Showing 6001 words to 9000 words out of 21264 words

Chapter 3 - Maitar Ido Book Compelet Shamsiyya Lawwali Rabo

acici ga abincin ki can tun ɗazu na ajiye miki shi” ta nuna mini da yatsanta na je na ɗauko.

Zazafen tuwon shinkafa ne da miyar kuɓewa sai ƙamshi yake da alamu kuma girkin gida ne,ido
kawai na ƙura ina kallon abincin wanda zuciyata ta shaida mini ‘an saka maganin mallaka’ da
mamaki na ɗago na dubi anty Sailuba na ce “wai anty tuwon nan tun na yaushe ne?”

Cike da masifa ta ce “babu ruwana da iskanci kamar ya na yaushe ne? Na sunan haihuwata.”
“Daga tambaya?”
“Ni na girka shi da kaina,kin samu ma na zuba miki sauran abincin mijina duk da uban kishin da
nake da ”

Anty Sailuba ta na da aure sai dai kusan shekara biyar ko ɓatan wata ba ta taɓa yi ba,ta na da
mugun kishi sannan ta na son mijinta sosai kamar ta mutu.Duk in ta ji labarin yayi sabuwar
budurwa haka za ta samo lambarta ko kuma ta je har gidansu yarinyar ta ci mata mutumci.
A zuci na ce ‘shikenan Bilal ka shiga uku , Allah kaɗai ya san bayan maganin mallaka wane iri
ake baka kuma’ a zahiri kuma cewa na yi “a'a gaskiya ba zan ci tuwon nan ba,yo ai in na yi
hakan kamar na nuna raini ne a gare shi ” na kuwa rufe abincin.
Anty Sailuba ta ƙure ni da ido kafin ta ce “ki ɗauka ki ci babu ruwana da shashanci”
“Allah anty na ƙoshi ba zan ci wannan ba” na bata amsa don kuwa na san abu da magani ba
zan cuci kaina ba.
“Ke kika sani yi ta zama da yunwar don kan ki” ta faɗa tare da ficewa.Ina zaune ina tunanin ina
zan samu abinci sai ga ƙawayena,da murna muka rungume juna kafin na ce “ ku shikenan tun
ranar nan ba ku neme ni ba”

Laila ta ce “ ke ɗin ce kin bamu tsoro sosai nitsewa kika yi cikin ruwa fa,hankali tashe muka je
nemo masu ceto har sarkin ruwa fa sai da ya shiga neman wai a bai gan ki ba ” sai ta yi shiru
hakan yasa Farida ci gaba da cewa “ amma Kaka na zuwa ta yi wasu bubuwa sai ganin ki muka
yi gaɓar ruwa kamar wacce aka jefo,to shine fa duk muka ji tsoro saboda mutane na ta

cece-kuce akan lamarin”
“Don mi?” na yi tambayar,sai da suka kalli juna sannan Laila ta ce “ wai Kaka bokanya ce” na
waro ido Farisa ta harare ni ta ce “ kamar ki ce ba ki yarda ba don dama tun tuni ana zarginta
da hakan”

Na haɗe rai na ce “ kun ga ban son wannan...” Laila ta katse ni “ to in ba boka ba wake bada
magani? Kar ki manta in ciwo ya ta'azzara har gidanku ake zuwa karɓar magani”
“Ni dai duk a bar wannan zancen yunwa nake ji” na faɗa don haka kawai na ji ban so a ci gaba.
“ Ina da kuɗi mu je tashar kwaɗayi ” Farida ta faɗa ta na buɗe tafin hannunta kuɗi ne kuwa
masu ɗan yawa,na ce “ ku je ku biyu ku sayo ni zan zauna nan kar anty Sailuba ta yi faɗa ” ba
su musa ba suka fita ai kuwa ina nan zaune sai ga wata mata ta kawo ƴarta ƴar shekara goma
a wanke mata gashi.

Zaunar da ita na yi na soma wanke mata da sauri don haka kawai ban so ace ita ma ƴar
mitsitsiyar nan an sayar da gashinta ga hajiyar birni.Sai dai duk saurin da nake a banza,ina daf
da idawa anty Sailuba ta dawo idonta duk sun yi ja sosai.Sama-sama suka gaisa da Uwar
yarinyar kafin ta samu wuri ta zauna ta na kallon yadda nake yin komai.Bayan na gama mata ta
biya kuɗi suka tafi,gashin yarinyar nake son ceta sai dai na rasa ta ya zan yi haka.

Anty Sailuba ta ɗauki masharcin da na shace mata kai ta shiga cire gashin da ya laƙe,ina ji ina
gani ta jefa shi cikin gwangwani.
Su Farida suka dawo,taliya ce suka sayo mini sai hanjin ligidi na karɓe na shiga ci yayin da anty
kuma ta aike su .
Haka muka yi ta samun customer har lokacin tafiya ta yayi gidan anty Hinda,ina zuwa sai na ga
ta haɗe rai amma ban damu ba na shiga taya ta sayar da abincin yau ma dandanan muka sayar
sai dai ko loma ɗaya ba ta bani ba.
Na yi rau-rau da ido na ce “ anty ina nawa”
“ Ni ai ba zan sake baki abinci ba,yau tun safe Kakar ki ita ta tashe ni daga bacci ta yi ta min
masifa ta na zagina wai kar na sake baki abinci to wannan ma yasa na yanke shawarar
sallamar ki” ta faɗa tare da ɗauko kuɗi ta miƙa mini.

Na ƙi karɓa ina bata haƙuri amma ta ƙi haƙura har gidanta na bita,muna shiga ƴarta budurwa
mai sunan Sharifa ta taso cike da wulaƙanci ta na cewa “ uwar mi kika zo yi gidanmu? Dama shi
talaka bai iya samun wuri ba,ɗazu don rashin mutumci kika turo mana wannan tsohuwar Kakar
taki ta zo ta yi wa mutane hauka.Duk alherin da muke yi muku ba ku gani ba har da wani cewa
an zuba miki guba a abinci”
Anty Hinda ta ce “ kin ga Sharifa zo ki ƙirga kuɗin nan mu ga ribar da muka samu” ta na
hararena ta karɓi kuɗin da ke cikin wata roba ta koma gefe ta na ƙirgawa ta na masifa “ daga
yau ni zan dinga taya uwata sayar da abinci sai ki tafi ba mu buƙata” da ta ga na ƙi gusawa ta
juye kuɗin ƙasa tare da cika robar da ƙasari ta watsa min a fuska har sai na ji tsoro.Duk wannan
bai ishe ta ba sai da ta wani ja ni ƙiiii ta cillo ni waje ,zuciyata ce ta soma tafasa yayin da duk
illahin jikina nake jin ya ɗau zafi kamar garwashin wuta.Ni kaina ban san lokacin da na ɗauki

hanyar Gulbi ba,kawai haka na ji a can ne kawai zan samu salama.Tun daga nesa da na fara
hango ruwan sai nake jin kunnuwana na amsa kira, ina isa daidai gaɓarsu na yi tsaye ina kallon
yadda suka soma yin zillo tuni munduwar wuyana ta fara motsi ta na ɗaukar wani haske.Ido
biyu ba cikin bacci ba na soma jin tafin ƙafata na yi mini ƙaiƙayi,ko kafin ƙyaftawar ido na rikiɗe
na zama Siren (sirène ) ina daga kwance gaɓar ruwa nake ƙarewa bindin nawa na kifi kallo sai
motsi yake ya na fitar da haske.Kamar wata kifanya na yi tsalle na faɗa ruwan,ƙasa sosai nake
nitsawa ina jin wani sanyi da daɗi na ratsa ni.

Idona buɗe suke taram haka kuma sheɗa ta daidai take babu alamun gargada irin in mutum ya
shiga ruwa.Ina tsaka da yawo cikin ruwan na soma jin dariya,na juya na soma bin inda sautin ke
fitowa har na iso kusan wani dutse.Wata budurwa da saurayi na gani su na wasa haɗi da hirar
masoya,su ma iri na ne rabi mutum rabi kifi.Budurwar na gani na ta nufo ni ta na cewa “ waooo!
Princess” ƙyafƙyaf kawai na yi da ido ina kallonta har ta iso gare ni ta na shafa goshina wanda
sai a yanzu na farga akwai wani tambari a jikinsa na haske.

“ Ya aka yi kika zo wannan ƙasar? Ko wani aiki kika zo yi?” abun mamaki kasa magana na yi
duk da kuwa na so buɗe baki,saurayin ne ya zo da sauri ya ja ta gefe ya na cewa “ Sarlah ya
kike tsayuwa kusa da ita ko ba ki tambarin Masarautar Goma ne da ita ba?” haka suka tafi suka
bar ni cike da mamaki.

Sama-sama na soma yi har na fito gaɓar ruwan ,so nake na koma gida.Sai bayan na fito ne
bindin ya ɓace na dawo da ƙafafun mutane,na saki murmushi ina jin wani daɗi yayin da kuma
zuciyata ta yarda ta lamunce mini tabbas ina da wata baiwa ba daidai nake da sauran mutane
ba. Ina zuwa gida na ga takalmin mutane a ƙofar ɗakinmu,ban nemi izini ba na shiga.

Sai na tarar da wata mata a zaune yayin da Kaka kuma ke ta wasa da ɗiyan wuri ta na zayyano
mata abubuwan da za su faru gobenta.Wato dibo Kaka take,macen ta yi godiya ta biya kuɗi irin
sosai ɗin nan kafin ta fice.Na dubi Kaka wacce ke ta faman ƙirga kuɗi kamar ba ta gan ni ba,na
yi gyaran murya na ce “Kaka...” ta yi saurin katse ni da “kin ga Sarah wuce ki bani wuri ban
ƙaunar ganin ki,rainon ki bai yi mini rana ba sam.Ban ga amfanin zama da ke ba don haka ki
kwashi inaki-inaki ki bar min gidana”


Wata irin dariya na soma wacce sama ban lura da ruwan da suka fara ɓulɓulowa daga ƙasa ba
har sai da suka kawo daidai wuyana.Tsit na yi ina kallon Kaka wacce ke ta ƙoƙarin fita daga
ɗakin amma ta kasa,“za ki mayar da ruwan nan ƙarƙashin ƙasa ko sai sun kashe ni ” ta faɗa a
tsorace ta na riƙe bango hakan kuma sai ya ƙara bani wata dariyar amma na gimtse munduwar
wuyana na lalubo na riƙe ina yi wa ruwa magana da idona,a sannu a hankali suka yi ƙasa har
suka ƙwafe.
Da wani irin saurin Kaka ta cillo ni waje ta na mai cewa “ashe duk yadda nake tunani kin wuce
nan,ke annoba ce ba zan iya zama da ke ba”

Zuwa wannan lokacin na fahimci Kaka ba da wasa take ba,hakan yasa hankalina ya tashi na
soma roƙonta “Kaka in kin kore ni ina zan je? Ke ce komai nawa ke kika raine ni ban san kowa
ba sai ke”
“Ban haɗa komai ba da ke wallahi tsintar ki na yi da tunanin za ki yi mini amfani a gaba ki gaje
ni ashe musamman da na ga ki na ɗauke da *MAITAR IDO* ashe ban san bala'in naki ya wuce
nan ba sai yau na ida ganewa Mamy Water ce ke ”
Idona na zubar da ƙwalla nake kallon Kaka,tuni kuma ƙwaƙwalwata ta soma hargitse wa.Ana
kiran sallar magrib haka Kaka ta jefo ni waje ni da jakar kayana ta kama gidanta ta rufe,kan
dakali na zauna ina ta wasiƙar jaki har aka yi sallar isha'i.Ganin dare na ta ƙara yi na miƙe tsaye
na soma tafiya,direct gidan anty Sailuba na nufa don ita ɗaya ce yanzu ta rage min wacce nake
tunanin za ta zame mini bango.Da sallama na shiga gidan,tun kafin na ƙarasa nake jiyo sautin
muryar mijinta Bilal ya na cewa “wallahi Sailuba ko mi za ki yi sai na ƙara aure,kuma goben nan
zan je na yi wa Hajiya bayani ta samo min mata cikin danginta tun da ni ko na nema ba za ki
bari ba” kai na kutsa na shiga ɗakin,anty Sailuba ta juyo ta na kallona a zuciye “uban mi kika zo
yi kuma yanzu cikin dare?” ban bata amsa ba sai mijinta da na ƙure cikin ido ina mai taɓa
munduwa ta ni kaina ban san dalilin yin haka ba.
“My Lub Baby wane ni na yi miki kishiya don Allah ki kwantar da hankalin ki ina mugun son ki”
Bilal ya faɗa ,ni kuma na saki murmushi ashe duk anty Sailuba ta ga komai.Hannuna ta ja
muka fito waje kafin ta ce “ke mine ne kika yi wa mijina? Ko ke ma bokancin kike yi kamar Kaka”
na girgiza kai na ce mata “a'a ina da MAITAR IDO ne mai sarrafa abin da duk nake so,kin ga
gashin Leemat ma ni ce nan na mayar da shi yanzu kuma na juye tunanin mijin ki babu ke babu
kishiya” anty Sailuba ta rungume ni ba tare da tunanin wannan ɗin fa abun gudu ne,ta ce “ina
na za ki je?” bayani na yi mata kan cewa Kaka ta kore ni daga gidanta sai a lokacin kuma na ji
hawaye ,ta goge mini su ta na cewa “sai ki zauna gidana” sai ta ja hannuna muka koma ciki.....




Ga waɗanda suke son fara payment ƙofa a buɗe take 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA Ecobank sai ki turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822
[29/07 à 09:28] MRS SADAUKI : *MAITAR IDO*

HoRrOR story☠️

Na
© Chamsiya Laouali Rabo
#MRS SADAUKI✍️

*FCWA ☀️*


9-10

Ko da muka koma ciki mijinta bai falo alamun ya na can ƙurya ,anty Sailuba ta kai ni wani ɗaki
ɗan madaidaici babu komai cikinsa sai dangin abinci.Ta je ta ɗauko tabarma da kuma wani
ƙaton bargo ta shimfiɗa min,“ ki kwanta a nan zuwa gobe da safe in Allah ya kai mu za mu sake
yin magana” kai na jinjina mata ta fice ta bar ni nan.
Na haye shimfiɗar na kwanta ina tunanin furicin Kaka wai ba ta haɗa komai da ni ba tsintata ta
yi.Na juya kwanci wani sashen zuciyata kuma na hasko min wulaƙanci da Sharifa ta yi min ƴar
anty Hinda.Na lumshe ido ina mai kai hannu na riƙe munduwar wuyana,‘ ko ya ake yi mutum ya
je wannan duniyar da Kaka ta kai ni ? ’ na tambayi kaina a zuci abun mamaki kuwa zuciyata ce
ta soma yin nauyi kamar an ɗora dutse kafin in samo amsar tambayata .Cike da jin daɗi na yi
bacci wannan daren,tun da asubah anty Sailuba ta shigo ɗakina “ tashi ki yi sallah” shine abin
da ta faɗa ,duk da ban taɓa yin ta ba hakan bai hana ni miƙewa ba na fito.Ƙofar falo na ga a
buɗe hakan yasa na fita,banɗaki na shiga har zan hau masai sai na tuna mafarkin da na yi a
jiya an nuna mini yadda zan ɗauki fansa ta wajen su anty Hinda .Na fita na samo baƙar leda
sannan na koma banɗaki,a cikinta na kasaye duk abin da ke cikina sannan na miƙe ina dariya
ni ɗaya.Da ido na yi wa ledar umarni ta ƙulle kanta kafin kuma na aikata can gidan anty Hinda.

Na fito na wanke jikina na koma ɗakina,gari na wayewa anty Sailuba ta sake shigowa tare da
samun wuri ta zauna.
Ta ɗan ja ajiyar zuciya kafin ta ce “ da farko dai ina yi miki godiya game da abin da kika yi min
jiya,na biyu kuma abin da zan ce miki babu kyau cutar da mutane ki bari”

“ Shikenan ya bar zancen auren?” ita ce tambayar da na yi mata.
Ta ce “ eh ya bari sai kuma ya ɓullo da wata matsalar wai za mu tashi daga nan mu koma can
gidan da ɗan uwansa ya gina kin san nan haya muke”
Na ce “ to ai hakan ba matsala ba ce kin ga kuɗin da yake biya na haya sai ku yi wani abu da
su”
Ta girgiza kai ta ce “ uwar mijina ƴar masifa ce ta bugawa a jarida,kuma kin ga ita ma a can
take.Yanzu dai mu bar maganar nan zo ki yi mini wanki ki share gida da kuma wanke-wanke kin
san halin Bilal shi ma wani sa'in bai da mutumci shi yasa kawai na ce masa ƴar aiki na ɗauke ki”
Tashi na yi tsaye na ce “ babu matsala anty in dai zan zauna a nan ko ƴar aikin sai na zama”
tulin kayanta da na mijinta na wanke ,na yi shara na yi wanke-wanke a ƙarshe na je na yi wanka
sannan ta zuba mini waina da miya sosai na ci na ƙoshi.“ Ki shirya za mu je kasuwa abokan
Bilal yau a nan za su ci abincin dare” Na ce “ kenan yau ba za mu buɗe shago ba?”
“ Eh gaskiya tun da kaji za mu sayo sai kuma mun yi gyaran su”

Da muka fito za mu tafiya kasuwa ta ƙofar gidan anty Hinda muka wuce,tun daga nesa na
hango ledar kashin da na yi tanadi ta na nan tsaye kamar haure jira kawai take lokacin da na
ƙa'ide ta faɗi ƙasa.Na yi murmushin mugunta har na matsu ƙarfe sha biyu ta yi,da muka shiga
kasuwa kuwa na yi ta gamuwa da abubuwan mamaki waɗanda normal mutane ba su iya

gani.Yawancin ƴan kasuwa duk su na da layar da za ta jawo musu customer su sayi kayansu ba
tare da sanin ita fa wannan layar ta na ɗauke ne da aljanu su ne kesa mutane sayen kaya ko ba
su shirya ba,wani abun ma bai da amfani sai ka je gida ka yi ta tunanin mi yasa ma ka saye shi
da ka bar kuɗin ka.
Kaji muka saye manya guda uku anty Sailuba ta miƙa min su na riƙe,daga nan muka wuce
wurin ƴan yaji.Mun yi tsaye ta na cinikin nawa tiyar yaji,yayin da ni kuma idona ya sauka kan
yaji wanda ake kira tsidagu irin ƴan mitsimitsi ɗin nan.
“ In ɗauki guda?” na tambayi mai sayar da yajin yayi murmushi ya ce “ ɗauka mana”
Cike da masifa anty Sailuba ta ce “ mi za ki yi da tsidagu kuma?” na ce “ kawai ya burge ni ne
sai na ɗauki ƙwaya gudan.Haka dai muka yi ta zaga kasuwa har muka zo wajen ƴan sayar da
nama,yadda na ga mata sun yi dandazo wajen wani alhalin duk ga ma su nama nan yasa na ji
ina son ganin shi ɗin kuma wace irin laya yake amfani da ita.Kamar dole haka na duƙa ina
kutsawa har na shigo gaba,sai dai kafin na miƙe tsaye sai idona ya sauka kan wasu ƙafafuwan
jaki a tsaye daram,a hankali na miƙe sai na ga ashe mai sayar da naman ne .Ido huɗu muka
haɗa da shi da farko ya ji tsoro kafin ya soma yi min magana da ido ba wai a bakinsa ba
ballantana ace mutane za su ji.
“ Mi kuma ya kawo macen Siren

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login