Showing 24001 words to 27000 words out of 51592 words

Chapter 9 - Shaukin So Book Compelet Mrs Sadauki

ta nufi inda ta ke jin
maganar su tana lalube,dariya suka sake yi tare da ci gaba da tsokanar ta suna guje-guje ita
kuma tana bin duk inda taji motsin su.
"Miyasa ba ki jin magana ne Laila ba na ce ki bar kula su ba?"cewar Nazifa ta na kamo
hannunta,hawaye na kawowa idonta tace "Ammy baki ji su ke tsokana ta ba?"kai Nazifa ta
girgiza tace "to ai ƙannanki ne sai ki yi haƙuri,tawo mu tafi Maman na bedroom"tsuki Sappa ta yi
wacce tun ɗazu ta ke zaune ƙasa da uban cikin ta ƙatoto haihuwa ko yau ko gobe tace "Allah
kiyaye mu irin mu babu masakai,can ku ƙarata ke da makauniyar ki,Twins ku zo nan kar ku taɓa
wacen abar ta liƙa maku nakasa"murmushin da yayi kuka ciwo Nazifa ta yi kafn ta wuce ɗakin
Maman,ba'a jima ba sai ga su sun fito Maman na yi mata a dawo lafiya.A zaune ta tsinkayi
malam Nur ya ɗora Twins a cinya ya na raba masu biscuit,har za su wuce Laila taji murya shi da
sauri ta waiga tana ƙyafƙyaf da ido kamar mai gani tace "Abih..."ɗagowa malam Nur yayi kallo
guda yayi masu ya maida hankalin shi gun Twins da suke mashi surutu ya na amsa masu.


Zuciya na yi mata zafi ta nufi bakin hanya ta samu abun hawa ya kaita gidan Samira wacce ake
bikin haihuwar da ta yi ta biyu,abun biki kawai ta bada ta samu wuri ta rakuɓe.Shikenan yanzu
ita da farin ciki sai dai ta gani gun wasu?haka dama maza su ke ba su da tabbas?miye laifin ta
dan ta haifi makauniya? wannan ne tambayoyin da Nazifa ta yi ta yi har bikin ya watse ta dawo
gida.


Cikin dare Sappa ta kasa bacci saboda naƙudar da ta tawo mata gadan-gadan,cikin tashin
hankali malam Nur ya fito ya shiga ƙwanƙwasa ma Maman ƙofa kasancewar ba ta da nauyin
bacci yasa ta ji bugun.
Ta na buɗewa ya shaida mata Sappa ce ke naƙuda da sauri ta koma ɗaki ta kimtsa suka nufi
asibiti,Twins kuma aka bar su wajen Balkis.


Gari na wayewa Nazifa ta je gaishe da Maman Balkis ke faɗa mata Sappa na asibiti wajen
haihuwa "Allah sauke ta lafiya"ta faɗa tare da komawa ciki ta fara girkin da za'a ta kai.
Ta na gama girki su ka shirya ita da Balkis da yara suka nufi asibiti,tun daga nesa su ke jin
kukan Sappa sun tsaya tunanin room ɗin da take sai ga malam Nur ya fito fuskar shi a kumbure

idon shi sun yi ja alamun kuka ya yi.Ba su tsaya tambayar shi mi ke faruwa ba suka shiga ɗakin
da ya fito,kwance suka tarar da Sappa sai fizge-fizge ta ke yayinda likitoci ke ƙoƙarin yi mata
allura barci.

"Maman lafiya ko jaririn ne ya zo ba rai?"cewar Balkis,kai Maman ta girgiza ta yi masu nuni da
ɗan ƙaramin gadon da aka shimfiɗe bbyn tace "a'a da ranta kawai dai da nakasa ne aka haife ta
da shi"da sauri Balkis ta zaro ido tana ƙarasawa bakin gadon,wata kyakyawar baby girl ta yi
tozali da ita mai hannu guda ɗayan kuma gundululu ne. Tausayinta ne ya ratsa zuciyar imani ta Balkis hannu na rawa ta ɗauke ta,ɗaya daga cikin nurs
ɗin tace wane suna za'a sa ga takardar babyn " *Jasmine* "Balkis ta faɗa a takaice tana
miƙawa Nazifa babyn.A nan free page ya ida mai son ci gaba sai ya biya 300 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank DM +22795045822




*Dama haka Allah ke ikonsa,in ka raina halittar wani kai ma sai ya jarabce ka ya ga ya za ka
yi.Ga Sappa dai ita ma ta haifi mai nakasa ko ya za ta kaya? Shin za ta yarda ita ta haifi Babyn
nan ko kuwa ? Mu haɗe a paid group*
[22/05 23:57] MRS SADAUKI: *SHAUƘIN SO*


```LoVe story```


By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI✍️}


*FCWA*☀️

________________________

23-24


"Zan ci mutumcin ki wlh in ba ki karɓi yarinyar nan ba kika bata abincinta,uwar mi za kiyi da shi
in ba ki shayar da ita ba?"Mamar Sappa ke faɗin haka tana mai miƙa mata babyn.Kai ta girgiza
cikin kuka tace "wlh Umma tsoronta nake ji,ban iya ganin ta"
"To kin dai ji da kunnenki tun ɗazu yarinyar nan ke kuka ta bata nono ta ƙiya sai zam-zam kawai
nake ɗura mata"cewar Maman ta na hararen Sappa wadda ta yi zaune kan gadon asibiti tana

rusar kuka.
Bisa cinyoyinta Umma ta aza mata Jasmine da ke ta kuka,rumtse ido Sappa ta yi ganin hannu
guda kawai ya fito ta rigar gudan kuma sai shatin shi kawai ake gani.Karrr ƙafafunta suka fara
zanzana suna rawa yayinda hawayen fuskarta suka ƙaru,wani wawan dundu Umma ta kai mata
a baya tace "in dai baki shayar da ita ba Allah ya isa nonona da kika sha ban yafe ba"jin furucin
mahaifiyarta yasa doli ta fara baiwa Jasmine abincinta.
Ƙofa aka ture tare da yin sallama,Nazifa ce hannunta ɗauke da basket ɗin abinci.Gaishe da su
Maman ta yi tare da tambayar Sappa ya jikinta amman ko kanzil ba ta ce mata ba,Maman tace
"ina kika baro ita Laila ɗin?" "Ta na can gida wajen Balkis tana koya mata karatu" "ah to yayi ai
gwara ita Balkis ɗin ta koya mata tunda shi uban ya kasa kaita makaranta" murmushi kawai
Nazifa ta yi tana kallon baby Jasmine da ke shan nono har yanzu kafin zuwa can ta saki alamun
ta ƙoshi hakan yasa Sappa maida rigarta tana turo baki.Tashi Nazifa ta yi ta ɗauko ta murmushi
kan fuskarta,gefen ƙyale ta sa ta goge mata baki.

Hararenta Sappa ta yi tace "munafuka wa ya sani ma ke kika yi min asiri na haifi wannan
masak..."da sauri Umma ta buge mata baki tace "in na sake jin kin aibata yarinyar nan sai na yi
mugun saɓa maki, banza daƙiƙiya da ba ta san abinda ta ke ba"mahaifiyar Sappai ke faɗin
haka,ita dai Nazifa har ga Allah ta ke jin son Jasmine. Abinci Maman ta zuba plate biyu ta miƙa ma Sappa guda su suka ci ɗayan,ba jimawa likita ya
shigo ya basu takarda sallama.
Kaya suka fidda kafin Nazifa ta fita bakin ƙofa ta kirawo ɗan taxi,shi ya taimaka masu wajen sa
kayan tare da faɗa masu kuɗin da za su biya.
Har ƙofar gida aka sauke su,da gudu Twins suka tawo gun Sappa tare da kama mata
ƙafafu.Hannun su ta ja zuwa ciki,direct part ɗinta ta wuce alhalin part ɗin Maman aka ce za ta
tsaya.


Cikin jimami Maman tace "ya kamata fa mu samu mafita kar jaririyar nan ta mutu,a bada kuɗi a
sayo madarar gwangwani a riƙa bata kina ga fah tun zuwan mu ta kama ƙofa ta rufe alamun ta
bar mana da ƴar"cikin takaici Umma ta kalli Maman tace "yanzu sabida Allah anty jaririya
uwarta da ranta da lafiyarta sai a shiga bata madara?"Maman ta yi saurin cewa "eh mana in dai
ba taimaka mata za muyi wajen kisan kai ba,wlh na fi ki sanin halin Sappa ke haihuwarta kawai
kika yi tunda kika ji tace ba za ta shayar ɗin ba to haka maganar take ba canji.Balkis tashi ki tafi
pharmaci ki sawo min madara "Maman ta faɗa ta na zuge zip ɗin bag ɗinta ta baiwa Balkis
5000.
Ruwan zafi Umma ta ɗora yayinda Maman tayi ma Jasmine wanka,ba jimawa sai ga Balkis ta
dawo riƙe da ledar madara da biberon.

"Yauwa wanke biberon ɗin sai ki kaɗa na bata,baiwar Allah yunwa ta ke ji"cewar Maman,
"toh"Balkis ta amsa ta nufi kitchen ba jimawa ta dawo da kaɗaɗar madara ta miƙawa
Maman.Ana saka mata tétine ɗin ta kama ta shiga sha zut-zut,baiwar Allah sai da ta sha sosai
sannan ta saki dandanan barci ya ɗauke ta.

A ɓangaren Sappa kuwa babu wanda ta gaya ma ta haihu,dan a cewar ta abun kunya ne a ce
ta haifi nakasasa mai hannu guda.
Ita ke dafa ma kanta ruwan zafi tayi kuma wanka da kanta,tun da aka sako su daga asibiti ba ta
ƙara sa su Maman a ido ba balle wata can Jasmine.Duk abinda ta ke buƙata malam Nur ta ke
gayawa ya kawo mata,dan sam shi ma bai marhaba da haihu Jasmine duk da malam Jabeer na
bakin ƙoƙarin shi wajen tunatar da shi amman fafur ya ƙi fahimta,a ƙarshe ma dai malam Jabeer
ne yayi ma Jasmine huɗuba.


Sati na kewayowa aka yanka ma Jasmine ragon sunanta ba tare da yin biki ba, Sappa da
malam Nur ko a kwalar rigarsu dan ba su san wainar da ake toyawa ma ba.
Da dare ya shiga part ɗin Nazifa sai ganinta yayi rungume da Jasmine tana bata madara
gefenta kuma Laila ce zaune ta na cin abinci tana karatun da Balkis ta kowa mata.
Baki ya taɓe a zuci yace 'uwar masakai tunda ke kin ji kina iyawa ai sai kiyi'ƙarasowa yayi ya
zauna ta ɗago ta kalle shi ba tare da tace komi ba.
Laila kuwa ido ta shiga juyawa tana ɗan buɗe ƙofofin hancinta tace "Abih...?Ammy Abih ya
shigo nan?naji ƙamshinsa"ido malam Nur ya waro cikin suɓutar baki yace "toh mayya"Nazifa
tace "Allah kiyaye ni ban haifi mayya ba"Laila kuwa tashi ta yi tana lalube tana cewa Abih,"kar ki
taɓa ni"ya faɗa da sauri ganin ta zo dab da shi cikin rashin sa'a ta ɗora hannunta bisa farar
shaddar shi,cike da murna ta ke furta "Abihhh"wata ɗunguza yayi mata yana mai tashi tsaye ya
tattare gun da ya ɓace ya nufi toilet ya na banbamin bala'i.


Kuka Laila ta fashe da shi ta na kiran sunan mahaifiyarta,wani mashi ne ya caki zuciya Nazifa
lokacin da ta ɗago Laila ta ga goshinta yayi ƙululu sakamakon bugewa da tayi da ƙafar kujera.
Tun daga wannan ranar Nazifa ke kafa-kafa da Laila da zarar ta ji muryar malam Nur ta na son
zuwa sai ta riƙe ƴarta,shi kam ba ƙaramin daɗi ya ke mashi ba dan a ganin kiran sunan shi ma
da Laila ke yi takura ce.Gefe guda kuma sosai ya ke tattalin Twins da saya masu duk abinda su
ke so,a duk lokacin da babu school kuwa da su ya ke tafiya makaranta.
Karamci da Nazifa ta yi na ɗaukar Jasmine yasa ta ciri tuta a zuciyar Maman da umma,wanda
kuma hakan ya fara damun Sappa sai ta fara kula ƴar makauniya ta na janta a jiki wani sa'in har
part ɗinta ta ke kwana.A tunanin Maman Sappa tayi hankali ne yasa take son maida alkairi da
alkairi ga Nazifa ba su san cewa aiki ne ta ke sa Laila ba ,ba tare da tayi la'akari da ƙaramtar ta
ba.




Lokacin da Laila ta shiga 10years zallar kyawunta da kamalarta suka fito wanda ba komi ya
ƙawata ta ba sai tarin ilimin da ta ke samu gun mahaifiyarta da kuma amarya Balkis.Cike da jin
daɗi da annushuwa Maman ke kallonta tace "yanzu dagaske Lailana kin hardace alƙur'ani hizib

sittin?"kai Laila ta ɗaga tana murmushin da ke fito da zallar kyawunta "gaya min duk abinda kike
so ni kuma nayi alƙawarin zan yi maki shi"cewar Maman,shiru Laila tayi zuwa can tace "ina so
nima idona ya buɗe na rinƙa gani kamar kowa kin ga shikenan Twins ba za su sake tsokanata
ba"kamar daga sama amsar ta zowa Maman,wasu hawaye ne suka zubowa Maman cikin
dauriya tace "in shaa Allah zan yiwa Abihn ki magana ya shirya mana visa mu tafi ƙasar waje
ayi maki gyaran ido"rungume ta Laila tayi cikin farin ciki.


Cikin satin da bai wuce biyu ba Maman suka fara shirye-shiryen fita ƙasar waje bayan ta sa
malam Nur ya je Bank ya ciri duka kuɗin account ɗin da suka yi saura dan tun auren Balkis aka
bata gadonta cikin su aka yi mata sayayya sauran ta baiwa mijinta kasancewar shi tallaka ne.


Cike da mamaki malam Nur ke kallon Maman yace "yanzu Maman saboda kawai a buɗe ma
Laila ido zaki sa na kwashi kuɗin account duka?"zaro ido Sappa ta yi jin wani za'a yi ma Laila
magani a take wani kishi da baƙin ciki ya turnuƙeta ta shiga tari.
"Eh tabbas kuma babu wanda isa ya hana dan haka ka fara shiri dan tare za mu tafi"wasu
hawayen farin ciki ne suka shiga ambaliya a fuskar Nazifa ita sam ba ta zaci gaskiya Laila ke
faɗa mata ba lokacin da ta shaida mata Maman tayi mata alƙawarin kaita asibitin waje.
Jasmine ce ta shiga tsale tana cewa "waiiii antyna za ta buɗe ido nima Maman sai a sayo min
hannu"dariya Maman tayi tana mai jawo ta zuwa jikinta.


Tsananin baƙin ciki da hassada ya haifar ma da Sappa ciwon mara,a ƙarshe dai cikin jikinta ya
fara zuba.
Tun da safe ta tafi asibiti,su na nan zaune jiran Dr ɗin abun ka da taron mata nan fa suka shiga
hira kowa na faɗin abinda ke damun shi har aka zo kan Sappa wacce ke basu labarin za'a
kashe maƙudan kuɗi saboda gyaran idon ɗiyar kishiyarta,ai kam suka shiga zuga ta kar ta
yarda.Baki ta ja tayi ƙyaci tace "ina fah zan yarda ina nan ina tunanin matakin da zan ɗauka,ki
na ga fah tashin hankalin da nake ciki ne ya haifar min da zubar jini"wata ɗaya daga cikin
wadda tafi nuna damuwa akan abun tace "nima ciki ya taɓa min zuba amman ina shan wani
maganin gargajiya ya ɗauke har sai da na haife ɗan cikina"Sappa tace "a ina kika same shi ni
inda ki na da shi da kin bani dan dama ba kasau nake son namiji ya duba ni ba"
"No babu matsala in ki na so sai ki tashi mu tafi na kai ki har gun da ake saidawa" "ok tashi mu
tafi"cewar Sappa.
Adaidaita suka samu suka nufi bakin asibiti ƙarama,wani ganye matar ta saye ta baiwa Sappa
lokacin da suka ƙara tarar adaidaita da za ta mayar da su."Ka fara sauketa sai na ga gidanki,in
ya so daga baya sai na kawo maki ziyara" "babu damuwa Maman Latif"cewar Sappa.
Hira suka tayi har aka kawo Sappa ƙofar gida ta biya duka kuɗin harda na Maman Latif,"nagode
sosai Allah bar zumunci ki ban number dan in naje gida na kira naji maganin in ya so jikin ki"
Sappa tace "ba damuwa"ta zaro number ta da ke jikin wata ƴar takarda ta baiwa Maman Latif.

Da zuwanta ta tafasa ganyen maganin ta tace ta fara sha,tun Sappa na jiran cikin ya bar zuba

har ta fidda rai.
Shirin barci ta yi ta tana tunanin ƙila maganin bai so jininta ba ne.
Sappa ba ta jima da kwanciya ba ta ji kamar ana dirowa cikin gidan,ji kake dif-dif-dif ƙatti na
dirowa.Ta window ta leƙa nan ta ga zabga-zabga mazaje fiye da goma ko wane fuskar shi rufe
da masque,ga manyan bindigogi a hannunsu.Da sauri Sappa ta saki labulen tana jin fitsari da
ragowa cikin sun fara zuba.
Part ɗin Maman suka nufa,ba su wani ɗauki lokaci ba suka ɓalle ƙofar.Duka suka shigo aka bar
biyu a bakin ƙofa,kamar a mafarki Maman ta ga mutane da baƙaken kaya sun yi ma gadonta
ƙawanya.Wani gigitacen ihu ta ƙurma wanda ya sauka har cikin kunnen malam Nur da ke tsaye
kan sallaya yana sallah.Ƙirjin shi ne ya buga da sauri-sauri ya sallamce ya nufi ƙofa. "Ina kuɗin da kika ciro daga Bank?kar kiyi garma dan zan iya harbe ki"ɗaya daga ciki ya faɗa
yana bugawa Maman kan bindiga ga hanci a take jini ya ɓarƙe,ta dafe wurin tana kuka wani ya
kai mata naushi da ƙafa yace "ba tambayar ki ba a ke?"azabar da Maman taji ne yasa ta nuna
masu drower,ba ɓata lokaci wani ya buɗe sai ga ƙatuwar bag.Zip ɗin ya buɗe ya ga ƴan
goma-goma rasss kwance ciki da hannu yayi masu alama suka fice daga gidan.......

My book is only 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank DM +22795045822 .DAGA WANNAN PAGE ƊIN BABU WATA DA ZA TA SAKE FITA
DUK MAI SO YA BIYA.


Please share
[23/05 09:38] MRS SADAUKI: *SHAUƘIN SO*


```LoVe story```


By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI✍️}


*FCWA*☀️

________________________


Littafin SHAUƘIN SO labari ne akan kishiyoyi biyu ,ta farko sun yi auren soyayya da mijinta
yana mugun sonta kamar zai mutu sai dai kash a haihuwar farko ta haifa masa Ƴa
makauniya,wanda hakan yasa alaƙarsu yin rauni.Yayin da ta biyun kuma aka yi musu auren

zumunci bai sonta amma sai ta haifa masa ƴan biyu kuma duka maza wannan yasa ta ciri tuta a
wurin mijin.

Shi me zai faru a gaba? Ku biyo ni a paid group only 300 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank DM +22789042227 ga waɗanda suke da lambata ta farko suna iya tura receip ɗinsu
ta can ba dole sai wannan da na bayar ba.
[23/05 11:29] MRS SADAUKI: *BAƘIN RUHI*


```LoVe aNd HoRrOr story```


By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI✍️}

*SADAUKARWA :* Ga dukkan iyayenmu MATA da suka tsaya tsayin daka don bamu kariya a
kan dukkan wani da ke son cutar da mu.


*FCWA*☀️

________________________


Happy sallah my dear fans, Allah karɓi ibadunmu Amen !!!

*Wannan labari da da kaso saba'in ya faru da gaske,don haka don Allah kar wacce ta ji
haushina yayin ganin abin da ya saɓawa ra'ayi*


01


“Kowanne ahali da nasa sirrin,haka kowanne ahali da nasu tabo ko ƙaddara ko kuma dai wani
al'amari wanda suke ɓoye wa.Motar tsautsayi ce ta ja ni na bankaɗe mayafin da ya luluɓe
baƙin sirrin gidanmu wanda silar haka yasa na baro ahalina domin tseratar da da gajiyayen
ruhina,wanda aka raunata shi ta sigogi da dama” na yi shuru saboda hawayen da suka cika min
ido.Ita kuwa Lubna banda aukin kallona babu abin da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login