Showing 12001 words to 15000 words out of 28768 words
kuma ga kulawar da su Momi ke ba ni. Tun waccan ranar kuwa ban ƙara saka M.J a
idanuna ba, saboda su Momi sun ɗau zafi sosai, Ammi ce ma wani lokacin nake jin su suna
magana a waya wanda yawanci roƙonta ya ke akan ta baiwa su Daddy hakuri akan fushin da
suke yi dashi. A yadda na fahimta, ko kaɗan abinda ya same ni bai damu M.J ba fushin da
iyayensa ke yi da shi ne kaɗai abinda yake damunsa. Kayana da ke gidansa kuwa tun
waahegarin da Ammi ta zo suka je da Jiddah aka kwashemin aka maida min gidan Daddy, part
guda aka waremin tamkar wata matar gida.
Gabaɗaya mun gama shirin tafiya Enugu sallamar likita kawai muke jira, dama na riga da na
jima da karɓar takardar shaidar kama Alpha dan damƙa shi a hannun hukuma a ko wani hali,
dan haka abinda kaɗai nake jira shine na ƙarasa warwarewa don mu tafi Keruba. Tafiyar ta
mutane bakwai ce Ni, Sa-Jid, Yaya Sadiq, sai wasu jami'aina na sirri guda uku da zamu yi
tafiyar tare.
A daren da na cika sati biyu ne a asibiti likita ya sallameni inda a washegarin ranar kuma zamu
wuce Enugu, tafiyar da bamu da tabbacin ko zamu yi nasara, haka dai muke ta shiri zuciyoyi
sam babu dadi.
Kasancewar tafiyar mota zamu yi yasa washegari da asuba bayan munyi sallar asuba muka yi
sallama da su Daddy muka ɗauki hanyar tafiya cikin motoci biyu.
Sallah kawai ke tsayar damu a hanya amma duk da haka ba mu isa cikin garin Enugu ba sai
wajen sha biyu na dare, hotel ɗin da muka kama ta internet muka nufa kai tsaye ba mu sha
wahalar ganewa ba saboda munyi amfani da google map, cikin lokaci ƙanƙani muka isa wajen.
Bayan karɓi makullan ɗakin ne muka wuce don kowa ya huce gajiyar da ke tattare da shi.
Kwananmu biyu muna huce gajiyar hanya kafin ranar asabar da yammaci muka shirya tafiya
garin Keruba kamar yadda aka kwatanta mana zuciyoyin mu cike da zullumi duk kuwa da
kasancewar a daren wannan ranar kwana muka yi sallah muna neman zaɓin Allah a cikin
lamarin. Sai Yamma lis kafin muka isa cikin garin wanda yake da kyawun tsari, duk da mun baro
arewacin Najeriya a bushe amma wannan yankin ko ina da damshi alamun dai basa dadewa ba
ta re da ruwan sama ba. Wani ƙaramin masauki muka kama don mu kwana a ciki kafin
washegari mu ƙaddamar da abinda ya kawo mu. Wannan dare kwana nayi a gaban maliccina
ina kai mai kukana ya taimaki ne akan abinda na sa gaba. Wallahi ban taɓa sanin cewa addu'a
na da wannan ƙarfin ba sai a washegarin wannan dare, ban taba tunanin abubuwa zasu zo
mana da sauƙi ba sai a lokacin na tabbatar cewa babu kamar hawayen wanda aka zalunta a
wajen Allah.
Washe gari kamar yadda aka faɗa mana cewa Alpha na fita zagayawa a gari cikin ɓadda kama
haka muma muka shirya ɓadda kama tamkar wani shirin film. Duk da cewa cikin Jiddah bai
wani girma ba amma a haka muka yi amfani da ita. Kasancewarsa mutum mai kaifin basira
yasa ba mu yi tunanin yin ƙaryar yin dressing da bandage ba gudun karya gane ƙarya muke yi.
Dole ta sa aka yi wa Jiddah rauni a jikinta, duk yadda ta so daurewa sai da ta kasa na gane
cewa tana matuƙar jin zafi a jikinta.
Kayan masu aikin Momi da muka karɓo muka saka sannan wata daga cikin jami'an nan ta shafa
mana wani abu a fuska da jiki wanda idan ba mutum ya sammu sosai ba bazai gane mu ba.
Tunda wuri muka yi wa hanyar da Alpha zai bi tsinkaye, cikin tsananin shiri da taka tsantsan.
A tsakiyar hanya muka zauna Jidda ta kishingiɗa ta yi matashi da cinyata, kasancewar a yanki
kudu kowa harkar gabanshi yake yi ya sa babu wanda ya kula da lamarin mu kowa ya zo wuce
wa yake yi batare da ya tambayi dalilin da yasa muke zaune a gurin cikin wani yanayin da babu
kyan gani ba. Mu na zaune a wajen har kusan mintuna talatin ni da Jiddah, yayin da su Saleem
ke can nesa a ƙasan wata bishiya suna zaune.
Tun daga nesa na hango tahowarsa, kallo ɗaya zaka masa ka fahimci cewa yana taƙama da
izza saboda yanayin yadda yake tafiya tamkar mai tausayin ƙasa, duk da shiri ne amma ni da
Jiddah mun gaji sosai kallo ɗaya zaka mana kasan mun galabaita. Magana nayi a hankali na
sanar da Jidda tahowarsa, ai kuwa tuni ta fara juyi kamar wacce ke naƙuda alhali cikin nata
wata 3 ne kacal, ƙamshin turarensa kaɗai ya isa sanar da cewa mai kuɗi ne na gaske, domin
indai hancina ya jiyo min ƙamshin nan daidai Abbana yana amfani da kalan turaren nan sanda
yake da rai, saboda akwai watarana da na dage sai ya bani kyautarsa shine Mami ke gayamin
kuɗin turare yakai dubu ɗari uku.
Cikin takun ƙasaita yazo ya wuce ta gefen mu ba ta re da ya kalli ko gefen da muke ba, take
naji hawayen rashin nasara sun sauko daga idanuna, har ya ɗan yi nisa naga ya tsaya sannan
ya juyo ya nufo inda muke, farin ciki ne ya kamani dakyar na saisaita kaina gudun matsala.
"Sannunku bayin Allah" Sautin muryarsa naji ta daki kunnena, zan iya rantsewa tun da nake a
duniya ban taɓa jin wata murya mai zaƙi irin tasa ba, mintsilin da Jiddah ta yi min a gefen cinya
ne ya dawo da ni da ga duniyar tunanin da na tafi. Cikin sanyi na amsa mai da
"Yauwa sannu" na kauda kaina gefe ina matsar kwalla.
"Me ya sa kuke zaune anan gurin da babu tsabta haka."
"Ƴar uwa ta ce ba lafiya cikinta yana ciwo, kuma akwai ƙaramin ciki a jikinta shiyasa na zauna
anan mu ɗan huta ta ce ba zata iya tafiya ba." Na faɗa cikin rauni.
"Subhanallah! Taimako ya kamata ke nema a kaita asibiti ai, ciwon cikin masu juna biyu ai ba
daɗi." Ya fada da alamun ruɗewa a tare dashi. Bance komai ba illa kwallar da na cigaba da
matsa kamar wacce ke cikin wani babban tashin hankali, wata tsadaddiyar waya ya ciro a
aljihunshi ya fara dannawa ya ce "Bari na kira ƴar uwata ta taimaka sai mu kaita asibiti."
Da "Toh" na amsa mishi. Magana yayi da wani yare da ban fahimta ba sannan ya cire wayar a
kunnensa ya tsugunna a gabanmu yana jera ma Jiddah sannu kamar wata matarsa. Ban san
cewa na da wani shiri a ƙasa ba domin bata faɗamin ba, ni a yadda muka tsara jami'ai ne zasu
zo su kamashi lokacin da ya tsugunna a wajen, sai dai ba zato ba tsammani batare da
dukkanmu biyun mun ankara ba Jiddah ta zaro wuƙa mai kaicin gaske da alama ma sabuwa ce,
cikin zafin nama ta kwace a jikina sannan ta caka mishi wuƙar nan a gefen ciki, wata ƙara ya
kwalla ya dafe gurin, kafin yayi yunƙurin guduwa tuni jami'an sirri da Gwamnatin Enugu ta bamu
suka zagayeshi wasu daga ciki kuma suka damƙi hannunsa suka maka mai ankwa, cikin
mintuna ƙalilan sai ga motar asibiti, nan aka sashi a motar tare da wasu jami'ai aka wuce da su.
Bansan a wani yanayi na tsinci kaina ba lokacin da na ga jami'ai sun kama Alpha har sun saka
mishi ankwa, wannan ranar na ɗaya daga cikin ranakun da bazan manta da su ba a tarihin
rayuwata, bansan me ya faru ba sai dai bude idona nayi na ganni a gadon asibiti, sai a lokacin
Yaya Sadiq ke fadamin wai sumewa na yi, a lokacin ne na fara tariyo abubuwan da suka faru
ina daɗa mamakin yadda kama Alpha ya zo min da sauƙi haka tamkar a mafarki, dole na gode
ma Allah da ya banj nasara akan makiyina sannan dole zan godewa Almajirata.Lol.
Murnar da na shiga a wannan ranar ko runtsawa na kasa yi, kwana nayi ina sallar godiya ga
Allah, wannan ranar kadai nake jira dama na ajiye aikin ƴan sanda, ranar da zan kama wanda
yayi sanadin mutuwar mutane masu gurbi na musamman a rayuwata, Abbana, Mami,
Kakannina, lukutar ƙanwata da kuma rigimammun ƴan biyun ƙannaina, a wannan ranar na ji ni
na kammala ba ni da wata sauran damuwa da ta ragemin. Har ƙaramar walimah muka hada a
resturant ɗin hotel ɗin da muka sauka, Sadiq ne ya ɗauki wannan nauyin.
Washegari kamar yadda ya zo a hukumance tunda Alpha ya amsa laifin da ake tuhumarsa
sannan yayi bayanin inda za'a samu Phalmata da yadda za'a kuɓutar da matan da ya ajiye a
Alpha Villa, bayan an damƙo Phalmata da sauran masu yi musu aiki ne aka wuce da su Abuja
inda anan za'a yanke musu hukunci, yaran nan kuwa kowa an haɗasu da jami'ai domin a sada
su da iyaye da ƴan uwansu, gabaɗaya mu ma Abuja muka nufa inda zamu haɗu da su Daddy
acan don zasu zo ganin yadda shari'ar zata kasance.
Sunayen manyan ƙasar nan da suke da sa hannu a miyagun laifukan da su Alpha ke yi ba zasu
kirgu ba, sunan Commissioner na daga farko-farko a cikin jerin mutanen, cikin kwanaki biyu aka
cafko kowannensu, masu muƙami kowa tuni Gwamnati ta karɓe abin ta, sai dai mu yi fatan
gyaruwar ƙasar mu.
Ranar da aka yi zaman kotu kuwa garin Abuja ta karɓi baƙuncin mutane da dama, sai da aka
cika kotun nan maƙil babu masaka tsinke domin wasu a waje ma suka tsaya don babu gurin
zama kowa nason ganin mutum ɗaya jal! da ya daɗe yana gallazawa mutane, bayan alkali ya
zo ne aka gabatar da tuhumar da ake musu inda lauyan Gwamnati ya gabatar da kansa, babu
batun lauyan da ke kare waɗanda ake tuhuma domin ba su da shi, cikin sauƙi ba ta re da
wahalar da shari'a ba aka zartar musu da hukunci, Al'amin da Phalmata hukuncin kisa ta hanyar
rataya inda sauran kuma hukuncinsu zaman gidan kaso na har abada. Daga haka Alƙali ya
sallami kowa sannan aka bada umarnin wucewa da masu laifi gidan yari, kotu fa ta hargitse
kowa da abinda ke fadi inda mutane da dama su ka so ɗaukar doka a hannunsu sai dai babu
hali.
Sosai na so ganawa da Alpha amma Sadiq ya hana ni gudun kada wani abun ya faru, haka ina
ji ina ganin muka bar garin Abuja zuciyata sam babu daɗi saboda yadda na so mu yi sallamar
ƙarshe da Alpha, sam a wannan lokacin sai nake jin tausayinshi na kamani matuƙa ta yadda
mace ɗaya ta lalata mishi rayuwarsa ta duniya, ko da yake shima yana da laifin biyewa son
zuciya don bai tsaya a inda Allah ya ajiye shi, yana da kyau na ɗaukar hankali wanda iya shi
kadai zai iya zama jarinsa don ga dukkan alamu mutum ne mai farin jini, dole daga baya na cire
tunaninshi a raina. Rayuwa kenan ban taɓa kawowa cewa al'amurana zasu warware cikin sauƙi
haka ba. Tsarki ya tabbata ga Allah ubangijin talikai wanda baya zalunci sannan baya barin
masu aikata zalunci.
Kwananmu biyu da dawowa Gwamnati ta shirya mana ƙayataccen Dinner wanda ya haɗa da
ƙarin girma, gabadaya jami'aina an musu ƙarin girma inda ni kuma Gwamnati ta tura ni ƙasar
Malasia domin yin course na musamman a harkar tsaro, na so naki karban wannan tayin amma
Daddy ya tursasa dole banj da wani zabi daya wuce hakan. Haka dai aka kammala taron Dinner
ɗin zuciyoyin mutane cike da murna.
Washe gari gaba ɗaya muna zaune a dinning mu na breakfast, M.J ne kawai bayanan a
wannan zaman, cikin nutsuwa kowa ke cin abincin da Momi da kanta ta sarrafa shi, wayar
Ammi da ke falo ce ke ta ƙara don haka ta kalleni ta ce
"Little miƙo min wayar nan kinji, na ga wanda ke kirana haka da safe ko karyawa ba za'a barni
nayi ba." Dariya muka yi duka kana na miƙe domin zuwa ɗauko mata wayar.
Da sauri na taho na bata wayar sakamakon wani kiran da ya shigo, mijinta da ga ƙasar Egypt
Dr. Adam ke wannan kira, cike da mamakin kiransa a wannan lokacin ta ɗaga, bai jira ta yi
magana ba ya riga ta, ai kuwa sai gani muka yi ta mike tana faɗin
"Alhamdulillahi Allah mun gode maka Ya Allah kai kadai ke yi a duk sanda ka so ya Allah muna
ƙara gode maka da ni'imomin ka gare mu." ba su dade ba ta sauke wayar a kunnenta fuskar ta
kaɗai ta isa fallasa farin cikin da ta ke ciki, zuba mata na mujiya mu ka yi cikin son ƙarin bayani,
ai kowa fahimtar hakan da ta yi ne ya sa ta ce "Wani abin farin cikin ya kuma samun mu, wallahi ashe labari mai dadi ne Dr. Ke san gayamin
tun dazu shi ke kiran wayar." cike da zumuɗi na ce
"Ammi meya faru ne"
Cikin fara'a ta ce
"Rahama ce ta warke daga Trauma ɗin da ke damunta, yanzu haka ta dawo hayyacinta harta
labarta ma Dr. Abinda ya faru waccan ranar shine ta ke daɗa tambayar duk ina muke."
Wani wawan tsalle na daka na rungume Ammi da ke tsaye cikin murna, hamdala duk mutanen
da ke wajen suka fara, an ɗau lokaci ana maida magana kafin Daddy ya ce
"Ai kamata yayi a kira Rahama ɗin ta video mu ganta ta ganmu ko hankalinta ya kwanta."
"Wallahi abinda na ce ma Dr. Kenan amma wai an yi mata allurar bacci saboda kukan da ta ke
yi."
"Toh masha Allah sai kuma ayi shirin tafiya koh" cewar Baaba. Dariya muka yi ganin yanayin
yadda ta yi maganar. Daddy ya kuma ce wa
"Insha Allahu kuwa sai tafiya a yau ɗin nan zuwa dare sai mu wuce. Tunda akwai private jet ɗin
kamfani na sai mu wuce gabaɗaya kawai."
"Haka za'ayi kawai Daddy amma dare kamar yayi nisa fa." Jiddah ta faɗa a shagwaɓe.
"A'a Mamana(sunan da Momi ke kiran Jiddah da shi kenan kasancewar sunan Mahaifiyarta ne)
babu kyau gaggawa aikin shaiɗan ne a bari zuwa daren mu shirya a nutse, zan kira Hajiyarku
(Mahaifiyar Jiddah) na shaida mata nasan itama za ta so ayi tafiyar nan da ita."
"Hakane ya kamata a shaida musu kam."
Bayan mun kammala breakfast ɗin ne duk muka miƙe don fara shirye-shiryen tafiya, inda
Saleem ya ɗauki Jiddah suka wuce gida don yin nasu shirin. Bayan na dawo daga rakiyar su
Jiddah ne na tarar Sadiq na ƙoƙarin fitowa daga falon don zuwa sashensa, wani tight and
friendly hug ya bani, dama nasan ɗazu kunyar su Daddy ya sa bai wani nuna ɗokin shi ba, cike
da farin ciki ya ce
"Little ina taya mu murna ragowar farin cikinmu ta dawo hayyacinta, bansan wani irin murna
zanyi ba wallahi." sassauta riƙon da yayi min yayi sannan ya riƙe hannuwana biyu ya ce
"Ku kaɗai ne farin cikina yanzu a wannan rayuwar, tabbas a yau na ƙara jaddadawa kaina
alƙawarin amanarku da Abbanmu ya bani, zan ɗau alƙawari har a gaban ubangijina bazan taɓa
bari ku ji kewa ko maraici ba, zan kasance Uwa, Uba sannan Yaya a gare ku ke da Rahama
bazan bari ko ku ƙara yin kukan baƙin ciki ba matuƙar ina numfashi a duniya." hawaye ne ya
silalo a kan fuskarsa, hannu na saka na share mai sannan na ce cikin zolaya
"Ka tafi ka shirya ka ji young Abbah."
Doka ya kaimin cikin sauri na sunkuya na wuce ciki da gudu, kai tsaye ɗaki na nufa don haɗa
kayana. Wayata na ɗauka na kira Jummai sannan na gayamata ta baiwa Raliya 1million sannan
ta sallameta idan da hali ma ta kaita har gaban danginta.
Ƙarfe bakwai na dare muka private jet ɗin Daddy ya ɗaga damu zuwa ƙasar Egypt and here
we're tare da Trauma Patient Rahama.
Dukan wasa Rahama ta kaiwa Zarah lokacin da ta kawo ƙarshen labarin. Kana daga baya ta
rungumeta tsam a jikinta tare da fashewa da kukan tausayin ƴar uwarta ta, sun jima a haka har
sai da Sadiq ya yi magana kafin suka tsagaita yin kukan.
Satinsu Daddy ɗaya a Egypt suka koma Nigeria inda aka bar Sadiq da Zarah saboda daga nan
zasu wuce Malasia.
Su ma kwanaki goma kacal suka ƙara jirginsu ya ɗaga zuwa ƙasar Malasia.
_Bari mu leƙa amarya da ango._..✍í ¼í¿»
*BY*
*JASMINE*í ¼í¼¸í ¼í¼¸
*ASP ZARAH*í ½í±©✈️
*BOOK 2*
*Page 9*
Sai dai kafin ta kai ga miƙewa Sadiq ya ruƙo hannunta ya zaunar da ita ba ta re da ya ce komai
ba abincinsa kawai ya cigaba da ci, tuni ta gane abinda ya ke nufi don haka ta zauna cikin
takura ta fara cin abincin, duk da bata kallonshi amma ta tabbatar kallonta ya ke yi don haka ta
ji sam zaman gurin bai yi mata ba.
Sun rigata gamawa don haka ne ma suka koma cikin falo suna hira. Duk da haka idon mayen
nata na kanta.
_Safwan Muhammad Habib shine sunansa matashin saurayi ɗan kimanin shekaru ashirin da
bakwai ɗan kwalisa, asalinsa ɗan Nigeria ne karatu ne ya kawo shi waje daga haka kuma suka
riƙeshi, babban likitane a ɓangaren da ya shafi mata da ƙananan yara._
_Ya fito ne daga gidan sarauta inda a yanzu haka mahaifinsa shin Sarkin Adamawa, cikin ƴaƴan
Mai martaba shida da matarsa Hajiya Zulaihat guda biyu ne maza, ɗansu na fari Mahmud sai
auta Safwan shiyasa Mai martaba ya ɗauki gatan duniya ya ɗora shi akansu ba kamar Safwan
ba ma da ba ya iya ɓoye son da ya ke masa ko a gaban waye, tun da