Showing 33001 words to 36000 words out of 39858 words
Chapter 12 - A Makabarta Ne Book Compelet By Sarat Alkasim
aiyana a ranta ina ma ace mamanta na raye ta kwanta
a jikinta ta ji É—umin jikinta kamar yadda kowacce 'ya take ji .
Ji ta yi ana goge mata hawayen dake kwaranya akan kyakyawar fuskarta; ta juyo sai ta ga
Ayan ne yana girgiza mata kai, murmishi ta yi ta tsayar da kukan sai ga wannan budurwar tare
da yara biyu sun shigo musu da nau'ikan abinci kala-kala sun dire musu a gabansu..
Sayyid ya miƙe tsaye yana kallon su ya ce.
"Bari za mu fita waje ni da yaran nan idan kun gama za mu dawo."
Da mamaki suka kalle shi tsohuwa ta ce.
"Haba dai É—an nan ai ka zauna ku ci abinci; ya za ka É—auke yara ku fita waje bayan kun zo a
gajiye?"
Murmishi ya yi kawai, wani irin azabbaben son ummunsa ke masa yawo a cikin zuciyarsa har
baya so ya daina kallon ta, amma kuma ba yadda ya iya dan ya riga da ya sadaukar da komai
dan farin cikinta. Ranar da yasa su Ayan suka dawo da ita gida da ƙyar ya iya saita nutsuwarsa
, yana jin in dai babu Ummu a kusa da shi to fa ya zama ba shi da amfani. Fita kawai ya yi su Iman suka bi bayansa da sauri,Suhaima na ganin haka ta tashi ta bi
bayansu duk yan falon suka bisu da kallon mamaki..
Tsohuwa ta kasa daure wa ta ce.
"Sulaiman wannan ko shi ne mijin na jikar tawa?"
Ta yi maganar ta na miƙe ƙafafuwanta dan ta ji daɗin zama.
"A'a Ummi wannan ba mijin jikar ki bane; ya taɓa zuwa gidan nan muka haɗu da shi nan
yake sanar dani Zaira na da É—iya zai kawo mana ita mu ganta, amma dai ban sani ba ko
soyayya suke a tsakaninsu saboda yadda yake kallon ita Æ´ar tamu."
Inna Laure ta gyaÉ—a cikin raÉ—a-raÉ—a ta ce.
"Hmm ku dai a bar kaza cikin gashinta kar a fige ta labarin ya canja salo, da kun san waye
wannan zankaɗeɗan mutumin da wannan yaran; da tuni kun suma aljannu ƙarara gasu nan
kamar mutane mu dai Allah ya kaimu gida lafiya."
Na'im na jinta ya girgiza kai yana murmishi; tsohuwa ta ce.
"Allah sarki amma ko Allah ya masa albarka. "
Ko da ta fita ba ta gansu ba a harabar gidan hakan ya tabbatar mata ƙila sun koma gida ne.
"Ummu!..
Taji ya kira sunanta daga bayanta; juyo wa ta yi fuskarta a dame suka haÉ—a idanu sai ya bata
tausayi, sosai ta hango soyayyar ta a cikin idanunsa a sanyaye ta ce.
"Sayyid me ya sa ka fito wai? Kuma ina yaran suke ne?"
Murmishi ya sakar mata sannan ya ce.
"Kin san dai mu bama cin abincin ku ko? Shi yasa muka fito kar ace sai mun ci."
Jinjina kai ta yi ta juya ta hango wata bishiyar Mangwaro dake harabar gidan ta kuma dawo da
kallon ta kansa ta ce.
"Ni ma na ƙoshi muje can mu zauna kafin su gama cin abincin."
"A'a ba za ayi haka ba Ummu ki koma ki ci abinci da kun gama zan shigo har su Ayan É—in.
Kamar za ta masa kuka ta narke fuska, ji take ina ma ace Sayyid É—in nata a matsayin jinsin ta
ya fito da tafi kowa dacen miji kamilalle. Sai dai kash shi É—in ba jinsin ta ba ne dole kuma ta rabu
da shi, inda take ƙara jin tausayin shi in ta tuna yadda ya sha gwagwarmaya duk dan saboda
son da yake mata ya bata kariya, ta na jin ƙaunar sa sai dai kuma shi ɗin ba mutum ba ne
ballantana in bai ce yana sonta ba ita ta tunkare shi ta ce ina sonka wane, kukan zuci take ta na
addu'ar Allah ya ba ta managarcin miji ko da kuwa wanda bai kai Sayyid É—inta ba ya zama yana
da nutsuwar Sayyid.
Ajiyar zuciya ta sauke ta ce.
"Kar fa ka tafi!"
Ta yi maganar ta na goge hawayen da ba ta san dalilin zuwansu ba, ji kawai take babu lalle ta
samu wanda zai mata zallar madarar so da ƙauna kamar Sayyid, in kuwa ta same shi to tabbas
ita É—in mai sa'a ce a duniya, ballantana ma da wahala ta samu mai son ta kamar shi É—in, shi ya
fara sonta fiye da komai nasa, duk da shi ba mutum ba ne amma ya iya nuna mata zallar so..
"Yi haƙuri Ummu kin ji! za ki samu wanda ya fini komai ma, za ki samu Ummana.
Jinjina masa kai ta yi sannan ta juya ta koma ciki ya bita da kallo , sai da yaga shigewar ta ciki
sannan ya isa inuwa ya samu kan wata kujera ya zauna...
Ta na shiga ta same su duk sun yi shuru suna sauraron Tsohuwa da take musu godiya cikin
kukan ta; a kusa da tsohuwar ta zauna ta na murmishi ta ce.
"Kaka kukan me kike bayan Allah ya haÉ—a fuskokinmu kafin mutuwa?"
"Kaiya Æ´ar nan ba dole na yi kuka ba; wannan mutanen arzikin masu zuciyar salihai nake yi wa
addu'a da suka riƙe ki amana tamkar su suka haifeki, ina ƙara muku godiya Allah ya faranta
muku duniya da lahira."
Amin Suhaima ta ce ta na kallon su Umma da fuskokinsu yake É—auke da murmishi, wani sanyi
ta ji ya ratsa sassan jikinta yau dai gata ga masu kama da ita, ba iya mutum É—aya ba duk kusan
mutanen gidan suna kamanni da juna, murmishi ta yi ta tashi zaune ta dubi wadda suke
tsananin kama ta ce. "Ya sunan ki?"
Kallon ta yarinyar ta yi alamun ba ta san mai take cewa ba; Sulaiman ne ya yi Æ´ar dariya ya ce.
"Suhaima Aminatu ba ta san Hausa ba, mu ne dai da yake muna fita zuwa Nigeria mun koyi
Hausa sosai ba kamar su ba da ko gaisuwa basu sani ba da Hausa."
Dariya Suhaima ta yi tsohuwa ta miƙe ta soma magana da yarensu,, gani kawai suka yi duk
mutanen palon sun bar gurin itama ta juya za ta fice Suhaima ta kamo hannunta ta ce.
"Kaka ina za ki je to?"
"So nake ku ci abinci tukun sai mu dawo."
Ok Suhaima ta ce sannan ta sake mata hannu ta wuce.
"Anty yau dai kin ga masu kama dake ko?"
Na'im ya faÉ—a yana murmishi.
"Wallahi kuwa kaga wacce tafi kama dani amma dai ba ta jin Hausa, ko Uncle zai bamu ita sai
mu tafi da ita ta koyi Hausa?"
"To ni ina na sani ki bari in sun dawo ki tambaye. Shi kawai."
Abincin suka ci sai yaba girkin suke; ita kuwa Suhaima farinciki ya hana ta ci abincin yadda ya
kamata, da an jima sai ta ce.
"Iko sai Allah! Ga dai masu kama dani."
Dariya suke mata in ta faÉ—a har suka gama sannan 'yan gidan suka dawo aka ci gaba da hira,
cikin hirar da suke ne Suhaima da take yin tambaya ta matso kusan Sulaiman ta ce.
"Uncle a baya mamana ce a wajan su Kaka, ku lokacin kuna ina? Sannan a da su Kaka ba
musulmai ba ne ina son sanin bayan kun bar mamana a wannan yankin me ya faru daku har
lokacin da kuka musulunta?"
Tsohuwa ta goge ƙwallar da ta zubo mata ta ɗaga kai ta kalli suma.
"Lokacin da za mu tashi daga wannan yankin mun nemi gidan Zaira mun rasa, ƙarshe muka
tafo ni da mijina muka bar ta a can. Dama tun farko akwai su Sulaiman lokacin da aka yi wani
faÉ—a ne aka tayar da bom muka rabu da su, sai bayan mun dawo yankin namu muka samu an
samu canji sosai wani mai kuÉ—i ya gyara mana garin nan a gidansa muka samu Sulaiman da
Abubakar. Mun sha murna da ganin juna sannan mun basu labarin Ƙanwar su an mata aure
amma mun rasa gidansu, sun sha kuka nan dai aka gyara mana gidanmu muka koma su kuma
suka ci gaba da karatu. Kullum kukan rashin ƴarmu nake, wata rana dai muka yi ɓaki a gidan
nan ashe su musulmai ne, a hankali suke nuna mana kyakyawar alaƙa irin ta musulmai har
muka ji imanin shiga wannan addini mai ni'ima da nutsuwar zuciya; ba ɓata lokaci muka karɓi
kalmar shahada. Wannan shi ne abin da ya faru, yanzu kuma alhamdu Lillahi komai ya wuce
sai tarihi."
Umma ta ce.
"Allah sarki dama rayuwa haka take wata rana sai labari."
Haka dai suka ci gaba da hira inda Umma ta ce gobe za su koma, Tsohuwa ta ce to abar musu
Suhaima ta yi musu ko wata biyu ne su kara sanin juna. Ba dan Umma ta so ba ta ce to sannan
suka tashi..
Sayyid dake zaune yana jiran su gama hirar sai jin muryar Suhaima ya yi ta na cewa, ita fa ba
za ta iya wata tare da su Umma a kusa da ita ba kawai dai za ta yi sati É—aya. Murmishi ya yi sai
ya iso cikin palon ya ce shi zai koma gobe zai dawo su tafi da su Umma, Sulaiman ya ce a'a ya
yi haƙuri kawai zuwa goben sai su tafi tare ya daure. Ba dan ya so ba ya amsa da to...
Washegari su Umma suka bar Suhaima a cikin danginta cike da kewarta, ita kuwa har da kuka
ta janyo su Iman ta rungume su a hankali ta ce da su.
"Yaran Mama fatan za kuke ziyartata ba za kuke barina da kewa ba?"
GyaÉ—a mata kai suka yi Iman ta ce.
"Mama za muke zuwa kullum muna hira dake, ki sani kodayaushe muna a tare dake da kin ji ki
na son ganinmu to za ki ganmu. "
Murmishi ta yi ta ce.
"To shi kenan ku gaishe da babanku sai kun zo."
Ta yi maganar ta na sakin su suka wuce suna É—aga mata hannu. Tun da suka fara magana
Sayyid na jinsu, jin ta ce su gaishe shi sai ya yi murmishi ya tsaya su kuma suka wuce dan yana
son mata sallama..
Kallon shi ta yi ta na murmishi ta ce.
"Sayyid to sai wani lokacin ina godiya da kulawar ka a gareni ina ma fatan samun mace mai hali
irin naka."
Ta yi maganar muryarta na rawa; jin ta na shirin masa kuka ya ce.
" A'a Ummu kada ki yi kuka; kin san abin da nafi shiga damuwa to shi ne naji kina kuka ki shiga
ciki da zarar ki na son ganina za ki ganni ina tare dake Ummu."
Goge hawayen da ya zubo mata ta yi ta na murmishi ta ce.
"Wai kai ma kana da zuciya kamar bil'adama."
Dariya maganar ta ba shi sai ya yi murmishi ya ce.
"Ummu kenan! Kamar yadda kuke jin zafi da raÉ—aÉ—i idan kun rabu da abin da kuke so; to haka
muma muke ji fiye ma daku, muna da zuciya kamar yadda mutane suke da ita, muna jin
sha'awar abubuwan da duk wani bil'adama yake ji, kawai mu mun fiku ƙarfi ne sannan
halittarmu ba É—aya ba ce da ku, amma muna jin duk abin da kuke ji ko ma in ce fiye da ku
mutane.
Ina jin ba daÉ—i da baki kasance jinsi na ba, amma kuma ba komai hakan ba zan iya goge
ƙaunar da nake miki ba, ina sonki sosai Ummu musamman lokacin da kika haifa min su Ayan.
A lokacin naji kin gama yi mini komai a rayuwa; kin bani yaran da nake ta son samu duk da ke a
zahiri ba ganinsu kike ba sannan ba ki É—auki cikinsu a fili ba." Murmishi kawai Suhaima ta yi in taji ya ce wai ta haifa masa su Ayan jin abin take
ban-bara-kwai wai ita ce ta haifi yara biyu tun ba yau ba.
"To sai wani lokacin.
Taji sautin muryarsa yana mata sallama; hannu kawai ta ɗaga masa dan a wannan gaɓar ba za
ta iya ce masa komai ba, duk da shi ba mutum ba ne amma ya iya magana mai daÉ—i komai
nasa irin na mutane yake mata kamar shi ba wata halittar ba ce..
Ciki ta koma cike da tunanin maganganun Sayyid har bacci ya É—auke ta...
Sai dà Suhaima ta yi wata ɗaya sannan ta birkice ta ce kawai ita su Umma take son gani su
mayar da ita.. Washegari sai kawai ganin Sayyid ta yi ya bayyana a É—akinta ya ce ta haÉ—a
kayanta ta fita ƙofar gida yana jiran ta ya mayar da ita gida; sake da baki take kallon sa duk da
ba tsoro ya ba ta ba amma ya zo mata zuwan bazata, sai da ya ɓace ta janyo akwatinta ta fito
ta na gyara zaman hijabinta ta ce Sayyid na waje yana jiran ta. Da mamaki Sulaiman ya dube ta
ya ce.
"Kai yarinyar nan! Yanzu yana waje ba ki sanar damu ba ya shigo ciki ko da ruwa ne ya sha sai
ki barsa a waje."
Murmushi Suhaima ta yi a ranta ta na cewa da kun san waye Sayyid É—ina da ba sai kun wahalar
da kanku ba.
Tsaraba ba kaÉ—an ba suka haÉ—a mata a nan ta dage sai an ba ta Aminatu sun tafi da ita; ita ko
Aminatu sai murna take da aka ce mata za ta je Nigeria da Suhaima, da gudu ta É—auko kayanta
ko wanka ba ta yi ba ta ce su tafi. Dariya duk suka mata tsohuwa ta ce su tafi dan ta ga inda
Suhaima take zama, haka dai suka fito har gurin Sayyid ya gaisa da yan gidan sannan suka
wuce zuwa bakin hanya...
Mota ya tara suka shiga zuwa cikin birni daret airport suka nufa, ita dai Aminatu sai kalle-kalle
take yau dai gata a birni. Jirgin su ya sauka suka shiga ciki.
Sayyid ya so kawai ya kai Suhaima gida cikin daƙiƙu kaɗan, amma ganin Aminatu sai ya
haƙura suka zauna a jirgin..
Jirgin su na sauka suka samu Na'im ya zo É—aukan su ya yi tsaye yana jiran zuwansu. Bai gansu
ba su kuma sun gansa Suhaima ta saki Jakar hannunta ta nufi Na'im cikin jin dadin ganinsa..
Bai ankara ba sai taji an faÉ—o kansa ya juyo da sauri sai ya ga Suhaima ce, dariya ya yi ya ce.
" Anty sannu da zuwa ku zo muje."
Sayyid ya musu sallama ya fice suma suka nufi gida..
Suna zuwa aka dinga murnar zuwansu sosai Umma ta ji daÉ—in ganin Suhaima, da har ta shiga
damuwa ganin sun ce ta zauna da su ta É—auka amshe abarsu za su yi, sai gashi ta dawo har da
ƙari ma suka mata na Aminatu...
Cikin sauri ta shirya saboda ta yi latti; da sauri ta fito ta É—auki tea a tsaye ta dinga sha ta na
cusa bredi hannu baka hannu gwarya ta dinga yi har ta cinye ta wuce da sauri. Na'im ta samu a
mota tare da Aminatu ta ce.
"To fa! Yau kuma Aminatu za ka É—auka ku shiga gari ko?"
Dariya ya yi ya ce.
"Kai Anty to ai so nake ta zama Æ´ar gari makarantar koyon Hausa zan saka ta."
Murmishi kawai Suhaima ta yi suka wuce zuwa school...
Bayan an tashi ta fito ta na tafiya a hankali saboda muguwar gajiyar da ta yi, dan yau sun sha
darasi sosai.
"Am Suhaima!.
Ta ji an kira sunan ta cikin wata kalar murya mai daÉ—in sauraro; ta yi saurin juyo wa suka haÉ—a
idanu ta ja da baya ta na zare idanu..
TAKU HAR KULLUM MAMAN NUSAIBA.
[3/21 00:33] Ummu Amjad: _*í ¾í·Ÿâ€�♀ï¸�í ¾í·Ÿâ€�♀ï¸�A MAƘABARTA NE í ¾í·Ÿâ€�♀ï¸�í ¾í·Ÿâ€�♀ï¸�*_
Daga Alƙalamin
_Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_
_í ½í´”í ½í³šJARUMAI WRITER'S ASSOCIATION í ½í³š_
SADAUKARWA GA MUTANE BIYU:
*AYUBA MUHAMMAD ÆŠANZAKI (Zakin Marubuta)*
*JIBRIL ADAMU RANO (Malam)*
مسب الله Ù†Ù…ØØ±Ù„ا Ù…ÙŠØØ±Ù„ا
í ½í´ší ½í´ší ½í´ší ½í´ší ½í´ší ½í´ší ½í´ší ½í´ší ½í´ší ½í´š
1�⃣4�⃣
Da mamaki yake kallon ta ganin yadda ta tsora daga yin arba da shi; riƙe baki ya yi ya soma
magana cike da mamaki.
"Suhaima!
Ya kira sunan ta cikin wani irin yanayi; yadda ta zaro masa fararen idanunta ba ƙaramin tafiya
da imaninsa ta yi ba.
Baki na rawa ta ce.
"Sa...Sayyiddd!
Taja sunan cikin rikicewa haÉ—in da zallar tsoro bisa kan fuskarta, jikinta duk ya É—auki rawa sai ta
ƙura masa idanu ta na binsa da kallon ƙurulla. Shi kam harde hannayensa a ƙirji ya yi yana
mamakin jin ta kirasa da Sayyid, to waye ma wani Sayyid da take haÉ—a sa da shi?
Ya tambayi kansa yana ciza lips ɗinsa na ƙasa.
"Waye kuma Sayyid Suhaima?
Ya yi maganar yana waro nasa idanun. Jin abin da ya faÉ—a sai taji ta É—an samu nutsuwa, sosai
ta dinga mamaki ganin mai kama da suffar da Sayyid ke bayyana a gareta, wata irin nannauyar
ajiyar zuciya ta sauke sannan ta soma ba shi haƙuri.
"Yi haƙuri Malam; ka yi min kama da wani ne da na sani shi ya sa kaji na kira ka da haka."
Ƙayataccan murmishi ya sakar mata sannan ya gyara tsayuwarsa cikin nutsuwa ya ce.
"Am dama ina son mu yi wata magana ne; tun wancan satin