Showing 9001 words to 12000 words out of 51592 words
Chapter 4 - Shaukin So Book Compelet Mrs Sadauki
ta fito
waje inda Ustaz ke jiran ta.
Sai da suka gaisa da Samira kafin su wuce gidan Maman,a falo duk suka tarar da ƴan gidan
ana zaman jiran Nazifa.Malam Nur ne yayi sallama yana gaba ta na biye da shi a baya,a ƙasa
ta zube tana mai kwasar gaisuwa cikin sakin fuska Maman ke amsawa kafin Balkis tace "ina
wuni anty amarya"ɗagowa Nazifa ta yi ta kalli inda ta ji murya ta sakar mata murmushi sannan
ta amsa akan idonta Balkis ke zungurar Sappa wacce sai cika take ta na batsewa,dakyar tace
"sannu"shi ma don ta ga irin kallon da Ustaz ke jifarta da shi ne,gaban Nazifa ne ya faɗi cikin
sanyi da ta ji duk jikinta ya ɗauka ta amsa ma Sappa kafin su tsaya ƴar kallon-kallon.Wata irin
muguwar tsana ce Nazifa ta hango cikin idon Sappa,cikin zuciyata kuma take tambayar kanta
'to ita kuma wannan wace ce?mi nayi mata ne daga gani na take hararena? ...'ba ta tsinke da
lamarin Sappa ba sai da ta ji ta ja tsuki ƙasa-ƙasa tare da cewa "baƙauya kawai"kallon Sappa
Maman ta yi dan ta ji sarai abinda tace.
"Sappa tashi ki ɗauko ma antynki ruwa mana,kun wani sa ta a gaba ku na kallo haka ake tarban
baƙi?"Maman ta faɗa cikin bada umarni,gunguni Sappa ta tafi ta na yi ta shiga kitchen Balkis ta
bi bayanta.
"Anty Sappa mi za ki yi da ruwan pampo ?ba dai amayar ce za ki kai ma ba?"Balkis ta faɗa
lokacin da ta shigo ta tarar da Sappa na zuba ruwan pampo cikin moɗar ƙarfe,yatsina fuska tayi
tace "eh mana ai su ta saba sha a gidansu ko ba ki ga ƴar talakawa ba ce"cikin rashin jin daɗin
zancenta Balkis tace "a haka kuma Ustaz ke son abar shi"ta na gama faɗi ta ɗauki jus ɗin da ita
ta haɗa da kanta ta fita,ƙanƙara ta zuba cikin kofi sannan ta tsiyaya lemun ta miƙa ma Nazifa
sannan ta ajiye sauran kusa da ita ko da buƙatar in ta ƙara.
"Na gode"Nazifa ta faɗa tana mai yin Bismillah ta ɗan kurɓi lemun cike da kunya, Ustaz na
kallonta ya na jin son ta na ƙara ratsa shi ya lura a takure take hakan yasa ta kasa cin fruits ɗin
da Balkis ta kawo daga baya.
Zamewa yayi daga bisa salon ya zauna ƙasan capet,trayn ya jawo gabansa ya ɗauki ayaba ya
ɓare tare da nufar bakinta "buɗe bakinki na ciyar da ke tunda kunya kike ji"ɗagowa ta yi ta kalle
shi sannan ta juya inda Balkis ke zauna Maman kuwa tuni ta bar gun, ɗan turo baki ta yi tare da
buɗe shi za ta yi magana kawai ya tura mata ayabar a baki ba ta da wani zaɓi hakan yasa ta
ɗan guntsira tana murmushi.Taratseeee kofin glas ɗin da ke hannun Sappa ya sulɓe,dukkansu
kallonta suka yi banda Nazifa da ta sunne kai zuciyarta na bugawa das-das.
Wata uwar tsawa Ustaz ya daka mata "keee!wane irin hauka ne wannan?so kike ki firgita min
mata ko miye ?maza ɗauko tsintsiya ki kwashe shi sannan ki goge wurin"wasu zafafan hawaye
suka karye ma Sappa ta ɗauko salade de fruits ne dan ta nuna ma Nazifa isa da su sun san
yadda ake shan shi kuma sun saba sai ga shi kogo ya juye da mujiya.Sanin halinsa ya sa ta yi
saurin tattare glas ɗin da ya fafashe ta kwashe sannan ta goge wajen tsaf,cikin kuka ta nufi part
ɗinsu.
Ajiyar zuciya Balkis ta sauke kafin tace "Allah yaye maki wannan baƙin halin"kusa da Nazifa ta
zauna tace "antynmu dan Allah ki yi haƙuri ki ci duk wannan abun saboda ke fah na yi shi"ta
faɗa tana mai sake jawo wani tray mai ɗauke da abinci,saving nata yi amman fafur Nazifa tace
sai dai Balkis ta sa hannu su ci tare. Kallon malam Nur Balkis ta yi sai ya jinjina mata kai hakan ya sa suka fara cin abinci shi kuma
ya nufi ɗakin Baba,bai fito ba sai da ya kwatanci sun kamalla sannan suka fito shi da
Baba.Gaishe shi ta yi tamkar uban da ya haife ta cikin kulawa Baba ke amsawa ya na tambayar
ta ƴan gida da kuma karatu.
Har Nazifa ta tashi tafiya amman Sappa ba ta sake fitowa ba,goma ta arziki Maman da Baba su
ka yi mata Ita kuwa sai zuba godiya take.Kafin Nur ya sauke ta gida sai da ya biya Kalla Transa
Mall yayi mata sayayya ƴan abubuwan da ba za a rasa ba.
Ganin irin hidimar da aka yiwa Nazifa ya sa Inna jin sanyi a ranta da tunanin ko ba ta da rai
Nazifa ba za tayi kukan maraici ba dan a yadda Nazifa ta tsaya ta na yabon Maman da Balkis
abun sai Masha Allah.
Samira da Rakiya sai buɗa kayan su ke suna fesa turarurukan,bayan sun gama gani ne ta ba
kowa rabon shi Inna dai sabulu kawai ta amsa ta ajiye ma Ɗalhat.
"Tashi ki raka ni gida zan wuce"Samira ta faɗa ta na mai ɗaukar ledar kayanta,hijab Nazifa ta
saka suka kamo hanya a nan ne Nazifa ta shiga ba Samira almarar Sappa ta ƙare da cewa "wlh
har cikin raina nake jin tsoron ta dan da alamu irin mugun kallon nan da take min ba ƙaramar
tsanata take ji ba"
Numfashi Samira ta ja tace "to Allah kyauta sauƙin ta dai ba ƙanwar malam Nur ba ce da kin
shiga uku kin san ƴan uwan miji in ba su son ka akwai matsala"
"Eh haka ne sosai, amman dai su na da alaƙa dan da alamu a gidan take zaune inda ma na ji
sauƙin abun da yake tana tsoron Noori"cewar Nazifa ta na mai tsayawa dan sun ɗan yi nisa da
gidansu alamu kuma sun nuna daga nan za su rabuwa,sallama su ka yi kowa ya tafi gida.
Da dadare bayan sallah isha'i malam Nur ya kirata a waya suka sha hira su ta soyayya wacce
rabin ta duk akan yadda bikinsu zai kasance ne da irin rayuwa da za suyi bayan aure.
Har sun yi sallama Nazifa ta yi saurin tsayar da shi tace "um..Ni kam Noori wannan wace ce
wadda na gani gidanku?"duk da ya gane wadda take nufi amman ya basar yace "wace fah daga
ciki?"fuska ta ɓata kamar ya na ganinta tace "ba Balkis ba ɗayar"
"Wai Sappa kike nufi?" "Um ita"ta ba shi amsa "kishiyarki ce"ya samu bakinsada furtawa,shiru
ta yi kamar ba ta ji ba sai da ya sake maimaita mata daga ƙarshe yace zai ƙara yi mata bayani
daga baya ya kashe wayar.A daren ranar nan juyi Nazifa ta aniya yi ba ta rumtsa ba,kalmar
kishiyarta ce ta tsaya mata a rai.
Washe gari ta kama asabar ranar zuwa makaranta tun bayan kawo kuɗin aurenta ba ta sake
zuwa ba sai yau da malam Nur ya bata umarnin zuwa.
Lati ta yi yau kasancewar ta yi ranar tashi,tun da ta shigo ƴan ajin ake kallonta ana ƙus-ƙus-ƙus
ita dai ba ta kula su ba gefen Samira ta zauna babu jimawa malam ya shigo.
Har zai fara karatu wata tace "malam yau ba a bulalar lati ne ?"duk ɗaliban kallonta su ka
yi,malam ya so yayi kamar bai ji ta ba amman kar ace yayi son kai saboda Nazifa ta zo late
kuma ya san saboda a ga yadda zai yi ne suka kitsa haka.
"Duk wacce ta san ta zo lati ta tashi tsaye"shine abinda malam Nur yace yana mai buɗe coffre
ya ɗauko dorinarsa,Allah ya isa suka fara jama Rabi'at kafin su fara miƙewa tsaye.
"Dan Allah ki tashi ki ba mara Ɗa kunya saboda ke ne suka tuna ma malam zancen bulalar lati
amman an fi sati rabon da ayi ta"cewar Samira ta na mai jimƙe hannun Nazifa , murmushi ta
sakar ma ƙawarta ta kafin ta mike tsaye.
Bulala goma-goma malam Nur ya shiga zabga ma Ɗaliban har ya zo kan Nazifa,daure zuciya
yayi ya shiga tsula mata bulala duk in ya shauɗa sai ta rumtse ido dan zafi har aka gama mata.
Zaunawa suka yi suna jinyar jikinsu dan duk juriyarka in malam Nur ya zane ka sai ka ji
jiki,karatu suka fara yi kamar kullum har lokacin shan iska yayi.
"Naziii..."shine abinda malam Nur ya faɗa ganin ta nufi ƙofar fita,dawowa ta yi tana turo
baki.Ajiyar zuciya ya sauke tare da furzar da huci yace "sorry"ɗagowa tayi tace "da aka yi mi fah
" "da dorina ta zane ki"baki ta sake turowa tace "ai kai ka sanya ta"ta a idasa maganar kamar za
tayi kuka "nooo!kar ki yi kuka zan ko hukunta ta dan ba za ta sake kwana duniya ba ƙonata zan
yi cikin wuta tunda har ta taɓa fatar amarya Nur"dariya Nazifa ta yi har da ƙyarƙyatawa nan dai
su ka fara karatun litattafai kamar kullum.
Bayan an dawo daga shan iska maimakon a cigaba da karatu sai malam Nur ya ɗauki rigar
rashin mutumci ya saka,nan ya shiga yi ma ɗaliban da suka sa ya ɗaki Nazifa masifa inda ya ke
cewa "ku a tunaninku har za ku iya yi ma malam Nur wani ƙulli wanda ba zai gane ba? Ribar mi
kuka ci da na daki Naziii?ke kuma da kika fi su fitsara sai suka turo ki ki min tuni da bulalar lati
ko?"cikin son kare kai suka fara rantse-rantse shi kuma ya katse su da cewa "mi yasa kwanakin
baya baku tunan min ba sai na yau? Duk ƙiyayar da kuke nuna mata na sani ba tun yau ba dan
haka zan ba kowacen ku hutun sati guda duk wacce ta san da sa hannunta ciki ta tashi ta
fita"ya na gama rufe baki munafukan duk suka fita waje.
Wannan abun da malam Nur yayi shi ya wanke zuciyar Nazifa da duk wani ƙunci har ta mance
da maganar wata Sappa.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya har aka zo yau saura kwana biyu biki,duk ɓangaren uku
shirye-shirye kawai su ke Sappa ta koma gidansu tun tuni mahaifiyarta sai ƙara gyara ɗiyarta
take.Inna ma ba a barta a baya ba sosai ta ke kula da Nazifa wanda hakan ya sa ta ƙara haske
ta yi wani fresh sai ƙyalli take da santsi.
Darul Mar'a malam Nur ya biya kuɗi tun daga gyaran jiki,farce,gashi da lalle,sosai ta yi kyau
kana ganinta ka ga cikakkiyar amarya ƙawayenta sai ɗaukar ta hoto suke.
Ranar ɗaurin aure duban jama'a suka shaida auren Nuradeen Ali Ɗan Masani da Nazifa Sa'id
Lawan da kuma Sappa Hamisu Kabeer,mutane da dama sai mamaki su ke jin mutum guda ya
auri mata biyu duk ɗaya rana.Ɗalhat da shi ya bayar da auren ƙanwarsa sosai ya girgiza jin ba
ita ɗaya ba ce,a zuci ya ke tunani "ƙila shiyasa Inna tace min zan ji wani a wajen ɗaurin auren
amman kar na tada hankalina,to ko shine abinda malam Nur ya zo ya gaya ma Inna a
jiya?"ganin dai bai dai amsar tambayar ya ƙarasa wajen baƙinsa su ka nufi gida kasancewar
ɗaurin auren masallaci ne.
Sosai Nazifa ke kuka wanda ta rasa na miye na farin ciki ko akasin haka,yau dai ta zama
NazNur.......
Please share
[11/03 12:31] MRS SADAUKI: *SHAUƘIN SO*
```LoVe story```
By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI✍️}
*FCWA*☀️
________________________
Page 11-12
An yi walimar biki ta kowanne bangare,zuwa dare kuma aka miƙa su gidan mijinsu.
Danƙareren gida ne na musamman mai part biyu,ko wace ciki uku da falo ne aka yi mata.
Nazifa banda kuka babu abinda take ta wani riƙe Samira tace babu inda za ta,a na haka sai ga
sallamar ango da malam Jabeer.
"Yawwa ga angonki nan ai yanzu sai ki sake ni"cewar Samira ta na kallon nata sahibin,sallama
suka yi masu da fatan alkairi na farin ciki mai ɗorewa kafin su wuce.
Murmushi mai ɗan sauti malam Nur yayi wanda har sai da ta ji shi cikin ƙahon zuciyarta,mayafin
da ta luluɓe ya ɗan ɗage nan kyakkyawar fuskarta ta bayyana wacce ta yi shaɓe-shaɓe da
hawaye,wani murmushin ya ƙara yi yana jin wani irin SHAUƘIN SO na ɗibarsa .
"Amincin Allah ya tabbata ga Shalele ƴar gatan malam Nur, Mama su Ayman da Laila"Nazifa
dai tun da ya fara magana ba ta ɗago ba sai da ya zo ƙarshen maganar ne ta yi saurin rufe
fuska tana dariya.
"Tashi ki yi alwala ki rama sallah da ba ki yi ba,ina zuwa"ya faɗa tare da fita ita kuma ta miƙe ta
shiga toilet ta ɗauro alwala ta gabatar da sallah magrib da isha'i wanda ba ta samu ta yi ba
saboda ɗawaniya biki.
Malam Nur ledodin da suka bari a falo ya ɗauki biyu ya fita zuwa ɓangaren Sappa wacce ta cika
ta yi fam kamar za ta fashe dan tun lokacin da suka shigo shi da malam Jabeer akan idonta.
Tura ƙofa yayi tare da yin sallama,can tsakiyar gado ya tsinkayota ta sha kwalliya kamar wata
aljana.Ido cikin ido su ke kallon juna,babu abinda malam Nur ya tsana irin wannan kwalliyar mai
sauya wa mutum kamanni,baki ta turo ganin yayi tsaye bakin ƙofa bai zo gun ta ba.
"Wa'aleykum salam"ta faɗa cikin jin haushi taɓe baki malam Nur yayi kafin ya ajiye mata ledar
gasasar kaza da ta fruits da jus,yace "sai da safe in Allah ya tashe mu ki zo ki kulle ƙofa"wani
irin dirowa Sappa ta yi daga kan gado ta na mai cewa "kai kuma ina za ka je?"banza yayi da ita
ya fice. Zuciyarta na zafi ta je ta rufe ƙofa ta dawo ta haɗe kai da gwiwa tana rusar kuka.
Malam Nur sai da yayi wanka a ɗakinsa tare da alwala sannan ya tafi gun amarya,a zaune ya
tarar da ita tana ƙare ma ɗakin kallo ba laifi Inna ta fidda kuɗi an yi mata katakai masu kyau
daidai ƙarfinsu.Gyaran murya yayi ta juyo ta na kallon shi sai kuma ta maida kai ƙasa tana wasa
da zoben hannunta,"amarsu a tashi mu yi sallah godiya ko?"ya faɗa lokacin da ya zo dab da
ita,miƙewa ta yi ta shimfiɗa wani tapis daga gaban nata malam Nur ya hau ya ja su sallah suna
gamawa su kayi ƴan ciye-ciye kafin su gabatar da sunnah Manzon Rahaman.
Asubah farin Nazifa ta farka,cike da jarumta ta miƙe ta faɗa toilet ta haɗa ruwan ɗumi ta yi
wanka game da alwala.
Har sai da ta gama raka'atil fajir sannan malam Nur ya farka,shi ya canza zanen gado ya wanke
a injin wanki sannan yayi wanka ya zura jallabiya zuwa masjid.
Sai da rana ta fito wantsar sannan malam Nur ya dawo gida dan wannan sabonsa ne duk
bayan sallah asubah masallaci yake zaunawa yayi ta azkar.Har zai shiga ɗaki sai kuma ya ji
motsinta a kitchen,a hankali ya ɗaga ƙafar shi zuwa can kitchen ɗin ya jingina da bango ya na
kallonta ta na zuba ruwan zafi a Flask,ba ta san da zuwan shi ba sai ji tayi yayi huging nata
yana murmushi mai sauti "Barka da asuba!"ta faɗa a kunyace lokacin da ya juyota suna facing
juna, hanci ta ya ja kafin yace "Barka da asuba wa?haka ake gaishe da miji ko ɗan sunan nan
na masoya ba za'a saka ba"malam Nur ya faɗa yana mai zuba mata ido,turo baki ta yi tace "to
ka sake ni sai na faɗa"waro ido yayi yace "au!sai na sake ki zaki faɗa?to bari ki gani"dariya ta yi
jin ya sungumeta kamar wata baby,kan bed ya direta ya luluɓeta da blanket "yi kwana kwanta
ki huta"ya faɗa yana mai dadaɓata tare da hura mata iska a fuska,lumshe ido ta yi tana jin
soyayyar mijinta na ratsata kafin wani lokaci har barci ya ɗauke ta.Murmushi malam Nur yayi ya
shiga wanka ya fito ya shirya cikin wata rantsatsiya gizner H color,zaman hullar kan shi ya gyara
ya ɗaura agogo a tsintsiyar hannunsa na dama tare da fesa turare ya nufi part ɗin Sappa.
A zaune ya tarar da ita a man falo,sanye da kayen barci tana kallon tv ta saka tray fruits a gaba
tana ci.Wani irin miƙewa tayi tana kallon sanyin idanunta wanda ke sheƙin amarci,ba tare da ta
amsa sallamar da yayi mata ta faɗa a jikinsa ta saki kuka.Duk ƙoƙarin hanata da malam Nur
yayi bai sa ta dakata ba,da sauri ya ɗagota yana cewa "lafiyar ki kuwa Sappa?mi ya ke damun
ki?yanzu a hakan ne kike zaune tsirara?"saurin sakin shi ta yi ta zuba masa ido cikin raunin
murya tace "yaya Nur mi yasa baka sona?mine ne wanda ake so ga ɗiya mace wanda ni ba ni
da?ko ban cancanta ka so ni ba ne?"kawar da kai malam Nur yayi gefe yace "tafi ki suturta
jikinki sannan ki zo mu yi magana"yadda yayi magana yasa ta jawo wata doguwar rigar abaya
ta hauda saman kayan barcin ta na mai zaunawa ƙasa kusan ƙafafunsa.
Huci ya furzar yace "Sappa ina son ki bani hankalinki nan ki nutsu ki fahimce ni, muddin ki na
son samun soyayya ta doli ne ki bi Naziii sau da ƙafa ban so ki yi wani abu wanda ranta zai
ɓace, ki zauna da ita lafiya ki ɗauke ta matsayin yayarki in kin yi haka ina mai tabbatar maki
zaki samu soyayya Nuradeen akasin haka kuma hummm kin san sauran"tun da ya fara magana
ta buɗe ƙofofin kunnuwanta tana sauraren shi daki-daki,wasu hawayen takaici ne suka zubo
mata amman ta danne zuciyata tace "in shaa Allah zan yi in dai ka so ni" dangwala mata yayi
da yatsa yace "good girl"kafin ya ke miƙewa yace "na tafi sai na dawo ki kula da kan ki"amsa
masa ta yi da "a dawo lafiya"tana jin daɗin kalmar ta kula da kanta da ya faɗa.
Nazifa kuwa sosai ta sha barci ba ta