Showing 27001 words to 30000 words out of 39858 words
Chapter 10 - A Makabarta Ne Book Compelet By Sarat Alkasim
basa
kawo komai hakan yasa Boka ya nemi da Janu ya ce ya sadaukar da cikin jikin Zaira a dawo
masa da jin daɗinsa, dama abin da take nema kenan ta ji daɗi sai ta ce suje indai zai yo
alƙawarin sadaukarwar, sannan a kawo mata wasu mutane kamar uku ta sha jininsu, inyaso
Zaira ta haihu sai a bata jariri ta sha jinin ,idan ya yi haka zai fi da yin suna a faɗin duniya duk
wani ɗan iska da masu mulki za su san da shi kuma suke zuwa suna neman taimako gurinsa.
Jin jawabin Janu sai Boka ya cika da murna, ya tura Aljannu da yake aika in haka ta taso su
kamo mutane biyu; daret ya kaisa wata maƙabarta a nan tasa ya yi alƙawarin bayar da jinin abin
da yake cikin Zaira, suka ɗaura wani ɓakin ƙyanle a jikin wani dutse suka rufe sannan suka dai.
Aljannun da ya tura ba muso suka shiga duniya suka samu mutane biyu matafiya suka kawo su.
Ita kaɗai ta shanye jinin mutane ukun kafin wani lokaci tuni ta dinga karkato da hankalin mutane
kan Boka; nan da nan jin daɗin sa ya dawo....
Shi Boka abin da bai sani ba; Janu ta haɗa kai da wani ɓakin aljani wanda yawanci A
MAƘABARTA yake zama, ta na zuwa tana karo sirrikan cutar da mutane da aljannu.
Ana tsaka da wannan halin na dawo daga tafiyar da nayi, nan Boka yake faɗa min abin da
suka yi da Janu. Sam na kasa yarda da wannan tsarin na Janu na ce masa kada ya kuskura ko
da Zaira ta haihu a sadaukar da abin da ta haifa, to dama shima ba dan ya so ba ya bada sai ya
ce taya zai kare abin da yake cikin Zaira ya tsira ko zai bata wani mutum ɗin a madadin abin da
yake cikin Zaira?
E na ce masa na ce zan same ta mu yi magana duk da ba wani shiri miki da ita ba saboda
zalincin da take yi; nan yake sanar dani indai aka haifi mace ya yi alƙawarin zai aura min ita
saboda yadda bake kyautata masa, naji matuƙar daɗi dan tuni na gano mace za a haifa sai ya
miƙo min ɓakin zare; ya ce daga an haifi mace in sa mata wannan aure ni da ita an gama.
Muna gama magana naje na same ta na sanar da ita komai..
Cikin ɓacin rai ta ce ba za ta taɓa yarda a canza mata ba dole jaririn da aka haifa za a bata , in
kuma ba haka ba to za ta kunno masifa kala-kala wanda ni kaina ba zan iya dakatar da ita ba,
faɗa muka yi sosai ta ita a kan jaririn cikin Zaira wanda su basu san me ake ciki ba..
Tun daga ranar Janu take gadin Zaira ta kuma sa ana bin ta duk inda za su je da Damisa, ni ma
ina ta bibiyarsu dan sosai naji ina son abun da yake cikin nata.. ..
Ranar Zaira ta tashi da nakuda, Janu na samun labari ta yi wa Boka kiran gaggawa ya zo.
Bayan ya iso ta ce da shi ga Zaira ce za ta haihu dan haka ya zo suje inda za ta ƙaro masa
ƙarfin tsafinsa, sanin ina biye da Zaira yasa Boka ya bi Janu suka wuce cikin Maƙabartar da
suka yi alƙawari.. Cikin mamaki yake kallon ta ganin ta kawo sa maƙabarta; dariya ta dinga masa ta na nuna sa
sai ga ɓakin aljani ya fito suka haɗu tare suna ta yi wa Boka dariya abin da ya firgita shi kenan,
ganin abin nasu ba na ƙare wa bane ya ce da ita.
"Me za mu yi a nan da kika kawoni? Ko nan ɗin ne inda za a ƙara mini ƙarfin tsafin nawa?"
Tsayar da dariyar ta yi ta soma bashi amsa.
"Boka kenan wai daka ɗauka da gaske tsafin ka za a ƙara wa ƙarfi? To ka yi kuskure dan yau
karshen ka ya zo, ɓakin aljani ya faɗa min indai ina son burina ya cika to lalle sai na kashe ka
zan samu cikar burina; kuma gashi na kawo ka nan..
"A MAƘABARTA NE ka min alƙawarin jinin jaririn ciki Zaira; sannan kuma A MAƘABARTA NE
zan kashe ka na sha jininka na cinye naman jikinka, A MAƘABARTA NE lamarin ya fara dan
haka dole A MAƘABARTA NE zan karɓi wannan mulki da nake nema shekaru ɗaruruwa. Ka
ɗauka da wai ina tare da kai zan na yi ta ma aiki? To ba ka isa ba ina so ne dama ka cika
lokacin da zan kawo ka nan shi ya sa nake tare da kai."
Tun da ta soma magana Boka ya tsora ta sai yanzu ya yi da-na-sanin biyo ta da ya yi, kafin ma
ya yi magana ta tsira masa takobi nan take ya mutu suka shanye jininsa ita da ɓakin aljani..
Bayan sun gama ta nufo gidan Boka dan ta kashe su...
Ina tare da Zaira da Damisa da kuma Dudu matar Boka labari ya sameni. Sai dai kash kafin na
yi wani yunƙuri sai ga Janu ta baiyana a nan, a lokacin kuma Zaira ta haifi ƴar mace wato ke
kenan.
Zabura Suhaima ta yi jikin na mugun rawa ta ce."
"Sa..Sayyid!"
Janyota ya yi jikinsa ya rungume ta tsam yana bubbuga bayanta, a nutse ya ce.
"Ki nutsu na ƙarasa miki labarin."
Tsayar da kukan ta yi; hakan yasa ya ci gaba da magana.
"Faɗa sosai muka yi akan sai ta dauke ki ni kuma na hana ta, hakan yasa muka dinga yaƙi a
tsakanin tawaga ta da tata tawagar. Hankalin Damisa ya tashi jin yadda ɗakin yake girgiza,
hakan yasa suka fito da sauri Zaira na rungume da Jaririyarta suka bar gidan; tafiya suka dinga
yi har suka iso wani gari suka tsaya a bakin gari.. Bayan na ci nasarar jikata Janu na bi bayan su Damisa na same su, nan na sanar da su komai
suka tada hankalinsu na nuna musu zan kare ku. Mun shiga cikin Ghana da su Janu ta cin
mana ta zo da baƙaƙen aljanu masu yawa.
In taƙaice miki dai a nan suka kashe Iyayenki ni ma sun so su kasheni na samu nasarar dauke
ki muka ɓace. Sai da na tsire musu na iso jikin wata bishiya na aje ki da jinin haihuwar ki a jikin
ki, ganin wasu mata da miji suna tafiya sai na sa motarsu ta tsaya na saki kuka, nan suka ɗauke
ki kafin su tafi na sa ɗiga miki wani farin abu wanda zai kare Janu ba za ta gano inda kike ba,
ɓakin zaren nan na sa miki daga lokacin kika zama matata, sai da naga tafiyarsu sannan na
tafi...
Ita ko Janu can maƙabarta ta kai su Damisa suka yi ta cin naman su, sannan duka binne
ƙasusuwansu A MAƘABARTAR. Amma duk da haka ta taso ruhinsu har kakanki ta soma
amfani da su tana cutar da mutane...
Ni kuma jinyar kaina na yi har na tsayin shekaru biyar, kuma har zuwa lokacin Janu ba ta gano
inda kike ba, idan ina son ganinki sai na bari zuwa dare na ɗauke ki na kawo ki inda nake mu yi
ta wasa, wani lokacin na zama yara mata kamar ke wani lokacin kuma na zama namiji.. Ana
haka Janu ta gano kina a raye zuwan ki na farko Makaranta na haɗu dake muka ƙulla soyayya
duk da kina yarinya ne ba ki san mai ake nufi da so ba; haka na tafi zuwa yankinmu sai kawai
naga Janu ta jaki zuwa Maƙabarta na yi sautin tarwatsa hanyar na ɗauke ki, na koma mace na
kaiki gida na baki abinci na kaiki wajan wasa, ganin iyayen naki na neman ki sai na aje ki a
bakin maƙabartar hanyar da suke wuce wa suka ganki..
Tun daga ranar nake baki kariya, kina jaririya na ɗaura miki wannan ɓakin zare wanda da shi
nake iya sarrafa tunaninki,sai na ɗauke ki mu bar yankin kar Janu ta kashe ki..
Kwalalo idanu Suhaima ta yi jin yadda yake bata wannan rikitaccan ahali nata masu zama da
aljannu; kuka ta sa masa ta na ƙoƙarin kwace ruƙon da ya mata amma ta kasa, a ruɗe take
faɗin ..
"To amma me ya sa na daina ganin ka na tsayin shekaru tun ina da shekaru 14 na fasa haɗu
wa da kai, zuwa yanzu kuwa ina da shekara 24 ko ma fi?"
Ɗago da ita ya yi ya ce.
"Janu ce ta yi nasara a kaina shi ya sa na kwanta jinya, nahiyar ma gabaɗaya na bari, lokacin
da kike shekaru 12 to a lokacin har mun haifi Ayan da Iman su 'yan biyu ne na ɗauke su muka
bar yankin. Sai bayan kin ƙara girma na fara basu izinin su zo su ganki saboda sun takura suna
son ganin ki, ranar farko tsorats ki suka yi hakan yasa na musu faɗa sosai na ce musu suke
zuwa a suffar mutane ba irin tamu suffar ba. Bayan na gama dawowa nan yankin duk na ga
abin ya dinga faruwa dake, da kaina na taso ruhin iyayenki na haɗa ku a mafarki."
Da sauri ta ce.
"E ai na gansu sau uku ne, sai kuma shi Kakana na gansa sau biyu."
"Wannan dai shi ne asalin ki kuma dama can Boka iyayensa sun jima da mutuwa sai shi kaɗai,
dangin mahafiyarki kuwa sun tashi sun koma Kasar su Ethiopia can inda suke. Sai wannan
lokutan ina yawo na gano inda suke kuma har yau suna son ganin ƴarsu."
Shuru Suhaima ta yi sai kuma ta kalli Sayyid ta ce.
"Kana nufin ka ce ni na haifi yaran nan? Kuma har yanzu ba ka musulunta ba?"
Gyaɗa mata kai ya yi ya miƙe tsaye ya juya mata baya; cikin nuna tabbatar da maganar tasa ya
ce.
"E ban musulunta ba, kuma ina matuƙar ƙaunar ki fiye da tunanin kowa. Shi ya sa ma na kawo
ki nan dan mu ci gaba da rayuwarmu mai daɗi kamar yadda muka saba a shekarun baya."
Jiki na rawa ta kuma cewa.
"To amma me ya sa ka sawa kanka sunan musulmai har da yaranka?"
"Saboda ina son sunayen ne, ki saki jikin ki mu yi zaman mu a nan ki ci gaba da haifa mana
yara mu tara su, sannan zan kaiki ki ga dangi mahaifiyarki."
Jin abin da yake faɗa ta fashe da matsanancin kuka; sai kawai ji ta yi ya rungume ta yana shafa
bayanta nan da nan jikinta ya yi sanyi amma ba ta daina kukan ba..
"Ni fa ban ga wani abin kuka ba a nan, nine dai mijinki kuma zan iya komai a kanki wadda
take addabar rayuwarki na kawar da ita ni da yaranki, dan haka ki daina damuwa. Kuma na miki
alƙawarin ba zan taɓa futo miki a suffar aljannu ba sai ta mutane, idan kina so ma zan je na
nemi auren ki a inda aka riƙe ki a mana aure sai na saya miki gida a cikin gari mu zauna mu da
yaranmu."
Saboda tsabar tashin hankali ba ta ma san hular dake kanta ta faɗi ba sai da taji ya mayar
mata yana lallaɓa ta, kalamai yake mata kunne yana saukar mata da hucin bakinsa.
Ita kan taga ta kanta miji aljani yara aljannu, sai ka ce a garin gaɓa-gaba, taya ma tana mutum
za ta auri aljani wannan ai haramun ne ko ita ba musulma ba ce ba za ta iya auren aljani ba;
wani sabon kukan ta saki ta ce.
"Sayyid ni dai ka rabu dani ka mayar dani gida, mu a addinin mu rahamun ne ka auri jinsin
aljannu kana mutum; kai ko ba musulma ba ce ba za ta auri aljani ba ta na matsayin mutum..
Ka yi haƙuri ka rabu da rayuwata na zauna a cikin mutane ba zan iya rayuwa a nan ba."
Ta faɗa cikin wani mugun tashin hankalin da yafi na baya, taya ma za ta Kubota daga hannun
Sayyid da yake ikirarin ita matarsa ce wai har ma da yara?
"Ba zan taɓa rabuwa dake ba, ke tawa ce ba mai rabamu muna tare.
Ta tsinkayo muryarsa ta ziyarci dodon kunnenta; ta yi hanzarin tashi ya hana ta, duka take kai
masa a ƙoƙarin ta na ya rabu da ita sai taji ya ce.
"Wannan ai dukan soyayya ne kike min, hakan ya ƙara tabbatar mun kina matuƙar so na."
Wani sabon kukan ta saki sai ya haɗa hannayensa ya tashi ta zauna; murmishi ya yi ya hura
mata cikar bakinsa a fuska. Kallon shi ta yi ta na kuka suna haɗa idanu ta ji masifar son shi ta
mamaye ta ,ji take kamar ta tsaga jikinsa ta shiga saboda yadda take ji, hannu ya buɗe mata ai
kafin ya gama buɗe wa ma ta faɗa kansa ya mayar ya rufe yana wani kalar murmishi..
Murmishi Ayan ya yi duk da bai ji daɗin kalaman maman nasu ba da ta ce za ta barsu; amma ya
ji daɗin yadda Baban nasa ya yi wa maman nasu, kallon su ya yi ya ce.
"Baba ka rabu da Mama ta koma inda take so mana; za mu ke kai mata ziyara ai; tun da ta ce
ba za ta iya zama a nan ba."
Ɗaure fuska Sayyid ya yi ya kalli Ayan ya ce.
Am so sorry my fans kwana biyu van yi post ba duk na yi busy ne, yau dai na fanshe muku two
fage na muku a ɗaya. Ina matuƙar godiya da ƙaunar ku a gareni masoya Allah ya bar
zumuncií ½í²ží ½í²ží ½í¸˜
_*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_
[3/16 23:22] Ummu Amjad: _*í ¾í·Ÿ♀️í ¾í·Ÿ♀️A MAƘABARTA NE í ¾í·Ÿ♀️í ¾í·Ÿ♀️*_
Daga Alƙalamin
_Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_
_í ½í´”í ½í³šJARUMAI WRITER'S ASSOCIATION í ½í³š_
SADAUKARWA GA MUTANE BIYU:
*AYUBA MUHAMMAD ƊANZAKI (Zakin Marubuta)*
*JIBRIL ADAMU RANO (Malam)*
مسب الله نمحرلا ميحرلا
1️⃣2️⃣
"Babu inda zan sake bari ta tafi ba tare dani ba; in har kaga Ummu ta bar nan to ni da ita da ku
be muka tafi wata nahiyar dan ci gaba da gudanar da rayuwarmu. Ba zan kuma yin sake
Ummu ta ƙara tafiya ta barni ba, dama ba son zaman inda take nake yi ba duk da babu abin da
suke mata na ɓacin rai." Tun da ya fara magana Ayan yake kallon shi cike da mamaki; ganin ran Baban nasu ya ɓaci a
kan kalamansa sai ya sunkuyar da kai tare da ita gabansa ya soma basa haƙuri.
"Ka yi haƙuri Baba kada ranka ya ɓaci a kan wannan ƴar maganar; naga Mama ta ce ba ta
son zama a nan sai mu barta ta zaɓi inda take son zama indai muna so mu faranta mata rai
Baba. Nasan kuma ta na sonka Baba ka yi haƙuri ka bar Mama ta koma inda aka riƙe ta."
Jinjina kai ya yi bai ce komai ba; ganin haka yasa Iman matsowa ta tashi Ayan ta na murmishi
ta ce.
"Kaga ka rabu da su tun da dai Mama ta dawo garemu ai bamu da wata damuwa kuma; kawai
dai mu yi ƙoƙarin faranta mata rai."
Kallon ta Sayyid ya yi yana jinjina kai dan ba ƙaramin faranta masa rai ta yi ba da kalaman ta.
"Iman ku tafi ku tono wannan kwalbar A MAƘABARTA wadda Janu ta binne ita da ɓakin
aljani; in ba'a tone ba ko da Janu ta mutu to fa ku sani ruhinta ba zai taba barin mu , maza
yanzu ku yi abin da na umarce ku."
Ya yi magana yana nuna musu hanya; da sauri suka kalli juna Iman ta kama hannun Ayan suka
ɓace a gurin. Dawo da kallon shi ya yi kanta ta yi luf a jikinsa idanunta a lumshe ka.ar mai
bacci.
"Ummuu...!
Ya kira sunanta cikin wata kalar murya wadda ta sa Suhaima buɗe idanu ta kalle shi; murmishi
ya sakar mata itama ta mayar masa da martani, magana ta fara cikin kasalalliyar murya.
"Sayyid ɗina..!
Ta ja sunan ta na yi masa wani irin kallon; ji take kamar ta shiga cikin jikina saboda wata
zazzafar ƙaunar sa da ta mamaye kowacce kusurwa ta jikinta. Ajiyar ta sauke sannan ta ce.
"Zan ci abinci."
Fuskarta ya kamo cikin hannayensa masu matukar laushi; ya sumbaci kumatunta tare da mayar
da ita jikinsa sannan ya ce.
"Wani kala kike so?"
Murya can ƙasa ta ce.
"Tuwon shinkafa da miya nake so."
Hannu ya ɗaga sama ya haɗe yatsunsa guda biyu ya ɓala su sai ga abinci ya bayyana a kan
trey; tashin ta ya yi ya ce.
"To gashi ki ci ki ƙoshi."
Da sauri ta gyara zama ta sa hannu ta ɗauko loma ba bismillah ta soma cin abinci da
sauri-sauri; shi kuwa sai wani kalar murmishi yake yana kallon yadda ɗan ƙaramin bakin bakinta
yake motsawa wajan tauna abincin..
Tana gama wa ya nuna mata waya kyakyawar roba a gefen kular abinci ta kalle shi; gira ɗaya
ya ɗage mata yana mata nuni da ta sa hannu.
Ba muso ta sa hannun da kansa ya wanke mata hannu da baki duk ta na kallon shi ta na
lumshe idanunta kamar wata ƴar ƙwaya; ganin bai ci ba ta ce.
"Sayyid kai