Showing 12001 words to 15000 words out of 21264 words

Chapter 5 - Maitar Ido Book Compelet Shamsiyya Lawwali Rabo

Wa ke son ƙanensa...” shiru na yi ina jan ajiyar zuciya.


Daddy ya ce “ saboda mutuwarsa ce nake ganin rauni a idon ka? Ka gaji ne da aikin sojan na
tsige ka?”
Wani irin halbawa zuciyata ta yi,da sauri na ce “ haba Daddy ya za ka ce haka? In na bar aikin
soja mi zan yi ?”

Ya miƙe tsaye ya na cewa “to in ka na son ci gaba da zama a ciki,ka fidda Abakar a ranka ko
sunansa kar na sake jin ka ambata” har ya kai bakin ƙofa kuma sai ya juyo muna kallon juna
kafin ya ci gaba da cewa “zuwa an jima sabuwar mahaifiyar ka za ta tare ban son jin wata
matsala ta fito daga gare ka” ya na gama faɗa ya fice.
Tsakanin baƙin cikin sharaɗin da ya gindiya mini da kuma kishin Ammyna da nake yi jin zai
kawo wata mace matsayin mata sai na rasa da wanne zan ji.Ɗaki na koma na kunna karatun
Alkur'ani ina saurare,a haka bacci ya ɗauke sai wuraren sallar zuhur na farka.Na yi wanka haɗi
da alwala na saka jallabiya na wuce masjid da ke nan cikin gidanmu,ni na ja su sallah bayan mu
gama na zauna nan na ci gaba da lazumi ban fito ba sai bayan sallar Asar.

“Babana yau mi za a girka ma na buɗa baki?” Granny ta tambaye ni,mahaifiyar Daddy ce a nan
gidanmu take zaune tun kafin ma a naɗa shi komanda sojoji.Muna gane wa juna ni da ita don ni
ɗaya ne kaɗai jikanta,kaf ƴaƴanta kuma tun su na jarirai suke mutuwa Daddy kawai ya tsaya.

“Tsohuwa mai ran ƙarfe ina kika shige duk yau ban gan ki ba” na faɗa tare da nufar ta ina ta
ƙoƙarin ƙaƙalo murmushi.
“Ina ɗakina,ai ba ka neme ni ba tun jiya ƙafar nan ta matsa min da ciwo” ta faɗa ta na nuna min
ƙafar wacce ta ɗan kumbura.
Kan capet na zauna na soma matsa mata ƙafar,cikin sigar zolaya na ce “ko sai an yanke ƙafar
nan dai?” ta dungure min kai ta na mai cewa “ka ji min shashanci in an cire gobe da mi zan
tarben amaryar ka?”
Fuska na kwaɓe ina mai kallonta,ta sakar min murmushi ta ce “Ammyn ka ta kira ni ai ,t sanar
da ni yadda kuka yi da ita.Ka na ji Babana ita wani sa'in rayuwa ita ke tsara mana yadda za mu
yi,ba kowanne lokaci ba ne abin da mu muka tsara zai zamana daidai” sai kuma ta canza
yanayin fuskarta kafin ta ci gaba da cewa “ka ɗauki misalin Daddynka mana,tun ya na yawo da
ragga Maimuna ke sonsa kawai daga samun canjin rayuwa ya wulaƙanta ta ita kuma ta ɗauki
abin da zafi mine ne na ɗaukar mataki maimakon ki bar wa Allah komai? ”

Na ja numfashi na ce “Granny wai mi ya gama Ammy da Daddy faɗa har suke gaba haka? ”
Ta shafi kaina ta ce,“Daddyn ka ya yi butulci,saboda amarya ya mari Ammyn ka da ta so nuna
masa kuskuren yin haka ya lakaɗa mata na jaki a ƙarshe kuma ya danƙara mata saki.A ranar
da za ta fita ta bugi ƙirji ta ce masa yadda ta fita daga gidansa,haka duk matar da zai auro za ta
fita.Wai ka na da ma labarin yau wata amaryar zai kawo?” Granny ta buge da tambayata.
Ni kuwa tun da na ji wulaƙanci da tozarcin da ya yi wa Ammyna na soma jin tsohon fushina na
sake bijirowa.Na yunƙura zan tashi,Granny ta yi saurin mayar da ni ta na cewa “ina kuma za ka
je? Faɗa min abin da za a yi ma na saka ƴan aiki yanzu nan”
“Duk abin da kika zaɓa Granny ya yi” na faɗa tare da miƙe wa na haura sama.Ina shiga ɗakina
na fahimci tabbas wani ya shigo ciki,to amma mi aka shigo yi? Kafin na kai ga lalubo amsa
idona ya sauka kan bed sam babu akwatin da na ajiye.
Waya na ɗauko na soma kiran Daddy amma bai ɗauka ba,na fito da sauri ina tambayar Granny
“ba ki ga wanda ya shiga ɗakina ba?”
“Lafiya mi ya faru?”
“Akwatina aka ɗauke” na bata amsa kai tsaye.
“Baturen nan ne dai ya ɗauko shi a gabana ya fita da shi”
“Joy?” na tambaye ta ta ce “eh shi fa” na dafe kaina,Joy shi ne soja na hannun damar
Daddyna.Da wannan takaicin na zauna zaman jiran shi,a nan falo na sha ruwa tare da taimakon
Granny har na je na bayar da salloli na dawo babu ko motsin Joy.Mu na nan zaune ni da
Granny,aka kawo amaryar Daddy wata ƴar ficiciya da ita ko kunyar aurenta bai ji ba. A gaban Granny aka kawo ta ,tun daga danginta har ita amaryar ƴan iya yi ne Granny ta yi
musu Allah sa albarka kafin ta nuna musu sashen Daddy suka wuce da ita.

Na dubi Granny cike da jin haushi na ce “yanzu wannan ce ya auro?”
“Babu ruwan ka,dama ya ce na ja ma kunne akan haka.Duk gani yake saboda tsamin ranka
matansa ke fita daga gidansa,sam ya ƙi yarda aikin Maimuna ne”
Na ce “Granny ya za ki ce aikin Ammy ne?”
“ A bar zancen to.Mi ka shirya wa goben?”
Ban bata amsa ba sai kwanciya da na yi na ɗora kaina kan cinyarta,ta ce “sai son jiki kamar
mage,ga ka dai ƙaroto amma da taɓi'a yara in ka karye ƙafar tawa ai shikenan”
Na yi ɗan murmushi na ce “granny don Allah yi min addu'a na yi bacci ko zan huta da baƙin
cikin nan da nake ji”haka kuwa aka yi ta soma yi min karatu,duk da ta na tsohuwa haka take
fitar da harufa yadda ya kamata.Sosai nake jin daɗin karatun sai dai baccin ya ƙi samuwa,a
ƙarshe ma ita ce ta soma yin gyangyaɗi a doli na miƙe na yi mata rakiya ɗakinta sannan na
wuce nawa.A wannan daren ban rumtsa ba sam, system na ɗauka na soma yin binciken da y
shafi aikina har aka kira sallar asubah bayan na dawo daga sallah na ɗora daga inda na
tsaya.Wuraren ƙarfe tara na tashi na yi wanka na shirya cikin ƙanana kaya wando jean da
rigarsa ,ko agogo ban saka ba na fita.
[29/07 à 09:31] MRS SADAUKI : *IBRAHEEM*
```soldier man```

© Chamsiya Laouali Rabo
#MRS SADAUKI✍️

*FCWA ☀️*

#Sadaukarwa ga duk waɗanda suka taɓa rasa wani jigo nasu a soja.Allah jadadda rahama a
gare ka Yayana AbduRashid



3-4


Tun daga nesa nake ƙare musu kallo,sai kace wani ƙaramin yaro sai ririta amayar yake ya na
bata abinci a baki ko kunya bai ji har da wani ɗora ta kan cinyarsa ita kuma uwar iya yi da
rashin kunya ta na gyara masa hullar kansa.
Na ɗauke kaina,har na ida sauko wa daga kan benen ban kalle su ba ina shirin zama kan kujera
na ji Daddy na wata irin dariya mai cike da tsantsar farin ciki ya na cewa “Baby ba fa haka ake
ɗora hullar ba,na faɗa miki kan zakin can gefe yake kallo”
“Uhum!Umhum! Ni dai haka ta fi min kyau Baby” ta faɗa cikin wata shagwɓar da tasa na yi
saurin ɗaga kai na kalle su ,aka kuwa ci sa'a shi ma Daddyn ya ɗago ya na kallon saitin da
nake.Da ido na tsure shi da su rai ɓace,da sauri na ga ya sauke ta daga kan cinyarsa ya ɗora ta
kan kujera.Ta taɓe baki ta na kallona,ashe kallon tsoro na yi mata a jiya tsohuwar yarinya ce
ƙaramin jiki ne kawai da ita ta ci uban bleachin ta yi fayau.

“Ibraheem ka fito?” Daddy ya tambaye ni,ban amsa ba na fasa zaman na wuce part ɗin Granny
ina jin zuciyata na tururi.A zaune na tarar da ita ta na shafa maganin ciwon ƙafa,na zauna kusa
da ita ina mai gaishe ta ciki-ciki.
Ta amsa da “lafiya lau ka ci abinci ne?” na girgiza kai ta ci gaba da cewa “da kaina fa na zaɓi
abin da za a dafa ganin jiya ba ka ci wani abin kirki ba” ban ce komai ba sai ƙafarta da na soma
matsawa.


“Babana ban son shirun nan,faɗa min mi aka yi?”

“Daddy ne” na faɗa cike da takaici.
“Mi yayi kuma?”
“Shi da matarsa ne...” na cije leɓen ƙasa kafin na ci gaba da cewa “kamar wani ƙaramin yaro
shine zai zo tsakiyar falo da girmansa da darajarsa ya na ba ƙaramar yarinya abinci a baki har
da ɗora ta a cinya? Granny in ni ɗansa ne na kawar da kai su kuma ma'aikatan gidan nan fa?”


“Don Allah fita batun su,bani makullin ɗakin ka zan sa a ƙara gyara shi kafin Ammyn ka su
ƙaraso” Granny ta faɗa .
Na ce “wato ke ma kin basa goyon baya ya ci gaba da yin haka?”
Granny ta ce “to mi kake so na ce Babana? Duk tsiyarsa dai ai ba zai koma saurayi ba,ban
makulli ka ji”
“Wai yanzu gaske kawo ta Ammy za ta yi? Allah ni ban shirya wani zama da mata ba” na faɗa
ina mai kwanciya kan lalausan capet ɗin.

Granny ta ce “yau na ga abin da ya fi ƙarfina wai tsohuwar da ƙirgen dangi! Yanzu Babana kai
ne ba ka shirya zama da mata ba? To halan so kake sai ka zama tuzuru sannan?”
Na turo baki tare da lalubo key ɗin na miƙa mata na ce “ni dai wallahi inda ma wurin ki ta zauna”
Ta na dariya ta miƙe tsaye ta ce “tun da ni aka aura ma ita ba.Tashi mu je ka ci abincin”
“A kawo min nan ba zan sake fita na ga kayan takaici ba”
“Ka ji wani zancen mutum da matarsa,kai ma ai ka kusa hutawa da zamana gwabranci can a yi
wa kaji zabbi hira suke” ban sake cewa komai ba har ta fita,can sai ga ɗaya daga cikin ƴar aiki
ta shigo da sallama ta kawo min abincin.
Da kaina na zuba na ci sama-sama kafin na sha ruwa na haye katifar Granny,wani bacci ma na
soma ji amma ina tunawa da Abakar ya bar duniya sai na ji ya fita idona.Da sauri na fito don
tambayar Daddy inda yasa aka kai min akwatina sai kuma na tarar da shi a tsaye ya na kallon
tv da ke manne a jikin bango.
Zuciyata har wani tsalle take tsabar yadda allurar soja ta motsa,bresking New ne ake ƴan
ta'adda sun kai hari a wani ƙaramin ƙauye da ke cikin Zamfara sun kwashe shanu da kuma
wasu samarin garin.

Daddy na kalla na ce “sai yaushe ne ƙasarmu za ta bar fuskantar ƙalubalen nan? Gagarar
mutane ne suka yi ko rashin iya aikin jami'an tsaro ne?” kallona yayi ba tare da ya ce komai ba
ya fita,da sauri na nufi matakalar da za ta sada ni da sashena.Bibiyu nake taka ta har na isa,ina
shiga ɗakin na tarar da Granny da ƴan aiki su na ta gyaran falon direct bedroom na wuce nan
ɗin ma akwai masu gyara shi.Falo na ce su koma na canza kayan jikina zuwa kakin soja,na
saka takalmi da belt na ɗora hulla sannan na ɗauki baƙin gilashi na manna.Ƴar madaidaiciyar
bindiga ta na ɗauko na soke a ƙugu kafin na fito,Granny ta tare ni ta na cewa “ina kuma za ka
je?”
“Wani ɗan aiki za mu yi ki sa min albarka ”
“Allah tsare ya dawo da kai lafiya”
Na amsa da “amen kafin na fito”


Ina saukowa ƙasa na ji matar Daddy na waya “iyeee ke tsohon ɗan duniya ne inda kin ga yadda
ya susuce jiya a kaina,na san tun da yake aure-aurensa bai taɓa samu mace haɗaɗiya kamar ni
ba”
Godiya na yi ga Allah da falon babu kowa masu tsaron gidan duk su na waje,da wannan
takaicin na fito na ɗauki motata na bata huta.
Sai da na hau kan titi sosai sannan na daidaita gudun motar na kira Ammy,har ta tsinke ba ta
ɗauka ba sai a kira na biyu.
“Ina kwana Ammy kin tashi lafiya?” na faɗa cike da kwantar da murya.
“Lafiya lau alhamdullah! Ga mu a mota muna hanya ina ta bacci sai da Maryam ta tashe ni”
cewar Ammy,na ɗan jan numfashi na ce “Ammy ni da na so na ce ku ɗan jira kar ku zo yau”
“Saboda me?”
“Ammy jiya fa Daddy ya kawo wata” na faɗa ina cije leɓena na ƙasa.
Ta ce “ina ruwana da matarsa? Ai ni bai gabana ballantana wata can banza”

“Zan sake kiran ki in na sauka Allah tsare hanya” na faɗa ,bayan ta yi min addu'o'in da ta saba
na kashe.Ina isa can babban Barack na tarar da sojawa birjit duk sun yi uban layi,na san bai
wuce umarnin Daddy ne ya na son tura su can inda abin ya faru.
Mota na parker sannan na nufi hanyar da za ta sada ni da ofishinsa,duk da ya na mahaifina
sannan kuma na kasance soja hakan bai hana masu tsaron ƙofar hana ni shiga ba.
“Shi ne ya bada umarnin kar wanda ya shiga”
“ Ku bar ni na ce akwai maganar da za mu yi” na faɗa a karo na biyu,amma suka ƙi nan fa muka
hau rigimar da ina tunanin ita ta jawo hankalin mutanen ciki har aka buɗe ƙofar.

Sergent Yakubu ne ya na ɗaya daga cikin waɗanda Daddy ke hulɗa da su ba a harakar aiki ba
kaɗai,“ku bar shi ya shigo” ya faɗa ya na bani hanya don na wuce.Na yi musu kallon banza
sannan na shige,a zaune na tarar da Daddy ya zube wasu duwatsu akan teburi alamu dabarun
yaƙi yake shirya wa.

“Daddy?” na furta ,shiru bai amsa ba na sake cewa “Daddy ina son zuwa don Allah ka sa a tafi

da ni ” nan ma ɗin shiru yayi har sai da Sergent Yakubu ya ce “ shugaba za ka ce”
“Ka dai barsa ya ɗauka nan a gida muke”


Shiru na yi ina kallonsa,ya ɗago ya shi ma ya na kallon nawa kafin ya ce “ a gabana za ka tsaya
da baƙin gilashi?”
“Ka yi haƙuri yalaɓai ban iya kallon tsakiyar idonka ne shi yasa,amma ina neman alfarma don
Allah ka tsara tafiyar nan da ni”

“Captain IBRAHEEM Isa ba za ka je ba” ya faɗa tare da miƙe wa tsaye ya mayar da hankalinsa
ga Sergent Yakubu ya ce “ daidai nan da nan za mu baza dakarun mu ta yadda za mu zagaye
abokan hamayya,ka ga duk yadda aka yi dai mune da nasara in sha Allah saboda kowanne
bango mun zagaye su”
“In kuma aka yi rashin sa'a kafin su isa su ƴan ta'addan sun bar wurin?” Sergent Yakubu ya
tambaya.
Daddy ya ce “ har yanzu dai su na wajen kuma ba zata ce za mu yi musu ”

“An bi didigi an gano inda suke?” na yi tambayar ni ma ina ƙara matsawa,Daddy ya ɗago a
hassale ya ce “ wai mi kake jira ne? Ba na sallame ka ba?”
“Don Allah Daddy ka bar ni na je”
“Ba za ka je ba fitar min daga ofis ko na sa a zo a fitar da kai ta tsiya ” ya faɗa cikin tsawa ya na
nuna min ƙofa.
Amma abun ka da soja na dake na ce “ Yalaɓai mine ne amfanina kenan in har wata matsala za
ta taso ba tare da na bai wa ƙasata kariya ba?”


“ Sai ka ajiye aikin tun da ba ka ga amfaninsa ba,Sergent Yakubu biyo bayana” Daddy ya faɗa
tare da kwashe duwatsun kan teburin ya nufi wani ɗaki da ke cikin ofishin.Haka na bi su da kallo
har suka shige ina jin lokacin da aka murɗa key ta ciki,na ja ajiyar zuciya tare da zagayawa na
zauna kan kujerar da Daddy ke zama .Kamar an mitsike ni na jawo ɗan ƙaramin aljihun table
ɗin,wani ƙonanen agogo na gani na ɗauke shi ina dubawa a kallon farko na gane na Abakar ne
don ga farkon sunansa nan da na mahaifinsa a jikin ƙarfen kamar yadda duk wani soja da za a
bai wa ita ake masa haka.Mayar da ita na yi na soma bincike har na kai ga liste ɗin sunayen
waɗanɗa suka mutu,a nan ne na gano ita gawar Abakar sam ba a ganta ba.Jikina har rawa
yake wurin maida komai yadda yake kafin na fito,tuni sojawan har sun shiga motoci riƙe da
bindigogi.

Na je kusa da babban Sojan da ke kula da duk wani yaƙi ko tafiya in ta kama na ce “ a wacce
mota zan shiga?”
“ Banda sunan ka a jerin sunayen da Shugaba ya bani ikon na tura” ya bani amsa.
“Saboda me?”
“Ƙila don ba ka daɗe da dawowa daga mission ba”

“Amma ya na ga har da waɗanda a tare muka dawo ɗin wasun su na ciki?”
Ya dube ni da kyau ya ce “ mahaifin ka za ka tambaya ba ni ba” ya na gama faɗa yayi gaba ya
bar ni nan.Ina ji ina gani motocin suka fita suka bar ni,ina cikin wannan takaicin Daddy ya aiko
kira na.Ina shiga Sergent Yakubu ya fita ya bar mu,“zan saka wani aiki ne ka cike min takardun
nan,sannan ka binciko min bayanai dangane da ƙauyukan nan” ya faɗa tare da miƙo min tulin
takardu.Na karɓa har zan fita ya ce “zo ka zauna a nan ka yi” ban musa ba na ja kujera na
soma cike takardun ,in jin idonsa a kaina amma na ƙi ɗagowa har sai da na ji muryarsa ya na
cewa “Ammyn ka ta kira ni ...” sai kuma yayi shiru ya na kallona,na ce “mi ta ce ma?”
“Za ta zo nan gida”
Na ci gaba da abin da nake kafin na amsa masa da “eh na sani”
“Zuwan nata ne ba na tunanin zai haifar ɗa mai ido,ka san halin ta ba ta ƙaunar zaman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login