Showing 12001 words to 15000 words out of 51592 words

Chapter 5 - Shaukin So Book Compelet Mrs Sadauki

tashi ba sai da shabiyun rana ta gota shi ma kiran Inna ne
ya tashe ta,bayan sun gaisa Inna tace " ki bani hankalinki nan Nazifa ina so ki saurare ni da
kunnuwan basira"da "toh Inna"ta amsa ta na mai yin zauna.
Nasiha Inna ta fara yi mata ta ɗora da cewa "Nazifa ina so ki ɗauki ƙaddara a duk yadda ta zo
maki,wani abu ba zai taɓa samun bawa ba face dama ya na rubuce a cikin allon
ƙaddararsa,sau tari abubuwa su kan zo mana ba tare da mun shirya zuwan su ba ko kuma ba
yadda mu ka tsara su ba,da haka nake cewa ki zama mai biyayya tare da duban uzirin
mijinki.Tun kafin aurenku Nuradeen ya same ni da maganar iyayensa za su gama shi aure da
ƴar uwarsa kuma bai da wani zaɓi sai na yi masu biyayya,ya faɗa min ne saboda ya kasa
tunkarar ki dazancen gudun kar hankalinki ya tashi ba dan ya na tsoronki ba sai dan gudun
ɓacin ran masoyi.Yanzu haka kishiyarki na nan cikin gidan da kike kawai dai an raba ɓangarorin
ne,ki riƙe ta amana ki zauna da ita da zuciya guda kar na ji kar na gani kin yi wani abu na
cutarwa"tunda Inna ta ambaci kalmar kishiya ta ji kamar an buga mata guduma amman kuma
sauran kalaman sun ɗaure mata jijiyoyi,hawaye ta goge tace "toh Inna in shaa Allah zan
kasance mace ta gari" "Allah maki albarka ya kuma baki ikon yin haka"cewar Inna sannan tayi
mata sallama.


Jiki ba ƙwari Nazifa ta shiga ta yi wanka tare da simple kwalliya ta saka riga da zane na
atamfa,kitchen ta nufa ta haɗa tea ta sha sannan taci sauran kaza jiya.Tv ta kunna ta zauna ta
na duba Channel sai ta. ji ana bubuga ƙofa,izinin shigowa ta bada aka turo ƙofar tare da yin
sallama.

Amsawa ta yi tana mai kallon Sappa wacce kallo guda za ka yi mata ka gane amarya ce,gaban
Nazifa ne ya bada ras dan ko babu tantama wannan ce kishiyarta .Wurin zama ta bata,zaunawa
Sappa ta yi ta na cewa "ina kwana anty amarya"amsawa Nazifa ta yi cikin sakin fuska kafin ta
bata ruwa.

Tv su ke kallo lokaci zuwa lokaci suna ɗan taɓa hira kafin daga ƙarshe Sappa ta yi mata
sallama ta koma ɓangarenta,Nazifa kuwa Samira ta kira suka sha hira daga ƙarshe Samira tace
tana nan tafe....




***JOS


Wanka Vani ta yi ma Tajdeen ta saka masa kayan da mijinta Jean ya sawo,sosai Tajdeen yayi
kyau ya fito asalin bafulataninsa.Cikin jin daɗin sabin kayan da ta saka ma shi yace "na gode
tanti"da sauri Vani tace "no daga yau da Mom za ka rinƙa kira na kaji ko?"kai Tajdeen ya ɗaga
yace "toh Mom"kan shi ta shafa ta na jin son ɗan har ƙasan ran ta,Jean da ke gefe ya na kallon
su yace "toh ni kuma da mi za'a kira ni ?"kallon Vani Tajdeen yayi alamun ya na son jin amsa
daga gareta "Dad ɗinka ne dan haka shi ma daga yau Dad za ka kira shi ka ji ko?"kai Tajdeen
ya jinjina alamun toh.

Hotuna Mom ta fara ɗaukar shi wasu ya na tsaye wasu kuma zaune kafin ta jawo shi su fara
selfie suna dariya inda a ƙarshe Dad ya shigo suka rinƙa ɗauka tare gwanin sha'awa.
Wasap Mom ta shiga ta saka hoton da suka saka Tajdeen a tsakiya kan profil (dp)sauran kuma
ta zaɓi masu kyau ta saka a status,inda ya ke shi ɗaya ta rubuta ```My son Deen``` a sama.

Cikin zumuɗi irin na wanda bai taɓa samun haihuwa ba suka kamo hannun Tajdeen zuwa
babban falon gidan,a zaune suka tarar da Raj,Ranvir,Rahul da kuma Père (père na nufin
father)wato dattijon.
Dukan su da murmushi su ke kallon Den in ka fidda Raj wanda tun zuwan Tajdeen ya ji ya tsane
shi har ƙasan ransa.

Hannuwa Père /father ya buɗe yace ma Deen ya tawo,cikin rashin sabon haka Tajdeen ya shige
jikin tsohon.Kansa ya rinƙa shafawa yana sa mashi albarka kafin yace "ya kamata ku tashi mu
ɗan zaga gari ta yadda jikallena zai saki jikin shi"dariya dukan su suka yi dan sun san halin Père
da son yara dan dai ma Allah ya jarabi babban yayan nasu Jean da rashin haihuwa kuma shi
kaɗai ne mai mata sai Raj wanda ake shirin aurensa.

Cikin gari suka shiga suna zagawa Tajdeen kuwa ya ware ido sai kallon abubuwan mamaki ya
ke yadda mutanen garin ke rayuwa irin ta turawa,mata na saka sutura wacce ita da babu kusan
ɗaya yayinda mazan garin su ka ɗauki shan giya da sauran kayan maye kamar ado.
Sai da Père ya ga alamun kamar Deen ya gaji sannan suka koma gida,Mom kuwa ta ja hannun
Ɗanta suka wuce part ɗinta ta sake yi masa wanka tana cikin shafa mashi mai Dad ya shigo
dariya yayi mata yace "abun nema ya samu ko?to a rage yi mashi wanka kar mura ta kama
shi"dariya ta yi tare da rufe ido alamun jin kunya kafin ta buɗe akwati ta zaɓo mashi wasu
kayan......



Please share
[14/03 16:00] MRS SADAUKI: *SHAUƘIN SO*


```LoVe story```


By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI✍️}


*FCWA*☀️

________________________

Page 13-14


Rayuwa mai daɗi Tajdeen ke fuskanta,ya ci abinda yake so ya kwanta wuri lafiyaye babu abinda
ya fi yi masa daɗi irin kayan jikin da ake saya masa tsadadi.
Soyayya da Vani da mijinta suke nuna masa ko ɗan cikinsu sai haka amman duk da hakan
Tajdeen bai sa ya mance Anya da Kaka ba dan kusan kullum sai yayi ma Mom hirar su,ita kuwa
ta yi ta dariya jin shirmen da Kaka ke yi.


Cike da kulawa take shirya Tajdeen cikin uniform ɗin makarantar da zai fara zuwa yau,
murmushi ta yi bayan ta gama shirya shi tace "iyeee ɗan Mom ka ga yadda uniform ɗin nan ta yi
maka kyau kuwa? Zo mu je ka duba madubi ka gani"kusan ƙaton madubin suka isa nan
kyakkyawar fuskarsa siririya irin ta Fulani ta bayyana,sai sumar kansa wadda ta ɗan toho ita ma
sai ƙyallin take.

"Na yi kyau Mom"Tajdeen ya faɗa ya na taɓa hannuwa alamun jin daɗi,jan shi ta yi zuwa waje
inda Dad ke zaman jiran su.
Mota ya shiga yana ɗaga ma Mom hannu yayinda Dad ya figeta zuwa waje.


Sun yi ƴar tafiya mai ɗan nisa kafin su ke tsayawa gaban ƙaton get ɗin école/school ɗin,hannun
shi Dad ya kama ya kai shi har cikin class ya zaunar da shi sai da lokacin fara karatu ya kusa
sannan Dad ya bashi kuɗi ya juya zai komawa ai kam Tajdeen yace bai san wannan ba.

Cikin shagwaɓar da ya ya koya tun farko zuwan shi cikin ahalin ya riƙe Dad yace "Please Dad
kar ka tafi ka bar ni ban san kowa ba tsoro nake ji"rage tsawo Dad yayi cikin sigar rarrashi yace
"ka zauna yanzu zan dawo ɗaukar ka da zarar kun gama karatu"kafaɗa Tajdeen ya maƙe yana
mai shigewa jikin Dad,wani ɗan yaro ne daidai sa'ar shi ya taso daga inda yake ya kama
hannun Tajdeen yace "Friend zo mu tafi ka ƙyale Dady"kallon Dad Tajdeen yayi ya jinjina masa
kai alamun su tafi kafin ya shafa kansu yana mai tambayar yaron sunan shi "Junior"ya ba shi
amsa,bye-bye suka ma Dad kafin suke zaunawa saman table Junior na yi ma Tajdeen hira har
Madam ɗin da za ta koya masu ta shigo.


Karatu ta yi masu daidai yadda kwanyarsu za ta ɗauka,sosai kam suka gane dama sunayen
abubuwa irin su dabbobi ,kujera,allon rubutu sune ta koya masu.

Lokacin shan iska na yi duk yaran suka nufi restaurant nan kowa ya shiga sayen abinda yake
so.Tajdeen na cin biscuit ya dubi Junior yace "mi yasa duk ƴan garin nan fatar ku iri ɗaya ce
tunda na zo ban ga baƙar fata ba,kuma na ji kuna Yaren Hausa?"amsa Junior ya bashi da "eh
mu ba African people ba ne asalin ƴan Indonesiya ne yaƙi ne ya shigo damu ƙasashen baƙar
fata" "minene Indonesiya?"Tajdeen ya sake tambayar shi"da hannu Junior yayi mashi alama da
oho kafin yace "ni ma ban sani ba na dai ji Mama na faɗa ne".Kallon students ɗin Tajdeen ya
shiga yi kamar mai son tantance wani abu zuwa can ya nisa yace "toh mi yasa ba'a sallah nan
garin?"kallon ban gane ba Junior yayi ma shi hakan yasa Tajdeen miƙewa ya fara gwada mashi
yana Allahu Akbar sai yayi ruku'u,dariya Junior yayi yace "minene kuma wannan?"tsayawa
Tajdeen yayi yace "ita ce sallah a gida na ga Anya da Kakata suna yi kuma friday muna zuwa
masallacin juma'a mu yi ibada da bautar Ubangiji"da sauri Junior yace "oh yanzu na gane nan
kuma duk saturday ne muna zuwa gidan bautar Ubangij,tashi mu shiga aji lokacin komawa
yayi"nan suka miƙe suka shiga Madam ta cigaba koyar da su har sai ƙarfe ɗaya ta yi sannan
aka tashe su.


Tajdeen na ganin Dad ya ruga ya rungume shi cike da murna "ina abokin ka?"Dad ya tambaye
shi "yanzu Mamarsa ta zo ta tafi da shi" "ok!to ya karatu ka na dai ganewa ko?"Dad ya faɗa
yana jan shi zuwa mota,"eh sosai ma"nan Tajdeen ya shiga karanto ma Dad abinda aka koya
masu inda bai yi daidai ba sai Dad ya gyara ma shi har suka iso gida.A zaune father yake yana
duba jarida sai ji yayi Tajdeen ya faɗa jikinsa yana ihu, rungume shi yayi yana jin son jikan nasa

yace "i miss You Deen shine ka tafi makaranta ba ka je ka yi min sallama ba ko?"zaman shi ya
gyara kan cinyar father yace "ai lokacin kana bacci kuma Mom tace ka sha magani ne na barka
ka huta"dogon hancin shi ya ja yace "haka ne maza tashi ka cire uniform ka zo ka ci abinci
sannan ni ma ka koya min karatun da aka yi maku"da "toh"ya amsa ya nufi ɗakin Mom da gudu
jaka a hannu yace "Mom na dawooo"rungume shi ta yi sannan ta cire masa uniform ta yi masa
wanka ta saka masa kayan shan iska.Abinci ta fara bashi a baki sai da ya ƙoshi sannan ta fara
mashi tambayoyi kan karatu.



Haka rayuwa ta cigaba da tafiya kullum Dad ke kai Tajdeen school in lokacin tashi yayi kuma ya
ɗauko shi yayinda Mom ita ke koyar da shi lesson.
Kasancewar Tajdeen mai kaifin ƙwaƙwalwa tun dama can farko hakan yasa karatu bai bashi
wuya dan yana fahimta sosai,a gida kuma kullum SHENNEL ɗin turanci da French ya ke kallo
wannan ya ƙarfafa ma karatunsa inda a ƙarshen shekara ya zo na ɗaya cikin ajinsu.


Hutun shekara wato vacances da suka shiga shi ya ba Tajdeen damar zama kullum a gidan
wannan lokacin ne kuma ya ƙara fahimta lalle Raj na baƙin cikin ganin shi a gidan hakan yasa
bai sakewa a duk lokacin da Raj ke wurin.


Shirye-shiryen bikin Raj bai ɗauki lokaci ba aka yi biki inda suka tare a gidan father ,tun
shigowar Avani ba su taɓa shiri da Vani ba wato Mom duk dan saboda Tajdeen a cewar Raj
father ya ɗauki soyayya ya ɗorawa Deen yanzu ko sun haifi yara ba su da wani gurbi sosai cikin
zuciyarsa,da yake ita ma Avani sokuwa ce sai tabi ra'ayin mijinta.


Tajdeen na da shekara goma sha biyu ya samu matsalar memory sakamakon dukan kawo
wuƙar da Avani ta yi masa tana ta buga kansa ga katanga ita niyyata ta kashe shi kowa ya huta
dan shekara cikin ta uku kenan da auren su har yanzu ba ta samu ciki ba.
Duka ahalin gidan tsaye suka yi cirko-cirko tsakiyar asibiti tunda Dr yace Tajdeen ya samu
matsalar memory ba su tsaya jin ƙarin bayani ba duk suka ruɗe.
Dad ne ya shigo da mota a tsiyace ko wani ƙwaƙwaren parking bai yi ba ya fito,"mi ya samu
Deen ɗin?"shine tambayar da yayi yana kallon Mom cikin kuka ta fara yi mashi bayani "mu na
can gidan bauta ne sai Avani ta kira tace Deen ya faɗo daga sama ya mutu sai..sai...."kuka ne
ya ƙwace mata jijigata yayi cikin tashin hankali yace "sai mi?"ganin ba za ta yi magana ba ne
Rahul yace "sai muka dawo gida shine muka tarar da shi cikin jini,sai muka kawo shi asibiti nan
Dr ya tabbatar ma mu da ransa matsalar memory ce ya samu"da sauri Dad ya dafe saitin
zuciyarsa wace ke bugawa da ƙarfi tun lokacin da aka kira shi aka shaida masa.

Riƙe shi Rahul yayi yana ƙarƙafa masa gwiwa na su gode ma Allah tunda da ransa kuma kar su
fidda ran zai samu sauƙi.Ihu suka ji game da kuka Tajdeen na kiran sunan Mom ,da sauri suka
nufi room ɗin da aka kwantar da shi.
Ƙoƙarin tashi yake amman ya kasa,an naɗe kansa da bandeji sai ƙarin ruwan da aka maƙala
masa a hannu.Rungume shi Mom ta yi tana hawaye tare shafar kansa,cikin kuka yace "Mom mi
na yi ma Mom ƙarama..."kasa ƙarasawa yayi ya dafe kai sakamakon wani irin sarawa da yayi
mashi,jini ne ya shiga ɓulɓulo masa ta hanci daidai nan kuma Dr ya shigo ya nemi alfarmar su
bashi wuri ya duba shi.Waje suka fito suka tsaya bakin ƙafo,kujera father ya samu ya zauna dan
wani irin jiri ne ke ɗibar shi.Can wajen kamar rabin sa'a Dr ya fito murmushi kan fuskar shi yace
"madallah an yi sa'a bai rasa memrynsa duka ba zai iya tuna wasu abubuwa waɗanda suka
wuce kamar na 2ans/years haka,sannan za'a sallame shi nan da 3days tunda jinin da ya toshe
wani ɓangare na ƙwalwar shi ya samu ya fito sai dai wanda ba'a rasa ba"Dr ya faɗa yana mai
miƙa ma Ranvir takarda da za'a sawo magani dan ya ga shine kawai ke da nutsuwa,"zamu iya
shiga yanzu?"Dad ya tambaya kamar zai yi kuka "eh toh amman da dai kun bar shi ya huta"kai
kawai Dad ya ɗaga gabanin ya kalli Rahul yace "ka ɗauki father ka mayar da shi gida zuwa
gobe sai ku dawo"kai Rahul ya jinjina tare da cewa "Tom. amman in ana buƙatar wani abu
fah?bari na kai shi sai na dawo" "kar ka damu ga Ranvir nan ai".
Miƙewa father yayi tsaye sannan yace "Vani wuce mu tafi tare sai ki girka abinda zaku ci ki tawo
da shi"ya na gama faɗar haka yayi gaba,ba dan Mom ta so ba tabi bayan shi ya rage daga Dad
sai Ranvir a asibiti.



Wani gigitacen mari ne ya kifa mata wanda sai ta ga gilmawar wasu taurari kafin ta dawo daidai
ta kuma jin wani,cikin ɗaga murya ya ke mata masifa akan bugun Tajdeen da ta yi.Ya daga
hannu zai sake kwaɗa mata wani marin father yace "ya isa haka Rajjj!"saurin juyowa suka yi
dan ba su san da shigowar su father ba sai jin murya shi da suka yi. Takowa yayi har tsakiyar falon ya nuna Raj da yatsa yace "duk laifinka ne da ace baka nuna ma
Tajdeen tsana ba da matarka ba ta yi kuskuren taɓa lafiyar shi ba,amman ba komi duniya ce"ya
faɗa yana mai wucewa part ɗinsa Rahul ya take masa baya.
Kallon ido cikin ido Mom ta yi ma Avani ta goge ƴar ƙwallar da ta ciko idonta sannan ta wuce
kitchen,tsaye ta yi ta rasa mi ke mata daɗi ashe bugun Deen Avani tayi shine ta yi mata ƙarya
tace faɗowa yayi a zuci tace 'kenan shine binda Deen ke son faɗa min?'......




****Maraɗi


Sai bayan sallah Zuhur malam Nur ya shigo gida, kyakkyawar tarba ya samu gun amaryasa
Nazifa.Bayan sun gama cin abinci ne suka fara ɗan taɓa hira da Samira wacce ta zo ta taya
ƙawarta aiki,kallon malam Nur Nazifa ta yi tace "ɗazu anty Sappa ta shigo nan"dariya yaƙe yayi

ya na jin zuciyarsa na bugawa "toh Masha Allah mi ta kawo maki?" "hira mana dan ta jima nan
kafin ta koma part ɗinta" "to yayi kyau"shine abinda malam Nur ya faɗa "ya kamata ka tashi ka
dubo ta tunda ka shigo baka leƙa ba"cewar Nazifa ta na mai komawa kusa da Samira ,ba tare
da yace komi ba ya miƙe ya nufi part ɗin Sappa can ƙasar zuciyarsa kuma ya na jin daɗin
zuwan da ta kai ma sahibarsa.

A zaune ya tarar da ita ta na kallo tana ganin shi ta miƙe tana mai mashi barka da
zuwa,amsawa yayi yana mai tambayar ta yadda ta wuni ta amsa mashi da alhamdullah.
Ruwa masu sanyi ta ba shi kafin tace "ko na zuba maka abinci ?yanzu anty Nazifa ta aiko min
shi"cike da jin daɗin haka ya sakar mata murmushi yace "no na ƙoshi sai dai zuwa an jima"baki
ta turo tace "da fah an yi sallah la'asar ƴan damu za su zo gidan zai cika da jama'a ina zan
ganka balle na baka abinci" "toh sai ki aje har baƙin su tafi,yanzu dai miƙo min télé
commande/remote"miƙa mashi ta yi ta zauna kusan ƙafafunsa tana kallon yadda ya ke binciko
tashoshi.




Zuwa bayan la'asar aka fara gudanar da Damu kamar yadda al'adar Maraɗi take a duk sadda
aka kai amarya ga washegari ƴan uwa da abokan arziki sukan taru gidan amarya danginta su
bayar da kyaututtuka ga dangin ango.
Bayan an gama gudanar da bikin Damun,dangin Sappa suka rakota har ɗakin Nazifa suka
damƙata amana tare da yi masu nasiha.
Malam Nur ma da ya zo haka ya tara su ya gindiya masu sharaɗan zama gidansa tare da
doguwar nasiha mai ratsa jiki.


Sai da malam Nur yayi sati guda cur a ɗakin Nazifa sannan ya koma ɓangaren Sappa ita ma
yayi sati guda,daga nan suka yi rabon kwana biyu-biyu.
Tun daga lokacin bikinsu babu abinda ya haɗa su na rashin jituwa, Sappa na bin Nazifa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login