Showing 24001 words to 27000 words out of 28768 words
sosai dan Daddy kwarai yake son nuna su Zarah
na da gata duk da ubansu baya raye, shikanshi sai da ya musu akwati bibbiyu ya shake da
kaya na fitar biki bayan kayan ɗaki da suka shirya da Momi da Ammi suka je har Italy dan
siyowa, hatta cokali abin banza a ƙasar waje aka siyo musu komai nasu daga can ne. Baaba kuwa tayi faɗan harta gaji amma sunƙi dainawa.
Babban Yaya kuma wani danƙareren Boutique ya gina musu wanda aka cikashi da kayan
siyarwa na manyan mutane da ko a ƙasar waje sai haka, inda aka shirya taron buɗeshi ranar da
za'ayi bridal shower ɗin amaren, bayan haka sai da ya saka musu makudan kudi a cikin account
dinsu.
Tun ranar Monday aka fara gudanar da shagulgula inda akayi Welcoming dinner ranar monday
a farfajiyar gidan Daddy an kashe kuɗi sosai amare kuwa sun sha kyau tamkar a sace su a
gudu, washegari ranar talata kuma akayi Fulani day mai ban sha'awa dan harta mutanen Yola
sai da suka zo a jirgi bayan angama ya kwashe su ya kuma, Ranar laraba kuma akayi shagalin
buɗe Boutique ɗinsu Mai suna *RAHAZAR BOUTIQUE* wanda ya samo asali daga farkon
sunan kowaccensu.
Washegari Alhamis ne za'a gabatar da Reception kuma a ranar Safwan da abokansu zasu taho
Gombe dama shi Mahmud tun ranar Monday yake nan saboda wani taro da suka gabatar
shiyasa bayan an kammala yayi zamansa kawai tare da wasu daga cikin abokanansu.
Fitowar Zarah daga wanka kenan saboda bata tashi da wuri ba dan gajiya dama kuma tana
fashin Sallah, turo ƙofar akayi a hankali kanta ta maida kan me shigowar Sadiq ne da Daddy
suka shigo kallo ɗaya zaka musu ka gane tsantsar damuwa a tattare da su. Hijab ta ɗauka ta
zura sannan ta gaida Daddy bai amsa mata ba illa zaunar da ita da yayi a gefen gado ya fara
magana kamar....✍
*BY*
*JASMINE*
*ASP ZARAH*
*BOOK 2*
Nasiha sosai Daddy ya fara mata me ratsa jiki, ƙirjinta ne ya fara dukan uku saboda yadda taji
yana ambatar karɓar ƙaddara, ko wacce ƙaddarar ce ta kuma samun rayuwarta, tunaninta ya
katse sanda taji Daddy na faɗin
"Zarah haƙuri da juriyar da na sanki dashi a wannan karon ma shi nakeso kiyi sannan ki
rungumi ƙaddarar da Allah ya ɗora miki da hannu biyu. Kiyi haƙuri Zarah yau da asuba Allah
yayiwa Safwan mijin da zaki aura rasuwa sakamakon ciwon ciki da ya kulleshi a jiya da dare."
Tamkar saukar aradu haka taji maganar Daddy a kunnuwanta bata kyma gaskatawa ba sai da
taji ɗan uwanta na maimaita batun Daddy ɗin.
Bata kuma sanin inda kanta yake ba sai buɗe ido tayi ta ganta kwance a gadon asibiti da ƙarin
ruwa a hannunta, a hankali ta fara juya idanunta tana ƙarema inda take kallo da mutanen dake
wajen, mutum uku ta gane a cikinsu Baaba, Jiddah sai Rahama da suka yi wujiga-wujiga
alamun tashin hankali ya bayyana a garesu, ƙoƙarin mikewa ta farayi da sauri duk suka ƙaraso
inda take suna mata sannu bata kula ba ta fara magana tana cewa
"Dan Allah kuce mafarki nayi na zahiri bane dam Allah kada kucemin Safwan ya rasu bazan iya
rayuwa batare dashi ba, wayyo Allah shin wani zunubi na aikata a rayuwata da nake ganin irin
waɗannan kaddarori." Kuka mi cin rai ta fashe da shi me cin rai.
Gabaɗaya tausayinta ne ya kamasu su kansu rasuwar Safwan ta jijjigasu matuƙa bare ita kuma
da kowa ya zauna da su a ɗan ƙanƙalin lokacin nan zai fahimci irin ƙaunar da suke wa juna.
Kwananta biyar kenan a kwance batasan wanda yake kanta ba tun ranar da aka faɗa mata
batun rasuwar Safwan ɗin. Bayan su Daddy sun kawota asibiti ne suka bi jirgi zuwa garin Yola
dan jana'izarsa, kwanansu biyu suka dawo kuma kafin su dawo sai da aka ɗaura auren
Rahama da Mahmud sannan Zarah da Jawwad dan Mai martaba ya ce baza'a ɗaga auren ba
sannan shi da kanshi ya baiwa Daddy shawarar a ɗaura aurenta da Jawwad ɗin sannan yace
shi da kanshi zai zo ya taushi Zarah idan anyi sadakar bakwai sai dai an dakatar da
shagulgulan da aka shirya.
Kuka takeyi sosai harda shiɗewa suna bata baki ganin taƙi yin shirune yasa Jiddah ta kira likita
yana zuwa kuwa ya mata allurar bacci nan bacci ya ɗauke ta sannan ya cigaba da dubata.
Sai da Zarah ta yi wata guda a asibiti kafin ta fara dawowa daidai tare da sakawa ranta cewa
lallai Safwan ya tafi ya barta saidai ya barta da rauni a zuciyarta da bazata taɓa warkewa ba, ta
kuma shiru shiru sam bata son hayaniya kullum cikin jan carbi da karatun alqur'ani take yi, a
haka likita ya bata sallama bayan nasihohi da aka mata.
A ranar da Safwan ya rasu harda M.J da Abdallah suka shirya zuwa jana'izarsa. Kuma a
gabansa aka ɗaura aurensa da Zarah, a ranar ji ya yi tamkar mafarkan da ya saba yi ne yake yi,
babu kalar addu'ar alkhairi da bai yima mai martaba ba godiya kuwa har saida ya dakatar da
shi, kwana yayi yana sallar godiya ga Allah da kyautar da yayi masa a lokacin da ya cire
tsammanin samu.
A haka suka gama kwanaki uku suka baro Yola zuciyar M.J cike da farin ciki sai dai a ɓangare
guda yana taraddin yadda zai fuskanci Zarah ko da wani idon zata kalleshi idan taji labarin ya
zama mijinta a karo na biyu.
Kullum sai yaje asibitin dan dubata sai dai yafi zuwa lokacin da yasan tana bacci, tana bashi
tausayi sosai saidai a ɓangare guda yana kishi idan ya tuna saboda wani take yin wannan
jinyar.
Kwanaki biyu da sallamo Zarah Mai martaba da tawagarsa suka zo, da kanshi ya nemi ganawar
sirri da Zarah, shima dai nasihar ya mata sosai kafin daga baya ya shaida mata batun aurenta
da Jawwad, aikuwa nan hankalinta ya ƙara tashi ta fashe da kuka, roƙonta mai martaba ya
shiga yi dakyar ya samu ta sassauta bayan ya shaida mata yau yake so dukkansu a wuce dasu
ɗakin mazajensu dan dama Rahama tare da masu ɗaukarta suka zo. Nisawa yayi ganin yadda
take risgar kuka yace
"Fadimatu bawai shawararki nake nema ba ina baki umarni ne a matsayina na uba gareki indai
kin bani wannan matsayin. Kiyi hakuri da yadda ƙaddara tazo miki mun sani duka cewa kina
halin da yakamata a tausaya miki amma hakan da aka miki shine gata kuma zai rage miki
raɗaɗin abinda kike ji. Ki sani cewa a yanzu Safwan babu wani abu da yake bukata a gurinki
face addu'a sannan bazai taɓa yin farin ciki ba matuƙar kika bijirewa iyayenki saboda kawai son
da kike mishi sannan bazai ji dadi ba idan aka tada ki ranar alkiyama a matsayin wacce bata bin
umarnin iyayenta, a yanzu akwai auren wani a kanki tunanin Safwan da irin soyayyar da kukayi
ba shine mafita a gareki ba domin dai hausawa sunje matar mutum kabarinsa, dama can
aurenku da Safwan babu shi cikin lauhul mahfuz, ta iya yiwuwa akwai tanadin da Allah ya muku
a lahira shiyasa bai saka kun zama ma'aurata a duniya ba. Shi kanshi Safwan ba zaiji dadin
kwanciyarsa a cikin kabarinsa ba matuƙar kin take dokar Allah saboda kawai son da kike mishi.
Matukar kin bani wannan matsayi na mahaifi dan Allah Zarah ki amince da wannan auren
sannan ki rikeshi hannu bibbiyu dan samun rabauta duniya da lahira, shin zaki iya yimin
wannan alfarmar."
Cikin sheshsheƙar kuka ta gyada kai sannan tace
"Na aminci Baba zanyi amfani da duk abubuwan da ka fadamin sannan zanyi ƙoƙari na cigaba
da ɗaukan hakan a matsayin ƙaddarata."
Kalamai masu taushi ya cigaba da gayamata har saida yaga hankalinta ya kwanta sannan ya
kira sauran mutanen gidan yayi musu maganganu masu ratsa jiki musamman M.J dan kusan
gabaɗaya fadan akanshi ne, da haka ya baiwa sauran iyayensu damar magana shikam Daddy
ya kasa furta komai dan gani yake kamar a yanzu bashi da wata kima a idon Zarah dan kila
zatayi tunanin saboda yana son ɗanshi ne kawai ya saka aka ɗaura auren.
Duk shiru sukayi kafin Momi ta bude baki ta ce
''Muhammad Jawwad a matsayina na mahaifiyarka matuƙar ka ƙuntatawa Zarah a gidan
aurenka ban yafe maka ba duniya da lahira ko bayan bana raye." daga haka ta mike ta fice a
falon. Kai kawai mai martaba ya kada sannan yasa aka kira mishi matan da suka zo tare ya
shaida musu su shirya Zarah su fara kaita ɗakinta kafin su zo su wuce da Rahama zuwa Yola.
Haka kuwa akayi da taimakon Ammi da Jiddah suka shiryata fes ta fito amarya sai dai kallo
daya zaka wa fuskarta ta baka tausayi saboda yadda ta kumbura lokaci guda tayi jazir saboda
kukan da take yi.
Sam Baaba da Momi sunki yarda suyi Sallamar ƙarshe da Zarah shikuwa Sadiq hannunta
kawai ya riko ya kaita har ciki sabuwar motar da Daddy ya siya musu ta fitar biki ita da Rahama
ya zaunar da ita a ciki sannan ya rike hannunta gam yace
"Ki sani a kowani lokaci zan kasance tare da ke sannan bazan taba bari a cuceki ba a wannan
karon matukar akayi yunkurin hakan sai inda karfina ya kare akanki, banaso ki saka damuwa a
ranki ki cire komai ki saka a ranki cewa ibadah zakije yi sannan ibada dole sai da sadaukarwa.
Zan kasance a tare da ke a kowani lokaci." Hannu ya saka ya share mata hawayen fuskarta sannan ya sake hannunta ya rufe motar ya ja
hannun Rahama dake fama risgar kuka suka shige cikin gidan.
Basu jima sosai a gidan Zarah ba suka yi niyyar komawa saboda tafiyar dake gabansu, hakuri
sosai Ammi ta kara bata kafin su bar gidan, itama dai Jiddah bata zauna ba duk da taso hakan
amma Ammi ta hana. Haka suka tafi suka barta ita ɗaya tana aikin kuka.
Rahama ma haka aka tafi da ita cikin kuka da kewar rabuwa da gida musamman Ammi dan
daƙyar aka rabasu saboda shaƙuwar dake tsakaninsu. A haka aka wuce da ita zuwa airport
jirginsu ya daga zuwa garin Yola.
Sai fatan zaman lafiya mai ɗorewa.
***************************
Zaman dai na Zarah da Jawwad ba'a magana dan kuwa zamane na doya da manja sai dai yana
iya bakin ƙoƙarinshi dan kyautata mata dan da gaske yake son gyara laifukanshi na baya.
Kullum safiya shi ke gyara ko'ina na cikin gidan daga falo har sauran ɗakuna hatta ɗakin da
Zarah take kwana shike tsabtacewa duk safiya idan yazo zai gayamata zai gyara ɗaki sai ta fita
zuwa falo ta bashi guri idan ya gama ta kuma, bata kuma fitowa sai idan ya gama breakfast
yazo ya gayamata ta fita duk da bawani abincin take ci ba kawai tsakura kawai ta tashi, idan ta
gama kuma yazo ya tattare kayan da taci abincin ya wanke kafin ya shirya ya tafi office dan ma
dai shine shugaba shiyasa bashi da wata matsala a fannin ƙorafin latti, da rana ma haka duk
abinda yake yi zai bari ya siya abinci a resturant ya kai mata.
A haka rayuwar tasu take kasancewa sai dai babu wata alaqa tsakaninsu dan kafin Zarah ta
mishi magana ma yana jimawa sosai sai dai idan abu ya kasance mai mahimmanci ne.
A haka aka shirya taron ƙarawa Zarah matsayi a wajen aikinta inda aka bata muƙamin
mataimakiyar Commissioner na ƴan sanda a jahar Gombe gabaɗaya, gagarumin taro aka
shirya Daddy da kanshi ya kira M.J ya shaida mishi bai ko yi musu ba ya amince inda shima
yasha alwashin zuwa batare da yayi tunanin komai a ranshi ba.
Taron ya ƙayatar sosai inda Zarah ta samu manyan kyaututtuka hatta su Daddy sai da suka
samu kyautar karramawa a matsayinsu na iyayenta. A haka aka watse taron aka watse.
Sosai hankalinsu Momi ya kwanta ganin babu wata alamun damuwa a tattare da Zarah ga
kuma yadda M.J yake bin umarninta kamar dai itace mijin. Sai dai shi kallo ɗaya zaka masa ka
gane cewa hankalinshi ba'a kwance yake ba amma tunda ba furtawa yayi ba babu wanda
yasan abinda ke damunsa.
Zamansu dai bai canza zani ba dan jiya iya saboda M.J ya maida kanshi tamkar bawa ya cire
duk wanj girman kai yana baiwa Zarah kulawa, a yanzu da ta fara fita aiki kullum yana idar da
sallar asubahi yake fara aiyukan gidan sannan ya hada musu breakfast. Idan ta gama karyawa
kuwa shi da kansa yake ɗaukar mata jaka ya kaita mata mota sannan ya bude mata idan ta
shiga ya rufe ya mata addu'ar dawowa lafiya kafin nan ya kuma ciki ya shirya ya tafi nashi aikin.
A haka rayuwar tasu take kasancewa har zuwa tsawon wani lokaci sai dai an samu sassauci
dan yanzu Zarah tana gaidashi wani lokacin kuma da kanta take dafa musu abinci musamman
idan ta fahimci baya jin dadi dan a zaman su sau biyi ciwonshi yana tashi kuma yana wahala
sosai.
Yau ta kasance weekend babu aiki dan haka ne tunda tayi sallar asuba ta kuma ta kwanta
saboda tana bukatar hutu dan a satin tayi aiki sosai ta gaji. Baccinta take yi hankali a kwance a
haka M.J y shigo dan gyara mata dakin ganin tana bacci ne yasa ya tsaya yana ƙare mata kallo
tare da jinjinar girman soyayyar da yake mata, ya dade a tsaye kafin ya fita ya ja mata ƙofar a
hankali ya koma kitchen da hada musu abinda zasu karya dashi.
A firgice ta mike zaune jikinta na rawa lokaci guda ta haɗa gumi har tana diga sosai hankalinta
ya tashi akan mafarkin da tayi...✍
*BY*
*JASMINE*
*ASP ZARAH*
*BOOK 2*
Take abinda ta gani cikin mafarkin ya fara dawo mata filla-filla sosai hankalinta ya tashi.
Zaune take a cikin wani haɗaɗɗen garden tana zaune tana hutawa iskar gurin na kaɗa ta, a
hankali ta fara hango wani haske na nufo inda take har ya iske ta, ware ido tayi sosai ganin
iyayenta cikin kyakkyawar shiga sai sheƙi suke yi. Da sauri ta mike da nufi isa inda suke sai
kuma ta tsaya ganin Mami ta ɗago mata hannun alamun ta dakata batason ta iso inda suke
sannan tace
"Fadimah ashe irin abinda kike aikatawa a gidan mijinki kenan saboda kinga kasa ta rufe mana
ido, kenan duk tarbiyar da na baki akan yarda da ƙaddara baki ɗauka ba ko so kike Allah ya
azabtar damu saboda kinki bin umarninshi, kinsan a rana sau nawa mala'iku ke tsine miki kuwa
akan halin ko'in kula da kikewa mijinki. Ki gaggauta gyarawa dan sauke fushin Allah akanki,
nima da kika ganni cikin jindaɗi ba komai bane sila face biyayyar da nayiwa nawa mijin shin
bakyaso ki shiga jindadi ki kasance tare da mu a ƙoramar alfarma. Mahaifinki yana fushi dake
sosai bayaso ma ya miki magana sai ranar da kika gyara halayenki. Na tafi kiyiwa mijinki
biyayya Fadimah kiyiwa mijinki biyayya kiyiwa mijinki biyayya." A nan zancenta ya ƙare saboda
hannunta da Abba yaja suka bar wajen, zama tayi a ƙasa tana kuka sosai har na tsawon lokaci
kafin taji an dafa ta ɗagowar da zatayi tayi arba da Nusaiba itama cikin shigar alfarma, kafin ta
iya furta komai Nusaiban ta ce
"Yaya Zarah kowa yana fushi dake harsu Kaka dake sonki duk sunyi fushi saboda abinda kike
aikawata, Kaka ta ce bataso taga kullum mala'iku suna tsine miki dan haka ne ma tace babu
ruwanta dake, har su Adeel duk sun daina sonki, nima kawai nazo ne na gayamiki idan baki
gyara halayyarki ba bazan kuma zuwa inda kike ba."
Kafin ta ankare ta neme ta ta rasa dan haka ne ta miƙe ta fara tafiya dan barin wajen, tana cikin
tafiyane ta hango wani a zaune kan wata kujera ta alfarma sai sheƙi take yi, tsayawa tayi daga
nesa tana ƙare mai kallo, juyuwar da zaiyi taga ashe Safwan dinta ne da mugun gudu ta nufi
inda dan isa gare shi, Dakata! Shine abinda ya faɗa da ƙarfi sannan ya cigaba da cewa
"Baki kasance cikin masu yarda da ƙaddarar da Allah ya jarabesu da shi ba dan haka karki zo
inda nake." bat ta nemi shi ta rasa, kuka riris take yi tana kiran sunayen su amma babu wanda
yazo.
Wasu hawaye masu zafi ne suka sauko daga idanunta, duk da ance mafarki ba gaskiya bane
itakam wannan gaskiya ta ɗauke shi dan a fahimtarta iyayenta dake kwance cikin kabari basa
jindadin abinda take aikatawa. Amma ya zatayi takasa cire Safwan din a ranta, bawai bata
yafewa M.J abinda ya aikata mata bane amma tana jin ciwo ace ta rayu da shi a maimakon
Safwan din da take buri.
Sai dai wannan mafarkin lokaci guda ya sauya tunaninta ta saka a ranta cewa zata yi ƙoƙarin
ganin ta sauke haƙƙin aurenshi da Allah ya ɗaura mata. Istigfari ta fara tana neman yafiyar Allah
dan tasan ba ƙaramin zunubi ta kwasa ba a zamanta da M.J din, shi Allah babu ruwansa da
tanaso ko bataso haƙƙin da ya rataya a wuyanta kawai zata sauke idan kuma takasa zunubi ne
a kanta, tabbas tasan hukuncin macen da bata yiwa mijinta biyayyah ba a gurin Allah kaɗai
hatta mala'iku da sauran halittu kullum cikin tsine mata suke yi.
Kuka ta ƙara fashewa da shi har da sheshsheƙa zuciyarta na mata zafi sosai, M.J dake tsaye
gaban Dinning yana jera abinci ya jiyo sautinta ai da gudu ya nufo ɗakin. Tana nan a zaune tana
kuka, da hanzari ya nufi inda take