Showing 3001 words to 6000 words out of 21264 words

Chapter 2 - Maitar Ido Book Compelet Shamsiyya Lawwali Rabo

ta ce“am...yau ba ki je wurin Sailuba ba ne?” ni

kuwa ganin ta saki ranta yasa na watsar da zancen ruwan dauɗar ta zuba a miya na ce “na je
yanzu ma can zan koma,dama biyo wa na yi na baki haƙuri abin da yasa jiya ban zo ba ruwan
Gulbi na faɗa sai bayan magarib na farfaɗo ” ta shiga tashin hankali sosai kafin ta ce “Allah
tsare gaba,to in kin tafi don Allah ƙarfe biyu na ɗaya na buga wa ki wuce can inda muke sayar
da abinci kin ga dai yau mai yawa na yi fiye da na kullum” da to na amsa mata kafin na koma
saloon har an kusa ida mata kitson ,yanzu ma da na dawo sai da ta tsokane ni “aci gwaigwai an
jiƙa dauɗa da sunan wanka”
Anty Sailuba ta ce “Leemat ban son haka fa” dariya ta yi tare da ci gaba da yi min sharri,tsabar
iskanci ma da za su tafi haka ta sa yatsa a fuskata ta na dirzawa ta na cewa “wallahi duk baƙin
ta ne na zata ko dauɗa ce” na ture hannunta ina hararenta ta dungure min kai ta na sa tissu ta
goge yatsanta ta ce “na shafo dauɗa” sai ta kai yatsan ga hanci ta na sunsuna wai wari nan fa
suka shiga yi mini dariya,ni kuma kawai sai na fashe da kuka bayan tafiyar su ne anty Sailuba
ke ce mini “ke wasa fa take yi miki kawai don a yi dariya” sai dai duk yadda ta so shawo kaina
ƙin yarda na yi kawai dai na haɗe abin a zuci na kammala mata aikin da zan yi kafin na wuce
wurin sayar da abincin.

Yadda na ga dandazon mutane duk sun yaɓe anty Hinda sai abin ya bani mamaki don mun sha
yin kwantai sai mun dawo da abinci gida yau kuma abun mamaki tururuwa saya ake.Ashe
farkon mamakina ne ban ma ga komai ba,sai da na ƙarasa na soma taya ta sayarwa hatta
yadda ake zuba abincin an rage awo amma haka muka sayar da shi tasss sai wanda ta zuba
mini .Sai da na wanke robobin da aka ci abinci sannan na zauna na soma cin abincin hannu
baka hannu akushi,daga nan gida na wuce amma har yanzu Kaka ba ta nan ganin haka na
koma saloon ba ni na koma gida ba sai wajen taran dare.
A zaune na tarar da Kaka ta na sauraren rediyo ,bayan na gaishe ta tare da tambayar inda ta je
na samu wuri na zauna.Amma sai na ga Kaka ta ƙure cikina da ido,ban kai ga tambayar ta
lafiya ba kuma na ji ya fara mirɗa mini.Maimakon in yi zawo a'a kumfa ne ya soma fito mini ta
baki kamar akuyar da ta haɗi leda.Kaka ta yi ƙyaci kafin ta bani magani na sha nan na soma
amai kamar zan amayar da hanjin cikina,“haba Hinda da ni kike zancen!” ta sake yin wani
ƙyacin.....




*Gajeren labari ne*
[27/07 à 16:37] MRS SADAUKI : *MAITAR IDO*️
️️️️️
HoRrOR story☠️

Na
© Chamsiya Laouali Rabo
#MRS SADAUKI✍️

*FCWA ☀️*

*NB:* Maitar ido iri-iri ce akwai ta tsafi,akwai kuma wacce ake haifar mutum da ita irin tace
wacce in mai ita ya kalli abu da ya burge shi ko akasin haka sai kuka abin ya lalace.Itaciyar bedi
ta sha mutuwa silar Maitar ido,wasu sun san su na da ita wasu kuma ba su sani ba.In sha Allah
a sannu zan faɗi alamominta da kuma yadda mutum zai yi rabu da ita.

5-6


Na sha baƙar azaba sosai kafin na samu aman ya tsaya,Kaka ta ce “je ki kwanta ” ban musa ba
na haye katifa a gajiye,sai dai tuna abin da Leemat ta yi mini yasa na ji baƙin ciki ya rufe ni.Na
yi ƙwafa kafin na ce “wai Kaka don Allah baƙin nan na wane ne na kwaso? Tsakanin Inna da
Abba waye baƙi?”
Abun mamaki tambayar tawa ce na ga ta razana Kaka,sai ta kasa bani amsa sai motsi take da
baki ni kuma na ƙara jin haushi na ce “a gaskiya ko ma dai wane ne na biyo ya cuce ni,yau an
wulaƙanta Ni an tozarta ni saboda kawai ni BAƘA CE(Sajida Nijar)”

Kaka ta ce “mi ta yi miki? Sannan wane mataki kike son a ɗauka kanta?”
Jin abin nema ya samu har da tashi na yi zaune ba tare da na san wannan ne farkon jefa
rayuwata a cakwalkwalin ruɗani,na ce “so nake ta zama baƙa kamar dai ni,sannan gashin kanta
wanda ta yi mini gori a ɓata shi ya zamana nawa ma ya fi nata kyau da tsayi”

Kaka ta saki murmushi wanda a cikinsa na hango tsantsar farin ciki kafin tace “Sarah kin
tabbata ki na son haka?”
Ba tare da wani tunani ba na ce “eh sosai ma Kaka”
Ta ce “kin shirya?”
“A shirye nake ai” na faɗa ba tare da na san shirin mi Kaka ke nufi ba,ta ce “to babu damuwa
yau za mu je ki ɓata rayuwarta da kan ki,don haka kwanta ki yi bacci tun kafin dare ya tsala ”

Cike da murna na kwanta ina tunani ƙila acid za mu je mu watsa mata sannan mu datse
gashinta,da haka bacci ya ɗauke ni.Na ɗauki lokaci mai tsayi a cikinsa kafin na ga Kaka na yi
min irin wannan abun na jiya,wasu ruwa ne take yayafa min ta na yin wasu surkullen da ita
kaɗai ta san ma'anar su.Abu guda na sani shine bacci nake,amma kuma abun mamaki sai na
irina ta miƙe tsaye ta na tambayar Kaka “har lokacin tafiyar tamu yayi?”
“Eh fito mu tafi jirgi na jiranmu” sai ta ja hannuna muka fito,ni kuwa sai ware ido nake na ga inda
zan ga jirgi sai dai ina abin ya wuce tunanina.Turmi Kaka ta kada kwance hannuna na cikin nata
muka shiga turmin nan kawai sai gani na yi ya tashi da mu sama.Da mamaki na tambaye ta
“amma Kaka dama turmi ya na iya tashi sama?” Ba ta bani amsar tambayar da na yi mata sai bayani ta soma yi mini,“leƙa ƙasa ki ga yadda
duniyar da muka baro take” na je na kama bakin turmin na leƙa sai na duk ga gidajen mutane

nan da kuma ababen hawa,na waro ido ina mamaki na ce “ya na ga garin duk yayi duhu alhalin
nan sama kuma hasken rana?”

“Duniya biyu ce mabanbanta,daren can shine safiyar wannan duniyar.A sannu za ki saba za ki ji
wannan ɓoyayyar duniyar ta fi waccan daɗi,tun tuni nake son kawo ki amma kika ƙi bani haɗin
kai sai yau da zafin ɗaukar fansa ya ci galaba a kan ki” ina shirin yi mata wata tambayar ta ce
“shuuut! Mun kawo Dutsen Muradi ki nutsu ki aiwatar da komai yadda ya kamata” Kan wani ƙaton dutse jirginmu na turmi ya sauka,yanzu ma Kaka ce ta kama hannuna muka fito
“ ki faɗi abin da ya kawo ki mana kin yi wani tsaye” Kaka ta faɗa ta na kallona,“ to ai ni ban san
ya zan yi ba” na faɗa ina ƙyafƙyaf da ido.

“Sunan ta za ki kira ”

“Leemat!” na faɗa cikin rawar murya,wani haske ne ya soma sauko wa daga sama mai gamar
gajimare kafin ya tsaya a gabanmu,ta cikinsa nake hango Leemat a kwance jikin wani matashin
saurayi sai shafar mata gashin da aka kitse yake.

Maimakon muradin gashin ya zube kamar yadda na zo da niyyar,a'a sai na canza ƙudiri na kafe
tsorayen da ido ina mai cewa “ ku zama macizai ta yadda saurayin kawai zai iya ganinsu” ko
baki ban rufe ba kuwa tsorayen suka fara motsi kafin su zama macizai su na fiddo
halshe.Saurayin ya fasa ihu tare da koma gefe ya na rawar sanyi tuni fitsari ya soma yi masa
zuba,sai haƙuri yake bai wa Leemat kar ta cutar da shi ita kuma ta na tambayar mine ne gashin
kanta yake yi mata nuni wanda yasa ta nufi madubi don dubawa sai dai kafin ta isa ne Kaka ke
ce min “ da zarar ta isa ga madubin mutuwa za ta yi don shi mirror bai ƙarya ki yi saurin dakatar
da ita”
Take na ruɗe jin zan yi kashin kai na ce “ ta yaya Kaka? Ya zan tsayar da ita ?” kafin kuma ta
bani amsa na ƙure ƙafar Leemat da ido nan take ta ɓangwale ta faɗi ƙasa timmm daidai nan
kuma Kaka ta yi wani furuci komai ya tsaya cak ciki kuwa har da tsintar kaina kan katifa kuma
numfashina ya dawo gangar jikina.

A firgice na tashi ina dafe zuciya,sai kuma na yi saurin sauka na ɗauko ruwa na sha ina mai
cewa “ na yi mummunan mafarki ” don ni duk a tunani mafarkin ne na yi ba gaske ba.Kan
shimfiɗa na je kwanta,sai kuma na shiga tambayar to ina Kaka ta tafi cikin daren nan ƙila ko
banɗaki.Ban kai ga samo amsa ba na ji wata uwar ƙara rudududuuu kamar ta sama za ta
faɗo,tsoro ya kama ni na ƙanƙame jikina.Ina cikin wannan yanayi Kaka ta buɗo ɗaki ta shigo
cakwal-cakwal da ƙafafunta na kaza,ido na murza na dai ga har yanzu ba su canza izuwa na
mutane ba sai kuma na tuna tun jiya fa haka suke har lokacin da anty Sailuba ta zo ta ja ni
muka tafi saloon.


Na buɗe baki da niyyar tambayar ta “ Kaka wai...” amma sai ta katse ni ta hanyar cewa “ rufe
mini baki tun da ke ba ƴar goyo ba ce,na taimaka miki don ɗaukar fansa shi ne kika baro ni can

don ki nuna mini wuyan ki ya isa yanka ƙarfin ikonki(ƙarfin tsafi shine sai miyagu ke ɓoye shi su
ce ƙarfin iko) ya ma fi nawa.Ina ce dai ni ce nan na raine ki tun ki na tsuman goyo,kuma ki sani
daga yau na raba hanya da ke sai ki yi abin da kika ga dama tun da kin ishi kan ki.Sai dai ki
sani tsohon kai ya fi sabon kai dafi ” ta na gama faɗa ta yi gaba ta nufi wani ɗan lungu da muke
aje kaya.Wani ƙaton bindi na ga ya na yi mata reto kamar jela,duk ɓaɓatun da gama yi sam ban
fahimci abin da take nufi ba don har zuwa yanzu duk na ɗauka mafarki ne na yi.

Kayan jikinta ta canza sannan ta raɓa gefe na ta kwanta,hakan ya bani damar ganin salewar da
gefen fuskarta yayi kamar wacce aka ƙona ga wuta.
“Mi ya same ki kuma haka?” na yi tambayar ina shirin ɗora hannuna kan ciwon amma sai ta yi
amfani da nata wurin buge ni tare da ɗora min yatsunta sak irin na mage don firgici har sai da
na yi baya “ in kika kuskura kika taɓa ni zan yayage miki fuska” a tsorace na kai kaina na jingine
ga bango.
Ƙiri-ƙiri yau Kaka ta fito mini da ɓoyayyar siffarta,“ don Allah ki yi haƙuri ni ban mi na yi miki ba”
na faɗa a tsorace ,“hum” ta yi wani ƙyaci kafin ta juya min baya ƙaton bindinta kuwa sai wani
motsi yake kamar yadda mage ke yi.
Muƙut! Na haɗiye wasu yawu kafin na ce “ wai Kaka wannan duk mine ne? Ƙafafuwan kaza ga
kuma bindin mage a bayan ki?”


Ba ta juyo ba ,amsa ta bani kai tsaye “ iya nawa kawai kika gani? Ke naki fa?”
“Ni ai banda ƙafar kaza”
“To ki duba wane kala gare ki” ta bani amsa .
Furucinta yasa na tashi zaune don duba ƙafafuna sai dai mi zan gani? A madadin ƙafafu wani
shabcecen bindi kifi ne tun daga wajen ƙuguna zuwa ƙasa na kifi ne.Ban san lokacin da na fasa
wani uban ihu ba ina motsa bindin mai ɗauke da wasu ababe kamar mafarfeci.

Ihun da na yi yayi daidai soma zubar ruwan sama masu mugun ƙarfi kafin ƙyaftawar ido
ɗakinmu ya cika da ruwa.Hankalin Kaka a tashe ta soma tsalle-tsalle don kamar yadda mage
ba ta son ruwa to ita ma haka take,ni kuwa maimakon ace na ji tsoron ruwan a'a sai na ji kamar
ma na zo gidana ne .Ko kaɗan ban ji irin wannan yanayin ba na son fiddo kai waje,hasali ma
wutsilniya na soma yi cikin ruwan ina yawo kamar wata ƴar ruwa.Munduwar wuyana ce ta soma
fitar da wani haske mai ƙuna ,tsabar yadda hasken ke da ƙarfi har sai yasa na wani abu ya caki
kwanyata da kuma daidai saitin zuciya ban ƙara sanin abin da ya faru ba sai a washegari na
tashi tuni kuma rana ta fito wantsar.Na yi miƙa na tashi zaune ina hamma,Kaka ta shigo ɗakin ta
na mai cewa “sai yanzu kika ga damar dawowa?”
Ban fahimci tambayarta ba hakan yasa na ce “Kaka ni da ke bacci ina kuma na je? Bari na yo
fitsari na baki labarin mafarkin da na yi cabbb wai Allah na gode ma da mafarki ne” sai na sauka
daga katifar na fita waje abun mamaki duk ruwa ne a kwance.Buta na ɗauka na raɓa ta inda
babu ruwan na je na shiga banɗaki,ina fitowa na wanke fuska da ƙafafuwana sannan na koma
ɗaki ina tambayar Kaka “wai ruwa aka yi jiya? Kuma ba lokacin damina ne ba”
“Sarah kar ki raina mini hankali ki dinga yin abu kamar ba ki san mi kike yi ba,wuce dai ki tafi tun

ɗazu Sailuba ke ta aikowa kiran ki” ficewa na yi na nufi saloon.Ina shiga na tarar da Leemat
zaune a ƙasa yayin da kuma ƙawarta Watsima ke kwance kitson da aka yi mata jiya sai faman
faɗin “washhh! Washhh” take yi yayin da ita kuma anty Sailuba ke ta masifa ta na cewa “ in ba
abun ki ba Leemat daga saurayi ya ce kitson bai yi ba shikenan sai ki kwance?Allah duk da kin
biya ni na ji zafi fa”
“Anty Sailuba wallahi a rayuwata dama ban son kitso ,saboda na ci kuɗinsa ne na zo kika yi
mini amma don wulaƙanci ba ki yadda ya fita daga ɗakin a guje ba kamar ya ga wata aljana”
Watsima ta ƙyalƙyace da dariya ta ce “In dai ya baki kuɗin iPhone ɗin ai shikenan ”
“Ai ban yarda ma na raɓe shi ba sai da ya damƙa mini ita ga hannu,ta na can na baro ta a caji
yanzu in gama wanke mini zan je na kunna ta na yi ta selfie ”

Daga wannan ban sake sanin abin da suke tattauna wa ba sakamakon duniyar tunani da na lula
‘ kenan dama ba mafarki ne na yi ba a daren jiya?’ na tambayi kaina kafin kuma na yi wani
makirin murmushi na ƙara cewa a zuci ‘ in dai haka ne kuwa Leemat ba zan bari ki yi selfie ɗin
nan ba,wato za a yi mana burga da dogon gashi ’ Ina nan zaune ina ɗinka hulla aka gama kwance mata gashin,anty Sailuba ta wanke mata shi ta
saka mata kwarkwaro sannan ta je ta zauna kan kujera aka ɗora mata tukunyar busar da gashi.
Sai da na kwatanci gashin ya kusa bushewa kafin na ƙurawa tukunyar ido ina bata umarnin ta ja
gashin Leemat ya shige can ciki ko minti biyu ba a yi ba kuwa tukunyar ta soma yin wata irin
ƙara ta na fitar da haƙi haɗi da ƙauri.
Hankali tashe anty Sailuba ta je za ta cire wayar lantarkin da ganga na kalli ƙawarta na ce
‘ɓangwale ki faɗi’ ji kake timmmm anty Sailuba ta faɗi tuni Leemat ta soma kuka haɗi da ƙoƙarin
tashi amma ta kasa saboda yadda tukunyar ta riƙe gashin gam.Hayaƙin da ya soma fita na
baiwa umarnin ya ƙara farashi ai kuwa shagon ya turniƙe da hayaƙi,Watsima sai tari take ta na
cewa ta shiga uku ba ta ganin komai yayin da kuma anty Sailuba ke kukan ƙafarta.Sai a lokacin
na miƙe na nufi Leemat,daidai gabanta na tsaya kafin na ƙuwara casque ido sai komai ya tsaya
cak na jawo ta ina cewa “yi sauri ki tashi tun da an samu kin fito”
Anty Sailuba da Watsima sai salati suke yi su na taɓa hannu ganin yadda gashin Leemat duk
yayi wani iri kamar an kaɗa taliya ƴar murje.Kan kujera anty Sailuba ta zauna da Leemat wacce
ke ta matsar ƙwallla,ɓarin mai aka yi mata iri-iri kafin a soma shatar gashin nan take ya soma
zubewa ya na faɗuwa ƙasa sai ga Leemat da ƙwaiƙwayayen gashi.... [28/07 à 06:36] MRS SADAUKI : *MAITAR IDO*️
️️️️️
HoRrOR story☠️

Na
© Chamsiya Laouali Rabo
#MRS SADAUKI✍️

*FCWA ☀️*


7-8

Wani irin daɗi yake ratsa ni ganin Leemat na kuka ta dalilina, wannan kuma bai rasa nasaba da
MAITAR IDOna don duk wani mugu ya na jin daɗin mugunta musamman ga waɗanda suka
taƙile shi.

Leemat za ta kwashe gashinta don tafiya da shi amma anty Sailuba ta yi saurin hanata “ haba
ke kuwa in kika tafi da shi a zai dinga tuna miki baƙin ciki,bari na baki mai ki dinga shafa wa
gashin in sha Allah zai dawo normal” cike da siyasa anty Sailuba ta yi mata wayo ta karɓe
gashin ta haɗa ta da mai ita kuma doluwar ta karɓa ba tare da ta san sayar da shi za a yi ba. Ko kuɗin gyaran gashin ba ta karɓa ba suka yi tafiyar su,ita kuwa anty Sailuba tamkar ma ta yi
murna da hakan .Ƙaton gwangwanin da take ajiyar gashi ta buɗe ta zuba kafin ta juyo ta kalle ni
ta tuntsire da dariya ta ce “ ikon Allah! Ki na ga fa jiya Leemat ta yi ta miki sharri yau ita ma
gashinta ya koma irin naki ” Na saki murmushin ni ma kafin na ce “anty yunwa nake ji”
“To

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login