Showing 21001 words to 21264 words out of 21264 words

Chapter 8 - Maitar Ido Book Compelet Shamsiyya Lawwali Rabo

Ganin Ammy ta samu ta yi bacci na miƙe na fita waje na kira lambar Daddy,bugu biyu ya ɗauka
kafin ya ce “ina jin ka” sam yanzu babu alamar tashin hankali ba kamar ɗazu da na sanar da shi
an kama Ammy kuma gani a hanya zan je ƙwato ta.


“Ya ake ciki ka aika sojojin ne?” na jefo masa tambayar ,shiru yayi bai ce komai ba har sai da na
sake maimaita tambayar sannan ya ce “ka ga Abraheemu aiki nake ” ƙittt ya katse kiran.Na bi
screen ɗin wayar da kallo ina juya maganar Daddyn.Karon farko da na tuna ina da wasu abokai
na biyu bayan Abakar ,zama na yi na dinga gwada wayarsu babu wacce ta shiga sai ta mutum
ɗaya ya na ɗaga wa ya ce “ya ne Soldier Man ya ƙarin haƙurinmu?”
“Alhamdullah! Shamssudeen don Allah ina son ganin ka akwai aikin da nake son ka yi min”
Ya ce “yanzu dai ina kan hanya mun je Katsina wani aiki sai gobe za mu koma Kano”
Na ɗan nisa na ce “fatan kun yi nasara?”
Ya ce “eh mun kama biyu daga cikin yaran Dagaci”
Da sauri na ce “yaran Dagaci ka ce?”
Ya ce “eh zuwa jibi za a wuce da su Abuja”
Wani irin daɗi na ji ta faɗi gasasa kenan.Na ce “to kawai zan bari har ku ƙaraso Abujar ido da
ido ma za mu fi fahimtar juna” nan muka yi sallama sai a lokacin kawai na je na yi
sallolina,Ammy na farkawa na bata jus ta sha magani kafin mu wuce gidanta.....

6
7
8

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login