Showing 3001 words to 6000 words out of 51592 words

Chapter 2 - Shaukin So Book Compelet Mrs Sadauki

yi ganin Samira da malam Jabeer sai hirar su suke cikin kwanciyar hankali,"ya dai
kun gama karatun?"cewar Samira tana kallon su "a'a ba mu gama ba"Nazifa ta bata amsa tana
hararenta.
Dariya malam Jabeer yayi yace "haba abun har da baƙar magana?"



"Eh ai ku kuka fara"malam Nur ya basa amsa nan dai suka yi sallama suka yo gida.



Tun daga wannan lokacin wata shaƙuwa mai game da ƙauna ta shiga tsakanin malam Nur da
Nazifa,Samira kuma da malam Jabeer.Wannan alaƙa ita ta ƙara danƙon abotar Nazifa da
Samira sai ya zamana ko a gida kullum suna tare don Nazifa ba ta da waya da ta Samira ce
take waya ita da malam Nur,babu yadda bai yi da ita ba akan ya saya mata waya amma fafur ta
ƙi don ta san Ɗalhat zai iya dukan ta.



Cikin canjin da ya samu na nishaɗi ya kalli mahaifiyar tasa yace "Maman ki shirya kin kusa
samun ƴa "yayi maganar yana mai sunne kai alamun jin kunya,cike da murna Maman tace "kaiiii
haba?Masha Allah yaushe za a kawo min ita na gan ta?"ƙeya ya ɗan sosai gafin yace "nan ba
da jimawa ba ke dai ki taya ni da addu'a"da sauri Maman tace "ai kullum cikin yin ta muke sai
dai mu ƙara".



Tsuki Sappa ta ja tana zumɓuro baki gaba tace "haba Mama sai kace dai an yi maki albishirin
kujerar Makka sai wani daɗi kike ji mtwsss"baki buɗe Maman ke kallonta kafin tace "yanzu
Sappa wannan ba abun murna ba ne? Tun yaushe nake jiran wannan ranar ta zo kuma
shikenan ba zan yi murna ba?"ƙara turo baki Sappa ta yi tace "to ai sai ki bari ki ga yarinyar wa

ya sani ma ko ƴar talakawa ce..."wata irin tsawa ya daka mata jin ta taɓa martaba ruhinsa,da
sauri Sappa ta miƙe ta nufi ɗaki don ta san ba ƙaramin aikinsa ba ne ya ƙara naɗa mata kashi
dama har yanzu ba ta warke da bugun da yayi masu ita da Balkis ba.


Haƙuri Maman ta shiga ba shi tana cewa "dan Allah ka barta ƙurciya ce"

Zaunawa yayi yace "ba wata ƙurciya iskanci ne kawai haka ranar nan ta yi min wata banza
wasiƙa ko yaushe aka haife ta ma da har za ta fara zancen soyayya"



"Soyayya???ita da wa?"Maman ta tambaya shiru yayi jin yayi suɓutar baki dan ko kaɗan bai so
Maman ta gane da Sappa na sonsa,ganin ta ƙure shi da ido tana jiran amsa ya miƙe ya shiga
wayar ƙarya.


Jikin Maman ne yayi sanyi ‘kar dai a ce Sappa son Ustaz take? Shine ta kasa faɗa min ta je ta
faɗa masa’Mama ke maganar zuciya kafin ta miƙe ta nufi ɗakinsu Balkis,kwance ta tarar da ita
tana kuka "ashhha! Yanzu Sappa kuka ne kike dama?me yasa tun farko ba ki gaya min kina
son shi ba shine za ki wani shige ɗaki kina kuka?Maza tashi ki goge hawayenki gida ba ta ƙoshi
ba ai ba za a baiwa dawa ba"cikin jin daɗi Sappa ta yi saurin miƙewa tana murna ta shiga toilet.








***Yamai


Wata tsohuwa ce zaune bisa tabarma sai mulmula dawo (fura) take gefe guda kuma wani ɗan
yaro ne da ba zai wuce shekara shidda zuwa bakwai ba sai tankaɗa gari yake yana barbaɗa ma
furar da take dunƙulewa ƴan mili-mili daidai na dala biyae.
Cikin gajiya da aikin yace "Kaka ki tashi mu tafi in mun je can sai ki ƙarasa mulmulewa"cike da
kulawa ƴar tsohuwar tace "ah Tujani saurin me kake haka ne? Ka fi kowa sanin duk lokacin da
za mu kaiwa gida dole a jira mu don furata ta tafi ta kowa duk kasuwar garin nan,ungo je ka
karɓo ƙanƙara "ta basa ƙaton tarmus amsa yayi ya fice da gudu ba jimawa ya dawo ya tarar har
ta jera kayan tallar.

Ɗan bokiti da nonon shanu ya ɗauka yayin da Kaka ta ɗauki ƙatuwar ƙwarya dawonta ta aza a
kai,tarmus ɗin ƙanƙara kuma suka yi kama-kama.
Har sai da suka kai bakin ƙofa Kaka tace "mun tafi sai mun dawo"ƴar ƙwalla baƙin ciki Saude ta
goge sannan tace "Allah ya tsare ya bada kasuwa, *Tajdeen* ka kula da kanka banda
yawo"tana gama faɗi ta ɗauki *Haleematu* ta ja hannun *Ismaël* suka shige ɗaki.


Wata uwar ashar Kaka ta aika mata tace "yau na ga ƴar baƙin ciki ni da jikana ba ni da ikon
tafiya talla da shi? To ta Allah ba taki ba mai farar ƙafa tun da Haliru ya auro ki ya tsiyace
abincin da zaku ci ma sai na je na nemo maku dan talauci amman da yake butulu ce ke shine
kike jin haushi don Tijani na taya ni talla..."cikin gajiya Tajdeen yace "Kaka mu tafi kika tsaya sai
surutu kike sai codtumer ɗinmu sun yi fushi sun fasa saye"dariya Kaka ta yi tace "mu je ɗan
jikallena ai uwar taku ce ta fiya mugunta"cikin jin haushi yace "ban so kar ki sake zagin Anya kin
ga ba ta yi maki komai ba"




"To ni mz na yi mata da take hassadata?"


"Ita ba hassadar ki take ba kawai ba ta so ina zuwa talla so take na yi karatu na zama
likita"ƙyaci Kaka ta yi suka ci gaba da tafiya har suka iso kasuwa dama babu wani nisa.


Tun kafin su zauna costomer suka fara zuwa,cikin ɗan ƙanƙanen lokaci Kaka ta fara ciniki dan
har ta kusa sayarwa sai habaici take yi ma sauran ƴan fura-fura sanin hali yasa babu wacce ta
tankata.


Wani mai mota ne ya parker kusan kullum sai ya zo sayen fura wani bi anan ake dama masa ya
sha wata rana kuma ya tafi da kayarsa.
Washe baki Kaka ta yi tana amsa sallamar da yayi dan ba ƙaramin burge ta mutumen yake ba
saboda in ya sayi fura sai yace ta riƙe canji ta sayawa jikanta wani abu.Shi kansa Tajdeen sosai
yake son mutumen wanda yace sunan shi Omar.

2000 ya bada yace a dama masa fura asa madara da suga,fura Kaka ta shiga damawa yayin
da Tajdeen ya tafi sawo madara da suga.Bayan ta gama ta miƙa ma Tajdeen ya kai masa cikin
mota,ɗaya gefen ya buɗe masa sannan ya karɓi roba da aka zuba furar.
Ƙatuwar wayarsa ya ba Tajdeen yana game sai dariya yake,sai da ya sha ya ƙoshi ya bashi
sauran ya shanye.

Yamma lis su Kaka suka shigo,sannu da zuwa Baffa yayi mata ta amsa tana mai cewa "yawwa
ga cefanen gobe nan shinkafa da wake za ayi mana da rana da dare kuma ayi tuwon laushi,
tunda ni ke kawo cefane ai sai abinda nake so"Baffa dai bai ce komai ba sai ƙwala wa Saude
kira da yayi.

"Sannu da zuwa"Saude ta faɗa tana mai sunkuyar da kai "riƙe abarki bayan kin gama ci min
mutumci ɗazu shine yanzu kike wani duƙe kai dan munafurci to ban so" kallon Kaka Baffa yayi
yace "haba mama gaishe ki ne fah ta yi ai sai ki amsa kafin ki ɗora da faɗan"


"Na ƙi na amsa ɗin ina ce saboda Tijani ta yi min rashin kunya "cewar Kaka tana hararen
Saude,gefen Tajdeen ta zauna ta shiga duba kayan wasar da Omar ya saya masa"Tijani
wannan karon dai babu wanda zaka bai wa kayanka don ba zan bari ka rarraba su ga waɗanda
uwarsu sam ba ta da mutumci"


Ɓata rai Tajdeen yayi yace "ai dai ƙannaina ne kuma nace maki ki bar zagin Anya (uwa) ban
so"yadda yayi kicin-kicin da fuska yasa Kaka dungure masa kai tace "na ji ɗan gaban goshi
uwar taka ce sai da haka".



Washe gari ta kama Monday kuma rana ce ta komawa school,tun asubah farin Anya ta yi ma
Tajdeen wanka dan yau ne za a rubuta sunansa cikin jerin ɗalibai.
Murna fal ransa ganin an saka masa
sabbin kaya kuma za a kai shi makaranta,duban mahaifiyarsayayi wacce ita ma kallo guda za
ka yi mata ka gane tana farin cikin haka a zuciyarta kuma murna take Tajdeen zai rabu da talla
zai fara karatu



Kaka ce ta leƙo tana goge ƙwalla tace "dama ni tun tuni na san kin shanye Baffan yara,dan
tsabar makirci shine kika saka shi ɗaki kika kitsa masa a kai Tijani makaranta dan baƙin ciki
yiiii"Kaka ta ƙarashe tana rusa kuka da sauri Baffa ya shigo kafin ya kai da magana Kaka tace
"in dai na isa da kai kar ka saki ka kai Tijani makaranta a bari har wata shekara duka-duka nawa
yake?"da "toh" Baffa ya amsa yana ficewa daga gidan rai jagule dan sam mahaifiyarsa ba ta
gyara masa kullum sai ta yi masa katsalandan cikin lamurran iyalansa.


Hannun Tajdeen Kaka ta ja suka nufi ɗakinta nan ta yi ta kwantar masa da hankali har da bashi

kuɗi abu ga yaro dandanan ya manta da wani son zuwa makaranta.



Lokacin zuwa talla na yi Kaka ta ɗauki ƙwarya dawo Tajdeen bokin nono kamar kullum suka nufi
kasuwa.
Can nesa da inda Kaka ke saida fura Omar yayi parking ya fito waya maƙale da kunnensa ya
jingina a jikin mota,da hannu yayi ma Tajdeen alama ya zo wanda tun tsayawar motar ya ƙure
shi da ido da sauri ya miƙe ya nufe shi da murna.
Kuɗin furar da zai sha ya bashi da gudu ya kai ma Kaka nan ta bashi kuɗi ya sawo madara.
Ganin ya tafi yasa Omar shigewa mota yabi bayan shi, Tajdeen na tsaka da tafiya yaji oder
tsayawa yayi da nufin mai motar ya wuce sai ya ga Omar ne.Seat ɗin gaba ya buɗe masa ya
shige yana murna shi kuma Omar ya danna ma mota huta ya fara gudu babu ƙaƙautawa............
[10/03 15:05] MRS SADAUKI: *SHAUƘIN SO*


```LoVe story```


By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI✍️}


*FCWA*☀️

________________________


Page 5-6


Cikin gajiya da gudun da suke Tajdeen ya dube shi yace "Uncle wai ina ne za mu je? Ka ga fah
mu na wuce shaguna(kanti)inda ake sayar da madara"murmushi Omar yayi yace "kar ka damu
wannan tafi ko wace kyau kuma ina son sawowa dayawa ne ta yadda kai ma kullum za ka rinƙa
shan guda biyar a wuni ko ba ka so?"baki Tajdeen ya washe cike da murna yace "ina so mana
amman ita Kaka ba za ka saya mata ba?"
"Zan saya mata mana har da duk ƴan gidanku"ya baa amsa,shiru Tajdeen yayi yana kallon
hanya yadda garin Niamey ya tsaru kai kace ƙasar waje ne.
Barci ne ya kwashe Tajdeen tun yana sa ran tsayawa har ya gaji yayi lamo,yafi minti talatin
yana barci sannan ya farka amman abun mamaki sai ya ga har yanzu motar gudu take kuma
sun baro cikin gari har sun shigo daji.
Cikin alamun tsoro ya kalli Omar yayi narai-narai da ido yace "ka mayar da ni wurin Kaka "wani

banzan kallo Omar ya watsa masa wanda ya sa shi fashewa da kuka.Bai hana shi ba hakan
yasa ya cigaba da rera shi yana kiran sunan Kaka,wata uwar tsawa ya daka ma shi yace "yi min
shiru ko na jefar da kai waje Zaki ya cinyen naman jikinka"tsit Tajdeen yayi ya haɗiye sauran
kukan sai hawaye kawai ke masa zuba. Ana kiran sallah la'asar suka shiga Dosso,a wani ɗan ƙaramin gida yayi horn aka buɗe
mashi.Hannun Tajdeen ya ja suka nufi ciki bayan ya parker mota,a falo suka zauna bayan wani
lokaci sai ga wani Alhaji ya fito.Gaishe shi yayi cikin ladabi ya amsa yana kallon Tajdeen wanda
idon shi suka ɗan faɗa saboda doguwar tafiya da suka yi. "Mi sunan ka?"shine abinda alhajin ya tambaya,shiru yayi ya ƙi bashi amsa dan izuwa yanzu
duk da ya ke yaro ya san ba sayen madara ba ne ya kawo su nan.


Wanka Omar ya shiga yayi kafin a gabatar ma shi da abinci,cikin plate ya zuba ma Tajdeen ya
karɓa ya fara ci dan yunwa ya ke ji sosai.
Bayan sun gama ne ya karɓi saƙo gun alhajin sannan ya ja hannun Tajdeen suka nufi inda ya
ajiye mota,titi ya hau nan ma ya shiga ba mota huta bai tsaya ba sai da dare yayi ya fiddo abinci
suka ci suka kwana a cikin motar da gari ya waye kuma suka cigaba da tafiya.
Daidai maraba da baƙi ta maradi suka tsaya ya buga waya ba jimawa wani ya zo ya karɓi motar
da suka tawo da ita,taxi ya tara aka ida shigowa da su cikin gari daga nan suka nufi tashar
mota.


Motoci duk sun cika,har zai juya yaji wani mutum na waya yana cewa Jos zai tafi ai da sauri ya
ƙarasa gun shi ya nemi alfarma in babu damuwa su tafi tare in ya so shi zai bada na mai,ba tare
da wata matsala ba mutumen ya yarda.
Ƙatuwar mota ce irin wanda ake ma lodi,kujerar kusa da driver ya zauna tare da ɗora Tajdeen
saman cinyar shi.
Sai da suka kwan suka wuni amman ko ƙamshi Jos ba su ji ba,ɓangare guda kuma har an saba
tsakanin Omar da Jean wanda ya kasance bagwari.


Suna tsaka da tafiya Tajdeen ya aza kuka yunwa ya ke ji,Omar ne ya sauka nemo mashi abinci
sai aka yi rashin sa'a a yayi hatsari bisa hanya.Tun Jean yana jira har ya fidda tsammani ,kuka
Tajdeen ya fashe da shi yana cewa "dan Allah ka kai ni wurin Kaka ni ban son nan"cikin
gurɓataciyar Hausar shi yace "wacece Kaka?ko wancan da ya tafi?"kai Tajdeen ya girgiza
mashi ya shiga yi mashi bayani,zufa ce ta karye ma Jean dan ko babu shakka ya gano sato shi
ne Omar yayi.
Cikin son kwantar mashi da hankali ya bashi biscuit da yi mashi alƙawarin zai kai shi wajen
Kaka,cike da murna Tajdeen ya fara cin biscuit ɗin shi kuma Jean ya cigaba da tuƙi har suka isa
Jos.

Wani tangamemen gida suka tsaya,tun shigowar shi mutanen gidan uwanda duk maza ne suka
fito ko wane murmushi kan fuskar shi.
Tsaye Tajdeen yayi ya na kallon jama'ar uwanda duk kusan kamar su guda haka ma
tsayi,hannun shi Jean ya kama suka ƙarasa.
Fuskar shi dattijon cikin su ya shafa yana mai ɗan rage tsayin shi yace "ina ka samo wannan
kyakyawan?"ya faɗa yana kallon Jean a nan tsaye yayi masu bayani,cike da tausayin Tajdeen
duk suka shiga taɓa kan shi suna mashi murmushi "mi sunan ka ?"dattijon ya tambaya lokacin
da suke shigowa babban falon gidan "Tajdeen"ya ba shi amsa "to daga yau za mu dinga kiran
ka da Deen kaji ɗan kyakyawan jikana"kai Tajdeen ya ɗaga yana murmushi wanda shi kan shi
bai san na minene ba....



****Niamey


Wajen minti talatin Kaka na jiran Tajdeen shiru,inda Omar ya tsaya da mota ta kalla da niyyar yi
mashi magana wayam babu shi babu motai maimakon hankalin Kaka ya tashi sai cewa tayi "ka
ga ɗan albarka mai tunani ya ga Tijani ya daɗe shine ya bi min sawun shi"ta fada tana mai rufe
furar da ta dama ma Omar murfi.Can wasu mitinan ta riƙe haɓa tace "yau ni na ga gantalale
daga bin sawun yaro ba kai babu shi balle daɗa madarar"ta kusa da ita ce ta tambaya "ni kam
Delu lafiya kike ta surutu ke ɗaya?"
"To ba doli nayi surutu ba tun ɗazu Tijani ya tafi sanye madara har yanzu bai dawo ba kuma shi
ma Umarun haka"ido ta fiddo waje tace "kar dai kice mai motar da ya ke zuwa nan sayan fura?"
"Eh shi fah,bari ki ga na tai na dubo su da kaina ƙila suna can shago(kanti)suna sayen kayan
maƙulashe sun bar ni nan da tashi zuwan kan fura"cewar Kaka tana mai tashi ta tafi gun mai
madarar da kullum Tajdeen ke sawowa,ba ta jima ba ta dawo hankali tashe tana gugar ƙwalla
da haɓar zane "ka rufa min asiri Umaru ka dawo min da jikana,oh waini ni Delu"kafin wani lokaci
wurin kancame kowa sai tofa albarkacin bakin shi ya ke dayawan mutane gani suke son banzar
Kaka ne ya jawo haka yayinda Ɗan Ladi ke ta ƙara maimaitawa ya ga lokacin da Omar ya saka
Tajdeen a mota ya wuce a guje.


Shaƙe shi Kaka tayi tace sai ya fito mata da jika ai da shi aka gama baki,dakyal aka taɓe shi ga
hannunta.Zaman ƴan bori tayi ta fasa ihu "wayooo ni Delu mi zan ce ma Haliru in na koma
gida?ubangi ma'aikin Allah ya tsine ma Umaru Allah gama ka da bala'in duniya, innalillahi ileyhi
raji'un jama'a ku cece ni ku karɓo min jikana"sosai Kaka ke kuka,ganin haka aka tsayar da mai
taxi aka sakata tare da kayan sana'ar ta sai wata da ta shiga dan kaita.



A tsakar gida suka tarar da Anya hannunta dafe a saitin zuciya,Haleematu na kuka amman ta
kasa ɗaukar ta saboda lugude da faɗuwa da gabanta ya ke.Tun kafin su shigo kukan Kaka yayi

masu sallama,da azama ta miƙe ta nufi waje kiciɓis suka yi da Kaka wace ake kokawa saka ta
gida amman fafur tace ba zata shiga ba doli sai da Tujani.


"Ina Tajdeen?"Anya ta tambaya murya na rawa zuciyarta na tsinkewa,"ya tafi da Tujanina ya
tsere da shi"Kaka ta faɗa cikin kuka kafin su an kare sai ji suka Anya ta yanke jiki ta faɗi.


Kukan Kaka ne ya ƙaru tana mai kwance kwagirin ƙugunta ta fiddo wayata tana cewa "na shiga
uku ungo kira min Haliru"mai taxi ya amsa ya shiga répertoire nan ya danna ma Baffa kira.Ba
jimawa sai gashi cikin tashin hankali,ciciɓar Anya yayi ya saka a taxi suka nufi asibiti Kaka kuwa
sai kuka ta ke har roƙon likita tayi ya bata gado yayi mata allura barci ko taji sanyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login