Showing 36001 words to 39000 words out of 39858 words

Chapter 13 - A Makabarta Ne Book Compelet By Sarat Alkasim

nake ta neman inda zan ganki
amma kuma Allah bai nufa ba, idan ba damuwa ban takura miki ba muje na kaiki gida."
Sunkuyar kanta ta yi ta na wasa da gefen hijabinta, ji ta yi jikinta ya mutu murus har bakinta
hakan yasa ta kasa ce masa komai.
Ganin haka yasa shi ƙara yin magana.
"Please Madam."
Ya yi maganar yana yin gaba; ita kuwa ji kawai ta yi ta na binsa a baya har gurin motar.
Suna zuwa ya buɗe mata gaba; a sanyaye ta shiga zuciyarta na bugawa da sauri-sauri, haka
kawai taga ya cika mata idanu ya mugun yi mata kwarjini. Ba ta san lokacin da ya tayar da
motar ba sai da taji suna tafiya; nannauyar ajiyar zuciya ta sauke ya kalle ta tare da yin
murmishi ya soma koro mata jawabi. "Am Suhaima tun ranar da na fara zuwa School ɗin nan na dinga jin matata na cikin wannan
school ɗin; sai kuma gashi a hankali Allah ya haɗa mu can kwanaki muka bigi juna ni da ke, har
kika fasa min waya kina ta bani haƙuri."

Ya kalle ta fuskarsa cike da farin ciki ya kuma faɗar.
"Ina zamu bi ne Gimbiya?"
Tun da ya fara maganar ta sunkuyar da kanta ƙasa ta na jin wani irin sanyi na ratsa zuciyarta,
yau dai gashi ta samu mai kama da Sayyid kuma ya furta mata kalmar so, lumshe udanu ta yi ta
na tunano yadda Sayyid ke faɗa mataza ta samu wanda ma ya fishi komai; sai dai ta na da
wahala a samu wanda yake mata son so kamar Sayyid ba ta gansa ba, kuma ba ma za ayi sa
ba a cikin maza. Ajiyar zuciya ta sauke har yanzu zuciyarta ta ƙasa goge soyayyar Sayyid duk
da shi ba mutum bane amma har ƙasan ranta take jinsa, saboda ya taimaka mata tun kafin ta
zo duniya yake ɗawainiya da ita har ta zo ta zama mutum bai gajiya ba, kuskure ɗaya ya aikata
a gareta; shi ne auren ta da ya yi har ta haifa masa jinsinsa wanda haramun ne aljani ya auri
mutum. Wannan lefin ta kuma yafe masa shi saboda alkhairansa ya yi yawa a cikin rayuwarta,
dan haka ba ta ganinsa a matsayin mugu dan ya aure ta wanda kakanta ne ya bada auren nata
dan ta rayu a doron ƙasa ya yi haka.
Ɗago kai ta yi ta dube sa a kunyace ta masa kwatancan gidansu, daga haka kasa cewa komai
ta yi har suka iso.

Hannu ta kai za ta buɗe ƙofar ya yi saurin kulle wa ta kalle shi da sauri, tamkar wani ya yaro
ƙarami ya shagwaɓe fuska ya ce.
"Please give me phone number sai mu ƙarasa maganar a waya, naga alama kunyata kike ji."
Rufe fuska ta yi ta na murmishi ta miƙa masa hannu ya bata wayarsa ta sa masa sannan ta
masa godiya ta fita a motar. Sai da ya ga ta shige cikin gida sannan ya juya kan motarsa ya
koma inda ya fito...

Ta na isa gida wanka ta fara yi ta ci abinci har zuwa lokacin Na'im da Aminatu basu dawo ba, ta
na gama yin komai ta haye kan gado ta janyo waya ta shiga WhatsApp.
Wata baƙuwar number ta ci karo da ita wadda bata Nigeria ba ce, da mamaki ta shiga cikin
number ta tarar da voice yafi goma ta soma ɗaga wa, muryar Uncle Sulaiman taji yana ce mata
sun yi kewarta ga Tsohuwa za ta mata magana...
Wani farinciki ne ya mamaye zuciyarta ta dinga ɗaga saƙon ɗaya bayan ɗaya ta na mayar musu
da amsa, bayan ta gama ta fita a number ta yi saving sai ta kuma ganin wata number an mata
magana; da mamakin ta ta shiga ta ga an rubuta saƙo kamar haka.
"Ummuna Uncle ɗin ki ya amshi number ki za ki ga ya yo miki magana, sannan ka su Iman
nan za su kawo miki ziyara."

Sake da baki Suhaima take ƙara karanta saƙon, tunani ta dinga yi to dama aljannu suna yin
social media ne? Kenan yanzu sai ka iya yin friend da aljani ba ka sani ba a social media?
Murna ta yi ganin ya kuma turo mata da wani saƙon.

"Ummu kenan! Wai kina mamaki ne dan na miki magana a WhatsApp? To ki daina mamakin
hakan dan duk abin da mutane suke muna shiga cikinsu mu yi mu'amala da su basu san me me
mutane bane; muma muna yin social media ɗin nan za ki iya ɗaura abota da aljani ba ki sani ba
Ummu, da haka wasu ke shiga jikin bil'adama in macuta ne su dinga cutar da mutum ayi ta
zuwa Asibiti amma a ƙasa warke wa...

Dariya Suhaima ta yi bayan ta gama karanta saƙon, wani abu ta tuna ta yi saurin danne voice ta
soma masa magana.

"Tab Wallahi Sayyid abin ya bani al'ajabi, a da in aka ce aljannu na yin social media sai nake
ɗaukar abin a wasa; sai gashi na ga zahiri a wajan ka. Yawwa wai ni ko dama ina so na maka
wata tambaya akan Uncle ɗina; shi wai me ya yi wa Janu ne ta kashe shi?"
Ta na ƙarasa faɗar haka ta saki, tana cikin number taga ya ɗaga sai dai bai dawo mata amsa
ba, sai can ya ce da ita ga su Iman nan za su zo mata da amsar. .Da murna ta amsa da to
sannan ta sauka sai ga kira ya shigo, kamar ba za ta ɗauka ba sai kuma ta ɗauka ta yi shuru ba
ta ce uffan ba.
"Assalam alaikum Girmbiyata ina fatan kin shiga gida lafiya dai ko?"

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce masa.
"Alhamdu Lillah fatan kaima haka ka isa lafiya."
Murmishi mai sauti ya yi sannan ya ci gaba da magana.
"Ni sanana Hamid dan cikin garin nan ne ni, har iyayena maganar gaskiya Suhaima ni ba da
wasa na zo ba, ina so ki bani dama na gabatar da kaina a wajan su Baba sannan na turo da
iyayena. Sunan Mahafina Alhaji Hamza na san ma za ki sanshi a garin nan ba ɓoyayye bane a
kaf garin nan.." Waro idanu ta yi ta ce.
"Minister kake nufi fa!
"Kwarai shi dai.
Ya ba ta amsa yana murmishi; jinjina kai ta yi kamar yana ganin ta ya yi ta roƙo ta bashi dama
ya zo ta ce ba damuwa ya zo kawai.
Sun jima suna hira sannan hira daga bisani suka yi sallama...

Washegari bayan sallar Isha'i Suhaima na zaune ta ba duba takardu ta ji saukar wani abu, da
sauri ta juyo sai ta yi arba da su Iman.
Da sauri suka zo a tare suka rungume ta suna murnar ganin ta, ɗago da su ta yi ta ce.
" A'a haka kuka koma?To ina Babanku yake?"
Da sauri Iman ta ce.
"Mama Baba ya ce yana gaishe da ke, sannan ya ce mu faɗa miki amsar tambayar ki."
Gyara zama ta yi ta ce.
"Ina ji Iman faɗa mini."

"Abin da yasa Janu ta kashe Uncle Abdallah shi ne; wata rana ta zo ɗaukan ki sai ta samu ke
da shi kuna zaune a palo, ta so shiga jikin ki shi kuma a lokacin ya kunna karatun littafin ku à
TV ya ƙure volume, hakan yasa jikin Janu ya soma ƙone wa da ƙyar ta gudu ta bar gurin. To shi
ne bayan ta yi jinyar kanta ta yi alƙawarin sai ta kashe shi har ke ɗin ba, to bayan ta kashe shi
aka soma bincike a kan kisan ,ko kwana biyu ba'a yi ba ta sa duk kowa ya manta maganar
kess ɗin aka manta da taya ma ya mutu.

Wannan shi ne abin da yasa ta kashe shi."

Goge hawaye ta yi ta ce.
"Allah sarki Uncle; ta sanadina ya rasa ransa Allah ya maka rahama.
Ta yi maganar ta na kallon Ayan da ya yi kikam kamar wani gunki, da mamaki ta ce.
"Yarona lafiya yau duk naga ba ka yin fara'a?"

Murmishi ya yi ya ce.
"Mama ina Inna Laure take ne? So nake na ɗan tsorata ta."
Itama dariyar ta yi ta ce.
"A'a Ayan kar ka tsora min Innata kasa ta sheka kwananta bai ƙare ba."
Murmishi ya yi suka ci gaba da hira anan yake faɗa musu haɗuwar ta da Hamid sak Babansu a
suffarsa ta mutane, dukkansu suka ce ta amince kawai tun da yana sonta, bata musa ba ta
amsa da to sannan suka tafi...


Cikin kwanaki kaɗan shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin Suhaima da Hamid, hakan yasa ya
faɗa wa mahaifinsa su zo nema masa auren ta, ko da suke zo Abba sai da ya kira Uncle
Sulaiman dan dama tuni ya faɗa masa zuwan nasu, ta waya aka yi magana da shi ya ce ai ko
mai Abba ya zartar aksn Suhaima to ba za su ce komai ba, dan haka komai yana garesa. Sosai
Abba ya ji daɗi matuƙa da wannan karar da ahalin Suhaima suka masa ya ce ya bai wa Hamid
auren Suhaima, hakan ya yi wa mai girma Minister daɗi aka sa biki wata ɗaya suka dawo gida
da labari mai daɗi...

Ranar Hamid da Suhaima kusan kwana suka yi suna hira farinciki ya hana su yin bacci a
wannan ranar..

Lokaci yana ta tafiya biki na matsowa, aba saura sati ɗaya ɓakin sai ga su Uncle Sulaiman da
dukkanin familynsu gabaɗaya babba da yaro ba wanda aka bari kowa ya zo, waɗanda ba su
taɓa zuwa Nigeria ba suka matsa Aminatu sai ta kaisu sun ga gari, Na'im ya ɗauke su ya dinga
jigila da su idan suka fita sai kusan Magariba suke dawowa gida, sosai suka ji daɗin Ƙasar.. Amarya ta sha lalle ɓaki da ja ta sha gyara sosai duk inda ta nufa sai ta baza ƙamshin ta take
wuce wa.

Misalin ƙarfe 2:pm aka ɗaura auren Suhaima Mukhtar da Hamid Minister Hamza akan sadaki
naira dubu ɗari, layin gidan taf ya cika da mutane sosai daga abokan Mahaifin Hamid da na
Abba da nasa shi kansa angon, Sani da Na'im ma sun gaiyato abokansu haka zalika su Uncle
Sulaiman ma ba'a barsu a baya ba duk wasu abokan kasuwancinsu sai da suka gaiyato su
ɗaurin aure, Inna Laure ma ba'a barta a baya ba itama duk yan ƙauyensu sai da ta gaiyato su
har da 'yan matan gidansu duk ta haɗo kansu aka kawo su a mota...

Kasancewar Suhaima ba ta da Ƙawaye daga ita sai Aminatu da Suhaila sai kuma friends na
school da suka zo mata kowa sanye da anko, tana zaune ya kira ya ce an ɗaura aure ai kuwa

ta fashe da kuka, shi kenan za ta bar su Umma ta koma wani guri...

Bayan La'asar aka tafi gurin dinner party; sosai Hal ɗin ya cika sai ga amarya da anko sun
shigo, haka aka rakosu har mazaunin su suka zauna aka soma gabatar da abin da ya tara su.
Shuru Suhaima ta yi ta na kallon gefe da gefe can ta hango Sayyid da su Iman zaune a kan
kujera suna ɗago mata hannu, wani sanyi ya ratsa ta ta musu alamar da su zo sai suka kalli
Sayyid ya jinjina musu kai suka tashi..
Suna isowa ta rungume su suna tayata murna, Hamid ya dubi Suhaima ya ce.
"Sweetheart waɗannan beautiful baby's ɗin fa? Ban taɓa ganinsu ba."
Murmishi ta yi ta nuna masa inda Sayyid yake ta ce.
"Kaga mahaifinsu can sun zo tayamu murna ne."
Kallon inda Sayyid yake Hamid ya yi; saurin juyo wa ya yi ya kalli Suhaima ya ce.
"To ai kama yake dani baban yaran."
Ƴar dariya ta yi ta ce.
"Ranar da muka fara haɗuwa shiyasa na firgita na ɗauka shine."
"Ikon Allah! Ai kuwa zan so ki haɗani da shi mu gaisa.
To Suhaima ta ce su Iman na gefenta a zaune; haka aka dinga shagali sai gaf da magriba aka
tashi..

Washegari aka yi walima bayan sallar Isha'i aka kai amarya gidan iyayen ango dake J R.A.
Bayan an yi mata nasiha, da murna dangin Hamid suka amshi Suhaima suka mata nasiha
suma sannan aka kaita gidanta dake bayan gidan...

Bayan an gama sayan baki ango ya raka amarya ya dawo ya kulle ko'ina sannan ya shigo ɗakin
da take lulluɓe da mayafi sai zuba ƙamshi take, wani irin sanyin daɗi ya ziyarci zuciyarsa
sakamakon yin arba da hannuwanta wanda suka sha lalle gwanin birgewa.
Lumshe idanu ya yi jin shi yake yafi kowa sa'a da Allah ya mallaka masa Suhaima a matsayin
mata, ƙarasowa ya yi kan gadon ya buɗe fuskar tata ya furta.
"Tsaki ya tabbata ga Allah da ya yi wannan halittar."
Murmishi ta yi; ya kamo fuskarta ya yi kissing ɗin ta a kumatu, wani irin yanayi suka ji a tare
kowa ya lumshe idanu.
Zuwa can ya umarce ta ta yo alwala, ba ta musa ba ta shige toilet shi ma ya nufi nasa ɗakin.
Wanka ta ta yi ta canja kaya zuwa wasu riga da wando na bacci masu mugun kyau ta ɗaura
hijabi ta zauna tana jiran zuwansa, ba ta jima ba sai gashi ya iso ya yi gaba ya tayar da iƙama
suka gabatar da nafila su..


Bayan sun gama ya gabatar mata da gasasshiyar kaza, da kansa ya ciyar da ita ta ci ta ƙoshi ta
na kan ciyarsa ya goge mata baki sannan shi ma ya ci, bayan ya gama ya ɗauke ta ya kaita
toilet suka yo brush suka fito, kwantar da ita ya yi shi ma ya kwanta tare da janyo ta jikinsa ya
mata masauki a kan ƙirjinsa. Tsuru Suhaima ta yi jikinta ya ɗauki rawa, hannu yasa yana shafa kanta a hankali yana rada
mata magana a kunne har ya samu ta nutsu, blanket yaja musu ganin yadda take ja baya ya

matse a jikinta ta sa masa kuka, kamar bai san ta na yi dan ya manta a ina yake...

Washegari da kansa yake mata wanka da ruwan dumi ta na masa mita shi kuma yana lallaɓa
ta, da ƙyar ta bari ya shirya ta ya kwantar da ita ya fita. Tea ya haɗo mata mai kauri ya shiga
ɗakinsa ya fito da magani a hannunsa ya dawo.
"Sweetheart tashi ki sha tea da magani."
Ya yi maganar yana ɗago da ita, kuka tasa masa ta ce.
"Ni ka sakeni mugu kawai."
Danne dariyarsa ya yi ya lallaɓa ta tashi ya bata tea ɗin tasha ya bata magani, bayan ta shanye
ya kwantar ya ita shima ya kwanta ya lallaɓa ta tana mita har bacci ya yi gaba da ita...

Haka suka ci gaba da amarcinsu, Suhaima na ta yi wa Hamid taɓara shi kuma yana biye mata,
ji yake kamar ya mayar da ita ciki saboda so da ƙauna.

Tuni yan biki sun koma gida Aminatu ta ce ita fa taga gari ba inda za ta je haka suka barta; Inna
Laure ma ta koma ƙauye haka ma yan Kaduna har Suhaila duk sun koma gida...

Rayuwar Suhaima da Hamid ba'a cewa komai soyayya suke zuba wa madarar, wata irin
kakkarfar soyayya ce ke ta guda a tsakaninsu ko wajan aiki ya tafi suna maƙale a waya har ya
dawo...

BAYAN WATA UKU


Yau ta tashi ba lafiya cikin damuwa Hamid ya kira Family Doctor ɗinsu ya zo ya duba ta nan ya
gano ciki a jikinta na wata biyu, murna a wajan wannan masoyan ba'a magana. Bayan sun
gama murna Hamid ya tafi raka Doctor waje sai ga su Ayan sun iso.

"Assalam alaikum Mama!.
Suka faɗa a tare; Suhaima ta kalledu da sauri ta miƙe ta rungume su ta ce.
"Kai gaskiya wannan rana ta yau ta musamman ce a gareni;tun da naji kun yi sallama jikina ya
bani kun musulunta."
"Kwarai ma kuwa Mama mum musulunta shi ne Baba ya ce mu zo mu miki albishi.
Ayan ya faɗa yana murmishi, itama faɗa musu tayi tana da ciki suka tayata murna suan tsaka
da hira sai ga Hamid ya shigo gidan.
Da mamaki yake kallon su Ayan ya ce.
"Beautiful yaushe kuka zo ban ga shigowar ku ba?"
Iman ta matso kusa da shi ta gaishe shi ya amsa yana ɗago da ita ya zaunar.
Suhaima ta gyara zama ta faɗa amsa cewa su Iman fa ba mutane bane, ta bashi labarin duk
abin da ya faru da ita saboda yanzu Hamid ya zama komai nata ba za ta iya ɓoye masa komai
nata ba..
Shuru ya yi yana jin gabansa na faɗu wa, wai tare suke da aljannu kuma wanda Suhaimarsa ta
haifa. Jin bai ce komai ba idanun Suhaima ya cika da ƙwalla dama wannan ranar take tsoro,ba

ta son faɗa masa wannan sirrin da in yaji ƙila ma ya ce zai rabu da ita. Kallon shi ta yi ta ce.
"Ba ka ce komai ba Sweetheart."
Kallon ta ya yi bai ce da ita komai ba, hakan yasa ta fashe da kuka ta rungume su Ayan ta ce.
"Nasan dama in kaji wannan sirrin ba lalle ka yarda ka zauna dani ba, shi ya sa ma naƙi sanar
da kai sai yanzu da suke zuwa yasa naga ya dace na faɗa ma a matsayinka na mijina uban
abin da zan haifa nan gaba."

Da sauri Hamid ya dawo inda take yasa hannu ya goge mata hawayen ya ce.
"Haba Sweetheart kina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0