabata har ta hakura, sannan ta ce ya
yi shiru yanzun tukunna kada Mom suji ba za Su yarda ba. Ya ce, “Shi kenan na gode da hadin
kanki.�
Da zai tafi ya ba kannenta dubu goma sabbin ‘yan dari biyar-biyar, ya ce su sha alawa babu
yawa. Ita kuma ta kawo mishi wasu ledoji guda biyu ta ce ga tsarabarsa, suka rako shi har
mota, ta zuba ledojin a kujerar baya.
Ya nufi dakin Hajiyar shi don ya gaisheta tare da yi mata sallama, ya kuma kwashi albarkar
safiya ya nufi Kaduna gurin aiki.
Ba ta falon ba ta dakin, don haka ya nufi falon Alhajin su. Ya same su har Badi’atu suna karin
kumallo ita da kayan Makaranta a jikinta. Ya tsuguna ya gaida su. Alhajin yasa mishi
albarka tare da masa fatan ya dawo lafiya. Ya kalli
Hajiya ya ce, “Hajiya zan je aiki.�
Ta ce, “Kafin nan wai kai ‘yammatan naka wadanne iri ne? ni dai ‘yata Nafisa na sani, kasan dai

sai mun bincika asali.�Ya ce, “Hajiya Aliya ce wadda dai ki ka sani asalin budurwata, ko Kaka
dai za ta ba ki labarin asalinsu.
Ta ce, “To dayar fa?� Ya ce, “Amna ‘yar family din Alhaji Baita Nasidi ce.� Ga mamakinsa sai
yaga Hajiyarsa ta dago daga kashingidar da tayi. Ta ce, “Wane Alhaji Baitan? Na Kano babban
dan kasuwar nan?� Ya ce, “Eh.�
Ta ce, ‘Yar kareren dangi ce ko?� Ya ce, “Hajiya ba karere ba ce, jikarsa ce, shi ya haifi Babanta
Alhaji Ibrahim Baita Nasidi.�
Tayi dan murmushi, “Lallai ka tabo babban gida.� Ya kalli Badi ‘atu “Je dakina a kan gado za ki
ga wasu ledoji guda biyu ki kawo min, yi sauri. Ya kai karshen maganar yana kallon agogon
hannunshi gudun yin latti (makara).
Ta ce, “Yaya bari in bi ka ka sauke ni.� Ya ce, “A’a ina Dircbanki? Ta tafi tana cewa, “Wai sai ya
kai Yaya Mustapha wani guri sannan zai kai ni. Bai ce komai ba ta fita zuwa dakinsa.
Ta dawo dauke da ledojin. Ya ce, “Ba Hajiya nata tsarabar da Amna tayo min daga Umra.�
Badi’atu ta soma zazzage kayan iyayen suna kallo. Ledar farko riguna ne masu kyau, dogon
hannu da gajeren hannu. Sai gajerun wanduna irin na ciki guda biyu._____
*🏚�RANA DAYA🏚�*

CHAPTER 7

*BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*

*Wannan littafin na kudi ne akan farashin 300,idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan
account number👇🏻*

```ACT<<0700549935
Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925```

*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 Ga masu son Audio na littafin RANA
DAYA shima muna dashi cmplt ku turo kudin ku ta account number din da muka bada can
sama👆🏻👆🏻ko ku turo katin Mtn ta wannan number 09068032427*



*08146017245 hohoho wani Kaya Sai amale shin kunsan kayatattun magungunan Mata na
maman haidar*
*Kayan maman haidar basuda matsala domin traditional medicine ne Kuma anahadasu da
ingantattun itatuwa masu karfi da Basu da illah*

🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀

*1 Gumbar kankana da ayu* 🍀🍀3 *Gumbar Madara da kwakwa*🍀🍀
4 *Kaza mekwai* 🍀🍀
5 *Zabo me zuma*🍀🍀

6 *Kaza me allurai🍀🍀 sahihiyar mallaka ba boka ba malam*🍀🍀
7 *Kwallin idonka inadona*🍀🍀🍀
8 *Tauwadar mata*🍀🍀🍀
9 *ketar larabawa magani me kankarowa mace kima da daraja*
10 *Maganin sanyi me fatattakarsa duk kuwa nacinsa Koda bakya haihuwa indai matsalar
sanyice gwada wnnn*
11 *Maganin nono. Sahihi*
12 *Maganin hips and bobbs*
13 *hodar. Ni I'ma koramar mata*
14 *nakasan Mara babban sirri*
15 *kafi jijjibi*
16 *daga Sha Sai wanka kasaitacce magani*
17 *Dan kwankwalati namata da mazajensu Kevin Mata*
18 *matsin kinfi budurwa dubu ko haihuwa nawa kikai Babu magana*


🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀
*Maman haidar Bata tsaya anan ba*
*Tana Saida hijabai dayadikan su akan darashin sari yadika dila dilahijaban. Yan gayu sannan*
*takawomuku hadaddan sabulun gyaran jiki da hadin dilka Mesa sheki da laushin fata gaman
kitso Wanda laraba ke amfani dashi inkin gwada saikin dawo kudai kunemeni awannan
number* 08146017245
🍀🍀🍀🍀🍀


Mun tsaya

Ta ce, “Yaya bari in bi ka ka sauke ni.� Ya ce, “A’a ina Dircbanki? Ta tafi tana cewa, “Wai sai ya
kai Yaya Mustapha wani guri sannan zai kai ni. Bai ce komai ba ta fita zuwa dakinsa.
Ta dawo dauke da ledojin. Ya ce, “Ba Hajiya nata tsarabar da Amna tayo min daga Umra.�
Badi’atu ta soma zazzage kayan iyayen suna kallo. Ledar farko riguna ne masu kyau, dogon
hannu da gajeren hannu. Sai gajerun wanduna irin na ciki guda biyu.

Daya ledar takalma ne sawu ciki kala biyu, sai turaruka da agogo mai kyau a kwalinsa. Hajiya ta
fadada fara’arta.
“Lallai abu yayi, masha Allah.� Alhaji ya ce, “An zo gurin, irin wadda ki ke so ko? Ma su kumbar
susa.� Ta cc, “A’a Alhaji, ai mu ma ba a tsiyace muke ba.�
Ya ce, “Amma tunda a ka ambaci Alhaji Baita ki ke washe baki.� Shatima ya ce, “Badi’atu
kwashe ki maida, amma ki bar ma su Hajiya turarukan.�
Alhaji ya ce, “Kwashe masa abinsa kin san dai na maza ne, me za ki yi da shi?�
Ya nufi hanyar fita yana fadin “Sai na dawo.� Hajiyar tana fadin “Allah Ya shi maka albarka, sai
ka dawo. Badi’atu ta nufi saman shi tana fadin “Don Allah Yaya ka jira ni.� Shi dai ya tafi yana
mamakin Hajiyarsa, a nasa sanin Hajiyarsa bata daga cikin mutane masu kwadayi.

Ginin Shatima da ke Rigachikun ya kankama, domin aiki ake yi babu dare babu rana, ko’in ce
ba-ji-ba-gani, Flat ne guda hudu aka yi su suna kallon juna, kowanne yana dauke da manyan
dakuna guda uku, kowanne da bandaki.Sai makeken falo da kicin babba, sai sito da ke manne
da kicin din. Akwai Baranda a gaban kowane gini, sannan ga fili ishasshe wanda zai dauki
sama da mota goma.
A tsarinshi yafi son sai ya kammala gininshi tsaf! Sannan zai tunkaro maganar aure. Yasan jan
aiki ya dauko, komai sai ya yi uku kila ma hudu, don har yanzun yana ji a jikinsa ta hudu tana
tafe.
Ranar wata Asabar suna tsaye a harabar gidan nashi da yake gini, lokacin ana yin rafta ne.
Munnir ya ce, “Gaskiya abokina kana matukar kokari. Dubi yanda aiki ya yi nisa sosai.� Shatima
ya ce, “Ba a magana. Yanzu haka na soma tunanin shiga asusun su Hajiyata da Alhaji.�


Munnir ya ce, “Ai ginin akwai shi da cin kudi. To yanzun kowace tasan da wata kenan?� Ya ce,
“Duk sun sani, yanzu zan tsara ma kaina yanda zan yi hulda da su kafin lokacin auran.�
Munnir ya ce, “Har da wani tsari da zaka yi musu?� Ya ce, “Sosai ma kaga dai zan dinga ziyartar
su ne bayan kowane karshen wata sau daya. Sannan kuma zan ke kiran su sau biyu a cikin
kwana goma.
Zan ke tura musu katin waya na Naira dubu daya a duk sati. In nayi haka ba zan gundure su ba,
suma ba za su gundire ni ba.�Munnir ya ce, “Kamar kiran da kace a waya sau biyu a kwana
goma ya yi kadan Shatima ya ce, “Ba ni da wani aikin kenan sai nasu, kiran ma awa dai-dai ne.�
Ya ce, “To in wata cikin su ta kira ka fa?� Ya ce, “In ina da abin yi ba zan daga ba, in bani da shi
zan daga in ji dalili, in abin mai mahimmanci ne in saurara, in ko shirme ne in ce ina da abin yi.�
Munnir ya ce, “To in wata tayo message fa?� Ya ce, “Zan karanta in na amsawa ne in ba da, in
ko akasin haka ne in share.� Munnir ya yi ‘yar dariya, “Lallai mutumina kana yin abubuwan ka
da tsari.�
Nafisa tana kwance cikin bargo, da zazzabi ta dawo daga Makaranta. Duk da ta sha magani
bata daina jin sanyin ba. mama tana gefenta tana yi mata dan fada cikin damuwa ta ce, “Haba
Nafisa, duk kin sa kanki damuwa tun daga ranar da ki ka san maganar nan kin bi kin damu.
Sai kin sa ma kanki wani ciwon sannan za ki ji dadi, shi fa ba zai fasa auren sauran ba, ke in kin
je babu lafiya yaushe za ki yi wata gama a idonshi.
Wayar Nafisa tana ta ruri, har sau biyu. Mama ta ce, “Ina wayarki ta shiga ne? ina jin kararta
daga cikin bargon.� Ta ce, “Bar ta kawai kila Mufida ce A na uku Mama tasa hannu ta ciro wayar
a kusa da filon da ta tada kai. Ta kalli wayar “Ai Shatiman ne ma ya ke kiran ki.�
Ta tashi zaune da sauri ta amshi wayar, Mama tayi murmushi sannan ta fita. Nafisa ta daga. Ya
ce, “Sweety ina ki ka shiga ina ta kira ba ki daga ba?�
Muryarta can kasa tana kuma rawa irin ta marasa lafiya. Ta ce, “Yaya bani da lafiya ne.� Ya ce,
“Subhanallah! Tun yaushe?�
Ta soma shesshekar kuka. “Na kwana biyu.� Ya ce, “Shi ne ba ki fada min ba? haba Sweety!
Ban so ba da ki ka yi haka, me ke damunki?�
Ta ce, “Zazzabi ne.� Ya ce, “To kin je asibiti?�Ta ce, “Mama ta ce muje na ce a’a, ina shan
magani a gida Ya ce, “Wa ya fada miki ana
zama da ciwo? Ina Mama din. ki bata.�

Ta yunkura ta tashi ta ce, “Bari in kai mata.� “Za ki iya tafiya amma ko?� Ta ce “Bari na kokarta.�
Ya ce, “Ban ji dadi ba Sweety, na kira ki muyi hira sai kuma in ji kina ciwo?�
Ta ce “Ga Mama din.� Ya gaida ta, sannan ya fara korafın ya ya za’ayi a biye ma Nafisa don ta
ce ba za ta asibiti ba?Mama ta ce, “Kaga Nafisa rigima ce da ita, tun daga ranar da ta ji cewa su
uku ne rana daya tasa ma kanta damuwa take wannan ciwon. Ya ce “Au! Dama wannan ne?�
Ta ce, “Shi ne.� Ya ce “To shi ke nan Mama bata wayar muyi magana. Mama ta mika mata wayar, ta nufi daki tana “Hello!� Ya ce, “Sweety kin bani mamaki,
kin san ya ki ke a zuciyata kuwa?�
Dadi ya rufeta, ta kara shagwabewa. “Ni Yaya
sai ina ganin don iyayenmu suka hada mu shi yasa
ka ke share ni, kuma ka fi son su.� Ya ce, “Ni na fi son wadda tafi sona, ke ga shi ma har yanzun
ban tashi daga Yaya a gurinki ba.�
Ta ce,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0