Showing 1 words to 3000 words out of 21264 words
Chapter 1 - Maitar Ido Book Compelet Shamsiyya Lawwali Rabo
[27/07 à 11:37] MRS SADAUKI : *MAITAR IDO*️
️️️️️
HoRrOR story☠️
Na
© Chamsiya Laouali Rabo
#MRS SADAUKI✍️
*FCWA ☀️*
1-2
“ Gulbi ya zo” Laila ta faɗa ta na mai ajiye hullar gashin dokin da na bata ta sharce mini.
“Za mu je mu yi wanka da zarar mun gama” Farida ta ɗora.
“Ni dai ba zan je ba,ina da aiki sosai” na faɗa ina mai ci gaba da saƙa sabuwar hullar gashin
doki.
Duk suka matso kusa da ni kowacce da nata kalaman har suka ci galaba kaina na yarda ba tare
da na san abin da ke jirana can gulbin ba.
Na ce “ amma za ku taya ni sayar da abinci ”
“Mun yarda” suka haɗa baki wurin faɗa .
Sunana Sarah ,Laila da Farida ƙawayena dukkanmu ba za mu wuce shekara sha uku-uku
ba.Muna da ra'ayi kusan duk ɗaya,ciki kuwa har son wasar ruwa ko ruwan sama ake yi sai mun
san yadda muka yi muka fito muka yi wanka.
Ƴar talakawa ce ni,boyi-boyi shi ne aikina ina taya wata mai gidan gyaran gashi aiki da kuma
mai sayar da abinci aiki duk don na samu abin da za mu rufawa kanmu asiri ni da Kakata.
Fitowa muka yi mu duka ukun na rufe salon ɗin kafin mu kama hanyar da za ta kai mu wajen
magudanar ruwa.Tun a hanya muke ta zancen har muka iso,duk tsaye muka yi muna kallon
yadda ruwan ke ta zubowa daga wani dogon tsauni su na cika makeken wurin da muke kira
Gulbi .
Tuni sun shige sun fara wanka,ƙafa ta ɗaya na saka da niyyar isa wurin su sai na ji kamar an
riƙe ni.
“Sarah ki shigo mana” shine abin da suke faɗa ,na amsa da “ tooo” ina mai ɗora ɗayar ƙafar
tawa ta dama a can gaba.
Dodon kunnena na ji ya tsira kamar wacce aka cakawa allura,kafin kuma na fara jin wani irin
zafi daidai saitin zuciyata yayin da wani abu ke min yawo a maƙogoro kamar wacce ta ci yaji.
Na ɗaga idona na kalli sararin samaniya sai na ga hadari baƙi ƙirin ya na haɗuwa ,ya na yo
ƙasa kamar zai rubto cikin ruwan gulbin.Wani tsoro ne ya ziyarce ni nan take, kwacaaaa na faɗi
rub da ciki cikin ruwan “Saraaaaah!” na ji muryar ƙawayena wacce ita ce ta ƙarshe daga nan
ban sake sanin inda kaina yake ba sai tashi na yi na gan ni kwance kan yamutsatsar katifar mu.
A hankali na tashi zaune ina mai dafe gaban goshina da ke yi min mugun ciwo.
“Kin tashi?” Kaka ta tambaye ni ta na tsure ni da ido.
Na ce “ eh! Amma....” sai kuma na yi shiru.
“Ki kwanta ki sake hutawa na san kin galabaita ” ta faɗa tare da miƙo min wata ƴar
madaidaiciyar ƙwarya,na karɓa da niyyar shan ruwan da nake kyautata zaton magani ne sai
kuma na tsaya cak ina kallon can ƙasan ƙwaryar da nake hango wasu halittu masu motsin rai.
“Kaka mine ne nan kika bani?” na yi tambayar ina mai maido dubana gare ta.
“Ruwan floris ne” ta bani amsa, floris wata itaciya ce mai warkar da dukkan wata cuta
musamman wacce ta shafi mugaye,na sha jin masana na faɗar ta don ba zan manta har a cikin
wani littafin Mrs Sadauki na RUHIN ALJAN na ta taɓa jin an yi amfani da ita.Sai dai sam
wannan launin ruwan ba su yi kama da waɗanda aka yi siffanta na floris ɗin ba,duk da hakan
dai bai hana ni na sha su ba.
Ƙwaryar na ajiye ko minti biyar ba a yi ba na soma jin goshina na yin wata ƙara kamar irin ana
son ɓara shi gida biyu.Dunƙulallar kwanyata ce ta fara motsi a cikin ƙoƙon kaina,yayin da
hasken abin da ya faru da ni a cikin ruwan ya dawo min.
Kifaye ne irin masu rabi mutum suka tarbe ni a ƙarƙashin ruwan ,tamkar wata sarauniya haka
aka dinga yi mini wanka da wasu ruwa sannan aka shafa min wani abu cikin tafin ƙafa ,mundun
wuyana wani matashin saurayi mai hatsabin kyawu ya cire ya saka a wuyansa kafin ya cillo ni
gaɓar ruwa.Na ja wani dogon numfashi bayan na gama samun flashback ɗin da aka gama yi
min,wuyana na shafa tabbas babu sarƙar munduwar (irin sarƙar nan da ake yi da kuɗi mai
tambarin kan mutum....)
Kaka ta matso kusa da ni ta na cewa “Sarah faɗa mini mi kika gani?” shiru na yi na ƙo bata
amsa sai ma kwanciyata da na koma na juya mata baya.
Ta yi wani “hum!” kafin ta fice,ganin haka yasa ni kuma na tashi da sauri na jawo wani tsohon
akwatin ƙarfe da Kaka ke ajiyar shi shekara da shekaru don ko da na buɗe ido na ganta da abin
ta sannan in ciwon mutum yayi ƙamari wasu na zuwa ta basu magani.
Sosai na yi mamaki ganin tsofin hotuna waɗanda za su kai ɗaruruwan shekaru a cikin akwatin.A
hankali nake dubawa har na zo kan wata sarauniyar kifaye,yanayin fuskarta kawai zai tabbatar
ma ita ɗin muguwa ce.Abubuwan ban tsoro na ta ci karo da su waɗanda na cika kallo kuwa sai
na ji idona sun yi wani zuuuuu! Kamar su na zuƙo wani abu.Jin kamar motsinta kawai sai na yi
saurin na mayar da komai na tura akwatin.
“Ku shigo” cewar Kaka alamun baƙi ta yi ,don dama jefi-jefi ta kan same su.
“Sarah ki fita waje ina har mu gama” Kaka ta umarce ni.
Fitar na yi kamar sauran lokutan da in ta samu ziyara haka za ta ce na fita ni kuma sai na yi
amfani da wannan na je wurin wasa sai dai yau wani abu ya shiga kwanyata na son sanin shin
mine ne Kaka ke yi da kullum take fiddo ni waje?
Sai da na bari an ɗauki kamar minti biyar sannan na yi ƙoƙarin tashi daga inda nake saboda
yadda zuciyata ke azalzala ta sai dai abun mamaki ji na yi ƙafafuna sun riƙe ba zan iya tashi ba
kamar wacce ta samu shanyewar jiki.Ina nan cikin wannan hali har baƙin suka fito waɗanda
suka kasance mata biyu ne uwa da kuma wata budurwa.Abun mamaki sai a lokacin ƙafafuwana
suka saki,Kaka ta bini da wani kallo ta na mai jingina da lanlaga-langan ƙyauren ɗakinmu.
“Tun yaushe kika fara jin wannan canjin?” ta jefo mini tambaya.
Na miƙe tsaye ina cewa “wane irin canji?”
“Na son ganin abin da nake yi” ta bani amsa kai tsaye.Na turo baki gaba na ce “to mine ne kike
yi?”
“Ki na son sani?” ta tambaye ni,na gyaɗa kai alamar eh tace “sai kin faɗa min mi ya faru da ke
cikin ruwa” ban san ko mine ne dalili ba haka kawai na ji ina son ɓoye mata,na ce “babu komai
ni da na faɗa ruwa ta ya za a yi na san abin da ya faru? Ki tambayi su Laila kawai”
“To shikenan” Kaka ta faɗa amma tabbas a cikin ƙwayar idonta ina ganin ƙin yarda da zancena
wanda kuma ban san dalili ba.
Da dare bayan mun ci abincin Kaka ta soma yi mini gatana irin ta ababen tsoro,don ina son irin
wannan labaran a haka na soma jin bacci kamar kullum sai dai na yau ya sha banban da
sauran baccin da nake yi don kuwa idona a rufe suke amma ras nake ganin Kaka wacce take yi
mini wasu abubuwa da na kasa gane su. Gashin kaji ne na ga ta maƙala bayan kunnuwan ta,ban gama mamakin dalilin yin haka ba har
sai da na ga ta rikiɗe ta zama kaza sannan ta tashi sama.Maimakon ni da ke kwance cikin ɗaki
na zamana a nan a'a duk inda Kaka ta nufa ina kallo,gidajen mutane ta dinga bi ta kasaye rufin
ɗakinsu ban san dalilinta na yin haka ba sai da ta gaji da yawo kafin ta dawo ta gida.Siffarta ta
ɗauka ta mutum daidai nan kuma baccin gaske ya ɗauke ni ban farka ba sai washegari,babu
sallah babu salati haka na fita na yi fitsari na wanke ido.Wata irin yunwa nake ji,sai yanzu na
nufi Kaka wacce ke zaune kan tabarmar kaba ta na zuba taba cikin leda.Tsaye na yi cak ina
kallon ƙafafunta da suke sak irin na kaza,da sauri na ɗauke idona da na ga za ta ɗago kai.
“ lafiya kika yi tsaye nan?” ta tambaye ni.
“Yunwa nake ji,kuma kin san jiya ban je na taya Lantana sayar da abinci ba ballantana ta bani”
na bata amsa,ko kafin ta ce wani abu Sailuba ta shigo gidanmu da sallama.
Da sauri na gaishe ta,ita kuma ta shiga gaida Kaka kafin ta maido dubanta gare ni ta ce “jiya ba
ki gama mini aiki ba kika rufe shago ina makullin yake?”
Na waro ido kafin na fara lalubar riga ta ai kuwa na ci sa'a ya na ciki,na fiddo na bata ta karɓa
kafin ta ce “mu je to ki ƙarasa” haka na bi bayanta muka tafi salon ɗin inda take yi wa mutane
gyaran gashi da farce ,ta na yin kitso kuma da lalle.
Tun da na ga mota a parker na san hajiyar birni ce ta zo,don haka duk muke kiranta.Duk bayan
watan-wata take zuwa ta na sayen gashin mutane da ya zubo wurin gyara,ban san iya lokacin
da suke tare da Sailuba ba amma dai na san wannan shine business ɗin su.
Bayan Sailuba ta buɗe ɗan madaidaicin shagon ta ɗauko wata ƙatuwar leda ta zazzage duk
gashin mutanen da aka tara, sai a lokacin Hajiya ta shigo ta karɓa ita kuma ta bata maƙudan
kuɗi ta karɓe ta na godiya tare da cewa “hajiya sai kuma in kin sake dawowa”har mota ta yi
mata rakiya kafin ta dawo sai fara'a take ta na ƙirga kuɗin.Karon farko da na ji ina son sanin
dalilin business ɗin sayar da gashin mutane,na ce “anty wai don Allah mi hajiyar birni ke yi da
gashi nan”
“Ina na sani Sarah ? Ni dai ba ta bani kuɗina ba? Can ita ta sani in ma dai dafa shi za ta yi ta
ci.Ɗauki tsintsiya ki share wurin kafin mutane su fara zuwa sannan ki ɗauki allon sanarwa ki
fidda shi waje” ta na gama faɗa ta fice ta bar ni da tambayoyin da bani da amsar su sai dai na
sha alwashin sai na binciko su.....
*Gajeren labari ne*
[27/07 à 12:52] MRS SADAUKI : *MAITAR IDO*️
️️️️️
HoRrOR story☠️
Na
© Chamsiya Laouali Rabo
#MRS SADAUKI✍️
*FCWA ☀️*
3-4
Cikin sauri na share shagon na goge tile da kuma ƙaton bancin da aka jera mayuyuka na wanke
gashi da kuma wanda ake shafa wa bayan an fiddo mutum daga tukunya.
Zaune na yi na ɗauki hullar jiya da ban ida saƙawa ba,ina tsaka da yi sai ga anty Sailuba.Leda
ta miƙo min ta dambu na karɓe na huda bakin ledar na soma ci ina shan ruwa har na gama.
Ɗan ƙaramin rediyo anty Sailuba ta kunna muka fara shan kiɗa,wasu ƴan mata uku ne suka
shigo ɗaya na santa ta na zuwa gyaran gashi, biyun kuma baƙin fuska ne.
“Sannun ku da zuwa ku zauna,Sarah kawo musu ruwan sanyi Watsima sai yau aka dawo ina ta
zuba ido shiru” anty Sailuba ta faɗa fuskar nan tata cike da fara'a don a haka take saye
customer ɗinta.
Kan kujera duk suka zauna yayin da Watsima ta biɗe kai ta na cewa “wallahi anty Sailuba
gashina duk ya lalace dubi yadda ya koma,shi yasa na zo ki gyara min shi da kyau biki ake na
ƙawarmu”
Ruwan sanyin na miƙa wa kowacce leda ɗaya,kafin na zuba idona kan gashin Watsima da ya
cicire a gaba sannan tsayinsa ya rage ba kamar wancan zuwan da ta yi ba.
Anty Sailuba ta shiga tatataɓa gashin ta na cewa “ doli gashin ki ya lalace mana Watsima,ba ki
zuwa saloon sai fa in za ku yi sabga da ace ki na zuwa akai-akai wallahi tsaf za ki ga ya miƙe
yayi tsayi.Bari na nuna miki wani sabon man tado gashi,zan saka miki shi yanzu in na wanke
miki kai in ki yayi miki kuma sai ki saya” ta faɗa tare da zuwa gaban table ɗin ta ɗauko wata ƴar
kwalba ta miƙa wa Watsima kafin ta ce “ wannan ƙawayen ki ne?”
“Eh su ne nake baki labari waɗanda na ce miki ƴan uku ake kiranmu ” ta bata amsa.
Anty Sailuba ta ce “ Allah sarki ga shi kuwa har kun so ku yi kama da juna,su ba za a yi musu
gyaran gashin ba?”
Watsima ta kalle su kafin ta ce “ kun yi shiru sai kace wasu kurame ita wannan kitso za a yi
mata ita kuma wai a ɗinka mata gashin doki ya haɗe da na ta”
Anty Sailuba ta yi dariya kafin ta ce “ Sarah zo ki yi mata kitso ki aje hankali sosai kin ga yau ta
fara zuwa ina son ayi mata wanda za ta jawo mana customers” ta ida zancen cikin raha.
Wacce aka ce zan yi wa kitson ta ce “ wannan ƴar yarinya ? Na zata ke za ki yi min” sai ta ɓata
rai.
Anty Sailuba ta ce “ wai don a yi sauri ne na ce haka,amma in ni kike son duk ɗaya ne .Watsima
ke zauna ta wanke miki gashin in ta gama miki sai ta ɗinka wa wannan gashin dokin”
Ita Watsima ta san ni sarai,shi yasa ba ta yi gardama ba ta zauna na shiga wanke mata gashin
nata.Bayan na tsane shi da towel sai na soma saka mata kwarkwaro daga nan ta shiga
tukunyar busar da gashi.
Na maido dubana ga wacce zan saka wa gashin dokin na ce “ kin zo da mèche ɗinki ko saya za
ki yi?”
“A'a saya zan yi ai ku na sayar wa ko?” ta tambaye ni,na bata amsa da “ eh bari na ɗauko ki
zaɓa” kalolin na kawo mata bayan ta zaɓa ta koma ƙasa ni kuma na hau kujera na soma saƙa
mata ita tsawon lokaci muna abu ɗaya don akwai wuya kafin na je na duba gashin Watsima tuni
ya bushe kuwa.Na kashe casque ɗin ita kuma ta fito ta zauna kan kujera,mai na ɗauko da
niyyar shafa mata sai kuma na ƙure gashin da ido.
Wani haske na ga ya dalle gashin wanda kuma ina da tabbacin daga cikin idona yake,haka
kawai na ji ina son gwada wani abu da ban san taƙamaimai mine ne ba.Can ƙasan zuciyata na
raya ‘ gashi tsiro ka yi tsayi’ ai kuwa haka na ga ya ƙara tsayin na saki murmushi ni ɗaya zan
sake ƙara gwadawa Watsima ta ce “ wai ba za ki gyara mini gashin ba ne na tashi?” da sauri na
shiga shafa mata mai sannan na shace.
Daga can anty Sailuba ta ce “ kin ga kuwa wallahi gashin ki har ya ƙara tsayi yanzu da kika
shiga tukunya,mutane sun kasa ganewa ka wanke gashi gida ba ɗaya yake da ka zo saloon ba”
Cike da murna ita ma Watsimar ke duba ƴar jelar gashinta da na ɗaure,ta ƙara tsayin ba ƙarya
wanda kuma ni kaɗai na san wannan sirrin.
“ A gaishe ki ƴar yarinyata aikin ki na kyau” anty Sailuba ta faɗa bayan na kammalawa ɗayar ita
ma.
Wacce ta ke yi wa kitson ta yamutsa fuska ta na kallona kafin ta ce “ ɗiyar taki dai ƙazama ce
dubi jikinta kamar almajira da wani baƙi nata kamar zunubi”
Anty Sailuba ce ta shigar min “ a'a yau dai ne ta tsaya da dauɗa shi ma don ba ta shirya ba na
je na kirawo ta amma ta na da tsabta”
Ta tuntsire da dariya ta na kallon kaina wanda yake ɗauke da kitso ƙire-ƙire saboda yadda
banda gashi kafin ta ce “ da wani gashi nata kamar gammo! Ko da yake yawancin ƴaƴan masu
salon suke babu gashi duk aci gwaigwai ne”
Zuwa wannan matakin tuni raina ya ɓace amma ban ce komai ba sai gashinta da na ƙurawa
ido, dogo ne mai santsi duk yadda aka yi ta gama iri da Fulani .A take kuma baƙin ciki ya kama
ni ‘ Allah sa gashin naki duk ya zube’ na faɗa a zuci ina mai ci gaba da kallon gashin yayin da
idona kuma sai vibration suke suna min wani zuuuu!
“ Je ki yi wanka ki dawo kar ki biye mata,ni kam mine sunan ki?” anty Sailuba ta buge da
tambayarta bayan ta umarce ni na je na yi wanka.
“ Leemat” ta bata amsa nan ne na san sunan nata da haushinta kuma na fita na wuce gida.
Ina shiga na tarar Kaka ba ta nan sai ɗaki da ta rufe shi ma ba kwaɗo,na buɗe na shiga.Jakar
kayana na jawo don fiddo kayan da zan saka abun mamaki kuma sai na tarar da munduwa ɗina
a sama .Cike da murna na ɗauke ta na mayar a wuyana,tsakar gida na fito na cika buta da ruwa
na je na yi wanka da wani guntun sabulu .Ina fitowa na saka kayan da na fitar kafin na nufi
gidan anty Hinda mai sayar da abinci.Ta na gani na ta haɗe rai na san fushi take da ni saboda
jiya ban zo ba,na sosa ƙeya na ce “ ina kwana anty?”
“Lafiya!” ta amsa mini da shi kafin ta ɗauko wani bokiti mai ɗauke da wasu ruwa kamar sauran
wanka don har da sabulu-sabulu amma haka ta buɗe tukunyar mita ta juye su.
Sai kuma na ga ta kalle ni a ɗan daburce kafin