Showing 15001 words to 18000 words out of 21264 words

Chapter 6 - Maitar Ido Book Compelet Shamsiyya Lawwali Rabo

lafiya”

“Shugaba wannan fa tsakanin ku ne bai kamata ka shigo da ni ciki ba” na faɗa ina mai kwashe
takardun,na fita.
Motata na shiga ban zarce ko ina ba sai ɗayar Compagnie ɗinmu inda a can wurin kwana
yake.Ɗakin na buɗe,duk yadda na so kar na yi tunanin Abakar abu ya cuttura.Rabi da rabi na yi
aikin,sallah kawai ke tsayar da ni sai dab da magrib na fito na nufi gida.Bayan na yi parking sai
da na ɗan zauna na wani lokaci kafin na fito,da sallama na shiga falon idona ya sauka kan
Ammy.Da sauri na je gabanta na gaishe ina mai gaishe ta,cike da fara'a ta amsa ta na tambaya
ta ya aikin na amsa “Alhamdullah”

Granny ta ce “baƙauyar amaryar ka ta zo,sai kuka take da rantse-rantse ita ba za ta haura
saman bene ba”
Shiru na yi ban ce komai ba,na miƙe na ce “Ammy zan je na yi wanka lokacin magrib ya gabato”
“A fito lafiya” ta faɗa ,ni kuma na wuce na fara taka matakala kenan na ji muryar matar Daddy
na cewa “Baby ga IBRAHEEM ɗin nan sai yanzu ya shigo,kaiii?” ta wani kira ni kamar ƙaramin
yaro ko waigawa ban yi ba na idasa hayewa.
Ina tura ƙofar falon wani ƙamshi ya ziyarce ni,na lumshe ido ina shaƙar ƙamshin kafin na wuce
bedroom.Allah na gani sam ban lura da ita ba sai da na ji uban ihunta,“na shiga uku na lalace
mugun abu soja na a gabana?” ido kawai na zuba mata duk uban ihun nan na zata tsoro ta ji
wai ashe murna ce take ta ga soja .Rikitatun idona na zuba cikin nata,da sauri na ga ta je bayan
labule ta ɓuya kafin ta fara leƙe ban ce mata komai ba na je gaban mirror na yi tsaye idona na
ga sun yi ja sosai.
“Je ki waje” na faɗa dakyar don so nake na canza kayan jikina .

Da gudu ta fita ta na bangaje ƙofa, cire uniform ɗin na yi kafin na shiga toilet wanka na yi haɗi
da alwala sannan na ɗauro towel daidai ƙuguna.Kan bed na tarar da ita ta zuba uban
tagumi,muna haɗa ido ta ja blanket ta rufa ta na karkawa har gadon sai da ya dinga rawa ta ce
“yi haƙuri....”cikin raunataciyar murya ta na mai fashewa da matsanancin kuka mai cin rai. Na rumtse ido,a duniya in akwai abin da na fi tsana to kuka ne shi yasa ma ban cika son yara
ba .Ina shirin fara shafa mai na ji sai ƙara ƙaimi take wurin kukan,zuciya cunkushe na nufi bed
na zauna tare da yaye blanket ɗin.Da sauri ta yi baya ta na curewa wuri guda,kamar mai koyon
magana na ce “ mine ne?” shiru ta yi bata bani amsa ba,“ ban son kukan nan ki yi shiru”

Cike da ƙurciya ta ce “ tsoro nake ji”
“Tsoron me?”
“Matakalar bene kuma ...kuma ni ban son nan wurin Ammy nake so kar ta tafi ta bar ni ban san
kowa ba” ta bani amsa ta na shasheka kamar ranta zai fita.

“Ni wane ne?” na jefo mata tambayar ba tare da ni kaina na shirya ba.Ta buɗe fuskarta ta tsure
ni da manyan idonta,kafin ta ce “abokin Ya Abakar wanda azzalumai suka kasheee” shaaa
kuma sai wasu hawayen tare da ɗaukar wani sanfarin kukan.Ji na yi tamkar ta taƙalo min wata
masifa daga can ƙasan zuciyata,raɗaɗin rashin Abakar ɗin ya dawo min sabo dal kamar yanzu
ne aka shaida min mutuwarsa.A duniya tun da nake ni ban taɓa rarrashi ba,don banda ƙanwa
sannan cikin aikin soja na girma ta yadda zuciyata ba ta san soyayya ba in ka fidda ta iyayena
da kuma abokina.Rasa yadda za a yi na rarrashe ta na,kamar wani mai jin tsoro haka na jawo
ta jikina tare da ƙoƙarin haɗe dafin da nake ji a cikin maƙogorona don na samu na yi mata
magana.....
[29/07 à 09:31] MRS SADAUKI : *IBRAHEEM*
```soldier man```

© Chamsiya Laouali Rabo
#MRS SADAUKI✍️

*FCWA ☀️*

#Sadaukarwa ga duk waɗanda suka taɓa rasa wani jigo nasu a soja.Allah jadadda rahama a
gare ka Yayana AbduRashid


*YA Ubangiji rahama don ƙarfin ikonka ka wanzar da Zaman lafiya a ƙasata Nijar da Nigeria da
ma duk sauran ƙasashen da ke fuskantar ƙalubalen rayuwar nan alfamar Manzon Rahama*



5-6


“Yi shiru mana,ban son kukan nan Mary . Addu'armu ya fi buƙata a wannan lokacin,ki godewa
Allah ɗan uwanki yayi mutuwar mazaje wacce ba kowa ne ke samun irin ta ba.Mutuwa a filin
daga,domin kare ƙasarsa” na faɗa tare da ƙara janta jikina ina goge mata hawayen da suke ta
faman yi mata zarya. Cikin muryar kuka ta ce “ abokin Yaya ina cikin damuwa na rashin ɗan uwana,amma Ammy ta
ce da kai da shi duk ɗaya ne duk kulawar da yake min kai ma za ka iya kuma zan fi jin daɗin
zama da kai fiye da in zauna wurin ta”ta yi maganar ta na faman cusa kanta a ƙirjina.

Na ce “ eh gaskiya Ammy ta faɗa ,kin manta Abakar ƙanena ? Kin ga ke ma ƙanwata ce.Daga
yau ban son ƙara ganinki ki na kuka,duk abin da kike so kuma ki sanar da ni”


Ta gyaɗa kai tare da cewa “ Ammy ta ce za ka kai ni ƙaton kanti ka saya min kaya”
Na ce “ eh sai in kin huta za mu je”
“ Yaushe kenan?”
“ Ko zuwa jibi haka”
“ Ba gobe ba?”
“ Za mu je goben to” na faɗa ina mai janye ta daga jikina tare da ƙoƙarin sauka daga bed ɗin,ta
ce “ kenan kai ne mijina?”
Dariya tambayar ta bani,na ce “ Mary shekarun ki nawa?”
“Sha tara” ta bani amsa,na juyo ina kallon ta ban san mi yasa ba sai nake ji a raina ina son jan
ta wasa na ce “ mai ƙarya dai ɗan wuta ne”
Ta buɗe baki ta na murmushi,na kafe ta da ido ganin fara'ar nan yasa na ji daɗi .
“ Na waɗa ma gaskiya ?”ta yi tambayar cikin Hausar ƙauyensu na Sokoto.
Na yi murmushi na ce “ eh faɗa min”
“Kai dai shekaruna Sha shida na”
“Sha shida ne za ki ce”
Ta turo baki ta ce “ ni wa ba zan iya yin Hausar ku ba,yawwa na ce ku nan kowa na da abun
hawa na? Gari duk ko ina motoci na birjit awar an taso daga sallar idi ”

Ban bata amsa ba na soma shafa mai da turare,ta madubi nake hango yadda take kallona.Na yi
gyaran murya na ce “ ki je ki ci abinci”
“ Ban jin yunwa”
“To koma falo zan shirya” da “toh” ta amsa ta fice.
Drower na buɗe na fiddo kayan da zan saka,ina tsaka da saka kayan kamar an ce in juya na
hange ta ta na leƙe na.Muna haɗa ido ta tuntsire da dariya kafin ta gusa,na girgiza a zuci ina
cewa ‘ yau na ga ikon Allah ’ bayan na gama na fita falon na tarar da ita a zaune ta ƙura wa
ƙofar fitowa ido.
Na ɗan haɗe rai na ce “ mi yasa kike leƙe na?”
Ta sunne kai ƙila ta tsora ta da yanayin nawa,ta ce “ Ammy ta ce kar na ji kunyar ka kai mijina
ne duk abin da za ka yi ni zan taya ka har saka kaya da wanka”
Na waro ido ina mamakin ya kuma Ammy za ta faɗi haka,na ce “ shi ne sai ki leƙe ni ?” ta ɗago
kai ta ce “ to mine ne in na yi hakan kai ai mijina ne” sai ta soma wasa da awarwaron hannunta
na duwatsu.


“ Na ji tashi mu sauka ƙasa” ta maƙe kafaɗa ta ce “ Allah tsoro naka ji”
“Nake ji ake cewa” na gyara mata da sauri kafin na miƙar da ita tsaye ta na turjewa muka fito.

“Kwarankwatse ba zan sauka ba” ta faɗa ta na shirin zubewa ƙasa ta riƙe ni gam.
Na ce “ to waye ya hauda ke saman?”
“Ammy ce da wata tsohuwa”
“To na ji ki nutsu babu wuya fa ki kalli yadda zan yi”
Ta ce “ Na wa san bene, kai hawar shi ta a ban yi saboda ina ganin jiri ”
Cak na ɗauke ta na soma sauka da ita ƙasa,ido ta rumtse gam har muka sauka na aje ta ina
mai cewa “ baƙauya” Ammy da Granny suka saka dariya ni kuma na fita zuwa masjid.Ina can
aka kira sallah,bayan an gama na shigo ciki muka je muka ci abinci gaba ɗaya Granny ta miƙe
ta nufi ɗakinta. Kusa da Ammy na dawo na zauna ji nake kamar kar lokacin ya shuɗe,“ Ammy yanzu tafiya za
ki yi?”
“Tambayata ce kake?” ta faɗa tare da kallona,na gyaɗa kai. Ta ce “ zuwa gobe in sha Allah zan
koma”

“Don Allah ki tsaya ko sati ɗaya ne ki yi” na faɗa .
Ta ce “ a'a ba zan jure ba Heemu,ɗazu ai ka ga rainin hankali da matar Ubanka ta yi yadda take
wani kiran ka da gadara so ta yi na tanka mata don kawai a yi faɗa ”
Na ja numfashi na ce “ Ammy mi yasa ba za ki dawo nan da zama ba? Ban son ganin ku a rabe
ke da Daddy ”

Sai da ta kalli Maryam kafin ta ce “ jeki sama Maryam ”
Ta ce “Ammy na dai je ɗakin waccan”
“Okay tashi ki tafi” ta miƙe da saurinta ta na gyara hijabinta wanda tun da ta yi sallah ba ta cire
ba.

Bayan tafiyar ta ne Ammy ta dube ni da kyau ta ce “ faɗa mini matsalar ka”
“Babu Ammy ni burina kawai ki dawo nan ɗin” ta girgiza kai ta ce “ na bar Daddynka har
abada,tun ka na goye na bar gidansa bai taɓa tunanin dawo da ni ba sai ni ce zan sarkawa? Ya
je yayi ta aure-aurensa wata rana sai ya auro aljana”

“Ammy na sani Daddy yayi laifi amma hukuncin da kika ɗauka ne yayi tsauri sosai ” na faɗa
cikin jimami ina tuno abin da Granny ta ce min game da mafarin rabuwar.

Ammy ta yi wani murmushin wanda ka ganinsa ka san na takaici ne kafin ta ce “ tun bayan da
na koma gida bai taɓa tako ƙafarsa ba sai da ka shekara goma a ranar da ya zo ya tafi da kai
ya saka ka makarantar sojoji,ya nuna min iko ya maido ka gidansa da ace ya na ra'ayina ai a
tare zai maido mu” idonta ne na ga sun cika da hawaye,da sauri na miƙe ina cewa “ kuka kuma
Ammy? Don Allah a'a” sai na shiga goge mata su.

Jiniya ce ta cika gidan alamun Daddy ya dawo,muna nan tare da Ammy amaryasa ta fito cikin
murna.Daddy na shigo wa ta yi tsalle ta rungume shi ba tare da ko kunyar escort ɗinsa ba da
suka yo masa rakiya.
Raina ne na ji ya sosu musamman da na ji Daddy na cewa “ za ku iya tafiya yanzu lokacin

iyalina ne” Ammy ta je ta miƙe na mayar da ita.

“Muuuah! Muuuah!” kawai kake ji amaryasa na masa kiss wanda ina da tabbacin da gayya take
yinsa ,shi kuwa Daddyn kamar wani soko yayi tsaye na yi imanin bai lura da mu ba da tabbas
ba zai tsaya ba.


“Mi kika girka min Bab...” sauran maganar ce ta laƙe a maƙoshinsa da muka haɗa ido da shi.Da
sauri ya janye ta daga jikinsa “ jeki ɗaki ina zuwa” ya faɗa ita kuma ta harare ni kafin ta wuce.
Daddy ya wani haɗe rai ya na mai ƙaraso wa inda muke,na taɓe baki tare da barin wurin na fita
zuwa masjid.


Daddy yayi gyaran murya ya ce “fatan kin sauka lafiya?”
Ammy ta ce “ lafiya lau alhamdullah har ina shirin komawa ma”
Ya shafi gefen wuyansa ya ce “ to madallah ” Ammy ta ƙure shi da ido ta na kallonsa kafin ta ce
“Isah sai yaushe za ka sanin ciwon kan ka? Aure-auren naka har ya kai ka auro karuwa wacce
ba ta san mutumcin kanta ba? A gaban ɗan cikin ka kake sumbatar mace? Ayir ɗinka wallahi ka
bani mamaki ....” Daddy yayi saurin katse ta da “ don Allah Maimuna ban son tsiyar gumi.Ina
ruwan ki da matata ? Wato kishi kike don kin gan kin koma tsohuwar akwala babu mashunshuni
haushi ya kama ki kin ga na auri ƴar shilla?”
Sam ba su ga zuwan Granny ba sai saukar marin da ta kifa wa Daddy,ya dafe kumci ya na
kallonta “ Mama...” da sauri ta katse shi “ rufe mini baki! Wato kai ba ka ƙaunar zaman lafiya
daga ta na faɗa maka gaskiya shikenan sai cibi ya zama ƙari?”
“Wace gaskiya Mama ? Kawai banda ikon sakewa da matata?”
“A gaban ɗanka? In shiriritar kuke so mi zai hana ku yi ta can sashen ku? Kai yanzu ba zubewar
girman ka ba ce da matsayinka da ikonka a gan ka kana abin yara? Dubi gemunka farin gashi
ne ya fara tsiro wa amma a haka kake rungumar ƙanƙanuwar yarinya a gaban ɗan cikin
ka.Maimuna mu je,ke ma da naki laifin ban ma san mi ya tsayar da ke nan ba” Granny ta faɗa
tare da jan hannun Ammy suka koma can ɗakinta.
Maryam na zaune ta na karatun Alkur'ani,yanayin da ta ga Ammy ne yasa ta yi saurin rufewa ta
nutsu sosai.

“ Tashi ki koma sashen ku Maryam ki tabbatar kin yi wanka kin yi sallar isha'i kafin ki kwanta”
cewar Ammy, Granny ta ce “a'a ki barta a nan har a jima”

Ammy ta ce “ to ni zan ɗan kwanta ” dama fashin sallah take hakan yasa Granny ba ta ce komai
ba.Karatun suka ci gaba da yi ita da Maryam inda ta yi kuskure sai ta gyara mata,Maryam ta ce
“ ya aka yi kika iya karatu Kaka?”
“To in ba abin ki ba ta ya ba zan iya ba tun da ba makarantar Boko na yi ba mai zurfi”
“ Tun ki na yarinya kenan kika iya?”

Ammy ta ce “ Maryam ba a tsare babba da tambayoyi”

Granny ta ce “ a'a bar ta mana ita ma in ta tsufa haka jikokinta za su tsare ta da tambayoyi”

Maryam ta ce “ ni dai gaskiya ban so na tsufa” Granny ta dinga dariya ta ce “ ai baƙin gashin
nan a sannu zai koma fari sol” Maryam ta hau kukan sangarta.
Ammy dai na jin su ba sake kula su ba,furicin Daddy sosai yayi mata tsaye a zuciya wai ta ƙi yin
aure saboda babu mai sonta.Wasu hawayen takaici suka zubo mata a zuci ta ce ‘ in sha Allahu
zan baka mamaki zan cire ka a rai na je na auri wani’ da wannan tunanin dai ta yi bacci.

A can ɓangaren Daddy kuwa cike da jin haushi ya nufi ɗakin amarya Zainabu,a yadda ya tarar
ta ci uban shiri cikin kananan kaya sai ya nemi fushin ya rasa.Ita ma cike da iya yi ta zo ta
rungume shi suka gama shiriritarsu,kafin ta yi masa rakiya zuwa toilet yayi wanka .Sai da ta cika
masa tumbinsa sannan ya je masjid ,ganin IBRAHEEM ne yau zai ja su sallar ya ji haushi sosai
don ya matsu ya koma ciki wurin amarya .

Cike da nutsuwa nake gabatar da sallar har muka kammala,kamar sauran lokuta a tare muke
komawa gida ni da Daddy.Da sauri na miƙe na isa gare shi,ina son yi masa magana ne akan
Ammy sai dai shi ya tari numfashina ya na mai cewa “ don Allah ka bar jan dogon karatu,wasu
ba sa iya jurar tsayuwar nan ka yi ta karatu sai ka ce muna ƙiyamul laili?”yayi maganar ya na
ɗaga ƙafa da alamu sauri yake.
Na ce “ yaushe soja ya fara tsoron tsayuwa? Duk sojawa ne sun saba dama to ai ni ban ga
wata damuwa ba don an ja dogon karatu.Aka yi tsayuwa akan lamarin duniya sai wurin bautar
Ubangiji ne za mu samu rauni?”

“To in fa mutum na da uzuri ? Irin hakan dai babu daɗi na faɗa ma”

“ Daddy na ga alamun kamar ka na sauri ga shi kuma ina son yin magana da kai” na faɗa ina
jan numfashi daidai nan muka iso ƙofar da za ta sada mu da babban falon gidan.
“Ya ce ba yanzu ba ka bari zuwa gobe”
“Amma Daddy...” shiru na yi sakamakon ganin amaryar ta sake fitowa cikin wata shiga ta riga da
wando duk sun matse ta rabin mamarta duk a fili .Da sauri na kawar da kai ganin ta rungume
mahaifina duk da kuwa ƙoƙarin hanata da ya so yi,“ Haba Zee ya za ki fito haka wuce gani nan
zuwa” “ Ni dai... Ni dai Baby na ƙi wayon mu je ƙafarka ƙafata na sh....” sauran maganar ban ji abin da
ta ce ba,na fi zaton Daddy ya toshe mata baki ne.
“ To na ji na baka minti biyu” ta faɗa kafin kuma na ji ƙarar takalminta alamun ta tafi.


“ Ibraheemu mi ka ce?” Daddy ya tambaye ni a ɗan daburce,sai yanzu na juyo na kalle shi da
jajayen idona da suka rine tsabar ɓacin rai .A nan tsaye na barsa na wuce part ɗina, matakalar
ma ban ganin ta da kyau.
Ina shiga ɗakina direct bedroom na wuce na kwanta rairan ina kallon sama,zuciyata sai tuƙuƙi
take.
‘ Wai mutumen da in za ka gansa sai ka yi fiye da sati guda ka na shan wuya,mutumen da in

shugaban ƙasa zai fita sai ya bayar da izinin zai iya fita babu wata matsala,mutumen kowanne
soja jininsa a akaifa yake in ya aiko kiran ka ko kuma in ransa ya ɓace shine waccar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login