Showing 9001 words to 12000 words out of 39858 words

Chapter 4 - A Makabarta Ne Book Compelet By Sarat Alkasim

faɗa wa Anty Suhaima? Ni fa kun ɗaure mini kai da yawa ki fahimtar dani Umma."
Mayafin ta ɗauka ta yafa ta lulluɓe jikinta sannan ta kalli Umma da ta ƙura mata idanu ta ce.
"Umma ki yi wa wannan ɗan rainin hankalin magana ni ta ƴar'uwata nake yanzu bani da lokacin
yin faɗa da shi, in ban da ma ka rainani ni yayarta ce ta biyu amma so kake ƙarfi da yaji kai ka
koma babba dan ka ga ka girma ka fimu tsayi ko? To ka fita idona karka sake tambayata."
Ta ƙarashe ta na tsuke bakinta dan kar ma ya sake faɗa mata magana..
Kwafa ya ja dan ya lura basa son shi da Suhaima su san abin da suke ɓoye musu, ita kuwa
Umma lokacin da Suhaila na magana kaɗan ya rage ta rufe mata baki jin ta na neman kira
musu ruwa; itama kanta Suhaila gane za ta yi katobara ya sa ta rufe Na'im da faɗa ta ci sa'a
kuma bai ce komai ba...

Sai gaf da Magariba likitocin suka fito daga pɗakin su uku biyu mata ɗaya namiji suna biye da
shi a baya, suna ganinsu namijin ya tsaya a gurin su Umma ya ce.
"Ku biyoni Office."
Na'im ya bi bayansa su kuma suka zauna zaman jiransa; bayan sun zauna Doctor ya shiga
masa bayani dalla-dalla..
"Babu wata matsala mai yawa kawai dai ta firgita ne ko na ce ta ga abin da ya firgitar da ita,
hakan ya haddasa mata bugawar zuciya da zazzaɓi mai zafi sosai har ruwa da jinin jikinta suka
ƙare. Amma Alhamdu Lillah abun ya zo da sauƙi zan rubuta maka magunguna sai take sha in
sha Allah za ta warware, amma fa kuke kulawa da ita sosai kar ta kuma firgita da taimakon
Allah numfashinta ya daidaita."
"To in sha Allahu Doctor hakan ba za ta sake faruwa ba, na gode sosai."
Cewar Na'im yana miƙa hannu suka sallama sannan ya kuma cewa.
"Za mu iya ganinta?"
"E amma sai gobe in sha Allah za mu sallame ku.. Miƙe wa ya yi ya fita zuciyarsa na
wasi-wasin lamarin gidan nasu.
Bayan ya dawo ya faɗa musu yadda suka yi da Doctor suka mata fatan samun lafiya, Abba
ya kira suka ce bacci take sannan suka shiga ciki. Kwance suka ganta kamar gawa hannu
ɗaya an sa mata ruwa ɗaya an sa mata jini, fuskarta ta yi wani irin haske ta koɗe kamar ta
kwashi watanni ta na cutar; bakinta ya bushe ƙayau kamar ta kwana ba ta sha ruwa ba.. Zama
suka yi suka sa ta a gaba suna kallon ta cikin tausaya wa halin da take ciki.
Washegari wuraren ƙarfe goma na safe aka basu sallama, zuwa lokacin Suhaima taji sauƙi
sosai sai dai rashin ƙwarin jiki haka suka dawo gida.

Suhaila ta haɗa mata ruwan wanka ta dawo ta taimaka mata ta shiga sannan ita ta dawo;
shuru ta yi ta na tunanin jariran nan so take ta sake ganinsu su faɗa mata abin da zai fitar da ita
daga wannan masifar da take ciki. Lumshe idanu ta yi kamannin yaran na mata zigo a idanun
zuciya, ganin dai zaman ba zai fishe ta ba ta daure ta watsa ruwan ta ɗauro alwala ta fito. A zaune ta samu Suhaila ta miƙa mata hijabi ta amsa ta na binta da kallo.
"Ya dai malama ko kin ga na canja ne kike mini kallon ƙurulla?" Murmishi Suhaima ta yi ta
juya ta tayar da sallar da ake binta daga ta jiya har ta yau duk sai da ta rama sannan ta zauna;
shayi mai kauri ta miƙa mata, ba muso ta amsa ta soma sha. Bayan ta shanye ta miƙe a hankali
ta isa bakin gadon ta zauna ta kalli Suhaila ta na ƙaƙalo murmushin yaƙe ta ce. "Anty Suhaila wai tun yaushe kike tare damu?"

Harara ta aika mata sai kuma ta mayar mata da murmishin ta ce.
"Ai tun jiya nake nan ke kina bacci shi ya sa ba ki san lokacin da na zo ba; yanzu ya jikin
naki? Don Allah Suhaima ki daina saka damuwa a ranki kin ji kar ki ja wa kanki ciwo kuma,
waye ya firgita ki wai jiyar?"
Kukan da take ƙoƙarin danne wa ne ya fito ta faɗa jikin Suhaila ta fashe da kuka wi-wi tamkar
ana yankan naman jikinta; jikin Suhaila ya yi sanyi sosai ganin yadda Ƙanwar tata ke kuka
bil'haƙƙi. Sai da ta yi mai isar ta sannan ta ɗago da ita ta ce.
"Ƙanwata ki faɗa mini me ke damunki? Ko Abba ne ya takura a kan maganar fito da miji?"
Girgiza kai ta yi ta tsayar da kukan da take ta ce.

"Anty ya zan yi da rayuwata ne? Da na kwanta bacci ita nake gani ta na son kasheni."
Waro idanu Suhaila ta yi cike da al'ajabi ta ce.
"Wace ce ke son kasheki?"
"Ni ma ban san ta ba, haka kawai nake ganinta a mafarki na faɗa wa su Abba amma sun ce
mafarki ba gaskiya ba ne, Anty ki taimakeni Wallahi tsoron ta nake ji."
Ta ƙarashe maganar ta na sakin wani sabon kukan ta shiga ba ta labarin aljana Janu da take
gani a mafarkin ta, amma ba ta faɗa mata jariran nan ba.. Ajiyar zuciya Suhaila ta sauke ta ce.
"Ki kwantar da hankalinki in sha Allah da kin samu sauƙi zan ɗauke ki mu tafi Kaduna akwai
wani babban Malamin addini zan kaiki wajansa mu gani ko zai gano abin da yake haɗa ki da ita
wannan aljanar, yanzu kwanta ki huta Umma ta ce gobe Inna Laure za ta zo gurin sadakar uku
na Uncle. Wai ashe basu ji mutuwar ba sai yau kin ji irin ɗibar albarkar da ta yi wa Abba kamar
za ta fito daga waya ta dake shi, Inna Laure ba dai masifa ba Allah ya kawo ta."
Wani sanyi Suhaimata ji ya ratsa ta ko ba komai ƴar'uwarta ta fuskanci damuwarta, bugo da
ƙari kuma ga Inna Laure za ta zo wadda ko kallon banza ba ta so a yiwa Suhaima lelenta take
kamar Auta..
"Allah sarki Innata Allah ya kawo mini ita lafiya har na ƙagara ma na ji muryarta. " Dariya
Suhaila ta yi ta ce.
"To ai shi kenan bari na ba ki guri ki huta nima baccin nake ji sai an jima." Jinjina mata kai ta yi
ita kuma ta fita daga ɗakin ta rufo mata ƙofa...

Gyara kwanciyarta ta yi so take ta yi bacci ko ta haɗu da yaran su ci gaba da mata bayani,
amma kuma wani ɓangaren na zuciyarta tsoro ya cika shi ba ta son ta sake ganin Janu. Ajiyar
zuciya ta sauke ta rufe jikinta da bargo ta dinga karanta Ayatul kursuyu ta na addu'ar ko bacci
ya shure ta kar ta haɗu da Janu da duniyar mafarkinta...
Zaune suke a tsakiyar ƙungurmin daji ita da wani tsoho da mata da mijin nan an ɗaure su da
sarka; Janu ce ta bayyana a gabansu cikin mummunar suffa hannayenta riƙe da dalleliyar
takofi mai kaifi da tsini sai walkiya take.. Idanu waje Suhaima ke kallon Janu ganin ta nufo
gareta, wata irin dariya ta yi mai haɗe da kuka ta tashi sama ta tsaye a kan mata da mijin nan ta
ce.
"Kina tunanin za ki iya kuɓuta daga tarkona ne? Kin yi kuskure da kike son sanin wani abu da
ya shafeni, ke ɗin mallakina ce an mallaka mini ke tun ma kafin ki san ke wace ce. Zan
maimaita abin da na yi shekarun baya idan har ba ki bani jininki na sha ba ko kuma ki bani na
wasu ki ceci kanki." Ƙirjin Suhaima ya shiga bugawa ta juyo da nufin da yi wa tsohon nan magana sai ta ga babu
kowa daga ita sai Janu a tsakiyar dajin, jefen Janu ta juyo baki na rawa ta ce.
"Janu to ni taya aka yi na zama mallakinki. Sannan waye ya mallaka miki kaina da kike son
kaini lahira?"
Wata gigitacciyar tsawa ta daka mata ta dawo gabanta ta ce.
"Ba zan faɗa miki ba indai har ba ki sani ba, to ki zauna a haka kasheki dai sai na yi na shanye
jinin jikinki yanzu a nan ba'a ko'ina ba."
Takobin ta sa ta yanki hannun Suhaima sai ga jini yana ta zuba, ƙara Suhaima ta ƙwalla jin wata
irin azaba ta karaɗe mata jiki, kafin ta motsa ta ga jinin jikinta na ƙara kwarara.

Ita kuwa Janu hannunta mai kama da na biri ta miƙa ta ba tarar jinin ta na shanye wa, ganin
zubar jinin ya ragu ta kuma ɗaga takobin ta yanki ciyar Suhaima.
"Inna lillahi wa inna ilaihin raju'un! Ta faɗa cikin tsananin azaba, ita kuma Aljana Janu ta dinga
lashe jinin dake zuba ta na yin wata mahaukaciyar dariya.
Tashi ta yi ta soka takofin a ƙasa sai gasu a cikin maƙabarta, ta miƙa hannunta gefe sai ga
sabon ginan ƙabari ya bayyana ta kwashe da dariya ta ce.
"Yau zan cika burina a kanki Suhaima, yanzu zan ci gaba da shan jinin ki idan na shanye tass
sai na faɗeki ta cinye naman jikinki, idan na gama kuma na binne kasusuwanki a cikin ƙabarin
nan."
Ta na gama faɗin haka ta kuma nufo Suhaima da numfashinta ya kai wa da komo wa, takobin ta
ɗaga za ta soka mata sai ga haske ya bayyana ya musu tsakani..

A fusace Janu ta dubi hasken ta kai masa sara ya kauce sai ya bayyana a suffar mutane, namiji
ne dogo sosai ya lulluɓe ko'ina na jikinsa idanunsa kawai ake iya hango wa; Suhaima ta ɗago ta
na kallon yadda suke fafatawa tsakanin shi da Aljana Janu, matso wa ya yi kafin Janu ta ankara
ya shuri Suhaima suka ɓace.. A ɓakin ƙofar gidansu ya sauke ta ya juyo ya hura mata iska, ji ta
yi jikinta baya ciwon komai ya juya zai wuce ta ce.
"Bawan Allah!"

Juyo wa ya yi bai yarda sun haɗa idanu da ita ba kuma bai masa ba ya dai tsaya.
"Kai wane ne? Sannan ya sunanka don Allah? Ina so na ga fuskarka."
Kyakyawan hannunsa ya kai kan fuskarsa ya soma ƙoƙarin yaye lulluɓin da ya yi....

Allahu Akbar! Allahu Akbar!

Sautin muryar Ladanin Masallacin Unguwarsu ne ya farkar da ita daga baccin da take; hawaye
sharr suka zubo mata a fili ta furta.
"Me ya sa ban ga fuskarka ba? Kai ɗin kuma waye?"
Rai ba daɗi ta miƙe ta yo alwala ta tayar da iƙama.

Wunin ranar haka Suhaima ta wuni ta na tunanin wannan wanda ya ceci rayuwarta, haka dai ta
kwanta har dare ta na fatan in ta yi bacci ta gansa ya buɗe masa fuskarsa ta gani....

Washegari Inna Laure ta iso Kano, ta na dira daga mota ta dinga sababi tun daga harabar gidan
har ta shiga cikin palon; bakinta har kunfa yake saboda masifa ta tsaya a tsaye.. Da gudu
Suhaima ta fito suka rungumi juna cikin nuna farincikin ganin juna. Da ƙyar aka shayo kan Inna
Laure ta daina faɗa sai dai ta ce baza ta ci abincin gidan ba Suhaima ta je ta sayo mata masa
da miya a nan bayan layinsu, hijabi ta sa ta fita cikin sauri...

Tafiya take ta na sauri, ta iso jikin wata bishiya dake bakin hanya tsaya ta na gyara hijabint.

"Yarinya!"

Da sauri ta ɗago kai; idanu ta zaro baki na rawa ta ce.


*To fa masu karatu ga dai Suhaima a inuwar bishiya ko mai zai faru?*


_*Taku har kullum Maman Nusaiba ce )*_
[3/5 16:23] Ummu Amjad: _*🧟‍♀️🧟‍♀️A MAƘABARTA NE 🧟‍♀️🧟‍♀️*_



Daga Alƙalamin

_Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_


_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_



SADAUKARWA GA MUTANE BIYU:

*AYUBA MUHAMMAD ƊANZAKI (Zakin Marubuta)*

*JIBRIL ADAMU RANO (Malam)*


مسب الله نمحرلا ميحرلا


0️⃣6️⃣


Baki na rawa ta ce.
"Baba." Kallon ta tsohon ya yi fuskarsa na dauke da damuwa bai ce da ita komai ba; ganin
haka yasa Suhaima ƙaraso wa inda yake zaune ta durƙusa cikin tashin hankali ta ce. "Baba ka
yi magana mana. Ba kai ba ne na gani jiya cikin mafarkina? Ko kaima so take ta kashe ka
kamar yadda take son ta kasheni ban mata komai ba? Baba shin ka na da alaƙa da ita ne? Ko
turo ka ta yi ka kai mata ni?"
Ta jero masa tambayoyi a jere kamar wata ƴar jarida tsoro da firgici sun mamaye zuciyarta.
Shi kuwa tsoho ya yi shuru sai ma soke sandarsa ya yi ya riƙe ta yana daga zaune ya sunkuyar
da kai har ta gama maganar bai ɗago ba, Suhaima ta kuma faɗin.
"Baba ba ka ce komai ba."

Ta yi maganar a sanyaye zuciyarta na ce mata ta gudu shi ma cutar da ita zai yi, wani ɓangaren
na zuciyarta na hana ta guduwar.. Ɗago kai ya yi ya dube ta kamar ba zai ce komai ba zuwa
lokacin jikin Suhaima rawa yake ganin yadda idanunsa suke wani irin haske, har ta yanke
shawarar tafiya ta tsinkayo muryarsa kamar daga sama yana magana.. "Ni ba cutar da ke zan yi ba, halisa ma na zo ne na ba ki haƙuri a kan abin da na aika miki
tun kafin ki zo duniya."
Baki sake Suhaima ke kallon tsohon to dama ya san ni wace ce kenan? To in ko haka ne bari
na masa tambaya ko zan samu mafita daga wajansa. Ajiyar zuciya ta sauke bayan ta gama
shawara da zuciyarta ta ce.
"Baba to ni kuwa mai ka aikata a gareni da har kake neman yafiya ta? Da alama dai ka san
wannan muguwar ko?"
"Kwarai kuwa na san ta sosai ma, mun yi zamani da ita lokaci mai tsayi da ya shuɗe. Da ban yi
mu'amala da ita ba yanzu da ki na cikin kwanciyar hankali, amma sai dai na kasa wannan
tunanin gashi yanzu ke da kika rage ta na son ɗauke ki ta sha jininki..
Baki Suhaima ta bude ta na jin wani hargitsatsen labari mai cike da ɗaure kai da rashin sanin
bakin zaren; jin ta ƙage da durƙushen ta gyara ta zauna ta ce.
"To in kuwa haka ne Baba bani labari ka na da wata alaƙa da ni ne?"
Murmushi tsoho ya yi ya ce.
"Kwarai kuwa yarinya ni kuwa nake da alaƙa da ke, ki bari ba yanzu ba zan ba ki labarin
rayuwarki. Zan warware miki zare da abawa idan na sake dawowa, idan kuma ban dawo ba zan
turo wani a madadina."
Yana gama faɗin haka ya miƙe tsaye da ƙyar, su Suhaima har da miƙe wa ta riƙe masa sandar
ya tsaya da kyau sannan ta ce.
"Baba to amma me ya sa ba za ka faɗa mini yanzu ba? Wallahi ina cikin damuwa da tashin
hankali, Abba da Umma sun ƙi faɗa mini abin da suke ɓoye wa."
"Za mu yi magana wani lokacin.
Kafin ta ɗago ta ga ya ɓace ɓat tamkar bai taɓa wanzuwa a wajan ba; rushewa ta yi da kuka ta
sunkuya ta ɗauki zoben da ya yada ta na kallo, zoben fara ce sol sai sheki take.. Kamar wadda
ake yi wa magana a kunne ta yi shuru, zuwa can kuma ta yi saurin saka zoben a yatsarta ta
hagu sannan ta miki jiki ba ƙwari; goge hawaye ta yi ta juya ta fice zuwa inda take son zuwa...
Ta na isa wajan mai masar ta miƙa dubu ɗaya ta ce.
"Maman Yusuf ki bani Masa ta ɗari uku, ko kuwa ma bani ta dubun kawai." .
Baki a washe Maman Yusuf ta amsa ta zuba mata a cikin leda, sai da ta miƙa mata suka haɗa
idanu Maman Yusuf ta waro idanu cikin zallar mamaki ta ce.
"Suhaima kece kuwa? Me ya faru dake haka na ga kin rame sosai?"
Murmushin yaƙe ta yi ta ce.
"Bani da lafiya ne shi ya sa."
Fatan samun lafiya ta mata ita kuma ta wuce gida.
Koda ta iso bakin get ɗin gidansu tsayawa ta yi ta saisaita nutsuwarta sannan ta buɗe ta shiga;
Inna Laure na zaune ta kafe ɗaurin ɗan kwali a gaban goshi ta na kaɗa kai sai ga Suhaima ta
Shigo.
"Yawwa ƴar albarka ɗiyar Innarta maza kawo mini masar nan rabona da abinci tun jiya, kwana

na yi ina kukan takaicin rashin faɗa mini mutuwar Abdallah. Yanzu in ban da rashin mutumci irin
ubanku taya za ayi mutuwa amma sam ya kasa sanar dani, wannan ai rashin sanin darajar
'yan'uwantaka ne."
Ta ƙarashe maganar ta na fashewa da kuka har da sauke ɗankwalin daga kanta ta rufe fuska
da shi; Shuru duk suka yi Suhaima ta iso gabanta a sanyaye ta ce.
"Innata ki yi haƙuri Abba ya kira wayarki ba ta shiga ƙarshe ma a kashe ake ce masa, shi ya sa
ba kiji a kan lokaci."
"Allah sarki Audu kwanaki ya kirani ashe hirar ƙarshe ce muka yi da shi, ba komai Suhaima na
yafe wa Mukhtar ba dan halinsa ba. Yanzu bari na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0