Showing 24001 words to 27000 words out of 39858 words

Chapter 9 - A Makabarta Ne Book Compelet By Sarat Alkasim

inda suke ya ɗaga takobin ya sara mata ta kuma kurma ihu azaba, a fusa ce ya ce.
"Shin za ki rabu da Mamana ko sai na aika ki can ne?"
Duk da raɗaɗin azabar da take ji hakan bai hana ta mayar wa da Ayan martani ba.
"Yaro koma baya da ubanka nake yi ba kai ba."
Sake kai mata suka ya yi ta kuma yin kururuwa dajin na amsa-koyawar muryarta, ta na wani irin
huci ta ce.
"Kar ka kasheni Ayan ita ɗin fa an sadaukar mini da jininta, dan haka ka rabu dani ku yi
rayuwarku ni ku bani ita na rabu daku; ina son shan jininta dan yana da garɗi sosai. Idan za ka
bar mini ita zan kirkiro maka wata sabuwar uwar mai kama da ita sak sai ka bani ita z..
Ba ta ƙarasa maganar ba Iman ta daka tsalle ta fille mata dogon hannunta; cikin azaba da zafi
ta juyo ta kalli Iman ta na numfashi da ƙyar ta ce.
"Karki kasheni zan baki ƙarfin tsafina ki ƙara ƙarfi, wannan uwar taki an bani ita."
Wani irin juyi Iman ta yi ta watsa hannun ta a kan Janu sai ga sarƙar dake hannun Janu ta
daure Janu gam-gam...

"Na haƙura da ita ku rabu da ni zan tafi na barta har abada ba zan, zan baku komai nawa ni
duka yankin ma zan bar muku na koma yankin da ba kowa na zauna. "Janu ta faɗa a
gakabaice ta na roƙon Iman dake murza zoben hannunta ta na ƙara matse Janu, duk inda
sarƙar ta kwance sai ta zuba mata wata irin azaba mai raɗaɗi."
"Kin yi ƙarya wallahi ki tafi ba tare da kin warware sihirin da kika yi wa Mama ba; kuma shi
wanda ya sadaukar miki da itan ba kin kashe shi ba? Saboda zalinci irin naki iyayenta sun
sadaukar da kansu dan ki bar musu ɗiyarsu ta rayu; sai kika yarda amma daga baya kika dinga
bin ta kina shan jinin jikinta ke muguwa, to yau ƙarshen ki ya zo Ayan ka fille mata hannun ɗaya
"Ta ƙarashe maganar ta na mai bai wa Ayan umarni da ya aiwatar da abin ta saka shi ya yi."
Kafin ta juyo ga Ayan buɗe bakinsa wani irin hayaƙi Green ya fito daga bakinsa ya sauka a kan
hannun sai ga shi a ƙasa...

"Waiyo! Waiyo! Ku rabu dani ba zan sake ba kar ki kasheni ku taimaka.
Haka take faɗa jin yadda ake yankar ko'ina na jikinta.

Sake kai mata suka ya yi ta kurma wata irin kururuwa; birgima ta dinga yi ta na kiran wani suna
tak ai ta na ƙoƙarin tashi. Cikin mugun sauri Ayan ya caka mata takobi; ta dinga juyi ta na
wuliliya zuwa can dajin ya ɗauki girgiza, wuta ce ta kama dajin gabaɗaya har da jikin Janu
wutar na ci amma ana jin sautin muryar ta ta na roƙon su Ayan... Sai da suka ji ta daina maganar sannan Sayyid ya janyo Suhaima ya sa hannu ya zare mata
wuƙar da Janu ya caka mata; kama su ya yi gabaɗaya suka ɓace a dajin..

Basu bayyana a ko'ina fa sai a cikin wani daji mai cike da furanni ga kukan tsintsaye; kan wani
gado mai mugun kyau ya kwantar da ita. Ayan ya matso kusa da ita ganin yadda jini ke zuba ya
dafe gurin yaan rufe idanunsa, can ya buɗe ya jikin ya raga zuba amma bai tsaya duka ba..
Tattaba jikinta ya yi yaji a sake ya rufe idanu ya ɗaura hannunsa akan saitin zuciyarta yaji ba ta
bugawa, a tsorace ya buɗe idanunsa wanda suka koma ja ya dubi Sayyid ya ce.
"Baba ta kashe Mama."
Saurin ɗauko ta Sayyid ya yi yana tattaba amma sam ba ta motsi..

Wani irin ƙara Ayan ya yi ya kwanta a kan Suhaima cikin tashin hankali ya ce.
"Mama kada ki mutu ki barmu muna sonki, Mama!
Ya faɗa cikin tashin hankali...




*mai ke faruwa da Suhaimar Sayyid?😢*





_*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_
[3/14 22:54] Ummu Amjad: _*🧟‍♀️🧟‍♀️A MAƘABARTA NE 🧟‍♀️🧟‍♀️*_





Daga Alƙalamin

_Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_


_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_




SADAUKARWA GA MUTANE BIYU:

*AYUBA MUHAMMAD ƊANZAKI (Zakin Marubuta)*

*JIBRIL ADAMU RANO (Malam)*

مسب الله نمحرلا ميحرلا

1️⃣1️⃣

Lumshe idanu Sayyid ya yi tare da kai hannunsa saitin zuciyarta; danna ƙirjinta ya yi da ƙarfi
amma shuru, Iman da ta yi lamo kamar marayan da bai ci komai ta dubi Sayyid ta soma
magana..
"Baba ka tashi Mama mana."
Kafin ya yi magana ta ja dogon numfashi sai tari ya biyo baya; saurin canja suffarsu suka su
duka suka dawo suffar mutane kamar yadda ta san su, gabaɗaya kan ta suka yo Ayan ya yi
saurin kiran sunanta.
"Mama ki tashi kasa ki tafi ki bar mu."
Buɗe idanunta ta soma yi a hankali har ta buɗe tarr; ta juyo jin hannunta a cikin wani lallausan
hannu ta kalli hannun sai ta ga nashi ne, yunƙurin tashi ya soma yi Sayyid ya ɗago da ita ya
zaunar duk sai jera mata sannu suke. Hannu ta kai kan gefen cikinta wanda zuwa yanzu jinin ya
daina zuba, da sauri ta kalle su ta ce. "Dama ba ciwo naji ba yanzu?"
Ta faɗi maganar ta na kallon su kamar ta samu TV; gyara mata zaman ya yi sannan ya ce.
"Kin warke ne yanzu nasan bakya jin ciwon komai ko? "Cewar Sayyid yana shafa summar
kanta; ita kuwa shuru ta yi jin wani sanyi na ratsa mata sassa jikinta, tunano abin da ya faru ta yi
ba shiri ya zabura za ta tashi ya kalle ta.
"Ya dai?"
"Wannan muguwar tana raye kuwa?"
Iman ta yi murmishi sannan ta cè.
"Mama ai yau mun shafe tarihin rayuwarta, daga yau kin daina jin tsoron yin bacci ko fita wani
guri."
Sororo take kallon Iman har za ta yi magana sai kuma ta fasa mata ta juyo kan Sayyid.
"Sayyid wai dama kaine baban su Ayan shi ya sa suke ce mini Mama?"
Gyaɗa mata kai ya yi yana murmishi; ita kuwa ta ƙura masa idanu tuna matsayin su Iman yasa
ta kuma faɗin.
"To dama ka yi aure ne? Kuma ina mahaifiyar su Ayan take ne?"
Kallon ta ya yi da kyau sannan ya ce.
"To ai 'ya'yanmu ne ni da ke."

A zabure ta kalleshi jin amsar da ya ba ta, cike da mamaki ta ce.
"Ni kuma? E to tun da naka ne ai ni ma sun zama nawa?"

"Ba irin haka nake nufi ba Ummu; ina nufin ke matata ce. "Ya faɗa cike da tabbatar mata
maganar tasa.
Tamkar wata zautacciya haka take kallon Sayyid; murmishi ta yi ta ce.
"Sayyid yaushe kuma muka fara wasa da kai? Ni fa rabona da na ganka an fi shekara goma

lokacin fa tun muna yara ni da kai, amma sai ka ce wai ni matarka ce a wa ya ɗaura mana
auren ne?"
Jinjina kai ya yi yasan dama za a rina; kamu hannayenta ya yi cikin nuna so da ƙaunar da yake
mata ya ce.
"Kwarai kuwa ni mijinki ne Kakan ki ya bani ke tun ranar da kika zo duniya." Wani irin sarawa
kan ta ya yi ta yi saurin runtse ido; wannan wacce irin kalma ce haka? Ita ɗin ce aka aurar tun
tana jaririya anya ma da gaske Sayyid ɗinta yake? To in ko haka ne kenan yasan inda za ta ga
ahalinta. Saurin buɗe ido ta yi ta ce. "To ka sanar dani a ina ahalin iyayena suke? Sannan taya ka aureni ban sani ba ina buƙatar jin
haka Sayyid ka daure ka fitar dani daga cikin duhun da nake ciki."
Sai da ya kamo hannunta ya murza a hankali sannan ya ce da ita.
"Ni ba bil'adama bane kamar ke."
Ƙuuuuu! Cikin Suhaima ya bada ta zaro idanu bakinta na rawa ta ce.
"B..Ban gane ba? Kai ɗin ne ba mutum ba?"
"Sosai ma ni ba bil'adama ba ne; kuma nasan kin san yaran nan suma ba bil'adama ba ne
kamar ke, dukkanmu aljanu ne ba mutane ba kuma nine mijinki uban 'ya'yanki gasu nan Iman
da Ayan." Luuu! Ta yi baya za ta faɗi ya taro ta ta dawo ta zauna; a ruɗe take kallon su nan da
nan ta tuna su Umma, yanzu shi kenan dama dan su kawo ta yankin aljanu ne suka ɗauke ta?
Shi kenan ba za ta sake ganin su Umma ba?
Saurin dafe kai ta yi ta ce.
"To amma taya ka zauna da kakana har ya ɗaura ma aure dani?"
Gyara zama ya yi ya ce. "Kada ki tsorata dani Ummu; ki kwantar da hankalinki ba wanda zai
sake cutar min da ke. Zan mayar dake gida bayan na ba ki labarin rayuwarki da kuma yadda
aka yi aka mallaka wa Janu ke, ina so ki nutsu da kyau kiji wannan labarin."
Cikin zaƙuwa ta ce. "To."

"A can baya wasu shekaru da suka shuɗe; akwai wani gagarumin Boka mai suna Kata wanda
yake a ƙasar Ghana a yankin Yamma. Boka Kata ya kasance yana aiki kamar yankan wuƙa,
hakan yasa mutane bila'adadin suke ziyartar shi a kodayaushe, yana da alaƙa da aljannu
kala-kala akwai mugaye, akwai masu saukin kai, akwai baƙaƙen aljannu. Akwai sheɗanun
aljannu, akwai masu haɗa soyayya tsakanin mace da namiji. Ni na kasance ɗaya daga cikin
wanda yake haɗa so koda kuwa namijin baya so sai na sa ya so budurwar, ko in macen ce ba
ta so sai na cusa mata son saurayin nata dole ta so shi kamar ta cinyeshi..
Janu tana ɗaya daga cikin sheɗanun aljanu, duk wani aiki na kisa ita ce nakasa mutum,
makanta, gurgunta,kurumta,hauka, sa mutum ya shiga duniya, sa mutum ya zama ɗan iska,
mayar da mutanen kirki abin tausayi, waɗannan kaɗan daga cikin aikin Janu kenan..

Muna nan tare da Boka Kata sai kawai naga wata mace a cikin jeji ta na gudu; a wannan
lokacin na sauko na tambayeta lafiya take gudu? Sai ta ce dani.
"Abin bauta ya taimake ka ana so a kasheni ne zan shiga duniya."
Jin haka sai ce da ita.
"To zan taimake ki idan za ki bini inda nake."
Ba ta musa min ba sai ta bini muka tashi gidan Boka Kata; koda muka je lokacin ya tashi daga

aikin ganin ɓaki na gabatar masa da ita, ganin nine na kawo ta bai musa ba ya bata masauki...

Haka yake kyautata mata ni kuma ganin Boka Kata ya samu abokiyar rayuwa sai na yi amfani
da tsafina na haddasa a tsakaninsu; gari na waye wa yaje ya faɗa mata yana sonta amma shi
dai Boka ne zata iya aurensa? A lokacin murmishi ta yi ta ce masa ita ma ai suna bauta wa
wani gunki ne dake cikin wani teku, a dokar garin nasu idan har baku haihu da saurayinka ba
kafin aure; to ba sai ace ba ka haihuwa daga ranar an sadaukar wa da sarkin garin kai, shi zai
yi yadda yake so da kai, ko ya dinga amfani da kai har ƙarshen wayuwarka,
Ko kuma ya mayar da kai baiwa. Ita kuma a garin nasu ta samu wannan matsalar; sun kai
shekara suna tare da saurayinta amma ba ta samu ciki ba, dan haka aka miƙa wa sarki ita ya
ce sai dai ta zama baiwarsa. Ita kuma taga ba za iya ba sai ta sulale cikin dare ta wata hanya
dake cikin dakin da aka kaita ta gudu, har zuwa safiya ta na tafiya sai suka dinga binta ƙarshe
dai ta samu ta tsira ta yo nan..

Ko da Boka Kata yaji labarin rayuwar wannan yarinya sai ya cika da mamaki; amma kuma sai
ya aje gefe ya tambayi sunanta, ta ce da shi sunan ta Dudu.. A ranar mu muka ɗaura aurensu
aka yi shagali da dare muma muka tafi yankin mu.. Haka suka ci gaba da rayuwa har ta samu
ciki, Boka Kata ya cika da murna ganin shi ma zai samu wanda zai gaje shi; Suna ta rainon
cikin, lokacin da ta kusa haihuwa sai ya kirani ya ce na duba mu gani me za a haifa masa..
Tsafi na aiwatar nan na gano Namiji ne a cikin matar tasa, ya kamu da murna jin abin da yake
so ne. Wata rana sai ta haifi ɗanta namiji mai kama da ita; aka sha shagali ranar Janu ta yi wata
tafiyar ba ta nan aka yi haihuwar amma na sanar mata komai .
Boka ya sa wa ɗansa suna Damisa; wannan suna nima ya birgeni sosai har ita uwar yaron..
Haka ya dinga girma har ya zama cikakken saurayi; tun daga shi ba su sake haihuwa ba, yana
fita farauta sai dare yake dawo ba. Da taimakon mu ya zama mai ƙarfin gaske amma sai dai shi
baya son yin aikin Bokanci, idan Boka Kata na nuna masa yadda ake aikin Bokanci da kiran
aljannu sai ya nuna baya so sài ya shiga jeji ya yi farauta..

Ana haka wata rana ina zaune cikin jejin da yake farauta sai na gansa da wata yarinya dauke
da kwano a hannunta suna hira, sun jima suna hira inda take faɗa masa su a yankin Ethiopia
suke garinsu yana da nisa ba mutane sosai a can inda suke, shi ya sa ma suka yo nan dajin na
wajan Ghana suka zauna suna ci gaba da kiwon dabbobinsu, ina jinsu suka gama hira shima ya
bata labarin shi sannan ya raka ta har kusa inda suak yada zango sannan ya dawo gida..
Wasa-wasa suka kalla soyayya nima na ƙara musu da ƙarfin son juna; a kwana a tashi Damisa
ya ce ai shi fa ya ga wata yarinya yana so a aura masa ita...

Sosai Boka Kata da Dudu suka cika murna jin ya yi maganar aure; bayan ya tafi ya kiramu ya
faɗa yaronsa ya ga wata yana so a bincika daga ina ta zo.. Ni na faɗa masa labarin da ta ba wa
Damisa, Boka Kata ya ce sai Janu ta dawo sai aje anemo masa auren ta. Haka kuwa aka yi sai
da Janu ta dawo Boka ya sanar da ita, da farko ta so kar ayi auren sai Boka Kata ya tambaye
ko da matsala ta ce babu. Amma dai yarinyar in ta gano uban mijin da za ta aura Boka ne za ta
sa su gudu ita da Damisa; a lokacin da take bayanin na gane ƙarya take sai kawai na ce ta
barsa ya yi auren, ba dan ta so ba ta bari Boka Kata da shi da Dudu da Damisa da ni da Janu

da sauran tawaga muka tafi inda suka yada zango..
Muna zuwa muka nemi auren yarinya, sai Mahaifiyar yarinyar taƙi amincewa har sai da muka sa
ta da ƙarfin tsafi ta amince da auren, nan ne aka faɗa mana sunanta Zaira, bamu dawo ba sai
da aka daura auren aka bamu ita muka dawo gida...

Tare suke zuwa farauta Zaira da Damisa, muna zamansu lafiya shi da ita..

Lokacin da ta gane uban mijinta Bokanci yake sai ta ce gaskiya mijinta ba zai yi Bokanci ba,
Janu taji haushi sosai jin kalaman Zaira amma ta rabu da ita; haka ta dinga cusa wa Damisa kin
yin Bokanci wato gadan babansa. Cikin ƙanƙanin lokaci Zaira ta samu ciki suna ta murna...

Cikin nata girma kuma ba daina fita farauta a tare ba.

Aikin Boka Kata ya soma ja baya babu mai zuwa neman a masa wani abu, a lokacin ne kuma
na yi wata tafiya zuwa gurin dangina dake can wata nahiya; ya kira su Janu ya ce musu ya aka
yi hakan take faruwa ne yanzu ba masu zuwa.

Janu ta dube shi ta ce.
"Matsawar ka na son aikin ka ya dawo yadda yake; to sai an zubar da jinin bil'adama."
Jin haka sai Boka ya kamu da farin ciki ya ce da ita.
"Ai samo bil'adama ba wahala zai yi ba ko yau zan kawo miki ku sha jini ku ci gaba da aiki."
Janu ta ce.
"Jinin wani naka muke so ba na kowa ba; ka sadaukar min da jinin ɗanka ko matarka ko cikin
dake jikin matar ɗan ka, in yaso da mun sha jinin sai ta samu wani cikin."
Jin haka sai Boka ya shiga tashin hankali dan yana mugun son abin da yake cikin Zaira ;
dukkansu baya son daya daga cikinsu asha jininsa, ita kuwa Janu dariyar mugunta ta yi ta yi
tafiyar ta ta na jadadda masa indai bai yi sadaukarwar nan ba to tabbas zai rasa komai..

Kullum haka za ta zo ta yi ta masa maganar sadaukarwar, shi kuwa Boka ya kasa sanar da
ahalinsa wannan al'amarin.. Ganin yana ɓata mata lokaci Janu ta haɗa kai da wasu aljanu suka
kwashe duk dukiyar Boka, riga basu bar masa ba duk suka kwashe, Boka na zuwa ya ga an
kwashe komai cikin mamaki ya kira Janu ya tambaye ta me yake faruwa da shi ne. Buɗar bakinta sai ta ce ai masu buƙatar shan jini ne suka kwashe kayan ita kuma ba yanda za
ta yi da su, hankalin Boka ya kuma tashi sosai..

A takaice dai Boka ya koma bashi da komai, shi kansa Damisa da Zaira idan suka fita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0