Showing 18001 words to 21000 words out of 21264 words
Chapter 7 - Maitar Ido Book Compelet Shamsiyya Lawwali Rabo
abar take
cewa ta basa minti biyu?’ na yi wa kaina tambayar a zuci ina jin farashin ƙunci,baƙin ciki da
takaicina su na ƙara yin sama.
A daidai wannan gaɓar mutum ɗaya ne kacal ke saurin yin nasara kaina wurin sauke
fushina,yanzu kuma ba ya tare da ni mutuwa ta yi mana yankan ƙauna.Haka na ci gaba da juyi
a bed ina ta ƙoƙarin tunkuɗe lamarin amma abu ya cuttura,sama da awa biyar ina cikin hali
guda.Dakyar na miƙe na je na shiga toilet,ko kayan jikina ban cire ba na sakarwa kaina
shower.Ina nan daga tsaye na ji kukan Maryam,Ammy kuma na yi mata faɗan doli ta koyi hawa
bene sannan ta jaddada mata nan ne ɗakinta kar ta saki ta kwana ɗakin Granny.
Ina jin lokacin da ita Maryam ɗin ke cewa “ Ammy shikenan ba zan sake komawa bacci ba tun
da kin tashe ni”
Ammy ta ce “ ni ma ai don baccin ya sace ni ne amma ai sam da ba zan bari ki kwanta can ba,ki
tabbatar kin yi wanka kin yi brush kafin ki kwanta” tsit kuma ban sake jin sautin muryoyinsu ba.
Na ja ajiyar zuciya kafin na tuɓe na yi wankan soso da sabulu na fito ɗaure da towel a ƙugu
,ɗan ƙarami kuma ina tsane gashina.
Zaune na tarar da ita ta buɗe trolly duk ta zubar da kayan da ke ciki sai wani turo baki gaba
take,gaban dressing mirror na tsaya na yi shafe-shafe sannan na zaɓo kayan bacci masu riga
mai sauka har ƙasa.Ina ganin lokacin da ta shiga toilet matse da kayan da za ta canza,da
wannan ni ma na saka nawa kafin ta fito na je na haye bed bayan na kashe ƙwan lantarki sai na
kunna fitilar bacci.
Tunani na soma yi kan shuɗaɗiyar rayuwarmu ni da Abakar,«aboki don ba ka da ƙanwa ne da
ka ji irin yadda nake ji,Maryam komai ce nawa.Farin cikinta ya fi min komai daɗi a duniya,aikin
nan ma domin ita da Umma nake yinsa.Na ci burin yi wa Maryam kayan ɗaki na kece raini a
matsayina na waliyinta maɗaurin aurenta» wannan na ɗaya daga cikin zantukan da yayi min
game da Maryam.
Yadda ta fado jikina ta bi ta kaina yasa ta katse min tunanin,“ ni wallahi sanyi naka ji ba don na
yi wa Ammy alƙawarin ba,in na yi wankan nan shegiya nakai ” ta faɗa cikin mita tare da gyara
kwanciyarta ta ja bargon da nake ciki ta rufa.Duk da ta rufa ɗin bai hana ta rawa sanyi ba,kamar
wanda aka yi wa doli na ɗan matsa kaɗan sai gani kusa da ita sosai.A hankali na ɗan kwanta ta
samanta na yi mata rumfa da ƙirjina,hannunta na ji gefen cikina ta sarkayo shi haɗi da riƙe wa
gam ta ce “ ina jin sanyi sosai”
Bargon na ida ja ya rufe mu har wajen kai,a hankali kuma na matsa fuskata kusan tata ta yadda
muna jin numfashin juna.Ƙamshin turarenta ne ya sakar min wata kasala da na kusanci
wuyanta,ban san lokacin da na saki wani gauron numfashi ba ina mai sake saka ta ƙirjina.Tuni
Maryam ta fara mitsirniya,gefen wuyanta na soma aika ma sumba kafin na yi sa'ar lalubo
bakinta na fara kissing.Sam ba ta yi ƙoƙarin hana ni ba da alamu ma ta na jin daɗin haka don
sai ƙara riƙe ni take, wannan yanayin da na tsinci kaina sam ba zan iya faɗar yadda yake
ba.Bugun zuciyata ne kawai ke ta tsananta ya na bada sauti na musamman,sama da minti
talatin kafin na janye daga jikinta na koma gefe ina mayar da numfashi.Blanket ɗin na janye na
maido shi iya ƙirji,idona a lumshe ina jin raina yayi ɗan sanyi ba kamar ɗazu ba.Na kai hannu na
jawo ta na ɗora kanta kan ƙirjina yayin da kuma hannuna ke kan bayanta.Murya can ƙasan
maƙoshi na ce “ kin bar jin sanyin ?” kamar wata munafuka ta ce min “ eh!” “ ok yi bacci” “
uhumm !” shiru duk muka yi ina ta mamakin kaina ,ɗaya ɓangaren kuma na sakawa Ammy da
alkhairi da ta haɗa auren nan...
[29/07 à 09:31] MRS SADAUKI : *IBRAHEEM*
```soldier man```
© Chamsiya Laouali Rabo
#MRS SADAUKI✍️
*FCWA ☀️*
#Sadaukarwa ga duk waɗanda suka taɓa rasa wani jigo nasu a soja.Allah jadadda rahama a
gare ka Yayana AbduRashid
7-8
Kiran sallar farin ne ya tashe ni daga dadaɗan baccin da nake.Ina ware ido na yi tozali da fuskar
Maryam kwance kan ƙirjina sai baccinta take,moments ɗinmu na jiya ya dawo min na ɗan yi
murmushi ina mamakin kaina .Janye ta na yi na nufi toilet na yi wanka,da na fito na shirya caf
cikin jallabiya ruwan ƙasa .Sai da na yi nafiloli sannan na wuce masjid ,bayan mun gamo sallah
na dawo gida har yanzu ba ta farka ba.
Blanket ɗin na yaye ina mai kiran sunanta “ Mary ? Mary tashi ki yi sallah” ta ware idonta kaɗan
kafin ta sake lumshe su har da gyara kwanciya ta ci gaba da baccinta.Na dafe goshi na ce “
Ammy kin kawo min aiki” ƙara tashe ta na yi,ta na gunguni ta tashi zaune ni kuma na fita na
ɗauki key na je na buɗe mota na ɗauko takardun Daddy ya bani.Ina komawa bedroom na ga ta
sake komawa bacci,raina ne na ji ya ɓace cikin ɗaga murya na ce “ keee! Tashi na ce har yanzu
ba ki yi sallar ba ne ko me”
A firgice ta tashi ta na kuka tare da zuba min manyan idonta,“ ba za ki wuce ba kenan?” na faɗa
ina nufo ta da sauri ta ruga ta shige toilet ina jin ƙarar shower na tabbata wanka take.Falo na
koma na soma yin aikina,wani iri nake ji na rasa gane mike damuna ma a yanzu.
MARYAM
Wani irin mugun tsoron Ibraheemu ne ya shige ta,duk yadda take da tsiwa sosai take shakkar
idonsa.Ta na shiga wanka ta soma yi kamar yadda Ammy ta sanar da ita kullum kafin sallar
asubah ta fara yin wanka ta yi kuma brush.Maclean ɗin da ta gani ta matsa ta wanke
bakinta,soso ma da nasa ta yi amfani sannan ta fito ta saka rigar sallah ta gabatar.Bayan ta
gama ta soma karatun Alkur'ani inda ta iya kafin ta zo wanda Granny ta yi mata,ganin ta na ta
yin gargada yasa ta yi shiru kar ta yi saɓo.
Miƙewa ta yi ta gyara shimfiɗar gadon ,ta fesa turare wanda tun jiya Ammy ta nuna mata
ma'ajiyarsa.Toilet ma sai da ta je ta wanke ta sannan ta fito ta haye bed sai bacci.
IBRAHEEM
Ina nan zaune ina aiki kiran Ammy ya shigo wayata, Allah na gani abin da yasa ban je na
gaishe su tun da asubah ba don kar ta yi min zancen tafiyarta ne.
Kiran na ɗauka ko kafin na ce wani abu ta ce “ ka sauko ƙasa” sai kuma ta kashe.
Na ja ajiyar zuciya ina jin wani yanayi kafin na miƙe,sai da na duba bedroom na ga Maryam ta
koma bacci sannan na sauka.
Ƴan aiki ke ta faman gyaran falo ana ƙara ƙawata shi ,haka na wuce sai gaishe ni suke.Sashen
Granny na wuce da sallama a bakina,bayan na gaishe su ne na maida hankalina ga Ammy.Ta
sakar min murmushi ta ce “ zan tafi Heemu sai in na dawo wajen suna”
Da sauri na sauke idona ƙasa ina cewa “Ammy don Allah ki zauna”
“ Mu je ka sauke ni na hau mota”
Na ɗago a karo na biyu na kalle ta,sam babu alamun wasa kan fuskarta hakan yasa na dubi
Granny na ce “ don Allah Granny ki sa baki mana”
Ta ce “Baba tun da ta ce tafiya za ta yi na san babu wanda zai canza mata ra'ayi,haka halin
Maimuna yake yadda ka san mutanen farko sai shegiyar kafiya ”
Ba don na so ba haka na ɗauki ƙaramin trollynta muka fito,har mota Granny ta yi mata rakiya ta
na mai cewa “ wancan tsohon ya ƙi fitowa haka za ki tafi ba ku yi ban kwana ba”
Ammy ta ce “ bai komai Mama ai na yi abin da ya kawo ni” addu'a sosai Granny ta yi kafin mu
wuce.Gidan Bus na kai ta don Ammy sam ba ta son doguwar tafiya cikin ƙananun motoci,har
muka kai ta na yi min nasiha game da zaman aure da kuma jaddada min girman amana .Har
ciki na yi mata rakiya,na kunna mata AC seat ɗinta kafin na fito.Ban baro wurin ba har sai da na
ga motarsu ta tashi,ina isa gida lokacin ƙarfe takwas na safe ya buga.Sashen Daddy na duba
alamun har yanzu su na ciki ba su fito ba,wani takaici ya rufe ni a haka na haye sama.
★A ɓangaren su Daddy kuwa ya na shiga Zeey ta cika bahon wanka ya shiga kamar wani
ƙaramin yaro haka ta yi masa wanka.Daddy irin mazan nan ne masu budurwar zuciya sam bai
ganin ya girma shi dai burinsa kawai ya ji shi jikin mace ,a kullum bai gajiya haka kuma bai
kwanan banza.Yawan buƙatarsa na ɗaya daga cikin abin da yasa ya yi wa Ammy kishiya don
an yi rashin sa'a ita ba kalarsa ba ce,auren kuma bai je ko ina ba ya mutu haka yake ta
aure-aure har Allah ya kawo shi ga Zee wacce ta kasance bazawara ba ta taɓa haihuwa ba
fitinarta yasa mijinta ya sake ta.Yanzu kuma da ta auri Daddy sai ta ga kamar tasu ta zo daidai
duk da ta fi zaton ta fi shi juriya, wannan kuma har da don ita da sauran ƙarfinta ba ta yi
shekarunsa ba.
A wannan daren tamkar sallah haka su Daddy aka ta more aure,sai kace wasu karnai.Sallar
asubah ma yau a ɗaki yayi ta,sai wuraren ƙarfe tara suka tashi suka yi wanka Zee ta taimaka
masa ya shirya cikin kakinsa na sojoji ta ɗora masa hulla sannan suka fito falo.
Jin ta yake kamar ƙwai ya na jin wata muguwar ƙaunarta,ba don komai ba sai don ta iya jure
nauyin buƙatarsa.
Kan dianing suka zauna,da sauri mai kula da lafiyarsa ya matso ya auna abincin da wata na'ura
aka tabbatar normal yake ba komai sannan Zee ta zuba musu suka fara ci ta na masa hirar
soyayya.
“ In ka tafi zan yi kewar ka sosai Baby ”.
“ Zan dawo ai kar ki damu,duk inda zan je ki na maƙale a birnin zuciyata ” Daddy ya faɗa ya na
wani murmushi.Zee ta rausayar da kai ta ce “ banda kallon mata Baby don in ka ce za ka yi min
kishiya zan kashe kaina”
Da sauri ya ce “ haba don Allah bari yi min zancen mutuwa,na yi miki kishiya akan me? Sai in
canzawa kika yi kika dinga min rowar kan ki”
Ta yi wani fari da ido ta ce “ haba Baby in na yi wa rowa ribar mi zan ci? Ai ni taka ce” cike da
murna Daddy ya kamo hannunta ya ce “ Baby kin ci kyautar mota ” Zeey ta yi wani irin ihu tare
da rungume shi,daidai nan Granny ta fito a gaban idonta.Ta girgiza kai cike da masifa ta ce “
Allah wadaran naka ya lalace! Yanzu kai Isah mi na faɗa ma?” da sauri Zeey ta janye daga
jikinsa ta duƙa har ƙasa ta ce “ ina kwana Mama?”
Ba ta amsa ba sai ci gaba ta yi da cewa “ daga yau ku dinga zama can falon ku kuna cin abinci
na soke fitowa nan,in kuma wallahi ka ci gaba zan bar ma gidan ka”
Hankalin Daddy ya tashi don ya tsani fushin Granny,haƙuri ya soma bata kafin ya je ya kama
hannunta ya zo ya zaunar da ita kan kujera.Da kansa ya zuba mata abincin cike da kulawa,ita
kuwa Granny hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba.
Ta saki murmushi ta ce “ Allah yi ma albarka ”
“ Amen Mamana ki daɗe ki yi ƙarko,sai kin yi Hajiya Mama uwar shugaban sojoji kike doli a
lalaɓa ki a sannu in ba haka ba a tayar da yaƙin duniya na uku” Daddy ke faɗa har da wani
sunkuya wa ya na yi wa Granny kirari.Ranta fari ƙal ta kai hannu ta ɗora kan kafaɗar shi ta ce
“tashi ya isa haka nan wuce ka tafi aiki kar ka makara” Sai da Daddy yayi kiran waya ya shaida fitowarsa kafin ya fita,masu take masa baya ne suka yi
masa rakiya har motarsa kafin su fice.
Zee kuwa kasa zama ta yi kawai ta miƙe ta bar Granny nan ta na cin abinci.Ɗaki ta
wuce,akwatin da ta zuba kayan matanta ta buɗe ta zaɓi waɗanda za ta yi aiki da su na daren
yau.Murmushi kan fuskarta ta soma jijiƙa su a gorar ruwa ta na girgiza wa,ita kaɗai ta san irin
tanadin da ta yi wa Daddy.A fili ta ce “ ba dai lamarin nan kake so ba,yau zan fito ma da asalin
maitata sai na gana ma baƙar wuya ” sai kuma ta kece da dariya.
IBRAHEEMU
Ina shiga ɗaki ko ta kan takardun ban bi ba na wuce bedroom, doguwar jallabiyar na cire na
tsaya iya wandon cikin.Hasken ɗakin na kashe na raɓa gefen Maryam,wannan tiririn da
zuciyata ke yi na baƙin cikin Daddy na can da wata baƙar amaryasa nake son na kashe.
Abin da na lura shine kiss na yaye damuwa,ban taɓa sanin haka ba sai jiya da na yi wa Maryam
shi.Bakina na ɗora kan lips ɗinta ,tun ina yi a hankali har na soma zaƙewa saboda abubuwan
da nake ji su na ratsa ni.Zuciyata ce ta ƙara ƙarfin gudu jin Maryam na mayar min da martani,ba
sai an faɗa min ba ita ma koyo take kamar dai ni tun da jiya ne muka fara sanin al'amarin.Kiss
ɗin ne na ji bai isa na haɗa da romance,rigar jikinta na yi nasarar cire wa na soma sarrafa
ta.Kuka ta soma yi min wannan yasa na mirgina baya ina mayar da numfashi,ta tashi zaune ta
ɗauki rigarta ina kallonta na ga ta mayar da abar ta kafin ta dire daga bed ɗin.Sam ban yin
ƙoƙarin hana ta ba sai ma haushin kaina da na ji,ƴar ƙanƙanuwa yarinya ta kwance min tunani
abun takaicin kuma ƙanwar abokina.Na ja wani numfashi tare da ɗauko pilow na rungume.Shiru
na yi ina tunanin kaina ‘ yaushe na samu wannan canji? Sanina dai sai lokacin damina kawai
sha'awa ke damuna,ko kuma in an yi ƙololuwar sanyi’ sai kuma na ja tsuki a fili wani sashen
zuciyata na bani amsar da ‘ ƙila don yanzu an yi maka aure ne an gama ka da mace ɗaki guda’
da sauri na miƙe na shiga toilet jin abin na sake yin gaba-gaba.
Shower na sakar wa kaina,ina tsaka da wanka na soma jin wayata na ruri.Kiran Ammy ne don
waƙarta ta musamman ce,a gaggauce na yi wankan na fito.Ina maida kiran amma ba a
ɗauka,gabana ne ya shiga faɗuwa ina shirin aika wani saƙon text ɗinta ya shigo ``` Heemu ƴan
ta'adda sun tare motarmu a hanya ba zan iya ɗaukar kira ba don tuni sun sauko mu ƙasa an
fara lalubar wasu ma```
Ji na yi kamar an buga min wani ƙaton dutse a kai,da sauri na saka kakina na soja da
bindigogi.Jikina har rawa yake,ko kallon inda Maryam take ban yi ba na fita da gudu-gudu.Ina
cikin mota na kira Daddy na shaida masa amma yake min zancen banza wai kar na je na jira
zai tura sojoji amma ina tuni na soma bibiyar layin Ammy na ƙure gudun mota.
Tsawon lokaci ina sharara gudu kafin kira ya shigo da lambar Ammy,na ɗauka da mamakina sai
na ji muryarta ce.“Sun yi tafiyarsu sun gudu! Sun bar mu lokaci guda bayan sun yi mana mugun
duka Heemu ” na rumtse ido haɗi da jan wani dogon burki ina sauraren yadda Ammy ke rera
kuka,dakyar na ce “ gani nan zuwa Ammy don Allah ki bar kuka ki na ɗaga mini hankali” “ Kar ka zo Heemu yanzu ai za mu tashi daga nan...” daidai nan kiran ya katse,a ta na'urar da
na jona nake bibiyar Ammy na ga sun fara gusawa daga wurin alamun motar ta tafi.Amma duk
da haka bai sa na koma ba,haka na ci gaba da gudun kusan a tare muka shiga gidan Bus ɗin ni
da motarsu.
Ko jira ban yi ba na nufi motar,ana buɗewa na shiga ciki na riƙo Ammy.Fuskarta ta yi ja sosai ga
sawun yatsu nan kwance raɗau,haka na fiddo ta na kai ta motata ina jin haushin kaina.Asibiti na
wuce da ita duk ƙoƙarin hana ni da ta yi a cewar ta lafiyarta lau kawai kanta ke ciwo,sai ga shi
da muka je asibitin an ce jininta ya hau.Ƙarin ruwa suka saka mata,ina daga gefenta zaune ina
saƙar zuci so nake yi na yi mat tambayoyi amma ina jiran har ta dawo hayyacinta.
Kamar ta san abin da nake saƙawa a rai sai cewa ta yi “sun tafi da wasu daga cikinmu Heemu”
Na dube ta da sauri,idonta na lumshewa take ci gaba da cewa “da dukkanmu za su tafi da mu
sai ogansu ya samu kira bayan ya dawo daga wayar ne yake cewa a tafi da iya maza kawai a
bar matan”
“Da yayi wayar ba ki ji abin da ya ce ba?”na yi tambayar zuciyata na mugun bugawa,Ammy ta
ce “ban ji ba,sai dai lokacin da ɗaya daga cikinsu yake tambayar ogan mi yasa ba za a tafi da
mu duka ba sai ya ce umarnin Dagaci ne”
Dagaci babban ɗan ta'adda ne shine shugaban duk wasu manyan-manyan ƴan daba don
ƙungiyarsu guda ce. Shiru na yi ina wani tunani haɗi da zargin da ban son ya zama gaskiya ,sai
dai duk yadda nake son tunkuɗe zargin abin ya cuttura sai ma wasu abubuwa da suka faru
masu kamanceceniya da suka shiga dawo min.