Showing 18001 words to 21000 words out of 51592 words
Chapter 7 - Shaukin So Book Compelet Mrs Sadauki
suka miƙe suka bar wurin.Ƙafafun Maman ya dafa zuciyarsa
na suya yace "kiyi haƙuri Maman sam hakan da kika yi bai dace ba,Naziii na bakin ƙoƙarinta
wajen kauce duk wata husuma, na lura tun ranar sadakar uku ta Baba da kika ƙullice ta har
yanzu baki sauko ba,a madadinta ina mai baki haƙuri..."saurin katse shi Maman tayi da cewa "ni
ce mai tada husumar ko? Saboda matarka kake gaya min magana har da cewa na ƙullace ta?"
"A'a Maman ba haka nake nufi ba wlh,kawai abinda kika mata ne yanzu bai dace ba a
matsayinta na surukarki ni ina ganin da ni da ita ai duk ɗaya ne a gun ki"hannuwansa Maman
ta jaye daga kan ƙafarta tace "ka tashi ka tafi kar jininka ya hau ka zage ni"da sauri Ustaz yace
"subahanallahi zagi kuma Maman ?" "Eh mana tunda an taɓa ƴar gwal ba zagina ba ai ko
dukana sai ka yi".
Murya malam Nur ya ƙara sanyayawa yace "Allah ya huci zuciyar Ummu Nur, Allah ya baki
haƙuri zan fita malam Jabeer na kirana kin san Yau za'a kai kuɗin aurensa"yana gama faɗa ya
miƙe tsaye Maman kuwa ta washe baki tana cewa "ah-ah Masha Allah ashe yarona an kusa
zama manyan mutane?toh Allah sa dai ta kirki ce zai auro Allah kuma yasa alkairi alkairi"da
"Amen"ya amsa yayi ficewar shi.
Sai bayan sun dawo daga kan kuɗin malam Jabeer ne ya shiga gun Nazifa,waya ya tarar da ita
suna yi ita da Samira.Kashe kiran ta yi ta tarbi mijinta "har kun dawo?Masha Allah yau burin
ƙawata ya cika malam Jabeer ya kai sadaki sai fatan kuma Allah ya nuna mana ranar
biki"Nazifa ta faɗa murmushi kan fuskarta,shi ma murmushin yayi yace "shikenan sai mu huta
da mita kullum sai yayi min hirarta sai kace gare su farau soyayya"
Dariya Nazi ta yi tace "ai bai kai nacinka ba ko ka manta lokacin da muna soyayya kullum ka na
gidanmu kuma hirarka ba ta wuce NazNur"tunda ta fara magana ya tsaya yana kallonta kamar
yau ya fara ganinta,jin bai ce komi ba ta ɗan daki ƙirjinsa tace "ya dai?"numfashi ya sauke yace
"ba komi kawai ina tunanin babyna ne,ko da wa zai kama cikin Ni da Ke?"
Dubansa ta yi tace "in namiji ne da kai zai yi kama in kuma mace ce da ni za ta yi kama" "na fi
son ki haifi namiji Saboda buri biyu,na farko don na saka masa sunan Baba, na biyu kuma don
na samu aboki"cikin rashin jin daɗin zaɓen da yayi na cewar ya fi son namiji tace "ka bar ma
Allah zaɓi dai shi ya fi,in kuma na haifi mace sai yaya kenan?"miƙewa yayi tsaye yace "in shaa
Allah namiji ma ne,sai da safe ki zo ki rufe ƙofa"ya faɗa yana mai ficewa saboda yau Sappa ce
da girki.
★
Kicin-kicin ta yi da fuska kafin a shagwaɓe tace "yanzu saboda Allah SapNur sai yanzu za ka
shigowa bayan ka san yau ni ce da girki shine ka tafi can ka yi zamannin ka?"sam malam Nur
bai kulata ba sai ma dariyar sunan SapNur da yaji tace sai ya ji sam bai yi daɗi ba.Cikin jin
haushi Sappa ta biyo shi ɗaki sai aka yi rashin sa'a har ya shiga wanka har za ta tafi kuma komi
ta tuna sai ta dawo ta zauna.Bai jima ba ya fito ɗaure ta towel, jallabiya ya saka yayi Sallah
raka'a biyu sannan ya fara tilawar alƙur'ani mai girma.
Wani maƙoƙon baƙin ciki ne ya tokare ma Sappa maƙoshi,cikin jin haushi ta ɗaga murya ta
yadda zai jita tace "malam alhuduhudu ai ka dakata da karatun ka ji da lamurran matarka,koko
har yanzu ilimin naka bai sanar da kai darajar mata a gun mijinta ba?"kamar zubar narkakar
dalma haka malam Nur ya ji maganarta ,cak ya tsaya daga karatun da ya ke ya waigo inda take
zaune ta hakimce bakin bed tana kalkaɗa ƙafa.Ido ya rumtse ya ci gaba da karatu ganin haka
yasa Sappa yin tataki har inda ya ke ta tsaya masa a kai tace "da kai fah nike"yadda ta yi
maganar tamkar uwarsa yasa ya harzuƙa ya miƙe ya kwaɗa mata mari tare da nunata da yatsa
yace "ki shiga hankalinki tun kafin ki sa na aikata abinda ba ya cikin tsarin rayuwata,wlh in kika
ci gaba da wannan shirmen zan maki ɗan banzan duka get out..."jiki na kyarma Sappa ta fita ba
shiri,tana shiga ɗaki ta fashe da kuka tana cewa "na shiga uku ni Sappa wato duk yadda zan yi
maka ban yi daidai ba na yi maka kissa da rangwaɗa ka wani share ni,na nuna maka fushina ka
koro ni "taɓata ta ji an yi da sauri ta juyo suka haɗa ido,alama yayi mata da ta zo gare shi ba
muso ta faɗa ƙirjinsa.Bayanta ya bubuga yace "toh ki yi shiru mana ba gani ba ko baki so na
komawa ta ne?"kai ta girgiza yace "to na ji ba zan tafi ba amman ya kamata ki san yadda za ki
rinƙa yi ma miji magana sannan ki rage saurin fushi duk abinda lalami da rarrashi bai bayar ba
to tashin hankali ba zai saka shi ba"ajiyar zuciya ta sauke tace "toh"kulawa ta musamman suka
shiga baiwa junan su tamkar ba yanzu suka yi faɗa ba,hakan kuma yana ɗaya daga cikin
jajircewar malam Nur na kwatanta adalci tsakanin matansa ba tare da ya tauye haƙin ɗaya ba.
***JOS
Sosai jikin Tajdeen yayi sauƙi kasancewar ya na samun kulawa ta musamman daga
iyayensa,tsakanin shi da Avani da Raj kuwa sai gaisuwa ita ma ba kullum ba .Duk da yanzu
Avani ta rage jin haushin Tajdeen sakamakon cikin da likita ya tabbatar mata da shi,da sannu ta
fara jawo Tajdeen jikinta abun ka da yaro sai ya manta cutarwa da ta yi masa ya ke zuwa gun ta
sai dai da zarar Raj ya shigo ya ke fitowa saboda kallon tsanar da ya ke jifar shi da kuma faɗan
da ya ke ma Avani dan mi take bari ya na shigowa.
Cikin Avani na shiga wata tara da ƴan kwani ta haifo kyakyawar ƴarta mace mai kama da
turawa,tun a ranar da aka haife ta aka yi mata laƙabi da *Mari* sai da aka ɗauki wata biyu
sannan aka yi biki.
Tunda Mari ta zo duniya Tajdeen ya ɗauki son duniya ya ɗora mata,kullum ya na ɗauke da ita in
kuma ya tafi makaranta bai da hira sai ta Mari dan wasu abokanansa har zuwa su ke kawai
dan su gan ta.
Zaune suke tsakiya falo ya sa Mari gaba sai wasa ya ke mata ita kuma tana wangale baki ta na
masa dariya,kuka ta fara alamun ta gaji yunwa take ji hakan yasa Tajdeen ɗaukar ta ya nufi part
ɗin Avani da ita ya na ɗan ririgata.
"Mi ka yi mata take kuka iyeee?"Raj ya tambaya kamar zai kashe Tajdeen,shiru yayi bai ce komi
ba sai jikinsa da ya ɗau rawa dan har ga Allah tsoron Raj ya ke.Wani gigitacen mari Raj ya
sauke ma Tajdeen wanda yayi sanadiyar ɗaukewar numfashinsa na wucen gadi,wata irin ƙara
Tajdeen ya ƙwalla tare da sakin Mari bai shirya ba.A gudane ya nufo waje jini na yi masa zuba
ta hanci,karo suka ci da Mom wadda ƙarar Tajdeen ta caki ƙahon zuciyarta ta nufi part ɗin
Avani.Jikinta ya faɗa ya na kuka,saurin ɗago shi ta yi tana bubuga goshinsa dan tsayar da jinin
amman abu ya cuttura.Ruwan sanyi father ya ɗauko tare da wanke masa fuskarsa nan jinin ya
tsaya,father na shirin shiga part ɗin Avani dan zaƙulo Raj sai Dad ya riƙe shi ya girgiza mashi
kai " ba komi ba ne ake ɗaukarwa mataki,Deen tamkar Ɗa ya ke gun Raj ya na da incin
hukunta shi ƙila laifi yayi masa"ya na faɗin haka ne tare da jawo hannun father zuwa kujerar
zaman shi.Cike da jin haushi Mom ta harari Dad murmushi kawai yayi mata,lamo Tajdeen yayi
yana shasheka kafin daga bisani barci ya ɗauke shi.
Washe gari bayan Dad ya sauke Tajdeen school sai ga shi da wasu takardu ya na yi ma father
bayani,shi kuma huci ya sauke yace "ban ƙi ta taka ba Jean amman ka na ganin shi Deen ya
na son aikin soja?kuma mi zai hana ka bari har sai ya girma?"kai Dad ya girgiza yace "a'a father
gwara ya tafi tun yanzu dan zai fi samun horo mai kyau kuma hankalinsa da namu zai fi
kwanciya"
"To Allah ya taimaka ita Vani ɗin ta yarda?" "Ban kai ga gaya mata ba sai yanzu ".
Sosai Mom ta yi murna da maganar da Dad ya zo mata na tafiyar Deen makarantar horon
soja,hakan ya sa Tajdeen na zuwa ta shaida masa nan ya hau kuka yace shi aikin likita ya ke so
cikin rarrashi Mom tace "Ɗana Deen aikin soja da na likita duk ɗaya ne"cikin kuka yace "a'a
Mom na yi ma...na yi alƙawari"sai kuma ya ƙyale ya na jin kan shi na sara masa sakamakon
wani abu da ya so ya tuno kuma ya kasa.Zuciyar Mom kuwa lugude ta shiga yi dan ita har ga
Allah ba ta son ya na yi mata zancen Anya kuma babu shakka ta tabbata abinda ya ke son faɗa
kenan,ɗaki ta kai shi ta ɓalli maganin shi ta ba shi dandanan barci ya ɗauke shi.
Da ya farka da maganar zuwan shi aikin soja ya tashi,cike da murna Mom ta rinƙa kwaɗaita
masa aikin.
Farin cikin da ya ga ta na yi shi ya zame masa ƙwarin gwiwa,hakan ya sa ya ɗaura ɗamarar
kasancewa kamar yadda su ke so.
Abu kamar wasa sai ga Tajdeen luntsum cikin makarantar yara ta sojoji wacce ke babbar jaha
ta Abuja,sosai kasancewar shi a nan ta yi ma shi daɗi duk da baƙar azabar da ake gana masu
amman samun abokan ƙwarai ya sa shi jin daɗin rayuwar,gefe guda kuma ya na jin kewar gida
da soyayyar ƴar ƙanwarsa. Kwance Tajdeen yayi bayan ya fito daga wanka,lumshe ido yayi gidan su na yi masa gizo bai
ɗau wani lokaci ba barci ya ɗauke shi mai cike da mafarka iri-iri,duk cikin su guda ne ya tsaya
masa ba wani mafarki ba ne yayi fa ce na yanzu girma ya zo masa alƙalami ya hau
kansa.Kasancewar shi yaro shiyasa bai gane komi ba dan a lokacin shekarar sha biyu da wasu
watanni za'a iya cewa yanzu cikin 13years ne yake,wani wankan ya sake yi ba wai na yadda
addini ya sharanɗa ba a'a sai dan kawai wanke ƙazamtar jikinsa.Cikin wani irin yanayi na shiga
sabon zangon rayuwa ya shirya tsaf ya nufi filin da ake buga wasa,tun kafin ya ƙaraso Irfan da
Faruk suka yi masa alama.
Hannu ya basu suka gaisa sannan ya zauna suka cigaba da kallo,Irfan ne ya kalle shi yace
"Deen sai na ga kamar yau ba ka cikin walwala why?"murmushi kawai yayi yace "ba komi"ba
dan Irfan ya yarda ba ya ƙyale shi dan sam ba haka ya san Tajdeen ba.
Har aka gama ƙwallon Tajdeen bai ce ufan ba Irfan da Faruk kawai ke hira,tun su na tambayar
shi lafiya har su ka ƙyale dan sun lura Deen irin mutanen nan ne masu zurfin ciki.
Ko da dare yayi bayan sun gama cin farar Macaroni da mai da maggi wata hira suka ɗora inda
Tajdeen ya haye ɗan ƙaramin gadonsa ya faɗa tunanin yarinyar da ya gani cikin mafarki jefi-jefi
kuma ya na sauraron hirar abokansa.
Yayi nisa a cikin tunani ya ji Faruk na cewa "Ni kam Tajdeen na tambaye ka"ba tare da ya juyo
ba yace "um ina jin ka"
"Miyasa ba ka yin sallah ne kullum sai na ga ka yi wanka ka shafa mai?"ita ce tambayar da
Faruk ya jefo ma shi,shiru yayi ya fara tunanin ina ya taɓa jin kalmar sallah da dai ya ji zai jawo
ma kansa ciwon kai sai cewa yayi "minene sallah?"waro ido su kayi a tare suka ce "minene
sallah kuma?"a yadda ya ji sun yi maganar cike da mamaki ya sa shi juyowa yace "eh mana ni
ban san mi kuke zance ba"kallon-kallon suka fara yi kafin Irfan yace "ka na nufin kai ba Musulmi
ne ba?"saƙe Tajdeen yayi zuwa can ya girgiza kai yace "Ni ban san komi Please telle me mi
kuke son faɗa ne ?sai naji kamar na taɓa sanin wannan kalmar"cikin ɗan ilimin da su ke da
suka shiga yi ma Tajdeen bayani akan addinin Musulunci har sai da dare ya tsala sannan suka
dakata tare da yi masa alƙawarin gobe sun ƙarasa mashi...
****Maradi
Rayuwar farin ciki Nazifa ke fuskanta gun mijinta inda kuma ɓangare guda ta ke fama da irin cin
kashin da Maman ke yi mata,ƙiri-ƙiri Maman ke nuna banbanci tsakaninta da Sappa
musamman yanzu da ita ma Sappai ke ɗauke da ciki sai ta yi ta ƙulla mata sharri iri-iri ita kuma
Maman ba bincike ta hau Nazifa da faɗa tun malam Nur na tare mata har ya kai ya zuba ma
sarautar Allah ido.
Yanzu abinda ya fi damun Nazifa shine wata sabuwar dokar da Maman ta kafa,in Nazifa za ta yi
girki doli sai abinda Maman ta zaɓa haka kuma in za ta tafi unguwa doli sai da izininta ko da
kuwa malam Nur ya yarje mata.
Duk wannan bai ishi Maman ba sai da ta ƙara mata da wata dokar na banda yawan baƙi a
cewar ta suna zowa ne dan su zuga Nazifa,hatta da Rakiya ƙanwar Nazifa in ta zo Maman ta
fara habaici kenan.A na haka har cikin Nazifa ya shiga watan haihuwa wanda yayi daidai da
bikin malam Jabeer da Samira.
Tun satin bikin Nazifa ta fara sallar dare tana roƙon Allah ya sa Maman ta barta ta je bikin sai
dai kash tana fitowa Maman tace "ina za ki Nazifa kika wani ci uban shiri ko haihuwa ce?"cikin
faɗuwar gaba tace "Maman wajen bikin matar malam Jabeer kin san yau ne"baki Maman ta ja
tace "eh lalle shine kike sauri zaki fice kafin na gan ki ko?" "A'a Maman niyyata sai na shigo na shaida maki kafin na tafi"Nazifa ta faɗa muryata na rawa
idonta na cikowa da ƙwalla "to ba za ki je ba,in kuma kin fita wlh akan aurenki"Maman na gama
faɗa ta shige ɗaki ta bar Nazifa tsaye......
Domin shiga paid group 300 ne cakal via2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank DM +22795045822
[21/05 13:50] MRS SADAUKI: *SHAUƘIN SO*
```LoVe story```
By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI✍️}
*FCWA*☀️
________________________
Page 19-20
Duƙewa Nazifa ta yi tana jin mararta na ƙullewa ga wani azababen ciwo da ya dirar mata lokaci
guda,zaunawa ta yi dirshen ba tare da ta shirya hakan ba.Zufa ce ta karye mata,banda sunan
Allah babu abinda take ambata jin ciwon sai gaba ya ke ƙugunta ma ya ɗauka.Tana nan zaune
sai ga Balkis kamar an jefo ta,da sauri ta nufi Nazifa tana cewa "anty Nazifa lafiya kika yi zaune
da ƙasa ai sai ki ɓata kayan jikinki"shiru Nazifa ta kasa cewa komi sai jakarta da ta miƙa ma
Balkis "kira Nurrr" ta faɗa kamar ranta zai fita,wayar ta ciro daga jaka bugu biyu ya ɗauka "anty
Nazifa ce ba lafiya ka tawo"shine abinda Balkis ta faɗa ba tare da ta ko amsa sallamar malam
Nur ba.
Su na nan zauna Balkis sai faman jera mata sannu take sai ga malam Nur,ba tare da ya tsaya
tambayar ta mi ke faruwa ba ya ja ta zuwa mota.
Gidan baya ya saka ta Balkis ita ma ta zagaya ta shiga ta ɗaya ɓangaren.
Su na zuwa asibiti aka tabbatar masu da haihuwa ce,gida malam Nur ya koma sai ga shi sun
dawo shi da Maman kamin daga bisani ya kira Inna ya shaida mata.
Su na nan zaman jira sai ga yayar Inna,sama-sama suka gaisa da Maman bayan malam Nur ya
gaisheta "Allah dai ya sauke ta lafiya"cewar Lami yayar Inna da "Amen "dukan su suka
amsa.Sai da Nazifa ta kwashe wajen awa uku sannan Allah ya sauke ta lafiya,ta haifo
kyakyawar ƴarta mace mai kama da ubanta.Cike da murna nurs ɗin ta fito ta shaida masu
Nazifa ta haihu da sauri malam Nur ya tambayi abinda aka samu nurs ɗin tace "mace"a take
fara'ar fuskar malam Nur ta ɗauke dan shi a tsarin shi ya fi son ya samu namiji daga farko.
Balkis kuwa har da tsalle jin sun samu baby girl,rashin jin daɗi malam Nur ya nuna ƙarara
wanda har Maman ta lura da hakan.
Ganin hakan yasa ita ma ta ji sam ba ta son mace namiji take so dan burinta bai wuce a maido
sunan Ali duniya ba wato marigayi mijinta.Lami kuwa ta na can inda nurs ke duba lafiyar
baby,bayan sun gama bincike suka naɗota a zane suka ba ta.
Jiki sukuku Lami ta nufi su Maman dan ba ta san yadda za su ɗauki al'amarin da likitoci suka
shaida mata ba,da sauri Balkis ta nufi Lami tana kallon babyn wadda kallo guda za kayi mata ka
hango zallar kamarta da malam Nur.
Karɓar ta Maman ta yi tana kallon yarinyar kuma sai Allah ya jarabce ta da jin mugun
sonta,kallon idon yarinya ta fara yi waɗanda su ke farare tass sai ɗan boule ɗin su wanda ya ke
kamar h color dan bai da baƙi sosai.
Murya na rawa Lami tace "ikon Allah kenan! Haka Allah ya nufa ta kasance a *makauniya* ,sai
mu yi fatan Allah sa makantarta ita ce alheri gare...."da sauri malam Nur ya katse ta yace
"Makauniya?kamar yaya?"kafin ya karɓi babyn daga hannun Maman ya ƙura mata ido, tabbas
idonta sun nuna ko a kallo za ka gane.A razane malam Nur ya ɗago ya kalli Maman ya na cewa
"Maman dagaske fah Makauniya ta haifa mini"ba Maman ba hatta likitocin