Showing 12001 words to 15000 words out of 39858 words
Chapter 5 - A Makabarta Ne Book Compelet By Sarat Alkasim
tafi gidan na marigayi akwai masu zuwa
gaisuwa za su zo daga garinmu..
Murmushin yaƙe ta yi ta shiga kitchen ta ɗauko mata kwano ta zuba mata; sauko wa ta yi daga
kan kujera ta zauna ta yi bismillah ta soma cin abincin, ganin Suhaima ta yi tagumi yasa ta
yatsar da cin abincin ta zuba mata idanu ta ce.
"Ƴata lafiyarki kuwa?"
Ajiyar zuciya ta sauke ta ce.
"Innata da sauƙi dai zazzaɓi na yi na kwana ɗaya shi ya sa."
"Subhanallah! Bari muje mu dawo mu zauna za mu yi magana Allah ya ba ki lafiya.. Amin ta
ce ta koma kan kujera ta kwanta tare da lumshe idanu; tunanin mafita ta shiga yi amma sam ta
kasa gano inda lamarin nan zai tsaya mata cikin daɗin rai, jariran nan suka faɗo mata a rai ta
buɗe idanunta ta sauke su a kan Inna Laure dake cin wainar ta na goge hawaye. Dariya abin
yaso ya ba ta ganin ta na cin abinci ta na kuka, sake rufe ido ta yi ta na jiran Innar tata ta gama
su tafi dama su kaɗai suka rage su Suhaila sun wuce tun ɗazu...
Bayan Inna Laure ta gama suka wuce zuwa gidan Abdallah, koda suka shiga Inna Laure guri ta
samu ta zauna ta na goge hawaye mutanen da suka santa suna mata gaisuwa ta na amsa
musu tare da musu godiya....
Yau aka yi sadakar bakwai, kuma har yau Inna Laure ba ta samu sun zauna da Suhaima ta faɗa
mata damuwarta ba.
Misalin ƙarfe goma da dare, zaune take ta rafka tagumi kwanciya take son yi amma tsoro
da fargaba sun hana ta kwanciya. Wutar dakin ce ta ɗauke, shuru ta yi ta ƙasa motsawa daga
kan gadon sai ji ta yi an tsikara mata wani abu kamar allura a gefen cikinta; da sauri ta dafe
gurin ta juyo, babu abin da ta gani ta shafa wajan ta jan bargo ta rufa jikinta na rawa. Garam! Ta ji an banko ƙofar ɗakin da ƙarfi, kin buɗe ido ta yi sai ma ƙara ƙanƙame jikinta da ta
yi; surutai ta dinga ji cikin kunnuwanta ba shiri ta miƙe zaune ta na zaro idanu.
"Mama! Mama!
Ta ji muryarsu ta kawo wa kunnenta ziyara; saurin juyo wa ta yi gefen da taji muryar tasu ai
kuwa ta gansa a samar ɗakin suna mata murmushi, itama murmushin ta musu suka yo
ƙasa-ƙasa zuwa kan gadon ta miƙa hannu ta taro su sai taji nauyi sosai. Waro idanu ta yi
ganinsu a siffar yara 'yan shekara shida, kasa daure wa ta yi ta ce. "Ya aka yi naga kun koma masu girma?"
Macen da take haƙarƙarinta ta ce.
"To ai mun girma ne, kuma za mu iya zuwa miki a duk yadda muke so mu zo; sai dai Baba ya
ce muke zuwa a suffar mutane dan kar ki tsorata da yawa."
Jinjina kai ta yi ita dai mamakin yaran nan take da suke kiranta da Mama , ga shi har maganar
Baba suke mata wanda ba ta san shi ko wani kala ba ne; ajiyar zuciya ta sauke ta ce.
"Ranar da kuka zo kun ce za ku faɗa mini matsalata , to yanzu ina jiranku ku bani amsa me
kuka gano game da mafarkin da nake da wannan muguwar kun ga jiya ma har yankar jikina da
dinga yi ta na shan jinina, ta na gaf da kasheni sai ga wani ya zo ya ceceni amma ban san shi
ko waye ba dan yaƙi yin magana ballantana na ga fuskarsa."
"Mama kamar yadda Janu ta faɗa an mallaka mata ke ta sha jininki ta yi yadda take so da ke;
idan ta so za ta iya sarrafa zuciyarki take amfani dake ta na cutar da mutane dan dama halinta
kenan. Yanzu haka ta na nan ta na son taga bayanki abin da yasa ma ba ta samu damar yin
hakan ba muna lalata wasu abubuwan da take yi ne a kanki, amma ba dan haka ba da tun
shekarun baya za ta yi abin da takeso da ke.."
Kallon rashin fahimta Suhaima ke yi wa yaran, tsoro, mamaki, al'ajabi, tashin hankali, duk sun
tattaru sun kawo mata ziyara a lokaci ɗaya ta numfasa ta ce.
"To waye ya mallaka mata ni?"
Kallon kallo yaran suka dinga yi wa juna ganin haka yasa idanun Suhaima kawo ruwa ta soma
magana.
"Kun yi shuru ba ku ce dani komai ba, waye ya mallaka mata ni kuma meye haɗina da wanda
ya mallaka mata ni?"
"Mama indai har kina so ki san hakan to ki fara tambayar su Abba su faɗa miki abin da suke
ɓoye miki, idan sun faɗa miki mu kuma zamu ƙara binciko miki komai. A halin yanzu dai muma
ba mu san waye wanda ya sadaukar da jininki ga aljana Janu ba; Baba ya sani amma yaƙi faɗa
mana." Namijin ya faɗa yana kallon Suhaima da jikinta ya yi sanyi; Tsayar da hawayen ta yi ta ce.
"To ya zan yi ? Umma da Abba sun kasa faɗa mini abin da suka ɓoye taya zan gano bakin
zaren matsala ta ne?"
Ta faɗa ta na kallon su; Hayewa jikinta suka yi suna goge mata hawayen ita kam Suhaima ba
shiri ta kallesu jin yaran sun yi nauyi, hannu ta kai ta rungume su ta soma magana.
"Har yanzu ba ku faɗa mini sunanku ba, idan har da gaske ni mamanku ce to ki faɗa mini
sunayenku."
"Sunanmu Ayan da Iman Mama kuma ke mamanmu ce.
Macen ta faɗa ta na kallon Suhaima; murmishi ta yi ta daga baki za ta yi magana taji ana buga
ƙofar, zaro idanu ta yi ta ce. "Kun ga ana buga ƙofa ku tafi sai mun sake haɗuwa."
Ayan ya ce.
"Ba sai mun tafi ba Baba ya ce mu jima ya bamu lokaci mai yawa." Ita dai Suhaima shuru ta yi
ta na kallon ƙofar, buɗe ƙofar ta yi ta shiga da sallama ta na cewa.
"Ke ƴar nan yanzu kina jina ina buga ƙofa amma kin kasa tashi ki buɗe mini?"
Kallon su Ayan dake lafe a jikinta ta yi, ta ce. "Inna na gaji ne kasa tashi na yi amma dai a nan
za ki kwana ko?"
"Kwarai ma kuwa ina so mu tattauna ne naga duk kin rame sosai, wani lokacin ma sai ki yi
tagumi me ke damunki ne?"
Ba ta ɓoye mata komai ba ta faɗa mata duk abin da yake faruwa da ita, sai dai itama ba ta ce
mata ta yi mafarkin an kashe Uncle ɗinta ba. Riƙe baki Inna Laure ta yi ta na gyaɗa kai ta ce.
"Ikon Allah yo ke kuwa Suhaima me ya haɗaki da mafarkin aljannu?"
"Mama ki tambayeta abin da Abba suka ɓoye.
Taji muryar Ayan na magana; jinjina kai ta yi ta ce.
"Inna wai kin san wani sirri ne da su Abba suka ɓoye mini?" Da mamaki Inna Laure ta dube ta
ce. "Wani irin sirri kuma Suhaima? Dama akwai abin da suka ɓoye miki wanda kike son sani
ne?"
Ajiyar zuciya ta sauke ta ce.
"E Inna akwai dai abin da basa so na sani."
To ki yi haƙuri gobe ni zan tasa shi Mukhtar ɗin gaba sai ya faɗa miki abin da kike son sani, ni
ba na son ganinki a cikin damuwa kwanta ki huta gobe za ki sani."
Baya ta yi ta kwanta su Ayan na manne a ƙirjinta suna jin su.
Sai da suka ga ta soma jin bacci suka ɓace daga jikinta...
Aljana Janu ce zaune a maƙabarta ta tasa Suhaima a gaba fuskarsa har fitar da wani hasken
wuta take saboda ɓacin rai, a fusace ta miƙe tayo kan ta sai dai ta na zuwa gef da ita aka yi
sama da ita aka watso ta gefe. Cike da mamaki take kallon Suhaima taga ba kowa a tare da ita,
idanunta ne ya sauka a kan zoben dake yatsar Subaima sai haske take, manya-manyan
idanunta baƙaƙe ta zaro ta ce.
"Ke! Wa ya ba ki wannan zoben?"
Ita kuwa tuni ta firgice sakamakon arba da idanun aljana Janu da ta yi, zata sake yi mata
magana wata ƙatuwar macijiya ta ɗauketa ta yi sama da ita...
Futsarin da ya matse ta ne ya farkar da ita, da sauri ta kalli zoben dake tsayarta ta na mamaki
yadda zoben ya ba ta kariya; miƙe wa ta yi ta shige toilet jin ana kiran salla...
Takwas duk Inna Laure ta kira su Abba ɗakin Suhaima shi da Umma suka shigo tare da Na'im
da Suhaila. Kallon Abba ta yi ta ce.
"Mukhtar ka saurareni da kyau."
Sunkuyar da kai Abba ya yi ya ce. "To Yaya Laure ina jin ki."
"Ina so ku faɗa wa yarinyar nan abin da kuka ɓoye mata wanda ni kaina ban san da wannan
sirrin ba.."
Dam! Ƙirji Umma da Abba da Suhaila ya buga,, ya kalli Inna Laure ya ga ba wasa nan ya ƙara
tabbatarwa kansa yau dai abin da ya ɗauki shekaru yana ɓoye wa sai ya faɗa, sirrin da ya
ɗauki shekaru yana ɓoye wa saboda farin cikin Suhaima amma yau gashi ta haɗa shi da wadda
ba zai iya mata wayo ta bar maganar ba. Gyara zama ya yi ya ce.
"Ki gafarceni Yaya Laure da ban sanar da ke wannan maganar ba."
"Ina jinka maza ka faɗa mini.
"Yaya Laure Suhaima ba mu bane asalin iyayenta, m.. bai ƙarasa ba Suhaima ta ƙwalla ƙara
sai gata a gaban Abba ta damƙi ƙafarsa cikin tsananin tashin hankali ta ce..
_*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_
[3/7 14:32] Ummu Amjad: _*í ¾í·Ÿ♀️í ¾í·Ÿ♀️A MAƘABARTA NE í ¾í·Ÿ♀️í ¾í·Ÿ♀️*_
Daga Alƙalamin
_Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_
_í ½í´”í ½í³šJARUMAI WRITER'S ASSOCIATION í ½í³š_
SADAUKARWA GA MUTANE BIYU:
*AYUBA MUHAMMAD ƊANZAKI (Zakin Marubuta)*
*JIBRIL ADAMU RANO (Malam)*
مسب الله نمحرلا ميحرلا
0️⃣7️⃣
Cikin tsananin tashin hankali ta ce.
"Ab..Abb.. Abba don Allah ka ce dani mafarki nake kamar yadda nake yi kodayaushe."
Tamkar wata zautacciya ta juyo ga Inna Laure data saki baki ta na kallon Abba da ya sadda kai
ƙasa, faɗa wa jikinta ta yi sai yanzu taji wani irin kuka ya zo mata ta soma yi wa Inna Laure
magana.
"Innata kin gani dan na ce sai na san abin da suka hana na sani, shi ne Abba ya faɗi wannan
mummunar kalmar wadda ko a mafarki naji ta ba zan sake komawa bacci ba. Innata don Allah
ki ce masa na haƙura da jin maganar ba zan sake tambayar su ba har numfashi ya ƙare , Inna
ki yi magana mana." Ta ƙarashe maganar da ƙyar ta jan numfashi. Kafin Inna Laure ta ɗaga hannu tuni ta saki jiki a
jikinta alamar suma ta yi; hankali a tashe Inna Laure ta soma jijjiga Suhaima amma shuru kake
ji babu alamar motsi, ɗago da idanunta ta yi wanda ya yi jajur saboda tashin hankali ta dubi su
Umma da ko ƙwaƙƙwaran motsi sun kasa yi, baki na rawa ta ce.
"Na..Na'imu kawo ruwa don Allah kar su kashe mini 'yata."
Jiki ba ƙwari ya miƙe ya nufi freezer ɗin ɗakin ya buɗe ya fito da ruwan ya kawo mata har ya
fara ƙanƙara; shi kansa ya shiga ruɗu, tashin hankalin da yake ciki ji yake kamar shi ne aka ce
ba ɗan Abba ba ne, tunanuka sun masa dirar mikiya masu cike da tambayoyi kala-kala. Indai
har ba Abba ba ne mahaifin Suhaimar sa to waye ya haife ta? Sannan me ya sa suka yada ta?
Anya kuwa Abba gaskiya yake faɗa musu?"
Na'im ya faɗa a cikin ransa bai san maganar ta fito fili ba sai jin muryar Inna Laure ya yi ta na
amshe zancen nasa.
"To ka dai tambayar mana shi Na'imu wannan ai masifa ce mai rawani, kai yanzu Mukhtar so
kake ƴar taka ta mutu ko? To Wallahi sai na yi ƙaran ka Hisba sai sun bi mata haƙƙinta na
sumar da ita da ka yi, wannan ai makasar ta kake nema. Ka faɗi abin da yarinya take son sani
wanda ya danganci mafarkinta ba wai ka tsoratar da yarinya ba da wannan ɓakar kalmar, bani
da mutumci Mukhtar ka sani Wallahi zan ci kwalarka na zazzabga maka mari, shin za ka yi
magana ne ko sai na yi maka dakan tsakwara ne?"
Ta faɗa tana fashewa da kuka, ita kanta hankalinta a mugun tashe yake da maganar ta Abba,
taya ma zai ce wai basu bane asalin iyayen ƴarta Suhaima wadda duk yaransa tafi son ta fiye
da su Na'im..
A sanyaye Abba ya ɗago ya kalli Inna Laure da take kuka wiwi ta na shafa fuskar Suhaima
wadda sai a lokacin ne numfashi ya dawo, amma sam ta kasa buɗe idanu.
"Yaya Laure babu abin da muke ɓoye wa Suhaima illa wannan sirrin, tabbas Suhaima ba mu
muka haife ta ba hasalima ba a ƙasar nan muka tsinci Suhaima ba."
Zabura Suhaima ta yi jin kalmar Abba take tamkar ana zuba mata ruwan wuta a ko wata kafa ta
jikinta, kallon Abba ta yi zuciyarta na mugun bugawa ta ce.
"Abba!" Ta faɗa da wata iriyar murya wadda duk wanda yaji yasan mai maganar ya kai ƙarshe a
tashin hankali; Suhaila ta dubi Umma ta ce.
"Umma wai da gaske ne maganar da Abba yake magana a kaina? Don Allah ku fitar damu cikin
duhu kar zuciyata a buga, taya za ku ce wai ba ku bane iyayen Suhaima dani aka je asibiti
lokacin da za a haife ta kuma aka fito da ita ni na fara rungume Suhaima a lokacin, amma
yanzu ku fito da wannan maganar wani lefi ta aika a gareku kuke son hawan jini ya kama ta
lokaci guda?"
Umma ta goge hawaye ta dubi Inna Laure ganin Abba ba zai iya magana ba ta ce.
"Suhaima ki tashi ki ji sirrin da muke ɓoye miki wanda bama son ko a mafarki kiji, an ce ranar
wanka ba'a ɓoyan cibi dan haka yau ni zan sanar dake komai."
Saurin tashi Suhaima ta yi jiki na rawa ta tabbata dai ba su suka haife ta ba kenan?
"Waiyo Allah rayuwata to su waye iyayena Umma?"
Ta faɗa jikinta na rawa har sai da Inna Laure ta riƙe ta ganin ta na neman faɗuwa.
Gyara zama Umma ta yi ta soma magana hawaye na sauko wa daga cikin idanunta. .
Shekaru ashirin da bakwai da suka wuce, ni da mijina mun yi auren soyayya; asalin mu 'yan
garin Kaduna ne iyayenmu suna Hayin rigasa. Mijina su uku ne a wajan iyayensu Inna Laure sai
Abbanku sai Abdallah. Suna da haɗin kai sosai ita Inna Laure kasancewar dangin babanta suka
riƙe ta ba a Kaduna ta zauna ba a can Katsina take a wani ƙauye, a nan aka mata aure shi ya
sa ba sosai take zuwa Kaduna ba dan ba ta saba da iyayenta ba; ba ta taɓa haihuwa ba amma
ba ta damu ba ko kaɗan ni kuma ina jin tausayinta sosai a lokacin ina amarya. Wata na goma
da aure na samu ciki ranar an sha murna a dangin mijina da ma nawa dangin, cikina na isa
haihuwa na haifi mace kyakyawa mai kama da mahaifinta. Ranar suna yarinya ta ci sunan
surukata wato Saudat muke kiranta da Suhaila; haka muka ci gaba da kulawa da ita a lokacin
Abbanku ya gama karatu yana koyar da yan jami'a dan aikin da yake so bai samu ba sai ya
amshi koyarwa. Ya karanci ɓangaren computer ne, to da bai samu aikin ba sai ya nemi na
koyarwar; sai da Suhaila ta yi shekara da haihuwa sannan ya samu aiki a nan Kano.
Tun da muka zo Kano ban san kowa ba ni kaɗai nake zama sai sannu a hankali na sama da
maƙotana; ana haka Abbanku aka tura shi ƙaro karatu a ƙasar Ghana. Ranar na yi murna ganin
yadda hanyar samu take zuwan mana a lokacin kuma na yaye Suhaila Inna Laure ta zo ta
ɗauke ta suka tafi ƙauye sai bayan wata ta dawo da ita. Muna ta shirin tafiya Ghana Abdallah ya
kira Abbanku ya ce matarsa ta haifi ɗa namji, ai kuwa mun sha murna sosai kasancewar saura
kwana goma mu tafi sai muka shirya ana saura kwana biyu suna muka tafi wajan suna.
Washegarin suna na tafi gidanmu na musu sallama, sun so na bar musu Suhaila amma na ce
babanta ba zai bari ba suka haƙura muka dawo; da Yamma lis muka shirya 'yan'uwa suka mana
fatan alkhairi sannan muka dawo cikin kewar dangi.
Lokaci na cika muka shirya tsaf zuwa muka wuce Ghana cikin farinciki musamman ma ni nafi
Abbanku murnar zuwa gari; muna sauka aka zo aka ɗauke mu aka kaimu wani gida, wanda ya
kaimu yake sanar da mu anan za mu zauna muka masa godiya ya tafi..
Washegari Abbanku ya fita zuwa wajan aiki, ranar sai dare ya dawo da har na tashi hankalina
ganin ƙarfe takwas ta yi bai zo ba hankali a tashe nake tambayar sa.
"Abban Suhaila lafiya dai tun safe sai yanzu ka dawo?"
Sai ya ce dani.
"Aiyuka ne suka min yawa sosai shi ya sa, yanzun ma ba dan na gama na dawo sai gobe."
Jin abin da faɗa sai