Showing 21001 words to 24000 words out of 51592 words

Chapter 8 - Shaukin So Book Compelet Mrs Sadauki

da ke tsaye kusa da
su sai da suka yi mamakin furucin malam Nur,ita kuwa Balkis fashewa ta yi da kuka tana girgiza
ma ɗan uwan nata kai tace "sam ban tsammaci haka ba daga gare ka yaya Nur,ina imaninka ya
tafi har kake faɗin haka?kar ka manta kai Malami ne ka san yadda Allah ya so ya ke yi ba wai
neman shawara ba"masu raunin zuciya irin su Lami sai da suka goge ƙwalla jin bayanin
ƙaramar yarinyar da ba tafi 18years ba amman babba mai hankali kuma malami ya kasa gane
ƙaddarar Ubangij zuwa ta ke ba tare da an shirya ba.


Maman ya miƙa ma babyn yana jin zuciyarsa na zafi,sam ya kasa ɗaukar lamarin ta yaya
ɗiyarsa ta farin za ta kasance Makauniya?laifin mi yayi ma Ubangijinsa? Da wannan tunanin ya
nufi ɗakin da ya ga an kai Nazifa ciki.A kwance ya tarar da ita hannunta sanye da ƙarin ruwa sai
numfashi take saukewa akai-akai,ka na ganinta ka san ta sha wuya ba ƴar kaɗan ba. Ido ya zuba mata yana jin zuciyarsa na bugawa yayinda ƙaunarta haɗi da SHAUƘIN SOnta ke
ninkuwa a ciki,ƙarasawa yayi ya tsaya kusan kanta yana kallon idonta da suke zubar da
hawaye.Kamar daga bisa yaji tace "ba kayi murna ba saboda na haifi mace ko?duk lokacin da
kace min namiji kake so ina samun kaina da tsinkewar zuciya dan ban san abinda Allah
za..."da sauri ya rufe mata baki ya shiga share mata hawayen tare da kwantar mata da
hankali,bai bar wurin ba sai da ya tabbatar ta saki ranta.


Maman da Lami ne suka shigo,tashi ta yi ta karɓi yarinya da ta fara kuka Lami na gwada mata
yadda za ta shayar da ita.Cike da kunya ta ke bata abincinta, Balkis kuwa na gefenta ta kasa ta
tsare sai kallon babyn take "amsar ta ai ta ƙoshi"cewar Nazifa tana mai miƙa ma Balkis
babyn,amsar ta ta yi tana dariya ta dawo ƙasa inda su Maman ke zaune bisa tabarma.

Malam Nur ne ya shigo bakinsa ɗauke da sallama, ledodin hannunsa ya ajiye ya na tambayar
Nazifa jikinta,gefe ya zauna yana latsa waya sai shating ya ke hankalinsa kwance kafin kuma
ya miƙe ya fita.Sosai Nazifa ta yi mamakin rashin ɗaukar baby amman sai ta bar shi akan ƙila
bai iya ɗaukar jarirai ba ne.


Kwanan Nazifa ɗaya a asibiti aka sallamo ta,amman ko take Sappa ba ta zo ba.Ƴan uwa na
nesa da na kusa kuwa suna ta tururuwa zuwa wajen barka,Samira dai ango Jabeer ya hana

yace sai ranar biki zai kawo ta.

Sha tara ta arziki Maman ta haɗa ma Nazifa ita da ɗiyarta,kayan jarirai kala-kala wasu ma sai ta
shekara ba ta sa su ba.Wannan bajintar ba ƙaramin daɗi ta yi ma Nazifa ba dan ko ba komi
hakan ya nuna ana son ɗiyarta.


Ranar suna yarinya ta ci sunan *Laila* ,malam Nur da Nazifa anko su ka yi na blue gizner.
Nazifa na tsaka da cin biki sai ga Sappa kamar wadda aka yi ma doli ta shigo ɗakin,kwalin
sabulu da kayan jarirai ta miƙa Samira ita ce kusa hakan yasa ta karɓa ta na godiya Nazifa
kuwa cike da mamaki take kallon Sappa dan har ta mance da ita.
Juyar da kai ta yi gefe sai cika ta ke tana batsewa wanda ba komi ne ya jawo hakan ba sai
kyautar gida sukutum da Maman ta bayar ga jikanyarta.

Malam Nur angon jego shi ma ya na can waje shi da abokansa suna taya shi murna,amsawa
kawai ya ke dan babu yadda zai yi amman har ga Allah bai son yarinyar.
Kafin bayan sallah magrib kowa ya watse ya rage ƴan gidan,wanka Nazifa ta yi ta fito ta na
shafa mai sai ga malam Nur.
Gaishe shi ta yi ya amsa kafin ya fara bincike "mi kake nema?"Nazifa ta tambaya shiru yayi bai
tankata ba sai ci gaba yayi da abinda ya ke.

Cike da jin haushin share ta ɗin da yayi ta fito falo inda Lami ke yi ma baby Laila wanka sai ƙara
take ta na kuka.Ka sa jurewa Nazifa ta yi tace "Inna Lami a barta haka nan tunda ba wata
dauɗa gare ta ba"dariya Inna Lami ta yi tace "oh!Ni yaran yanzu babu ta ido ƙiri-ƙiri kuke nuna
son ɗiya" "ba haka ba ne Inna Lami kawai na ga sai kuka ta ke ne ya kamata kuma a barta
haka"cewar Nazifa ta na mai ɗauko ƙaramin towel wanda za a naɗe Laila,"ba wani son ɗiya ne
mana,mu lokacin mu yaro ko wuta muka ga zai taɓa ba zamu janye shi ba saboda kunya
amman ku da ya ke yaran zamani ne wankan ruwan zafi ma ba ku haƙuri ayi ma yaren ku"kai
Nazifa ta sosa alamun jin kunya kafin ta ce "ruwan ne da zafi ko sirkawa bakwa yi"aza mata
baby Laila ta yi kan towel ɗin da ta riƙe tun ɗazu tace "ke kike ganin zafin su amman ita daɗinsu
ta ke ji saboda yanayin jikinta da ya ke da taushi balle ma yau da ta sha ɗauka jikinta yayi ciwo
doli a gasa ta"Nazifa dai ba ta ce komi ba sai gashin Laila da ya kwanta luf ta ke shafawa.

Su na nan zaune malam Nur ya fito daga ƙurya ɗakin "ungo wannan ko buƙatar wani abu ta
taso "malam Nur ya faɗa yana miƙa ma Nazifa kuɗi karɓa ta yi ta na kallon shi sai ya kuma
cewa "eh gobe za ki koma gida shan kunu kamar yadda kuka buƙata,ban san lokacin da za ku
tafi ba ƙila ina bacci sai ku shiga taxi"ya na gama faɗin haka ya fice.

Wani abu ne ya caki zuciyarta sam ta kasa yarda wannan malam Nur ɗinta ne,tunda ta haihu
komi na shi ya canza.Jiki baƙwari ta miƙe ta nufi bedroom shimfiɗar da Laila ta yi ta koma can
ƙarshen gado ta yi tagumi ta na tunanin rayuwa,ganin tunanin ba zai ɓarkata mata komi ba yasa
ta miƙe ta ɗauro alwala ta fara jan casbi.

Washegari misalin ƙarfe goma na safiya Inna Lami ta taro mai taxi,kayan da za ta buƙata ne
kawai za ta tafiya da su.Sallama su ka yi ma Maman sannan suka wuce gidan Inna,yaya Ɗalhat
ne ya shigar masu da kayan ya kuma sallami mai taxi.


Cike da begen jikanyarta Inna ta rungume ta dan rabonta da ita tun a asibiti,sosai yarinya ta
ƙara yi mata kyau.
Yaya Ɗalhat ne ya matso yace "Inna kin kama ɗiya kin riƙe ba ki da niyya ba iyayenta"dariya ta
yi tace "mi ake da kishiya,ɗiyar taku ma da ba wani kyau ne da ita ba sai dogon hanci kamar
biro"dariya shi ma Ɗalhat yayi ya karɓe ta ya manna a ƙirji ya na jin son babyn,bisanin ya miƙa
ma Rakiya wacce ke zumɓuro baki ta yi gajen haƙurin a bata.

Nazifa kuwa babu abinda ya dameta sai ɗumamen tuwon masara ta ke ciki ta na kallon diramar
su.Sai yamma lisss Inna Lami ta tafi gidanta bayan ta karɓi sha tara ta arzikin da Nazifa ta yi
mata.




Sosai Nazifa da ƴarta su ke samun kulawa wajen Inna da ya Ɗalhat da kuma Rakiya,dan kowa
na iya ƙoƙarin shi wajen kyautata mata wannan ya sa damuwar Nazifa ta kawar duk da shi ma
malam Nur ɗin na zuwa ganinta kusan kullum sai dai bai ɗaukar Laila,da ya ga Nazifa na
damuwa da hakan ne ya ke shafa kanta duk in ya zo wani sa'in kuma yayi kissing nata a goshi
ya ɗauki hotonta.



A kwana a tashi asarar mai rai,Nazifa ta yi arba'in har ta koma ɗakinta inda rainon Laila
kwankwacakwam ya koma hannun Maman da Balkis,kullum tana part ɗin Maman sai dare
kawai ake maido ta ko kuma in ta yi kuka.
Wannan abu shi yayi ma Sappa kaluluwa a zuciya ji take kamar ta jawo watan haihuwarta kusa
ta haihu ko nan ta rage haushi da tunanin kuma Maman za ta so ɗanta fiye da na Nazifa.



Zaune take a falo Balkis na matsa mata ƙafafunta da suka kumbura,gefe kuma Maman ce ke ta
faman koyawa Laila zama ta sakata tsakiyar ƙafafunta.
Lokaci zuwa lokaci Sappa ke kallon su 'Allah sa ta faɗi ta fashe baki da goshi 'hine abinda kawai
take rayawa a zuciya.

Kamar daga sama kuwa sai jin kukan Laila ta yi ta faɗi ɗin kamar yadda ta so,da sauri maman
ta cirota ta shiga ririgata amman ta ƙi yin shiru hakan yasa Maman tashi tsaye ta goyeta a baya
ta shiga kewayen ɗaki.
Takaici,baƙin ciki da hassada su ne suka turnuƙe Sappa barin tausar Balkis ta yi ta nufi Maman
tana yi ma Laila wasa daga goyen tsit ta ƙyale tana sauraren ɗan kacau-kacau da Balkis ke
kaɗawa,tsabar baƙin ciki yasa Sappa sarƙewa da yawun bakinta ta shiga tari kamar ranta zai
fita.

Harararta Maman ta yi tace "lafiyarki kuwa?minene kike ci wanda ya ƙware ki?"ƙyafƙyaf da ido
Sappa ta yi ta turo baki cikin jin haushi,baki Maman ta taɓe tace "ki shiga hankalinki Sappa ba
ruwana da sarkarci dan na ga har yanzu kin ƙi ki sauwa daga mugun halinki,jikanyar tawa ma
banda iko na kula kawai dan ki na kishi da uwarta?"cikin jin haushi Sappa tace "toh wai ni mi na
yi?ni ai ban faɗi haka ba" "to minene ya ƙware ki?in ba kin ji zafin hakan ba?ko ko kece ɗin a
ban sani ba mai yin tarin baƙin ciki in kin ji haushin abu?"shiru Sappa ta yi dan sarai ta san da
Maman ta yi mata farin sanin da ko uwar da ta haife ta albarka.


Ana cikin haka sai jin sallama su ka yi,malam Nur da ƴan uwansa maza bakwai sai mace
datizuwa wanda ke nuni ƴaƴanta ne.Kicin-kicin Maman ta yi da fuska kamar ta ga mala'ikan
mutuwa,gaisheta suka yi ta amsa da "lafiya"gabatar da su malam Nur yayi kafin daga bisani ya
ƙara da cewa "wannan ce mahaifiyarsu kuma ba komi ne ya kawo su ba sai rabon gado"daram
ƙirjin Maman ya buga sai ido da ta fiddo tana kallon samarin bakwai wanda su ke a jere ras
gabanin ta kalli Nuradeen da Balkis ƴaƴanta biyu rak.....



My book is only 300 via
2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank DM +22795045822
[22/05 16:28] MRS SADAUKI: *SHAUƘIN SO*


```LoVe story```


By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI✍️}


*FCWA*☀️

________________________

Page 21-22



Cikin dauriya Maman tace "to sai a ka yi yaya in za a yi rabon gado?"kallonta duk suka yi banda
Rahinatu da ta sunne kai dan ita har ga Allah tsoron Maman ta ke.Ganin duk sun ƙyale Maman
ta ci gaba da cewa "in rabon gado za a yi ai malumai ke yinsa ba wai tsakankanin magada
ba,in banda masifa da zanzana irin ta tallaka duka-duka yaushe ne alhajin ya rasu da har za'a yi
maganar rabon gado sai kace masu jiran mutuwar"cikin jin haushin wulaƙancin da ake yi masu
Suleyman ya miƙe tsaye yace "ku tashi mu tafi tunda da alama wannan matar ba ta san arziki
ba,kawai daga zuwa za ta wani rufe mu da masifa"baki buɗe Maman ke kallonsa kafin tace "ka
ga masifa nan kusa da kai,uwar ka ita ce masifafa shege ɗan Zina kai miye naka cikin rabon
gadon?in banda sa kai uku"duk miƙewa suka yi suka fice Rahinatu na matsar ƙwalla.
Kusa da Maman malam Nur ya matsa yace "haba Maman miye haka? ƴaƴan mijinki fah ƴaƴanki
ne minene na tozarta su?"
"To Baba dake ni.Nace ka dake ni na taɓa ƙannan uwarka"cewar Maman tana juya masa
baya,cike da tsoro malam ke kallonta dan abun Maman ya fara barin bashi mamaki sai dai
tsoro.
"Allah ba ki haƙuri"ya faɗa ya na mai zaunawa ya fara kallon tv.


Maman kuwa ɗaki ta shige ta fara zagaye tana neman mafita dan tabbas Rahinatu sai ta fi ta
samun kuɗi ita da ke da yara 6 kuma maza,yatsa ta cije tace "miyasa ma na biyewa ruɗin
zuciya na yi ta shan magani dan kar na haihu mtsw..."haka dai ta yi ta saƙa da warwara har sai
da kanta ya fara ciwo sannan ta kishingiɗa ta yi barci.

Washegari sai ga su Suleyman sun sake dawowa da maganar dai ta rabon gado,malam Nur shi
kansa sun bashi haushi hakan yasa ya nemo malamai masu ilimi kamar yadda Shari'a ta zartar
haka aka raba masu gado bayan an cika wasiya Baba an fidda ma Suleyman kaso daga ciki.
Wannan rabon gadon sosai ya ɓata ran Maman ganin Rahinatu da ƴaƴanta sun ɗauki wajen
kaso 85 cikin ɗari na dukiyar Alhaji ,tun tana masifa tana cewa an cuce su har ta kai ta kasa
dangana ta fashe da kuka.
Sai da ta yi mai isarta sannan ta ƙyale,malam Nur da Balkis Maman suka ba duka kuɗin dan tun
ba yau ba ta shaida masu kasuwanci za ta fara.


Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya yau ƙunci gobe daɗi,Maman an fara kasuwanci sayar da kaya
na Lome da kanta take zuwa dan sam ba ta da yarda.
Duk in ta tafi sai tayo ma jikokinta sayayya Laila da ƴan biyun Sappa wanda malam Nur ya

ɗauki son duniya ya ɗora masu .
"Maman wannan ai sun yi ma Amar da Anas yawa sai dai ko Laila tunda ita ta nada ƙiba"cewar
Balkis wacce ke zaune tana duba kayan da Maman ta sawo,fizge kayan Sappa ta yi tace "ina
Makauniya ina wannan kayan?ai na masu ido ne"da sauri Nazifa ta ɗago tana kallonta,murguɗa
baki Sappa ta yi tace "eh ko ƙarya ce ba Makauniyar ba ce kike wani kallona kamar wacce ta yi
maki ƙage"wasu hawaye ne suka zubo ma Nazifa a zuci take cewa 'kenan dagaske Makauniya
ce?zargina ya tabbata' kallon Maman Nazifa ta yi wadda ita ma ƙwalla ta cika ma ido "ki yi
haƙuri Nazifa ni nace kar a sanar da ke"cewar Maman tana kwashe kayan da aka baje a capet.
"Maman kenan ke kin san da haka?"Nazifa ta sake tambaya "eh kowa ma ya sani daga ke sai
Sappa ne a baku sani ba,ita saboda irin wannan ranar yasa na hana a shaida mata ke kuma
saboda kar ki tada hankalinki".
Ɗaukar Laila ta yi ta fita direct part ɗinta ta wuce,hawayen idonta ta goge sannan ta ƙura ma
Laila ido wacce yanzu take wata na biyar da haihu.Da ɗan yatsar ta yi kamar za ta tsone idon
Laila dan tabbatarwa amman ba ta ƙyafta ba, rungume ɗiyarta ta yi a ƙirji ta saki wani marayan
kuka na tausayin kansu su biyun. A fili ta furta "wannan dalilin ne Abbanki a bai son ki,shin kyautar Ubangijin ce yayi fatali da ita
har ya ke ƙyanƙyamin ta?miye laifin ki a ciki dan kin fito Makauniya alhalin ba ke kika yi kan ki
ba?shi malami bai yarda da ƙadara ba to ina ga jahili wanda bai san Allah ba?"ba ta san da
shigowar shi ba sai ji ta yi ya daka mata tsawa yace "ya isa haka!ni namiji nake so shine kika
tashi ki haifo min mace,macen ma Makauniya.Da wane kike so in ji rashin cikar burina koko
ɗawainiya da ita?ita kanta mace rauni ce to yaya kike gani in ta kasance da naƙasa?"wasu
hawayen baƙin ciki Nazifa ta goge tace "ai Nakasa ba kasawa ba ce nufi ne na Allah,kai da
kuma ba ka da ita babu tabbacin haka za ka zauna har ƙarshen rayuwarka domin ba'a gama
hallitar ɗan Adam ba har sai ya koma ga mahall...."wani gigitacen mari ya ɗauketa da shi tare
da nuna mata yatsa yace "zo ki nakasa ni ƴar baƙin ciki, Makauniya dai ce ki riƙe abarki"ya na
gama faɗa ya juya zai fita a fusace har ya kai bakin ƙofa ya ji tace "ai ba ita ta yi kanta ba"bai
saurareta ba dai yayi gaba.


Cigaba ta yi da kuka tana yi ta na fyace majina,Laila kuwa sai wasa take da ƴan hannun
mahaifiyarta da suke ƙara.Aje ta Nazifa ta yi ta shiga wanka,ta na fitowa ta saɓa ƴarta a baya ta
goyeta.Hijab da jaka ta ɗauka ta rufe ɗaki tana shirin fita ta ji Maman na ƙwala mata kira ta
window,kewayawa ta yi cikin ɗakin ta yi tsaye ta sunkuyar da kai ganin Maman na yi mata
kallon mai saman ruwa.
"In dai kin san yaji ne za ki yi to ki kwance min jika dan ba da ita kika zo ba,ki barta a gidansu
kafin ki tafi naku gidan.Gare ta farau makanta da har zaki ɗaga hankali in ke ma baki sonta sai
ki bani na raineta,tunda ku Allah ya baku kun ce baku son kyautar wasu na can suna neman ko
kuturwa ce Allah ya ba su"Maman ta faɗa da alamun faɗa-faɗa ,kukan da ta ke riƙewa ne ya
kubce mata tace "Ni Maman ina son ƴata a yadda ta ke shi ne...shi ne dai a bai so "taɓe baki
Maman tayi tace "to sai mi?ni ban ga abun damuwa ba tunda mu muna son abar mu,kin ga
miƙo min ita tafi ki ɗora girki ki ci ki ƙoshi in kika biye ma namiji takaici ne zai kashe ki"kwance
goyon Nazifa ta yi ta miƙawa Maman ,baiwar Allah Laila sai barcinta take.

Ɗaki Nazifa ta koma tana jin zuciyarta ta rage nauyi, zantukan Maman ne kawai ta yi zaune ta
na tunawa ta na ɗan jin sauƙi.Tun daga wannan lokaci Nazifa da ƴarta ke fuskantar tsangwama
gun malam Nur da Sappa yayinda Maman ta ke ƙarƙafa ma Nazifa gwiwa,tun lamarin na
damunta har abun ya zame mata sabo.


Cikin shirin fita ta fito tana jaye da hannun Laila wacce yanzu ta ɗan girma tana cikin shekara ta
biyar.Da shigar su part ɗin Maman Amar da Anas suka shiga yi ma Laila dariya su na tsokanar
ta"ƴar makauniya..."cikin jin haushi Laila ta ƙwace hannunta daga na Nazifa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login