Showing 9001 words to 12000 words out of 28768 words
ba zata
iya bude baki tayi magana ba, tabbas ta daɗe bataji ko a labari ba wacce ke da irin ƙaddarar
Zarah, domin da ta fita daga wannan take kuma shiga wata batare da ta warke ƙuncin da ke
ranta ba.
Numfasawa Zarah tayi sannan ta cigaba da cewa.
Ba kowa bace face Almajirata wacce na daɗe da fara manta abinda ya gudana a tsakaninmu,
ina tsaka da wannan baccin nayi mafarkinta ta zo min tana hawaye tace
"Kamar yadda na ɗaukar miki alƙawarin cewa zan barki a baya amma zan kuma dawowa domin
taimakonki, Batula ban taɓa nesa daga inda kike ba saidai kawai ina ɓoye kaina ne saboda
alƙawarin da na miki na rashin bayyana a gareki. Sai dai a yau na bayyana gareki ne domin
taimaka miki akan abinda kw jefa rayuwarki cikin ƙunci. Ki riƙe wanna littafin duk wasu bayanai
da zaki buƙata na Alpha yana ciki baki da buƙatar zuwa wani waje domin samo su." Ta ƙarashe
maganar tana mikomin wanj ƙaramin littafi dake hannunta, cike da rauni na miƙa hannu na
karɓa ina kallon jikin littafin, ɗagowa nayi da nufin tambayarta saidai kuma banganta ba. A
daidai nan na farka daga baccin a firgice ina faɗin "Kin bani littafin.?" a gaggauce Jiddah ta
matso kusa da ni ta riƙeni tana ƙoƙarin maida ni na kwanta.
Bansan abubuwan da nake furtawa ba a lokacin sai dai naji Jiddah na faɗin
"Littafin yana cikin motar Saleem bari na kira shi ya shigo miki dashi." daga haka na maida
kaina ina sauke numfashi a hankali. Shuɗewar mintuna goma ne ya dawo dani hayyacina, a
lokacin ne kuma na fara jin raɗaɗin raunukan dake jikina, haka nayi ta daurewa har zuwa
lokacin da wata Nurse ta shigo, ganin idona biyu ne yasa ta kuma suka dawo da likita ya ƙara
duddubani tare da tambayata inda kemin ciwo, nan na faɗa mishi ina jin zafin raunukan jikina
cikin sanyayyar muryata ta marasa lafiya, take ya haɗa allurai yayi min sannan suka fice a ɗakin
suna mai ƙara yimin addu'ar samun sauƙi.
Fitarsu ke da wuya Baaba da Jiddah suka ƙaraso kusa da gadon nawa suna jeramin sannu
kamar zasu aro baki, da taimakon Jiddah na samo na miƙe zaune bayan ta saka filo a bayana
na jingina da gadon, zafin da nakeji ya ragu sosai sakamakon allurar rage zugi da akamin,
wannan ne ya bani damar yi musu ƴan tambayoyi game da mutanen da nake da tabbacin zasu
zo dubani, nan Jiddah ke gayamin Daddy da Momi suna hanya sunje gida su dawo ne, Saleem
kuma ya fita samo musu wani abu su ci kafin Momi ta kawo abinci sai Sadiq da ta nunamin
wanda kw zaune a can gefe. Sai a lokacin na juya a hankali na kalli inda take nunamin ai kuwa
na ganshj zaune yana aikomin da murmushin da iyakarsa fuska nima na maida masa martani, a
hankali ya miƙe ya tako zuwa inda nake ya dafa kafaɗa ta cike da kulawa yake tambayata ya jiki
na amsa mishi. Shiru ya biyo baya kafin ya nisa yace
"Little meya faru ne? ina mijinki yaje ne da bai samu damar kawo ki asibiti ba sai su Jiddah ne
suka kawo ki? Meyasa tun zuwanmu ba muga yazo domin duba lafiyarki ba ko baya ƙasar ne?"
"Habu ka kiyayeni fa, yarinyar na gadon jinya zaka tasa ta a gaba kana yi mata irin waɗan nan
tambayoyin da basu shafi lafiyarta ba." Baaba ta faɗa cikin hargowa.
Murmushi nayi mai ciwo sannan na kalleta nace
"Baaba ina jin ƙarfi sosai a jikina yanzu,karki ga laifinshi dan yamin waɗannan tambayoyin.
Yaya kasan meye a tambayarka akwai gyara, a yanzu zaifi dacewa ka dinga danganta Yaya
Jawwad a matsayin Yayana ba miji ba, domin a yanzu yadda nake nan babu igiyar aurensa a
kaina." Na faɗa ina zamewa da nufin na koma na kwanta.
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, Allah yasa kunnuwana ba daidai suka jimin ba." Abinda Momi
ta faɗa kenan wacce suka shigo a tare da Daddy suka tarar ina wannan zancen, gabaɗaya
muka juya gareta muna kallonta har ta ƙaraso inda nake ta zauna tana fuskantata tace
"Zarah dan Allah me naji kina faɗa yanzu? Kice min ba abinda naji kika faɗa ba dan Allah.?" ta
ƙarashe maganar tana riƙo hannuna ɗaya da babu ciwo, tausayinta naji ya kamani zuciyata tayi
nauyi, tabbas nasan banason auren nan nayi biyayya amma mutuwar aure sam babu daɗi
musamman ga mace mai irin aikina lokaci guda mutane zasu juya maganar zuwa wata daban,
ciwon ƴa mace na ƴa mace ne, nasan tabbas Momi tana jin wani irin yanayi a cikin ranta
kwatankwacin yadda nakeji, ban taɓa son M.J ba har gobe amma ban taɓa fatan ace aurenmu
dashi ya rabu ba. Cikin murya mai rauni na ce
"Ehh Momi hakane aurenmu da Yaya Jawwad ya rabu a daren jiya." wasu hawaye masu ɗumi
naji suna zubomin saboda hoton abinda ya faru a wannan daren daya bayyana cikin
kwakwalwata. Salati suka saka gabaɗaya illa Jiddah gwanar kuka da tuni ta fara zubda hawaye,
shikuwa Sadiq yana tsaye a gefena har wannan lokacin sai dai babu wanda zai iya tantance
yanayin da yake ciki.
Daddy ne yayi ƙarfin halin tambayata yace
"Daughter me ya faru ne kin saka mu a cikin ruɗani."
Cikin nauyinsu da nakeji na labarta musu abinda zan iya tunawa, ai kuwa tamkar waɗanda ke
jiran ƙiris nan suka soma fashewa da kuka hatta Daddy sai da yayi hawaye illa Sadiq da kallo
ɗaya zaka mishi ka firgice da yanayinsa na tsantsar ɓacin rai da yake ciki.
Nan suka fara jajanta abin kowa da abinda yake faɗi akai musamman Momi da saida Baaba ta
tsawatar mata saboda ɗiban albarka da take yiwa M.J ba ƙaƙƙautawa.
Tare muka wuni a asibitin har Daddy kowa da kalar kulawan da yake bani, cikin wuni ɗaya kuwa
tamkar wacce ta daɗe tana jinya naji na samu ƙarfin jiki sosai, duk waɗannan abubuwa dake
faruwa zuciyata a ƙage take dare ya ratsa na samu na karanta littafin da Saleem ya kawomin
wanda dashi nakeson amsa musu tambayoyin da suke ta yimin akan littafin musamman Jiddah. Sai wajen ƙarfe goma na dare su Momi da Saleem suka yi mana sallama aka barni da Baaba
da Jiddah domin kwana da ni, duk yadda akaso Jiddah ta je gida ta turje hakan yasa aka barta
mu kwana tare.
Kaɗan-kaɗan muke hira har bacci ya rinjayi Baaba ta kwanta ta barmu ni da Jiddah muna hirar,
ganin baccinta yayi nisa ne yasa na fito da littafin daga ƙarƙashin filon da nake kwance na yafito
Jiddah tazo gefena ta zauna muka buɗe littafin a hankali mu ka fara karantashi cikin zumuɗi.
*ASALIN LABARIN WANZOWAR ALPHA*...✍
_ Nima na shaida nasan kuna haƙuri da ni sosai musamman ƴan VIP da yanzu bana
iya muku update kullum. Dan Allah kuyi haƙuri abubuwa suna yimin yawa ne amma zan dinga
ƙoƙari in sha Allah. Kamar yadda nasan kuna yi inaso ku cigaba da sani a addu'o'inku
akan abinda na sa a gaba. Ina son ku irin totally
*BY*
*JASMINE*
*ASP ZARAH*✈️
*BOOK 2*
*Page 6*
_Mafarin Lamarin_.
Asalin sunansa Al'amin, ya kasance ɗa na biyar ga Malam Mudi da matarsa Inna Habi, sauran
ƴan'uwansa uku mata da namiji ɗa inda ya kasance auta, bayan haihuwar Al'amin ne Malam
Mudi ya ƙaro aure inda ya auri wata bazawara da ake kira da Phalmata, tun daga lokacin kuma
rainon Al'amin ya dawo hannunta.
Saboda kulawar da take bashi yasa Inna Habi ta bayan ta yayeshi ta tattara kayansa ta
maidawa Phalmata riƙonshi gaba ɗaya.
Shekararsa takwas kacal a duniya Allah yayiwa Inna Habi rasuwa, a wannan lokacin duk
sauran yayyinsa sunyi aure illa ɗan'uwansa guda da shima yake shirin yi. Tun ƙuruciya
Phalmata ke koyawa Al'amin dabarun sace kuɗin mutane da zarar sunyi sake sai dai duk da
haka bata gaza wajen ganin cewa ya samo ingantaccen ilimi saboda wani buri da ke ranta,
baya ga haka itama tayi karatu kuma ta ɗanɗani daɗinsa.
Tun girmansa sai ya kasance ya kara haɗuwa da abokai masu irin tarbiyarsa, tun daga wannan
lokacin lamarin satarsu da fashi ya shahara, sai dai suna yin komai ne cikin basira basa taɓa
bari su bar shaidar da za'a gane su.
Bayan kammala karatunsa na Jami'a ne Allah yayiwa mahaifinsa rasuwa, a wannan lokacin ne
Phalmata ta baiyana masa shirinta na zamewarsu shahararrun ƴan ta'adda da zasu addabi
ƙasa da duniya baki ɗaya. Suna kashe duk wanda suka nemi dukiyarsa ya hana, sannan
muddin suka kwallafa rai akan abu sai sun samu. Haɗewar sunan Phalmata da Al'amin ne ya
samar da sunan ALPHA wanda mutane da dama suke tunanin sunan na mutum ɗaya ne.
Shararsu ne tasa gwamnati ta shiga neman hanyar da zata kamasu gadan-gadan, sai dai sun
siye baki mutane da dama daga sama wannan dalilin ne yasa duk sanda zasu tura yaransu yin
fashi suke hada baki da manyan jami'ai domin a dakatar da tsaro a inda zasuje ɗin.
Sun yi nesa da inda mutane suke sannan sun alkinta kansu ta yadda babu wanda zaiyi tunanin
saninsu ko yasan wani abu dangane da su.
A yanzu haka suna rayuwa ne a garin Enugu a cikin wani ƙauye da ake kira Keruba, wani abun
mamaki shine duk da a cikin mutane suke amma hakan baisa mutane sun shaida su, dalili kuwa
shine, wani madaidaicin gida kamar ko wanne gida da kuka saba ganin mutane na rayuwa a
ciki, amma a ƙasan wannan gida rantsatstsiyar fada ce tamkar ta sarakai wacce aka yiwa laƙabi
da _ALPHA VILLA_.
Babu wanda yasan a inda ƙofar dake sada mutane da Alpha Villa take a cikin wannan ƙaramin
gida, a duk lokacin da mutum zai shiga ko fita sai an shaƙa masa hodar dake saka bacci na
wasu mintuna.
Ta hanya ɗaya ne kacal zaku iya nasarar kama Alpha a sauƙaƙe.
A kowacce ranar Lahadi yana ɓadda kama ya fito daga wannan gidan don ya zaga gari, yakan
kwashe awa guda da rabi yana zagawa kafin daga baya ya koma mazauninsa. Babban lagon
Alpha guɗa ɗaya ne, wato mace mai ciki. Yana matuƙar tausayin mace mai ciki ko da wucewa
tayi ta gabansa sai yaji hawaye na neman fitowa daga idonsa. Saboda haka idan kunason
kama Alpha dole ku nemi wata mace da ke da ciki don samun lagonsa.
Mun daɗe mu na karatun wannan littafin har dare ya ratsa sannan mu ka gama, ajiyar zuciya
mu ka sauke a tare ni da Jidda bayan na rufe littafin na maida shi inda yake, kallon juna mu ka
yi cike da rauni kafin Jiddah ta ce
"Na samo mana mafita."
"Mafita? Wace iri?" na tambaya.
"Mai ciki ake nema kuma gani sai ki zame min ƴar jagora."
"Ke baki da hankali ne Jidda kinsan me kike faɗa kuwa."
"Wallahi idan kika kuma mu sa min akan abinda na faɗa ban yafe hakkin ƙaunar da nake miki."
Jiddah ta fada tana mikewa ta koma kusa da inda Baaba ke kwance itama ta kwanta, ta barni
sororo ina jimami.
Na jima a zaune kafin daga baya na tura littafin ƙasan filo,sannan na sulale na kwanta zuciyata
cike da tunanin mafita.
Washe gari tunda farar safiya
Sadiq ya iso asibitin, kallo ɗaya za'a masa mutun ya gane cewa bai runtsa ba, Baaba ya fara
gaidawa sannan nida Jidda muka gaishe shi ya amsa yana tambaya ta ya jiki. Zama yayi a
gefena yace lafiyarki"
Cikin mamaki muke kallonsa ni da Jiddah kowa da abinda yake saƙawa a ranshi.
"Amma Yaya me yasa ba zaka barni anan ba."
"Ina so ki yi nesa da M.J banaso ya kuma ganinki bare wani abu ya shiga tsakaninku ko da
kuwa kalmace ta fatar baki."
Baaba da ke zaune can gefe ne ta ce
"Haka ba shine mafita ba Sadiq a barta anan ɗin kawai, ai an riga da anyi kuskure ba za'a kuma
bari kalan haka ta faru ba."
Ganin Baaba na son jan maganar ne yasa ya ja bakinsa ya yi shiru bai kuma magana ba. Mu
na zaune a haka su Daddy suka shigo shi da Momj da Saleem, hannun Sa-Jid ɗin ɗauke da
kwandon abinci, gaishe-gaishe aka yi suna ƙara tambayata ƙarfin jikin. Momi ce ke faɗamin
cewa Ammi ta kira waya tana gaishe ni, sannan ta ce zasu taho a satinnan, cikin jindaɗi na
amsa ina ƙara jaddada ƙaunata a zuƙatan waɗannan mutanen. Jidda ce ta zuba mana abincin,
dafa dukan cous-cous da farfesun kayan ciki, sosai naji daɗi abincin kuma na ci sosai irin
wanda na jima ban ci ba saboda a lokuta da dama ba na samun damar yin girki saboda aiki,
dama kuma M.J ba abincina ya ke ci ba bare nayi tunanin dafa mishi.
Ƙamshin turarensa ne ya fara sanar da ni zuwansa, mu na zaune su ka turo ƙofar ɗakin shi da
Hajara cikin kyakkyawar shiga irin na masu morar amarci, da alama hankalinsu kwance yake
kamar tsumma a randa.
Da sallama a bakin Hajara, Baaba ce kaɗai ta iya amsa sallamar hatta Daddy kai ya kauda
gefe. Ganin haka ne yasa suka gaida Baaba kaɗai sannan suka nemi guri su ka zauna. Jim
ɗakin ya yi babu wanda ya tanka, Daddy ne ya ciro wata farar takarda daga aljihunsa sannan ya
baiwa Sadiq ya miƙawa M.J da kansa ke a sunkuye, cikin son ƙarin bayani ya kalli Daddy sai
dai ya kauda kansa gefe, hakan yasa shi buɗe takardar don ganin abinda ta ƙunsa. Cikin
razana ya ɗago ya ce
"Kotu! Daddy me na yi?"
"An haɗa baki da kai wajen cutar min da ƴata."
Da matuƙar mamaki mu ka ɗago a tare muna kallon Daddy, Baaba ce tayi ƙarfin halin cewa
"Sulaimanu wanj zance nake ji haka, wa za'a kai kotu."
"Ba wani abin tashin hankali bane fa Baaba, komai zai zo da sauƙi." Daddy ya faɗa.
"A wani garin marasa hankalin aka taɓa aikata haka Sulaimanu? Kana nufin kenan
Muhammadun ya fi ƙarfin ka eyeee. Kai ba za ka iya masa hukunci ba kenan har sai ka
dangana da wasu a waje, kai ne uban ko shine? Ban yarda ba, ban amince ba, matuƙar na isa
da kai toh ban yarje maka ka kai ƙarar Muhammadu kotu ba." Baaba ce ta yi wannan zance. "Baaba laifin da Jawwad yayi mai girma ne, ko da Gwamnati ne ta ji labarin abinda ya aikata ba
zata barsa ba, ki bari kawai a hukunta shi." Cewar Momi
"A'a ban yarda ba a nemi wata hanyar hukunta shi amma ba ta hanyar kotu ba."
"Ko da yaushe wannan tsohuwar sai kin kaucar da mutane akan hanya." Sadiq ya faɗa.
"Ka kiyayeni fa Habu, ba na wasa da kai."
"Shikenan Baaba za'ayi yadda kike so, amma wannan karon Jawwad ya ɓata mana rai matuƙa
dan haka zan yanke masa hukunci mai tsauri." Inji Daddy.
"Yauwa ɗan albarka ai idan rai ya ɓaci hankalj baya gushewa."
Daddy ne ya maida kallonsa inda M.J da Hajara ya ce
"Ka tashi ka tafi banaso na ƙara ganin fuskarka."
"Dad-dy!" M.J ya faɗa cike da rauni.
"Ehh ka tafi Jawwad ba ma so ƙara ganin fuskarka a cikin mu." Momi ta faɗa cikin hawaye.
Gwiwarsa ya zube a ƙasa da nufin ba ta haƙuri sai dai ta riga shi da faɗin
"Ka bani kunya Jawwad, wallahi da nasan akwai ranar da zata zo da zaka yi sanadin shigata
baƙin ciki kamar yadda nake ji a yanzu, da tun kafin Allah ya bani cikin ka zan roƙe shi ya
hanani cikin ka, Allah ya jiƙan Rahama ko da ɗaure fuska nayi cikin wasa sai hankalinta ya
tashi, kai da nake tunanin zaka maye min gurbinta sai gashi kaine mai son kashe ni da baƙin
cikin ka, Allah ya w...."
"Kul! Kada ki yarda ki ƙarasa, kin san munin da tsananin da fushin iyaye ke jawo wa ƴaƴan su
kuwa? Banason ƙara jin kunyi mugun furuci akan yaron nan." Baaba ta katse Momi da ke
magana cikin tsananin fusata.
Gabaɗaya ya firgice da kalaman iyayensa, ya san fushin su akan sa babban musiba ne a
gareshi, hawaye ne suka fara sintiri a kuncinsa.
"Matuƙar na buɗe ido na same ka a ɗakin nan ban...✍✍
*BY*
*JASMINE*
*ASP ZARAH*✈️
*BOOK 2*
*Page 7*
..."Matuƙar na buɗe ido na same ka a ɗakin nan ban yafe maka ba." Momi ta yi wannan furucin
cikin zafin rai.
Da hanzari ya miƙe ya fice Hajara ma ta miƙe ta bi bayan shi ba ta re da ta ce komai ba. Nan
Baaba ta rufe Momi da Daddy da faɗa, ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba, su dai sai haƙuri
kawai suke bata, daƙyar suka samu ta daina faɗan.
A wannan ranar ma tare muka wuni da su cikin kulawa, wajen ƙarfe tara na dare ne muna
zaune sai sallamar Ammi muka ji, cikin mamaki nake kallonta Momi kuwa sai dariya ta ke min
tana faɗin dama taki sanar da ni ne saboda zumuɗi irin nawa. Cikin murna muka gaisa tana
tambayata yanayin jikina, ko da lokacin tafiya yayi sai Ammi ta ce nan zata kwana, daƙyar aka
samu Jiddah ta bi Saleem suka tafi gida. Tare muka kwana da Ammi tana bani kulawa kamar
zata maida ni ciki.
Kwana na goma a asibiti kuma naji sauƙi sosai sakamakon kulawar da likitoci suke bani a gefe
guda