Showing 6001 words to 9000 words out of 51592 words
Chapter 3 - Shaukin So Book Compelet Mrs Sadauki
a ranta.
Sai da Anya ta sha ƙarin ruwa sosai kafin a samu ta farka,hawaye ne ke zuba kan fuskarta tana
jin abun kamar cikin mafarki .Tun tafiyar su kasuwa take jin faɗuwar gaba ashe iftila'in da zai
faɗa mata ne,a hankali ta fara motsa baki "innalillahi wa'inna ileyhi raji'un allahuma ajirni fee
musibati wa'akhlifni khairun minha"sai ta rumtse ido tana mai cigaba da yi mashi addu'a a zuci
ta na mai roƙon Allah kar ya ba shi ikon cutar da Tajdeen....
***Maradi
Kwance take bisa darduma hannunta riƙe da carbi tana ja,a zahiri tasbihi take amman a zuci
tunanin malam Nur ne fal ranta.
Sallama wani yaro yayi yace "wani yace a kirawo mashi Nazifa"ras gabanta ya faɗi kafin tace
wani abu Inna tace "je kace ga ta nan zuwa"kafin ta kalli Nazifa wadda ta taushi zaune "ki tashi
mana ki ga ko wanene" "toh Inna "ta faɗa tana mai miƙewa ta saka takalmi.
A can ƙarƙashin wata itaciya ta hango shi,sanye ya ke da wani farin yadi ya taje sumar kan shi
sai walƙiya ya ke baƙin gilashi ne a idon shi.Sai da tayi wata sanyayar ajiyar zuciya kafin ta
ƙarasa gun shi bakinta ɗauke da sallama.
"Tare da sahibata abun alfaharina"shine malam Nur yace fuska ta rufe da hijab alamun jin kunya
kafin tace "ya gida ina Maman da su Balkis"kwaɓe fuska malam Nur yayi yace "shine ni ba za a
tambaye ni ya nike ba?toh duka lafiyar mu lau"dariya Nazifa tayi tace "laaa to kai ba ga ka a
gaba na ba?hum to naji ya kake ?"bai bata amsa ba sai kallon ta da ya tsaya yi hakan yasa ta
sunne kai ta fara wasa da yatsun hannunta, murmushi yayi dan kunyar ta na ɗaya da abinda
yasa ya ke sonta "ya dai babyn Nur?"ba tare da ta ɗago ba tace "daidai" "ok shine kuma kika
ƙyale ni"yadda yayi maganar a shagwaɓe yasa tayi saurin ɗagowa ta dube shi "kuma ni za'a ayi
ma shagwaɓa?"tsayuwar shi ya gyara tare da cewa "eh mana in ban yi maki ba wa zan yi
ma?"tana shirin magana yaya Ɗalhat ya karyo kwana layin wanda ƙarar tsohon Babur ɗinsa shi
ne ya shaida mata da zuwan shi yadda malam Nur ya ga ta firgita ne yasa shi kallon Ɗalhat
wanda ya ajiye mashin a ƙofar gida ya doso inda su ke.
"Keee!wuce maza gida,kai kuma wa ya baka izinin zuwa da har za ka wani parker mota kana
wanke ƙawanta da ƙarya salon ka yaudare ta"shine abinda Ɗalhat ya faɗa cikin ɗaga murya tun
kafin ya iso inda su ke.Cikin rawar murya Nazifa tace "yaya Ɗal..."wata uwar tsawa ya daka
mata tare da nuna mata gida da gudu ta ruga ta na mai fashewa da kuka ......... [11/03 11:32] MRS SADAUKI: *SHAUƘIN SO*
```LoVe story```
By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI✍️}
*FCWA*☀️
________________________
Page 7-8
"Assalamu alaikum"malam NUR yace wa Ɗalhat yana mai miƙa masa hannu alamun suyi
musabaha wani
banzan kallo yayi ma shi tare da ɗaga ma shi hannu yace "bari abarka abinda zan faɗa maka
ka fita hanyar ƙawanta,kar na koma sake ganin ka nan"murmushi malam Nur yayi "babban
yaya kar ka yi min haka mana ai duk wanda yace ya na son naka ya gama maka komai a
duniya"ya faɗa yana ɗan jan gemu,taɓe baki Ɗalhat yayi ya kuma cewa "Ni ba zaka yaudare ni
da salon ustanzanci ba haka kuma ba zan bari ka yaudari ƙanwata ba in dagaske kake sonta ai
sai ka turo magabatan ka"yana gama faɗar haka ya juya ya shige gida ba tare da ya tsaya jin ta
bakin malam Nur ba.
Tsakar gida ya tarar da ita kwance tana kuka gefen ta kuma Inna na rarrashin ta,da sauri Inna ta
miƙe tana kallon Ɗalhat wanda sai kumbura ya ke yana batsewa "Inna miyasa za ba ki barin ta
fita zance?yanzu sabida Allah salon a rinƙa yi da ni ana cewa ba mu bata tarbiyya ba ido na
ganin ido ta fita zance duk wanda ya wuce yana kallon ta kuma abun takaici wai Ɗan masu
kuɗi..."
Saurin katse shi Inna ta yi da "in ban barta yin zance ba kai zaka auren ta?nace kai za ta aura
ko kuwa ba ka ga girma take ba?shi wanda ka kora ɗin ka san wane ne? malaminsu ne na
makaranta wanda ta ke faɗa ma saboda karatun da ya ware ya ke koya mata na musamman
sauran ɗaliban ke jin haushin ta,ina ce kai ma da kanka har daɗi ka ji ganin tana ta samun ilimi
ko?"wani huci ya furzar yace "Inna ki yi haƙuri sam ban yi tunanin shi ne ba dan a yadda na gan
shi bai yi kama da malamin makaranta ba,amman in shaa Allah ba zan sake korar shi ba in ya
zo"ɗagowa Nazifa ta yi fuska shaɓe-shaɓe da hawaye ta kalli yayan na ta tace "da gaske ya
Ɗalhat?"kai ya jinjina mata,cike da murna ta tashi ta wanke fuskarta ta nufi gidan su Samira.
Gidan babu kowa sai Samira zaune kan kujera tana wankin kaya gefe guda kuma wayarta na
fidda sautin waƙa.Sallama Nazifa ta yi kafin Samira ta kai ga amsa mata ta kuma cewa "Allah
ya shirye ki ke yanzu waƙa ce kike sauraro ko kunya ba ki ji matar malam guda?"sheƙeƙe
Samira ta ɗago tana kallonta tace "to sannu ustaziya miye na jin kunya daga sauraren waƙa sai
ka ce wata ta gamtsi wadda ba ta kamata ba " "waƙa dai sunanta waƙa malama dama bege
kika saurara da ya fi wannan shirmen"ruwan wankin ta watsa mata a fuska tace "wallahi ke ce
shirme ba ni ba"dariya Nazifa ta yi "kan ki dai ake ji"ta faɗa tana ɗaukar waya ta loda lambar
malam Nur amman a kashe.
Cikin sanyi jiki ta labarta ma Samira abinda ya faru "to miye na damuwa tunda yanzu ya Ɗalhat
ɗin ya amince ya dinga zuwa?"
"Samira ba za ki gane ba ne ta yaya kamilin mutum kamar malam Nur a jefe shi da mugayen
kalamai? Ni wallahi in da na san gidansu da na tafi na bashi haƙuri"cike da mamaki Samira ke
dubanta tace "haƙuri?eh lalle yanzu na yarda da maganar ɗalibai da su ke cewa kin fi son shi
fiye da yadda shi ya ke son ki,wannan rawar kai har ina?yanzu ke sabida Allah sai ki je gidan na
su dagaske?"kai ta ɗaga mata alamun eh, baki Samira ta ja tace "to ADS ne gidansu kuma duk
ɗan adaidaita sawun da kika ce ma ya kai ki gidan Ali Ɗan Masani zai kai ki"dafe ƙirji Nazifa ta
yi tace "ki na nufin ɗan Alhaji Ali Ɗan Masani ne?"tsuki Samira ta yi tace "sai ki yi,ni ma jiya naji
malam Jabeer na yi ma shi kirari"jikin Nazifa ne yayi sanyi dan duk yadda take zaton malam Nur
na da kuɗi ba ta zata jinin Alhaji Ali ba ne "gaskiyar yaya Ɗalhat,ni yanzu mi ma zai yi da ni ƴar
talakawa u
wanda abincin da za su ci ma ya na yi masu wuya wata rana?"
"To shine mi dan ya na Ɗan masu kuɗi ke kina ƴar talakawa?ina ce dai akwai ƴaƴan masu kuɗin
dayawa a makaranta amman ya nace sai ke ko?"
"Samira ina jin tsoron kar danginsa su ƙi karɓata,na san malam Nur ba dan wani abu ya ke
sona ba in ma akwai bai wuce ilimi shi ma Allah ne ya bani" "hum!su kuma su suka ba kan su
kuɗin ko?Nazifa ya kamata fah ki nutsu ki gane da tallaka da mai kuɗi duk Allah yayi su kuma
shi kaɗai ya san manufar yin haka,dan Allah ya baka arziki ba ya na nufin ya fi son ka da kowa
ba ne in kuma yayi ka talaka ba wai dan bai sonka ba ne a'a hakan dai ya ga yafi dacewa da
rayuwar ka"wani lumfashi Nazifa ta sauke tace "na sani amman abinda nake nufi ni ba class
ɗinsa ba ce ya fi ƙarfina"
Cikin jin haushi Samira tace "kawai ki ce dama ba ki son shi tun farko amman zancen wani ba
ajin ki ba ne bai ma taso ba,kyawu ma na banza kin fi shi kuɗi kawai zai gwada maki su kuma
ba komi ba ne face dauɗar duniya in baka kashe su ba ka mutu ka bar su"
"Tabbas haka ne Allah sa dai mu dace"cewar Nazifa ta na mai shiga galerie inda hotunan
malam Nur su ke,da "Amen"Samira ta amsa mata kafin ta miƙe ta fara shanya kayanta...
A ɓangaren malam Nur dakyar ya kawo kansa gida dan baƙin ciki da tiririn da zuciyarsa ke yi
masa,tun da ya ke ba'a taɓa yi masa cin fuska ba sai yau.
Ya na isa gida direct part ɗin shi ya wuce ba tare da yayi la'akari da Baba wanda ya ke zaune a
falo yana duba wasu littattafai.
Toilet ya shiga ya sakar ma kansa ruwa,a ƙasan zuciyarsa kuwa "innalillahi wa'inna ileyhi
raji'un"kawai ya ke nanatawa har ya fara jin sauƙin abun.
Cikin kayan ƴan balo (ƙwallo)ya shirya ya feshe jikinsa da turare sannan ya ɗauko system ɗinsa
ya kunna, hotunan ta ne ya ke kallo wasu ta na dariya wasu ta shagwaɓe fuska .
Bai san lokacin da murmushi ya kubce ma shi ba da ya zo inda ta washe baki tana dariya
kyawawan haƙoranta fari tas waɗanda suka samu ƙawanyar wushirya,sai dimple (point beauté)
ɗin ta mai ƙara mata kyau da ya lotsa.Ya shagala sosai da kallon hoton hakan yasa bai ji
shigowar Baban nasa ba,sai jin ya dafa kafaɗarsa a razane ya ɗago ya sauke idonsa kan fuskar
mahaifinsa wanda shi kuma ya ke kallon hoton Nazifa wanda ke bisa system.
Miƙewa yayi ya na ɗan sosa kai yace "um...Baba ina wuni?"murmushi Baba yayi ba tare da ya
amsa gaisuwar da yayi ma shi ba yace "wacece wannan?"i'ina malam Nur ya fara
"dama...dama ita ce wadda nake gaya ma Maman ina so"wani murmushin Baba ya sake yi yace
"shine tace ba ta sonka wanda hakan yasa ka shigo gida rai ɓace ba tare da ka gaishe ni ba ka
wuce ɗaki sannan ina ta yi ma sallama ba ka ji ba?"
Kai malam Nur ya sunne yace "ba wai cewa ta yi ba ta sona ba" "to mine ne?"
"Yayanta ne yace min wai wani in dagaske na ke in turo magabatana dan shi bai barin
ƙanwarsa na zance "
"To shine mi? Ai hakan ne daidai ka bani address ɗin gidan za mu je in shaa Allah ai mu dama
maganar auren mu ke so"tsabar jin daɗi Ustaz bai san lokacin da ya rungume Baba ba.
Ƙarfe goman dare Maman ce a ɗaki sai saffa da marwa take ,ta rasa sukuni tun lokacin da
Sappa ta shaida mata tana son Nur.
Wani gwabron numfashi ta sauke kafin ta nufi part ɗin Baba,a zaune ta tarar da shi bisa tapis ya
na tasbihi da yatsun hannunsa.Bayan ta gaishe shi ya amsa ya zuba mata ido ya na kallo duk
wunin yau yanzu kawai ya ganta sam babu walwala a tare da ita a kwana biyun nan yana lura
da ita. Gyaran murya yayi hakan ya sa ta ɗago suka haɗa ido,kamar daga bisa ta ji yace "mi ke tafe da
ke ?Na ga da magana a bakinki"gyara zama ta yi tace "eh dama akan maganar auren yaran
nan ce, Ustaz da Sappa shine nace bari na same ka na nemi alfarma ayi bikin ɗaya rana da na
wacan ɗayar da ya zaɓa amman dan Allah kar kace ba ka yarda ba dan wlh Sappa na matuƙar
son Ustaz wanda har son yayi mata mugun illa yanzu haka kullum sai an yi mata ƙarin
ruwa"Maman ta ƙarashe maganar ta na sakin kuka .
Sororo Baba yayi yana kallonta,sam abun ya zo ma shi banbarakwai, amman shi kansa shaida
ne yadda akan ciwon Sappa wanda kullum ƙaruwa ya ke.Nisawa yayi yace "ba damuwa zan yi
wa shi Nur ɗin magana" cike da jin daɗi Maman ta shiga yi ma Baba godiya sai kace ba mijinta
ba ne.
Washe gari zuwa 12 na rana sai ga valises (akwatina)kala biyun da Baba yasa a kawo ana
shigowa da su,a falo aka ajiye su.Cike da murna Maman ta shiga buɗa akwatinan,kaya ne na
azo a gani a cicike "Maman akwatinan ɗin wane ne?"cewar Balkis wadda fitowar ta kenan daga
ɗaki "na matan yayanki ne ɗaya na Sappa ,Seat ɗayan kuma na ɗaya amaryar"cike da murna
Balkis ta fara tsalle kafin kuma ta ruga zuwa ɗaki sai ga shi sun fito ita da Sappa wacce duk ta
rame,a bayyane ta nuna farin cikinta gabanin ta sunkuyar da kai jin Maman na cewa "wane kika
ɗauka kalar zai ba koko jajayen?"ba ta ce komai ba sai Balkis da tace "Maman bari mu duba
wanda kayan ciki suka fi kyau sai anty Sappa ta ɗauka"
"Duk kayan kala ɗaya ne ai"cewar Maman murmushi kan fuskarta.
Malam Nur kuwa ya na can maƙale da waya shi da sahibar shi ya na shaida mata cikin satinan
za'a kawo komai su yi aurensu su huta,kwaramniya da ihun Balkis ya fito da shi falo turus yayi
jin zancen da ake wai har da Sappa zai aure.
Ransa ne ya ɓace fuskar ta yi kicin-kicin jijiyoyin kansa duk suka fito,cikin furzar numfashi yace
"wace Sappai ?"ba Sappa da ke kusa da shi ba hatta Baba da shigowar shi kenan sai da ya
razana,cikin tashin hankali ya ƙaraso tsakiyar falon ya durƙusa saman ƙafafun shi tare da game
hannuwa yace "dan Allah Maman kar ki min haka wlh ni a matsayin ƙanwa na ɗauketa kuma ni
banda tsarin zama da mata biyu Nazi ita ce ruhina,rayuwata da komai naw...."ƙarar faɗuwar
Sappa ne ya hana shi ƙarasawa da sauri duk suka nufi gun ta inda ta faɗi a sume........
[11/03 12:08] MRS SADAUKI: *SHAUƘIN SO*
```LoVe story```
By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI✍️}
*FCWA*☀️
________________________
Page 9-10
Ruwa masu sanyi Maman ta zuba ma Sappa nan ta shiga sauke ajiyar zuciya,bakinta ɗauke da
sunan Nur.Baba, Maman da Balkis dukansu suka juyo suna kallonsa yadda ya nuna halin ko a
jikinsa,hawaye Maman ta goge tana mai ci gaba kallon shi cikin ido hakan yasa ya ƙarasa cikin
cool voice yace "Sappaaa..."ƙyalewa yayi ya ja dogon numfashi sannan ya cigaba da cewa "ki
yi haƙuri kin ji?in shaa Allah ni da ke mutu ka raba" Sappa da ke kwance cikin ruwa da sauri ta
buɗe idonta tarau kan kyakkyawar fuskar Ustaz wacce take sharrr saboda ambaton Allah.Kai ya
jinjina mata ganin ta yi masa ƙuri ta na son gasgatawa,ido ta lumshe tana jin wani sanyi na
ratsa gangar jikinta ba ta san lokacin da murmushi ya suɓuce mata ba.
Kanta Maman ta shafa tace "Balkis ja ta ku tafi ɗaki ta canza kaya"da "toh Maman"ta amsa ta
na mai taimaka ma Sappa ta miƙe a kunyace.
Ustaz kuwa gidansu malam Jabeer ya wuce ya na jin zuciyarsa babu daɗi ,a ƙofar gida ya
zauna yana jiran fitowar shi.Seat ɗin mai zaman banza malam ya zauna yana mai gyara
hullarsa yace "ya dai NazNur ka kira ni na zo kuma ka wani duƙe kai ko sallamar da na yi ba ka
amsa min ba"ajiyar zuciya malam Nur ya sauke kafin ya ɗago fuskarsa ya kalli malam Jabeer
"subahanallahi mi ya sami idon naka suka yi ja haka?"cikin ɓacin rai ya ba shi amsa da "sun
ƙaƙaba min auren Sappa Jabeer yanzu mi zan ce ma Nazi ?da wane ido zan kalleta na gaya
mata su biyu zan aura?"
Zama malam Jabeer ya gyara yace "ban gane ba yi min dalla-dalla"nan malam Nur ya bashi
labarin komai da ya faru ya ɗora da faɗin "ka san dama ta sha gaya min ta na sona to ban zata
rashin kunyarta ba har ta kai haka shine ta yi min gami da iyayena su kuma suka yanke
hukunci ba tare da neman shawarata ba"
Jinjina kai malam Jabeer yayi kafin yace "to shi aure lokaci ne kuma matar mutum
kabarinsa,yanzu yadda za ayi ka bari har sai an sa date ɗin bikinku sannan ka gaya ma Nazifa"
"Ka na ganin hakan shine mafita?" "Eh tabbas"nan dai malam Jabeer ya cigaba da kwantar ma
abokin nasq da hankali tare da nuna masa mahimmancin yi wa iyaye biyayya ba dan bai sani
ba sai dan ƙara yi ma shi tuni su ma sunada haƙi kansa.
Cikin sati guda kacal Baba yasa aka yi bincike dangane da tarbiyyar Nazifa inda ta samu
kyakkyawar shaida hakan yasa ba ayi ƙasa da gwiwa ba aka kai lefe tare da tsayar da rana
aure nan da wata biyu.
Mahaifiyar Sappa ba ƙaramin daɗi ta ji ba ganin zumuncinsu zai ƙara ƙarko ita da ƴar
uwarta,Sappa kuwa tun da aka kawo lefen ta ƙara ɗaukar son duniya ta ɗorawa Ustaz dan
yanzu ƙawayenta SapNur su ke kiranta.
Tun wayewar safiya yau take yawan jin faɗuwar gaba,ko dan za ta je gaishe da iyayen Nur ne
oho.A haka dai Samira ta tsantsara mata lalle ta yi wanka sannan ta shafa mata hoda,za ta yi
mata kwalliya irin ta zamani tace ba ta so.
Wani rantsantsen less ta saka mai ratsin ja,hijabi da kalmi da jaka ta fitar jajaye hakan ba
ƙaramin fiddo ta kayan su kayi ba.
"Masha Allah"shine abinda Inna ta faɗa Rakiya da Samira kuwa sai kallonta su ke yadda ta fito
sak amarya.Hotuna Samira ta fara ɗaukar ta a wayar da malam Nur ya saya mata kafin