Showing 18001 words to 21000 words out of 39858 words
Chapter 7 - A Makabarta Ne Book Compelet By Sarat Alkasim
har da kuka na rabuwa da juna dan mun shaƙu ba kaɗan ba. Haka na tubure na ce
ranar za mu tafi a lokacin an yi la'asar, ticket ya nema mana na jirgin dare sai ma muka ci sa'a
akwai na ƙarfe shida ba ɓata lokaci muka wuce zuwa airport...
A Kano muka sauka daret muka wuce gidanmu, sai bayan mun huta ne na kira Maman Sani na
sanar da ita mun dawo gida; sai gata sun zo ita da yaranta uku Sani da Maryam da Ma'ida...
Bayan kwana biyu muka tafi Kaduna muka zaga dangi kowa sai murna yake idan yaji an ce an
yi wa Abbanku transfer ya dawo Kano da aiki; sati muka yi sannan muka tafi ƙauyen su Inna
Laure. Kamar ta goya mu ,Suhaima kuwa dama ba ta yardar kowa ya taɓa ta ta na lafe a jikina,
amma abin mamaki muna zuwa ta bar jikina ta koma gurin Inna Laure ta goye ta duk da ta
girma amma haka ta goya ta.. Ranar Abbanku ya koma ni kuma sai da muka yi kwana uku
sannan muka soma shirin dawowa, ai kuwa Suhaima ta ce ba ta san maganar a raba ta da
Innarta ba ; kasancewar magani muke nema sai na keɓe da Inna Laure na faɗa mata ga abin
da yake faruwa da Suhaima, amma zan barta a nan a nema mata maganin gargajiya ko Allah
zai sa a dace.. Inna Laure har kuka ta yi na barta muka dawo gida ni da Suhaila.
Ranar Monday aka mayar da Suhaila School amma kullum mita take yaushe Suhaima za ta
dawo, sai na ce mata sai zuwa sati za a kawo ta...
Alhamdu Lillah da taimakon Allah da taimakon surukin Inna Laure Malam Habu; Suhaima ta
samu lafiya watan ta uku a can ana mata rubutu ta na sha ana shafa mata rass Allah da ikonsa
ya ba ta lafiya.. Haka aka dawo da ita naji farin ciki ganin yadda ta yi sharr abin ta, Suhaila kam
jan ta ta yi aka kaisu gidan Abdallah sai murna take.
Tun da aka kawo Suhaima ba ta taɓa fita ba ko ta yi wani abu makamancin wanda ta dinga yi a
Ghana; amma duk da haka Inna Laure sai ta bada magani an kawo mata har da rubutu, sosai
suka shaƙu da an musu hutu ita ta ce ƙauye za ta tafi, ita kuma Suhaila sai ta ce ba ta zuwa
ƙauye ta wuce Kaduna gidan Ƙanwata..
Wata rana muna hira ni da Abbanku na ce da shi.
"Yanzu dai Alhamdu Lillah Abban Suhaila komai yana tafiya lafiya, amma ba ka tunanin
wannan abin da yake faruwa da Suhaima ko yana da gami da alhalin ta? Ni fa ina jin tsoron kar
wata rana asirin mu ya tonu gashi ba wanda muka sanar wa da maganar nan sai iyayenmu
kawai suka sani." Kallona ya yi shi ma ya cè.
"Gaskiya da dai abin na bani tsoro, ballantana ita a cikin jinin haihuwar ta dan rashin imani irin
na mutane aka jefar da ita, ko mai ta yi wa wanda ya mata haka? Kawai ki kwantar da
hankalinki babu abin da zai faru sai alkhairi tun da an yi wa tufkar hanci."
Na gamsu na bayanin sa na na ce.
"Haka ne ni fa ina tunanin aljannu ne ta kwaso A MAƘABARTAR nan, amma dai tun da Allah ya
raba ta da su Alhamdu Lillah za mu ce."
"Umma waye ba shi da lafiyar?"
Da sauri muka juyo jin muryar Suhaila a bakin ƙofa; sosai na tsorata na dube ta na ce.
"Me kika ji muna cewa?"
Fuska a dame ta ce.
"Umma na ji kun ce wai Suhaima ta na ciwo to ba ku so ta sani ne?"
Ajiyar zuciya na sauke jin ba ta fahimci komai ba sai kawai na ce mata ta iso ciki, zaunar da ita
na yi na soma tsara mata magana ta yadda za ta yarda da maganar.
"Suhaila 'yar'uwarki wani ciwo ne take mu kuma ba ma son ta sani?"
"Wani ciwo kenan? "Ta faɗa ta na zaro idanu.
"Yawwa kin san ciwon zuciya ko?"
Gyaɗa mini kai ta yi na ci gaba da magana.
"To shi ne take ɗauke da shi tun kuna ƙanana, to shi ne bama so ta sani dan kar ta saka kanta
cikin damuwa; idan har ta sani ba za ta yi farinciki ba kuma ƙarshe ma zuciyarta ta buga ta
mutu."
Dafe ƙirji Suhaila ta yi ta ce.
"A'a Umma kar a faɗa mata ku ɓoye ya zama sirri daga ni sai ku kar wanda ya ji."
Wani sanyi naji jin ta yarda da maganar na ce.
"Yawwa ķe ma ko kaɗan karki faɗa mata sannan zan miki albishir mai daɗi. "
Da sauri ta dubeni ta ce.
"Umma kamar wanne?"
"Zan sake haifo muku wani ɗan'uwan ko mace."
Da sauri ta rungume ni ta na dariya ta ce.
"Da gaske Umma za ki sake haihuwa." Jinjina mata kai na yi alamar tabbatar wa sai ta mike ta
wuce ta na kiran Suhaima dan ta mata albishir zan musu sabon baby.. Abbanku ya ji daɗin
wayon da na yi wa Suhaila duk da lokacin ta na shekara 12 ne ita kuma Suhaima shekara 8 ba
ta cika ba ma...
Bayan wasu watanni na haifi baby boy, murna sosai muka yi sai ɗaukan sa Suhaila take in ta
gaji ta miƙa wa Suhaima shi ; washegari sai ga Inna Laure ta iso..
Ranar suna yaro ya ci sunan Na'im naji daɗi dan ni na zaɓa da kaina aka sa masa sunan; haka
aka yi suna aka watse ni kuma Abbanku ya ce ba inda zan je na yi zamana, ba dan na so ba na
zauna..
Haka rayuwarmu ta ci gaba da tafiya har duk kuka girma Suhaila ta na gama JSS3 ɗan yayata
wadda da mamanta da mamana uwa ɗaya uba ɗaya suke, ya ce shi fa son ta yake a musu
aure sai ta ci gaba da karatu. Da farko Abbanku ya ce a'a dan lokacin shekaru ta 18 ne, amma
su Baba suka ce ai ba komai a mata kawai. Ba'a wani daɗe ba aka musu aure ta cigaba da
karatun ta a can Kaduna...
"Wannan shi ne asalin abin da ya faru; ko da kika fara mugayen mafarkai a tunaninmu ciwon ki
ne zai dawo wanda tun kina ƙarama kika yi sa, to shi ne yasa hankalinmu ya tashi matuƙa dan
kar a goma gidan jiya..."
Idanun Suhaima ya yi jajur saboda kukan da take, tashin hankalin da take ciki ya wuce gaban
kwatance ta yi kalli Umma ta ce.
"Umma ko da ace iyayena suna raye ba zan taɓa son su ba kamar yadda nake son ku, kune
komai nawa ban san kowa ba sai ku dan haka kune iyayena tun da ke kika shayar dani kika
reneni , dan haka kece mahaifiyata Umma."
Ta faɗa ta na faɗawa jikin Umma; rungume ta Umma ta yi ta dinga bubbuga bayanta ta ce.
" Suhaima ke Ƴata ce ki daina kukan kin ji." Ta faɗa ta na shafa bayanta idanun ta suka kai kan
zoben dake yatsar ta, da sauri ta ce.
"Wannan zoben fa?"
Ɗago wa ta yi ta ce.
"Wannan zoben wani tsoho ya bar ta nan dai ta faɗi yadda suka yi da tsohon, ta ƙara da cewa.
"Umma ina so ku kaini Ghana tabbas maganar Aryan haka take A MAƘABARTA NE lamarin ya
fara. Dan haka ina so naje wannan maƙabartar dan na gano komai da ya shafi iyayena."
Inna Laure ta ɗaura hannu biyu a kai ta ce.
"Na shiga uku Suhaima su waye kuma Aryan?"
Kai tsaye ta ce mata.
"Inna 'ya'yana ne su, kuma zan so mu sake haɗu wa kafin ku kaini Ghana."
Kwalalo idanu waje suka yi Na'im ya ce.
" 'ya'yanki kuma to kamar ya ya?"
_*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_
[3/9 21:48] Ummu Amjad: _*í ¾í·Ÿ♀️í ¾í·Ÿ♀️A MAƘABARTA NE í ¾í·Ÿ♀️í ¾í·Ÿ♀️*_
Daga Alƙalamin
_Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_
_í ½í´”í ½í³šJARUMAI WRITER'S ASSOCIATION í ½í³š_
SADAUKARWA GA MUTANE BIYU:
*AYUBA MUHAMMAD ƊANZAKI (Zakin Marubuta)*
*JIBRIL ADAMU RANO (Malam)*
مسب الله نمحرلا ميحرلا
0️⃣9️⃣
" 'Ya'yanki kuma to kamar ya ya? "Ya faɗa cike da al'ajabin Suhaima.
Ajiyar zuciya ta sauke ba ta kuma ce musu komai ba ta yi shuru kanta a ƙasa; wani irin zafi
zuciyarta ke mata ga tunanuka barkatai, wanda suke neman tarwatsa mata ƙaramar
ƙwaƙwalwarta..
Inna Laure ta matso kusa da ita, ɗago da fuskarta ta yi cike da alhinin ganin ƴar tata a cikin
wannan halin; a sanyaye ta ce.
" Ƴar Innarta!" Kuka ne ya ci ƙarfin ta sai ta faɗa jikin Inna Laure ta fashe da sabon kuka; jikinta
ya ɗauki ɓari tamkar mazari, Inna Laure ta dinga bubbuga bayanta cikin son kwantar mata da
hankali ta ce.
"Suhaima kada ki ce mini kukan rashi iyaye ne kike? Mu ne iyayenki har gaban abada ki daina
kukan kin ji. Ko da a ce waɗanda suka haifeki sun fito ba za mu bari su raba mu da ke ba; ki yi
haƙuri don Allah ki daina maganar zuwa Ghana nan hankalina tashi yake, tashi ki daina kukan
kar ki sake tunanin komai tun da ki na da Allah ki na da mu. "Ta faɗa cike da damuwa; ita kanta
hankalinta a mugun tashe yake ba ta taɓa tunanin Suhaima ba ɗiyar ƙanenta ba ce, ko da a
mafarki ne ta ga haka ba za taɓa ba wa mafarkin muhimmanci ba, amma gashi dai yau sirrin
ɓoye ya fito fili..
Tsagaita kukan ta yi ta soma magana cikin raunatacciyar murya.
"Innata ya zan yi? Yanzu su Umma ba su suka haifeni ba kenan? Su iyayen nawa a ina suke?
Kuma me ya sa suka jefar dani a lokacin da na zo duniya? Me na musu Innata? Wallahi ko da
na gansu ba zan taɓa yafe musu wulaƙanta ni da suka yi ba; indai da son ransu suka jefar dani
to ba na son ganinsu ko a mafarkina su yi zaman su a inda suke, ni ma zan zauna da waɗanda
suke so na da ƙauna ta..
Na tabbata wannan tsohon ya san inda iyayena suke; gashi kuma ban san ta ina za mu sake
haɗu wa ba, Inna ina jin zuciyata na tafasa, ji nake kamar ana zuba mata zuwan zafi tafasashe."
Kuka sosai take ta na sunbatu Inna Laure na rarrashin ta; su Umma kuwa kasa magana suka yi
kowa tausayin halin da take ciki yake yi, ganin sun kasa shayo kanta Na'im ya miƙe daga inda
yake ya iso gaban Inna Laure cikin kwantar da murya ya soma mata magana.
"Anty Suhaima ki yi haƙuri mana; ko wani bawa fa da kalar tashi ƙaddarar ke taki a haka ta zo,
ki gode wa Allah da ba a mugun hannu kika tashi ba; sannan ki ƙara gode wa Allah da ya sa
kika faɗo a hannun musulmai ba kiristoci ba. Tashi kinji in sha Allah komai zai wuce. "Ya faɗa
yana miƙa mata hannunsa." Tsayar da kukan ta yi Inna Laure ta tashe ta daga jikinta; kallon Na'im ta yi ya mata alama da ta
zo garishi, hannunta ta sa a cikin nashi ya kama ta ta tashi ya miƙar da ita. Su ko su Umma
suna kallon su, da ƙyar ta tsaya a kan ƙafafuwanta jikinta na rawa, ganin haka yasa Na'im haɗa
ta da jikinsa ta kwanta kanta a kafaɗarsa. Kasancewar ya fita jiki da tsayi sai ta koma kamar ita
ce Ƙanwar shi ne yayan; ɗakinsa suka nufa su Inna Laure suka raka su da idanu har suka
wuce....
Inna Laure ta jinjina kai cikin damuwa ta dubi Abba.
"Wallahi Mukhtar ba ka kyauta min ba, ai na ɗauka sirrinka sirrina ne amma sai ka ɓoye mini
wannan."
Ƙara sunkuyar da kansa Abba ya yi ya ce.
"Yi haƙuri Yaya Laure Baba ya ce kar na sanar muku ke da Abdallah; shi ya sa ma ban sanar da
ke komai ba game da Suhaima."
"Ba komai ya wuce ni yanzu Suhaima nake tausaya wa, yanzu hankalinta kacokan ya karkata
zuwa ga asalin iyayenta, ba mu san taya aka jefar da ita ba, ko kuma sato ta aka yi Allah
amsanin gaibu."
Ta ƙarashe maganar ta na sa haɓar zaninta ta goge hawaye; ta ci gaba da magana.
"Yanzu dai mu samu a hana ta zuwa Ghana nan, ba kowa ta sani ba kuma ƙila ma iyayen nata
ba a nan suke ba; mu samu a shayo kanta a mantar da ita damuwar da take ciki ina son ta
sosai yarinyar nan, akwai hankali ga nutsuwa."
Suhaila ta miƙe jiki ba ƙwari ta wuce ɗakinta suka bita da kallo, tattauna wa suka yi sosai a kan
lamarin sannan su Umma suka fita a dakin aka bar Inna Laure zaune ta rafka tagumi.
Ko da suka shiga ɗakin zuwa lokacin jikin Suhaima ya ɗauki zafi; a dame ya ja ta suka zauna a
bakin gado ya ce.
"Anty Suhaima don Allah ki yi haƙuri komai zai wuce; bana son ganin ki cikin damuwa duk bana
jin daɗi."
Ɗago wa ta yi ta dube shi hawaye na bin kuncinta ta ce.
"To Na'im me zan yi? Da ina tunanin mafarkan da nake ne damuwata; ashe ma ni tsintacciya ce
iyayena suka jefar da ni, yanzu a ina zan gansu?"
Kuka take sosai har da shiɗe wa take, ganin haka ya gyara zama ya janyota ya shigar da ita
jikinsa; da sauri ta maƙale shi ta ci gaba da kukan ta na sunbatu..
"Na'im rayuwata ba ta amfani in dai ni ba jinin gidan nan ba ce, wa ya sani iyayena ko a wata
duniyar suke; ko ma na gansu na tsane su tsana mai tsanani tun da suma suka tsaneni sai n...
Ba ta ƙarasa ba ya yi saurin rufe mata baki da hannunsa jin ta na neman yin saɓo;
"Ki daina magana Anty kin ji jikinki har zazzaɓi ya rufe ki, kar ki kuma cewa kin tsani iyayenki ko
ba ki son ganinsu; yanzu ba ki da tabbacin ta ya ya suka rabu da ke, dan haka karki yanke
hukunci a kansu. "Ya faɗa yana ɗago da ita.."
Ba ta yarda sun haɗa idanu ba ta kuma koma wa ta kwanta; shi kuwa Na'im wani irin tausayin
yayar tasa yake ji na ratsa masa ko'ina na jikinsa, shi kansa yana son sanin iyayenta da dalilin
rabuwa da ita a lokacin da take buƙatar su..
Matsa wa ya yi kan gadon ganin ta na rawar sanyi ya lulluɓa mata bargo shi kuma ya jingina da
jikin gadon; ƙoƙarin raba ta da jikinsa ya yi amma sam taƙi yarda sai kawai ya haƙura ya zuba
mata idanu cike da tausayin ta; addu'a ya dinga tofa mata a ta na lumshe idanunta, daga
ƙarshe wani wahalallan bacci ya yi awon gaba da ita. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke ya
lallaɓa ya raba ta da jikinsa ya maye mata gurbinsa da pilo, da sauri ta rungume pilon ya ƙara
rufa mata bargon har kanta sannan ya fita a ɗakin...
Kafin Yamma ta yi tuni jikin Suhaima ya yi tsanani; ko idanunta ba ta iya buɗe wa lokaci ɗaya
ƙafafuwanta suka lauye ta kasa tafiya da su. Hankalin su Umma ya tashi suka dinga yi mata
addu'a ta na ƙyarma ta na fisge-fisge, zuwa can ta daina yi duk suka zuba mata idanu;
wasa-wasa har bayan Isha'i Suhaima ba ta farka ba, Inna Laure ta ɗauko wani magani a cikin
leda ta dubi Umma ta ce.
"Bintu kawo garwashi a mata turaren iska kar abin ya ƙara gaba."
Umma dai ba ta iya cewa komai ba ta je ta hura gawashi ya kunnu ta sako a kaskon turaren
wuta ta kawo; amsa ta yi ta buɗe ledar ta dauko garin maganin ta afka a ciki...
Cikin minti ɗaya hayaƙin ya gauraye ɗakin ta kuma fito da 'ya'yan habbatussauda shi ma ta afka
a kan garwashin ta na cewa.
"In sha Allah za ta samu sauƙi wannan 'ya'yan habbatussauda ɗin zai ba ta kariya in sha Allah."
Tari Suhaima ta dinga yi ta na juya kanta jikinta na rawa, a firgice ta tashi zaune idanunta a
lumshe za ta sauko daga kan gadon; Na'im dake kusa da ita ya ruƙo ta da sauri ganin ta na
ƙoƙarin kwace jikinta.
"Ku sakeni na tafi.
Suka tsinkayo muryar Suhaima; da sauri ya kuma matse ta ta na fisge wa ya shiga karanto
mata Ayatul kursuyu a cikin kunne, hakan yasa ta dinga mimmiƙe wa ta na wani irin kururuwa.
Sai da ta yi lakwas sannan dukkansu suka sauke ajiyar zuciya suna hamdala ganin ta samu
bacci; mayar da ita ya yi ya kwantar ya ƙara tofa mata addu'o'i sannan ya rufe mata jikinta.
Inna Laure ta zauna ta na ta na faɗin" Allah ya ba ki lafiya."
Sai wuraren ƙarfe 11: am na dare suka bar ɗakin aka bar ta tare da Inna Laure; shi kuma Na'im
ya shiga ɗakinta ya kwanta a kan kujera.
Bacci take amma yatsina fuska take ta na juya kai; Inna Laure ta tsaya a kanta ta na mata
addu'a har ta daina juye-juyen sannan ita ma ta kwanta a ƙasa...
"Mama! Mama!
Buɗe idanunta ta yi a hankali ta na kallon ɗakin; can ta hango su a ƙofar ɗaki suna kallon ta.
Kamar an cire mata ƙaya haka