Showing 27001 words to 28768 words out of 28768 words

Chapter 10 - ASP Zahra Book 2 Complete By Jasmine

yana tambayarta meya faru sai dai bata bashi amsa ba.
Zama ya yi yana rarrashinta tare da bata haƙuri dan a zatonshi shine ya mata laifin. Sun dade a haka kafin ta sassauta kukan tana sauke ajiyar zuciya, toilet ya shiga ya hada mata
ruwan dumi sannan yace taje tayi wanka, mikewar da zatayi jiri ya É—ebeta luuu! Ta kuma zata
fadi ya tare ta. A hankali ya É—auke ta ya shigar da ita bayin, da kanshi ya mata wankan ganin
lokaci guda zazzaɓi me zafi ya rufeta sai rawar ɗari take yi. Riga kawai ya zura mata bayan ya
fito da ita sannan yaje ya hado mata tea me kauri ya haÉ—o da Paracetamol, dakyar tasha Tea
din kaÉ—an ya bata maganin sannan ta kuma ta kwanta.
Ganin har rana jikin nata yaki sauki ne yasa ya kira Abdallah ya mata allura sannan ya É—aura
mata drip, falo suka koma suna tattauna matsalar M.J din Abdallah na ƙara bashi shawarwari
akan wannan ce kaÉ—ai damar da zaiyi amfani da ita wajen sasanta tsakaninsu da Zarah, sun
dade kafin ya maj sallama ya tafi.
A takaice dai sai da Zarah tayi sati tana jinya har su Momi sai da suka zo dubata, ranar da
Sadiq yazo gaisheta da jiki saida yayi mamakin abinda yaga M.J na yi mata, M.J É—an kwalisa da
shan ƙamshi amma shine ya ƙasƙantar da kanshi akan mace, dan a kitchen ma ya taddashi
yana soya wainar fulawa wai Zarah take son ci, tun abin na bashi mamaki har ya koma tausayin

M.J din ganin gabadaya bashi da wani lokaci da zai yi abin kansa sai wanda tace dashi, hakan
yasa ya musu sallama ya tafi a yanzu hankalinshi ya kwanta da auren nasu.

Shikuwa M.J duk wannan abin da yake yi sam baya damunshi musamman da a yanzu ya samu
sake har kwana yake yi a É—akin Zarah kuma bata hanashi wani lokacin ma har hira suke yi
sosai musamman idan suna kallon labarai aka taɓo harkar tsaro nan zasu zauna suna
tattaunawa akan halin da ƙasar mu ke ciki ta fannin tsaro.

Da haka zaman nasu ya fara daÉ—i ko bayan da ta warke, kullum tare suke bacci watarana a
É—akin M.J din ko a É—akinta, tare suke tashi su kimtsa gidan kowacce safiya dan Zarah ta tubure
batason me aiki duk da M.J yaso ya É—auki me taimakamata dole ya hakura tunda ta nuna
bataso. Tare suke fita ya sauke ta a wajen aiki kafin ya wuce nashi wajen aikin idan an tashi ma
haka zai zo ya É—auketa su wuce gida wani lokacin kuma gidan Momi suke wucewa.
Da haka dai har M.J ya hillaceta haƙarsa ta cimma ruwa, aikuwa ranar ya sha kuka da nadamar
abubuwan da ya aikata mata har sai da ciwon shi ya tashi, hakuri kuwa har sai da ta nuna
zatayi fushi sannan ya daina bata.

Zaman da ya biyu baya babu laifi zamane na aminci da kyautatawa juna duk da har a lokacin
Zarah ba sonshi take yi ba kuma bata manta da Safwan cikin ranta ba dan kullum idan tayi
sallah sai ta mai addu'a shi da iyayenta da sauran musulmai magabata.

Babu irin gatan da M.J baya mata wani lokaci har tausayi yake bata idan taga irin kulawar da
yake bata, komai nashi ita ne duk abinda ya samu ita.

A cikin watannin da suka biyi baya ne watarana M.J ya tashi da wani irin zazzabi me zafin
gaske, sosai hankalin Zarah ya tashi dan har sumewa yake yi da ya farfaÉ—o kuwa zai kuma ba
shiri ta kira gida ta sanar sannan ta kira Abdallah suka É—auke shi sai asibiti.
Kwananshi biyu amma duk allurai da magungunan da ake bashi kamar ba'ayi har anfara
tunanin ko ciwon bana asibiti bane.

Ranar da Baaba tazo asibitin ne ta gane ainihin musabbabin ciwon, suna zaune harda su Momi
da Jiddah dan lokacin dare ne anyi sallar isha'i ma, kallon Zarah tayi sannan ta kalli M.J ta
tuntseri da dariya sosai har tana saukowa daga kan kujerar da take, kallonta suke yi cike da
mamaki, Sadiq ne ya rike baki ya ce
"Momi bari na kira likita inajin matar nan ba kalau take ba."

Jin abinda ya faÉ—a ne yasata tsagaitawa ta kalleshi ta ce

"Zan saba maka fa Habu ni kake dangantawa da taɓin hankali."

"Alama kika nuna ai" ya fada yana kauda kai.

Tsaki tayi sannan ta maida kallonta ga M.J dake kwance cikin ciwo tace

"Wato dai kai Muhammadu da gaske kake so ka zama mijin tace koh? Ita ke da cikin amma
kaine kake mata laulayin."

"Laulayi kuma Baaba.?" Momi ta tambaya.

"Yoo ai sai kuyi kuma sau nawa akayk muka gani Zara'u ce fa ke da ciki shi kuma yake mata
laulayin cikin dama ana samun haka wasu lokutan idan mata ta samh shigar ciki ta hanyar
mijinta kaÉ—ai ake ganewa dan wasu ciwo suke kamar ba zasu rayu ba."

Wani irin farin ciki ne ya sauka a zuƙatansu babu shiri Momi taja hannun Zarah suka fice kai
tsaye sashin da ake bincikar masu ciki ta kaita dan ayi mata awo saboda itakam ta yarda da
batun Baaba dan a zamanin baya ma kafin wani daga cikinsu ita da marigayiya yasan yana da
shigar ciki Baaba ce take fara ganewa ta fada musu kuma idan anje asibiti a tabbatar. Kasancewar an sansu a asibitin ne yasa babu ɓata lokaci aka shigar da Zarah ɗakin scanning
din aka kwantae da ita sannan aka jona mata na'urorin, mintun biyu tsakani kuwa sai ga hoton
cikinta ya bayyanah da É—a kwance, farin ciki ne ya rufe Momi ba shiri ta fadi acan gefe tayi
sujjadar godiya ga Allah.
Wani zuben zinari me matuƙar tsada dake hannunta ta cire ta baiwa matashiyar likitar tukwici.

Basu dawo ɗakin ba sai da aka gama buɗewa Zarah file na masu ciki sannan ta riƙo hannunta
suka dawo nan take shaida musu fa akwai cikin a jikin Zarah har na wata hudu ma, hamdala
suka fara yi tare da gode ma Allah hatta M.J dake kwance sai da ya mike ya zauna sannan ya
riko hannun Zarah dake gefenshi yana zuba mata godiya. A daren yace bazai kuma kwana a asibitin ba tunda angano silar ciwonshi dole haka likita ya
sallameshi suka koma gida inda aka bar Baaba dan kulawa da Zarah.
Sanda Rahama taji labari kuwa tayi murna sosai duk da itama a lokacin tana da ciki har ya
shiga watan haihuwa.

Tunda cikin Zarah ya bayyana kuma sai ciwon da M.J yake yi ya ragu nan ya cigaba da baiwa
matarshi kulawa baya ko kunyar Baaba dake gidan hakan yasa ta tattara kayanta tabar gidan
dan tace ba zata iya zama ayi abin kunya a gabanta ba.

Sati biyu da faruwa haka Rahama ta haifi Æ´arta mace. Gabadaya suka tattara suka nufi Yola da
sha tara na arziki.
Anyi shagalin suna sosai irin na gidan sarauta,yarinya taci sunan mahaifiyar su Mahmud
Zulaihat ana kiranta da Afrah, satinsu guda suka juyo suka bar me jigo cikin kulawar dangin
mijinta dan su gidan sarauta basu yarda da al'adar wankan gida ba.

Watan Afrah huÉ—u da kwanaki Zarah ta sauka lafiya ta haihu Æ´an biyunta macw da namiji

kyawawa masu kama da ubansu. Farin ciki kuwa ba'a magana a gurin dangi. Nan aka fara cika
gidan Æ´an uwa da abokan arziki kowa na zuwa ganin Æ´an biyu.

Ranar suna kuwa ansha mamaki kwarai sunan da M.J ya sakawa yaran, macen Fadimatul
Zarah namijin kuma Safwan inda za'a kirasu da Amrah da Amran. Mutane da dama sun jinjina
wannan abu da ya yi, ita kuwa Zarah tayi farin ciki matuƙa har ta kasa ɓoye hakan.

Mai Martaba da kanshi sai da yazo ya yi godiyar wannan kara, inda yawa yara kyautan manyan
filaye guda biyu bayan kuma kaya da aka kawo musu.
Yara sunzo da goshi dan sun samu kyaututtuka da dama na ban mamaki.

Kulawa sosai suke samu daga wajan iyayensu da sauran dangi. Musamman mahaifinsu ma
daya É—aura son duniya akansu.

Haihuwar Zarah ba da dadewa ba aka yi auren Sadiq wanda ya tara manyan mutane sosai
sannan an kashe kuÉ—i sosai.

A haka rayuwa ke tafiya awanni na shudewa su bada kwana daga nan satika har watanni.


Watarana su Zarah sun fita shopping, a hanyar dawowarsu ne suka kusa kaÉ—e wata almajira, ko
da suka fita suka duba ba kowa ba ce face Hajara, ƙafarta ɗaya an guntule sai sanda take
amfani dashi. Ko da ta ganesu nan ta durƙusa tana basu hakuri sosai tana basu labarin
abubuwan da suka faru da ita dan har prison sai da aka kaita sanadin wannan Alhajin daya
mata ciki, gashi iyayenta ma duk basu da lafiya suna kwance Æ´ar uwarta ce kawai ke taimaka
musu itama mijinta ya ɗauke ta sun bar ƙasar.
Sun tausaya mata sosai nan M.J ya mata kyautar maƙudan kuɗaɗe bayan sun yafe mata.

Shekararsu Amran É—aya da watanni mahaifinsu ya kwanta ciwo zazzabi me zafi ya rufe shi, ba
shiri ya É—auki Zarah suka tafi asibiti aikuwa kamar yadda yayi tsammani tana da shigar ciki na
wata biyu murna ce ta kamashi ita kuma Zarah ta nuna sam bataji dadi ba saboda yaranta
basuyi girman da za'a yayesu duk da dai babu inda basa zuwa da ƙafarsu sannan kuma suna
cin abinci sosai.
Shawarwari likita ya basu na yadda zata kula dasu kafin cikin nata ya girma. Da haka suka
dawo gidaa.

Sanda Ammi taji labarin cikin Zarah ta kanta ta shiryo ta taho Nigeria ta É—auki su Amran ta wuce
Egypt da su dama kuma yaran sun santa gashi basa da kiwa ko kadan dan haka ne bata sha
wuya da su.

Tabar M.J yana cigaba da rainon cikin matarshi da a yanzu ma yake fatan ta haifo mishi Æ´an
biyun.

*KARSHE*


*ALHAMDILILLAHI NAN NA KAWO KARSHEN WANNAN LITTAFI NA ASP ZARAH, ABINDA
NA FADA DAIDAI ALLAH YA BANI LADARSA INDA NA KUSKURE KUMA INA ROƘON ALLAH
YA YAFEMIN.*
*MASOYA INA GODIYA SOSAI DA IRIN ƘAUNARKU A GARENI, ALLAH YA SAKA DA
ALKHAIRANSA YABAR ZUMUNCIN DAKE TSAKANINMU. INA GODIYA SOSAI DA HAKURIN
DA KUKAYI DANI TSAWON WANNAN LOKACIN. SON SO FISSABILILLAH*


*KU TSUMAYE NI A LITTAFINA NA GABA DA ZAI FARA ZUWA MUKU NAN DA WANI
ƘANƘANIN LOKACI ME SUNA AL-MUSTAPHA. FREE BOOK NE NAYI SHI DOMIN KU
MASOYA, YAZO DA SALO NA MUSAMMAN KADA KU BARI A LABARTA MUKU*.



*TAKU HAR KULLUM*
*JASMINE🌸🌸*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login