Showing 1 words to 3000 words out of 30509 words
Chapter 1 - Mummunan Zato Book 1 Complete Halima Abdullahi Mashi
____________________________
*í ½í³—MUMMUNAN ZATOí ½í³—*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*
*ÆŠandano page 1*
*Wannan littafin na kudi ne masu son DOCUMENT book 1&2&3 Complete ₦600,masu son
PAGES ₦400 idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account numberí ½í±‡í ¼í¿»*
```ACT<<0700549935
Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925```
*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin
shirya sai kiyi magana*
*Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427*
Ya shigo gidan cike da fara'a yana faÉ—in "ina Umman yaran gidan nan ne?" Daga ciki ta amsa
da cewa "gani Abbansu" ya iso cikin kitchen ɗin, tsaye take tana haɗa lemun soɓarodo yayin da
A'isha ke jera ƙwanuka domin raba abinci, tace sannu Abba, yace yauwa ƙawallin Ummanta,ya
dubi Umma "ina da babban baƙo fa" ita ma ta dube shi cikin kulawa"daga ina?"
Ya fadada murmushin sa "zakiyi mamaki idan nace miki Alhaji Sadiq Usman kt ne" cikin
mamaki take dariya " lallai munada babban bako yau kam zanga wannan Alhaji Sadiq naka" ya
juya tare da cewa " muna falo na" tace "to".
Ta amshi rabon abincin daga hannun Aisha tace "kawo nan in zuba musu,ki kai musu abin
sanyaya makoshi,kafin na zuba masu abinci ko? Aisha tace "to Umma" nan ta shiga hada kaya
kan tire,lemun zobo ne mai dan karen sanyi tare da ruwan leda shima mai sanyi guda hudu sai
kofuna guda biyu.
Tayi sallama falon Abba,inda suka kaure da hirar yaushe gamo? Suka amsa mata cike da fara'a
ta shiga kan tebur ta daura tiren sannan ta dan jaa teburin zuwa gabansu,durkusawa tayi
gwuiwa biyu a kasa tana zuba musu zobon cikin kofuna tana ce da bakon " Uncle ina wuni?"
Ya dube ta " lafiya lau yar Uncle "gabanshi ya yi wani mugun faduwa ya daure yace "yaya
karatu?"
Tace "Alhmdllh, yaya hanya?" Yace "lafiya lau hanya,me sunan ki? Ta mike ta mika musu zobon
sannan tace " sunana Aisha".
Ya dubi Abba yace " yanzu ya'yan ka nawa Mustapha?" Abba cikin fara'a yace "su hudu ne"
Aisha fita sannan ta dawo ta kawo masu abinci Ummanta tana biye da ita cikin fara'a suka shigo
ta gaisa da Alhaji Sadik Usman dan mutan KT,ta zauna tana zuba musu abincin tana cewa "yau
dai naga Alhaji Sadiq KT" Alhaji Sadiq ya dubi Abba yace " Friend kace kaima ko yaushe kana
labari na?"
"Sosai ma" inji Abba ya cigaba da cewa "ai kai ba abokin da za a manta dashi bane"
Sukayi dariya.
___________
Kwance a masaukin baki na sukuni (Guest House) da ke nan cikin Dutse,Alhaji Sadiq ne zurfi
ya yi cikin tunani,ko shakka ba ya yi Aisha yar abokinshi Mustapha ita ce yarinyar da duk sanda
ya yi Istihara yake gani cikin mafarkinsa,kuma ita ce Malam Mamuda ya kwatanta masa cewar
ita ce uwar ya'yansa.
Sai yanzu ya tuna wata tattaunawa da suka yi da Malam Mamuda ya sanar da shi cewa
yarinyar da zata haihu da shi tana wani gari ne mai nisa da Katsina,kuma a cikin Istiharar ta shi
yana zaton akwai matsaloli can kasa cikin al'amuran,ya sani matsalolin ba za su wuce na
kaddarar da ke faruwa kan duk matar da ya aura ba,ya sani ba kowa zai yarda ya ba shi auren
yarsa ba matsawar yasan wane ne Alhaji Sadiq K.T.
Mikewa ya yi yana kai komo cikin masaukin nashi,ko dai ya sanar da aminin nashi matsalarshi?
To in ya gaya mishi anya zai yarda ya ba shi auren yarsa Aisha? Me zai yi yanzu? Alwala ya yi
cikin toilet ya fito ya cire kayan barcin shi ya maida jallabiya ya tada kabbara zabin Ubangiji ya
shiga nema tare da addu'ar Allah ya kawo mishi mafita cikin lamuranshi,cikin barcinshi yake
ganin yarinyar zaune tare da wasu yan yara guda biyu masu kyau da kuma kama da shi.
Da safe ya fito cikin yadin boyel fari tas,ya murza hula kube fari ya fi yawa jikin
hular,takalmanshi sawu ciki ne suma farare kamshin sa tun fil'azal ya na tashi.
Alhaji Sadiq kyakkyawan Bakatsine ne,dogo mai cikar zati yana da kyau,tare da
kwarjini,wankan tarwada ne fatar shi kurum in ka kalla ka san cewa ta goge da hutu,kamshinsa
kawai zakaji ka san ya kama kasa,gidan Friend din ya nufa wanda ba ya da nisa daga
masallacin dake bakin titi wato kan layin in an fito.
Aisha ce sanye da dogon hijabi ya fasa shiga layin ya tsaya,ya sauke gilashin motar,ya leko "ina
za ki je ne Aisha?" Ta dubi gurin motar,ta dan saki fara'a.
"Sannu Uncle,Ina kwana?"
Yace "lafiya lau Aisha,ina zaki je?" "Zan je hadda ne."
"Ina Abbanki?"
"Yana gida,yanzun naji ya ce za yaje gurinka."
"To shigo in kai ki."
"Ba nisa Uncle,kuma gurin lungu ne mota bata shiga sai dai mashin."
Ya miko mata sabuwar dari biyar "ki hau mashin din"
"A'a ka bar shi,Abba ya ba ni."
"Eh amshi nawa."ta amsa sannan ta ce "nagode" ya ja mota ya tafi.Tafiya take amma ranta cike
da tunanin kyautar da ya yi musu ta jiya,dubu hamsin ya basu wai a sai musu sweet bai samu
ya yi masu tsaraba ba.Kai gaskiya Uncle yana da kirki,ya burge ta musamman ma da ta ji
taimakon da ya yi ma Abbansu,Allah ya ba shi haihuwa,ta kula burin shi kenan,in ta yi la'akari
da yanda ya yi ta nuna sha'awar su.
Ya fito da mashin don zuwa masaukin Friend din nashi sai kuma ya hango motarshi tana
shigowa cike da fara'a suka tari juna.Tafawa suka soma yi tare da kiran juna,Friend kamar
yanda suke yi zamanin suna B.U.K "ina zaka da?" "Gurin ka na nufa" "da kaje ma sai dai mu
dawo don kunu nake son sha,sukayi dariya sannan suka nufi cikin gidan,kunnun tsamiya Umma
ta yi da kosai,ya ci sosai ya ce "kai na dade rabona da na ci wani abu kamar yau. Ina son
wadannan abubuwan amma ba na samu"
"Ban gane ba ka samu ba iyalinka ba za ta yi maka ba?" Dan tsaki ya yi sannan yace "kasan
matanmu mace tana ganin kana da hali shi kenan sai ta kwanta wani kato dole za ka dauka
yana muku girki kana biyan shi"
"Allah ya kyauta " inji Abba "amin dai" Abba yace "Yauwa inason in tambaye ka,shin ka taba
neman taimako daga Malamanmu na addini domin samun haihuwa? Sannan me likitar suka ce
kan matar ka?" Alhaji Sadiq ya gyara zama ya sani yana da abokai da yawa,amma ko da wasa
bai hada su da Mustapha ba,dan shi yana da amana tare da zurfin tunani,in ya baka shawara
za ya yi wuya kaga rashin fa'idar abin.Tuno hakan yasa shi sanar wa abokin nashi abinda ke
ranshi game da matsalarshi,ya dube shi friend ka san wata matsala? Abin ala'ajabi duk inda
muka yi yawon ganin likita sai ace Jummai ba za ta haihu ba,saboda ta yi amfani da kwayoyin
hana daukar ciki kuma sun lalata mata mahaifa su ko Egypt da muka je cewa sukayi an taba
mahaifarta ne sakamakon cire ciki da ta yi.Abin ya bani mamaki sosai,amma ta musa min,kuka
sosai ta yi tare da ce min sun mata sharri ne ban da tacewa tunda yar'uwata ce dole ne na rufa
mata asiri.
Abba ya ce "to me ya hana ka ka kara aure?"
Yayi dan guntun murmushi irin na damuwa din nan,sannan ya ce " Abokin Alhajinmu ya ba ni
auran yarshi Murja,karamar yarinya mai kyau da kyan hali,aka yi bikinmu,amma cikin rashin
sa'a a ranar da ta cika sati biyu ta ce ga garinku nan? Tana sallar asubahi ya ci gaba,ranar da ta
cika kwana arba'in da mutuwa aka daura min da kanwarta,abin al'ajabi kwanan ta goma ta ce
ga garinku nan,cike da zargin wani abu Abba yace " ba a gwada ta aka san mene ne
musababbin mutuwar ta ba?" "Likitoci sun gwada ba wata guba ko duka ko irin toshe numfashi
din nan sam,bayan yan watanni bayan rasuwar ta na hadu da wata yarinyar layin su
Hajiyarmu,Jamila ta dawo Islamiya na tsaida ita,dabi'unta da yanayin maganar ta sun sata shiga
raina,ta nuna min gidansu zuwana uku manya suka shiga maganar saboda an san juna
tsakanin gidanmu da na su,Hajiya Jummai matata itace ta hada min akwatuna matsayin
gudunmawarta,don itama tana son ta ganni da dan kaina kamar yanda kullum take min korafi.
Bayan biki na shiga yin amarci tare da sabuwar amaryata.
Ranar dana cika kwana bakwai na bar dakinta,ran kwana tara na dawo mata.Ina cikin yin
auratayya da ita sai na ji yarinya bata motsi sai na tsaya na dubata,abin al'ajabi sai gawa."
Ya yi shiru,sannan ya furzar da wani huci mai zafi saboda tuno tashin hankalin da ya shiga
ranar,ya dafa Abba sannan ya ce, "wallahi Mustapha ba zan iya shaida maka tashin hankalin da
na shiga ranar ba" Abba cike da mamaki yace "ikon Allah,ba ka samu malamai ba don taya ka
addu'a? Duk da cewa mutuwa ta Allah ce".
Ya cire hularshi ya ajiye "me ka ji ma tukunna" ya cigaba "Alhajinmu da kanshi ya tashi muka je
gurin Malam Mamuda,Malami ne mai takawa ba irin na tsibbu ba addu'a muka bukaci a taya mu
da ita sai ya ce za yayi Istahara kan al'amarin ya bukaci mu tafi bayan kwana biyu uku mu
dawo,sanda muka dawo cewa ya yi mu ma muje mu cigaba da addu'a,ya ga matsaloli da
yawa,sannan kuma zan samu haihuwa ko nan kusa ko bayan shekaru.Sannan matar da zata
haifa man yaran yarinya ce karama,kazalika akwai sanayya kuma tana nesa da garin
katsina,yar fara ce mara jiki.jin haka na soma neman aure a wajan Katsina,farko na auri
Rukayya a Kano,kwananta sha daya itama ta ce ga garinku nan,faruwar haka sai mutane suka
shiga cewa kila ma arzikina da yake bunkasa ina cikin kungiyar asiri ne,wasu su ce yankan kai
nake yi sai jama'an gari suka shiga tsorona har ma ba a barin yara su bi ta layin gidana,ban
damu ba.
Wata rana na je Kaduna don siyan wasu injina da banki ya yi gwanjonsu,saboda bashin da yake
bin wani kamfani.
Mun fito cikin kamfanin inda na dudduba injinan,wata yarinya na gani yar siririya ta min yanayi
da yarinyar da Malam Mamuda ya ce min zata haihu min take na ce ke mai gyada
kawo,wadanda muke tare sun sha mamaki ganinsu mutum kamar Alhaji Sadiq K.T ya sha karfin
wannan gyadar,nace "gyadar ta nawa ce?" Ta ce "dari uku" na bata dari biyar,"je ki bawa
almajirai sadaka,ta ce "to ba canji" na ce "ina ne gidanku in ba nisa je ki samo" ta ce "Badikko
ne" na ce jeki na bar miki.
Bayan munyi sallama da Manajan Bankin duk da ya so mu tattauna sai na sallame shi na ce
mishi nan zan kwana,gobe zan zo mu tattauna.Injina sun min,don haka inaso sai gobe zan zo
na shiga mota na ce da direba mu bi yarinyar nan,ya ce "Yallabai ban san in da ta yi ba ,na
nuna mishi wani titi nan naga ta bi,mu bi mu na kan titin Ahmadu Bello way ne,ita kuma ta bi
titin da zai kai ta gidan Gwamnatin Kaduna ne.
Muna bi kuwa sai ga ta can ta yi nisa, kadan-kadan muke bin ta har muka ga gidan su,ba tare
da bata lokaci ba nasaka direbana ya yi sallama da Maigidan,na gabatar da kaina matsayin mai
son 'yarsu kuma na yi musu bayanin daga inda nake.
Ban samu matsala ba,cikin wata biyu suka bani auren yarinyar,abinda ya tsaya min a rai shi
ne,yarinyar ba ta sona sam,sai ina ganin zata so ni nan ba da jimawa ba,da zaran ta
haihu.Yarinyar nan kwananta tara itama ta rasu.
Na tsorata kuma daga kanta na yi alkawarin na daina aure,kuma na hakura da haihuwar,haka
muka ci gaba da zama ni da Jummai.Hamshakiyar mace ce mai son hutu,tana da masifa tare
da raini ga talaka....
######
[12/8, 08:05] Ummi Tandamaí ½í¸‡: ____________________________
*í ½í³—MUMMUNAN ZATOí ½í³—*
*NA*
*HALIMA ABDULLAHI K/MASHI*
*ÆŠandano page 2*
*Wannan littafin na kudi ne masu son DOCUMENT book 1&2&3 Complete ₦600,masu son
PAGES ₦400 idan kuna bukata zaku turo kudin ku ta wannan account numberí ½í±‡í ¼í¿»*
```ACT<<0700549935
Halima Abdullahi Access bank sai ku turo shidar biya ta wannan number 09028485925```
*Ko kuma katin Mtn ta wannan number 09068032427 idan baki shirya siya ba ki bari sai kin
shirya sai kiyi magana*
*Masu son tallata masu hajar su suyi magana ta wannan number 09068032427
Hamshaƙiyar mace ce mai son hutu, tana da masifa tare da raini ga talaka amma game da
zamantakewata da ita tana min biyayya. Mun shafe ku san shekara Bayan rasuwa Hafsat,wata
rana naje Zariya sai na yi shawara na ƙarasa Kaduna in gaida Iyayen Hafsat, domin duk matan
da na aura ban yada iyayensu ba, duk sanda muka fitar da zakka ina aika musu, haka nan
Azumi ko sallah.
Cikin yardar Ubangiji na gaishe su tare da musu ihsani,sai na É—auko hanyar tafiya daidai
shataletalen Bankin Habib nan Shehu Musa Ƴar'adua House, tsautsayi kurum ban san ya ya
aka yi ba kurum na buge wata yarinya,tana ɗauke da tiren ƙwai duk da ba taji ciwo ba,sai da na
kai ta asibitin Fotifo don su dubata, sannan na kai ta gidansu da ke Abakwa.
Wannan ne silar auren Amina itama sai ta bi Æ´an'uwanta,kai wannan yasa nima na san babu
lafiya,mata shida? Jummai kam kuka take tana ƙara wa tana faɗin wannan sai wani ya ce da sa
hannun ta,na ce babu saka hannun ki Jummai ba ke ki ke halitta ba, kuma ba zaki iya kashewa
ba so kada ma ki saka ma ranki wannan."
Ya dubi Abba "My Friend ka san wani abu?" Abba da tsananin al'ajabi ya hana shi magana ya
ce "ina jin ka sai ka faɗa". "wallahi sai da nayi aure tara ban da Jummai fa, kuma ban taɓa
maida wata É—akin wata ba,sai dai itama na bata wani É—akin. Ta taran ma an kai ta kamar yau,
washegari ta yi sallar Asubahi ta koma ta ɗan kwanta ashe ƙwanciyar kenan.Tun sannan na
haƙura domin sai na ke ganin kamar ni ne ma ke kashe su,ji nake kamar sun rataya a wuyana.
Ranar na je gaida Malam Mamuda ya ba ni addu'o'i tare da nafilfili sannan ya bani Istihara na je
na yi da kaina tunda na soma Istihara É—in nan wata yarinya na ke gani yawa yawan mafarkan
da nake yi na kan ganta da yara,na kan ce to ni dai na haƙura ba zan kuma taƙalo wani aure
ba.
Abba ya yi nannauyar ajiyar zuciya, sannan ya ce, "shin Friend ba ka zargin maiÉ—akinka ko?
Kasan mata sun tsani ba haihu ba wasu su zo su haifa.Alhaji SadiÆ™ ya girgiza kai sam ba na
tunanin haka zahiri Jummai tana da masifa tare da rowa, wulaƙanci da sauran wasu halaye,
amma ba ta shige-shigen malamai ina ganin maƙonta ma ba zai barta ta iya bawa malamai kuɗi
ba, nafi tunanin ko ina da wasu iskokai ne. Abba ya ce"kenan nima ina ganin friend lokaci ya yi
da zan ga irin taimakon da zan maka na daÉ—e inason in ga nima na maka wani abu amma
hakan bai samu ba, saboda duk wani da zan yi tunanin baka kafini ta ko'ina nima lokaci ya yi da
zan nema *maka* mafita gurin Ubangijinmu."
Alhaji SadiÆ™ ya ce "na ji daÉ—i sosai Friend Allah ya ja mana gaba,sai dai ka san irin gurin
Malaman da za ka gurin su saboda aƙwai masu kauce hanya" Abba ya ce "kada ka damu ni
kaina bana ra'ayin su" Alhaji SadiÆ™ ya ce "dama kuma ina son maka albishir da cewa in har mun
gama daidaitawa kan maganar kamfanin da na yi maka maganar shi a Jigawa, zan damƙa kula
da gyaran shi a hannunka, sannan in an kammala gyaran ina mai farin cikin shaida maka insha
Allahu kaine za ka zama Manajan kamfanin"kallon shi kurum Abba ke yi ya ma rasa me zai ce,
Alhaji SadiÆ™ ya yi murmushi ya tuno sanda suke makaranta duk in kaga ya yi shiru yana mishi
irin wannan kallon to ya yi mishi alkhairi,don haka ya dafa shi tare da faÉ—in"a'a Friend kada ka ji
komai" Abba ya miƙe tare da tuno baya.wannan kalmar Sadiƙ ke furtawa in yaga yayi shiru ya
kasa godiya sai ya ce dole inji komai Friend sai yaushe ne ni zan taimaka maka? Haka shi
kuma kan ce lokacin yana zuwa,sai kuma suka saka dariya, tare da tafawa saboda sun tuno
baya, sannan Abba ya ce"nagode Friend, Allah ya shige mana gaba, kuma kaima Allah ya cika
burin zuciyarka," "amin" inji Alhaji SadiÆ™.
A gajiye ya fito daga cikin motar,yana saka ƙafa cikin falon Hajiya Jummai tana isowa gurin,
rungume shi ta yi tare da faÉ—in "Oyoyo Abubakar SadiÆ™ É—in a" shima matseta ya yi a jikinshi
yana shaƙar daddaɗan ƙamshin ta.
"Na yi missing É—in ki da yawa"
Cikin jin daÉ—i ta ce, "har ka kai ni?" Ya kalli manyan idanunta "Na ma fiki,yau fa kwanana huÉ—u a
Jigawa" tace "to zamu gani anjima" ya shafi wani sashe na jikinta tare da faÉ—in