Showing 3001 words to 6000 words out of 28768 words
samu sauƙin abinda ke damunshi, shiryawa
yayi ya fita zuwa gurin aiki domin bazai iya zama a gidan ba. Yana tafe zuciyarsa cike da tunani
kala-kala, bai ankara ba hannu motar ta kwace mishi cikin rashin sa'a kuwa ya bige budurwar
dake ƙoƙarin tsalleke titin tana sanye ta dogon hijabi har ƙasa milk colour, da hanzari ya taka
birki ya kashe motar cikin tashi hankali ya fito ya sameta a zaune tana ƙoƙarin miƙewa alamun
motar bata taɓata sosai ba.
"Sannu kinji baiwar Allah, kiyi haƙuri, daure ki mike na kaiki asibiti a duba ki."
Cikin sanyin murya tace
"A'a banji ciwo ba ka barshi kawai." tana mikewa da kyar tamkar saniyar dake naƙuda.
"Kar muyi haka dake dan Allah muje na kaiki ko da Pharmacy ne a duba ki."
Babu musu ta bishi tana takawa dakyar har ta ƙarasa inda yake tsaye ya buɗe mata ƙofar motar
yana jera mata sannu babu adadi. Bayan shigarta ne shima ya shiga motar ya tada ta suka bar
gurin zuwa asibiti.....��
_Kai na na mini ciwo_.í ¾íµº
*BY*
*JASMINE*í ¼í¼¸í ¼í¼¸
*ASP ZARAH*í ½í±©â€�✈ï¸�
*BOOK 2*
*Page 3*
Da kwatance take nuna masa hanya ya Isa har ƙofar gidansu bayan ya kaita Pharmacy an duba
lafiyarta duk da ba wani rauni sosai ta ji ba, ita ta fara shiga cikin gidan jim kaÉ—an kuma Na'ima
ta fito ta gaidashi tare da faÉ—in ance ya shiga daga ciki, babu musu kuwa ya bita har cikin gidan
inda aka shimfiÉ—a masa tabarma a tsakar gurin Inda su Malam ke zaune tare tare da Hajara. Bayan gaishe gaishe ne M.J ya kuma basu hakuri akan abinda ya faru, nan suka nuna babu
wata matsala, miƙewa sukayi duka inda aka barshi da Hajara bayan ta kawo mishi sihirtaccen
zoɓon da Ummansu ta haɗa mishi, duk da yake mutum ne mai ƙyanƙyami amma haka bai
hanashi shan zoɓon ba ganin kamar yanayin mutanen baiyi kama da ƙazamai ba. Sun daɗe suna hira kamar da ma can sun saba duk da shi ba mutum bane mai yawan magana
amma ya sake sosai yana hira da ita, ya jima kafin ya musu sallama ya tafi bayan yayi musu
ɓarin naira tare da alƙawarin zai dawo ya duba jikin Hajara, haka sukayi sallama zuciyar
wannan ahali cike taf da farin cikin samun wannan arziki da sukayi.
Yana tafe amma zuciyarshi fal tunanin mutanen da yau ne ya fara haÉ—uwa dasu musamma Æ´ar
su da ta riƙe mishi zuciya lokaci ɗaya yaji kamar sonta na barazanar kamashi, lokaci guda kuma
zuciyarshi ta aminta cewa ya samu kalar matar da yake nema a fannin tarbiyya duk da yanason
mace wacce tayi karatun boko, fata yake a cikin ranshi Allah yasa babu wanda ya riga shi
domin kam bazai yarda yayi rashin wannan kamilar mace ba. Da wannan tunanin ya isa office
amma ya kasa taɓuka komai tunanin yadda zai ɓullowa su Daddy da zancen ƙara aure ne ya
dameshi musamman da bayaso auran ya wuce nan da wata É—aya ko biyu.
⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡
Cike da ƙosawa Jiddah ta kalli Raliya dake faman zubda hawaye tace
"Kina daɗa ɓata mana lokaci fa idan ba zakiyi magana bane ki faɗa tun wuri mu samawa kanmu
masalaha."
"Bansan ta yaya bane zaku isa ga inda Alpha yake domin nima bansan hanyar inda yake ba
bare nayi muku jagora." ta faɗa gami da sunkuyar da kanta ƙasa.
Cikin ɓacin rai Jummai ta kawo mata duka saidai bata kai ga isarta ba Zarah ta tare ta tana
faÉ—in.
"Sassauta Jummai abinda ta faɗa gaskiya ne amma tsaya muji ƙarashan zancen" komawa baya
Jummai tayi tana huci kamar wani firgitaccen zaki.
"Ke muke saurare Raliya bamu da lokacin da zamu cigaba da zama anan."
Shiru tayi na wani lokaci kafin tace
"An haifeni ne a garin Jos, ni kaÉ—ai ce Æ´ar da iyayena suka haifa kuma mahaifina hamshakin
mai kuÉ—i ne na ban mamaki yana da dukiyar da shi kanshi bai san adadinta ba, watarana sai
harƙalla ta haɗasu da Alpha batare da yasan ko shi waye ba. A zahiri Alpha dukiyar mahaifina
kaɗai yaso karɓa amma ganin mahaifin nawa yasan wasu daga cikin sirrikanshi yasa watarana
da daddare yazo har gida ya same mu ni da iyaye ya basu zaɓin ko ya barsu a raye ya kasheni
ko kuma ya barni a raye ya kashe su. Haka ina ji ina gani ya bani bindiga na kashe iyaye na da
kaina, daga nan ban kuma sanin inda kaina yake ba sai lokacin da na farfaÉ—o na tsinci kaina a
Alpha Villa." wani gauron numfashi taja mai bayyana abinda take faÉ—a yana mata zafi a rai kafin
ta cigaba da cewa
"Bahagowar Rayuwa muke yi acikin wannan gida ni da wasu daga cikin matan da yanayin
rayuwa yakai su wannan wajen, na daÉ—e kafin nasan wasu daga cikin abubuwan dangane da
Alpha a lokacin ne nagane cewa ba shi ne yaje ya samu mahaifina ba wani yaronsa ne domin a
yadda ake bani labari babu wanda ya taɓa ganin wani ɓangare na jikinsa wanda za'a iya shaida
shi dashi, tun daga lokacin na É—au alwashin sanin wani abu dangane dashi. A haka na cigaba
da neman kusanci da shi har zuwa lokacin da nayi nasarar ganin faratanshi waÉ—anda zan iya
ganewa a ko'ina idan naga mai kalansu ko shi É—in, bayan ya gano ni ne kuma ya saka aka
shigar dani É—akin duhu inda anan yake horar da yaran dake mishi akai. Ta haka ne nasan Alpha
sosai har na kamu da sonshi matuƙa duk da har yanzu bai taɓa bayyana kanshi gareni. Na
rantse da sarkin dake busamin numfashi wannan ne iya abinda nasani game da shi ko da kuwa
zaku bani qur'ani na dafa iyaka gaskiya ta kenan." daga haka ta cigaba da rera kuka a hankali
ta barsu kowanne da abinda yake saƙawa a ranshi.
Zarah ce ta fara katse shirun ta hanyar tambayarta tace
"A wani mataki kika tsaya da karatu kafin afkuwar wannan lamarin."
"Ina shekarar farko a jami'ar Jos na fara karantar Mass com."
Shiru suka kuma yi duka na wani lokaci babu mai tankawa kafin Jiddah tace
"Akwai wani ɓoyayyen al'amari da kika sani dangane da rayuwarsa ko wani nasa?"
Kusan mintuna uku kafin ta É—ago tace
"Ehh na taɓa karanta wani kundin sirri a ɗakinsa, akwai wata da naga hotonta da sunanta
Phalmata."
A tare suka kusan haÉ—a baki wajen faÉ—in
"Phalmata.??" fuskar Zarah da Jiddah cike da mamaki.
"Meye alaqarsu da ita."
"A yadda na karanta na fahimci cewa ita kishiyar mahaifiyarsa ce kuma tare suka fara duk
wannan harkallar, a yadda na gani ma ita kaÉ—aice yanzu a duniya tasan sirrikanshi na da dana
yanzu. Inajin idan kuka nemeta zata iya sanar daku komai akansa musamman a yanzu da suke
halin gaba zaku fi samun ingantattun bayanai."
"Kinsan wani abu dangane da inda zamu sameta ne."
"Eh toh ita É—in fasihiyar na'ura ce bayan haka kuma tana Æ´an tsibbace tsibbace, ina ganin ta
hanyar tsibbu ne kaÉ—ai zaku iya isa gareta."
"A ina take.?" Saleem ya tambaya cike da ƙosawa domin shi burinshi kawai yaji inda zasu samu
wannan matar
"Tana garin Dutse a Jigawa."
"Zaki iya tuna adireshinta da kika gani a kundin."
"Eh zan tuna harda fuskarta ma domin yanzu ba ita kaÉ—ai take aiki ba kamar dai Alpha, idan ba
sanin wani abu nata akayi ba zata iya haÉ—a mutum da wata daga cikin masu yi mata aiki a
matsayin itace."
Miƙewa Zarah tayi tana gyara tattarewar da kayanta yayi saboda tsugunno da tayi, kana ta kalli
abokan tafiyar tata tace
"Muje koh? Jummai ke kuma zuwa gobe ki wuce da ita gidanki ta cigaba da zama acan amma
ki tabbatar da tsaro."
"Toh ranki ya daÉ—e Allah ya tsare."
Da haka suka fice zuwa inda motarsu take, kai tsaye office É—in Zarah suka wuce domin
tattaunawa.
"Zamu É—aukarwa Raliya malamin dazai dinga koya mata zane-zane domin lallai da taimakonta
ne zamu samu zanen hoton Phalmata da yatsun Alpha." cewar Zarah bayan sun zauna zaman
tattaunawa akan matsalar.
"Nima nayi tunanin haka, amma bakya ganin koyamata zai ja lokaci? Ina ganin a neme mai
zanen kawai ta dinga fasalta mishi ya zana koh."
"A'a Saleem yarinyar tana da kwakwalwa sosai zata koya cikin ƙanƙanin lokaci musamman idan
muka mata barazana, da kanta zata fi iya zana komai da ta sani ba kamar idan faÉ—a take yi ba."
"Wannan haka yake, amma tsawon wani lokaci kenan.?"
"Sa-Jid yau muna É—aya ga wata, a cikin sati É—aya Raliya zat gama koyan zane tare da yi mana
zanen da muke buƙata, a sati biyun da zasu biyu baya na binciko inda Phalmata take ne, a
satin ƙarshe na wannan watan kuma zanje Abuja na neme takardar shaidar kama Alpha kunga
kenan a wata É—aya zamu gama wannan task É—in muje na gaba wato binciko inda Alpha yake
tare da kamashi."
Tafi suka mata cikin jinjina da barkwanci, Saleem ne yace
"Wani lissafin Æ´an sanda ne kaÉ—ai zasu iya shi."
Murmushi kawai tayi sannan tace
"Zanyi magana da Daddy idan yaso shi sai yayiwa M.J maganar tafiyarmu Zamfara"
"Shikenan wato har yanzu kunƙi sasanta kanku" cewar. Saleem
Bata ce komai ba ta fara haÉ—a abubuwanta domin tafiya gida, tare suka fito ta shige motarta
bayan sunyi sallama sannan suma suka tada motarsu suka wuce.
A kwanakin da suka biyo baya sam Zarah bata zauna a gida ba saboda ta tsaya kai da fata
wajen ganin Raliya ta koyi abinda suke buƙata, a ɗaya ɓangaren kuma suna shirye-shiryen
tafiya Zamfara ita da É—an'uwanta Sadiq da kuma Jiddah da Saleem domin tafiyar da zasuyi ba
ƙarama bace saboda adireshin da Raliya ta basu yana da nisa da garin dutse sosai dan haka
suna buƙatar su shirya sosai.
Wannan dalilin ne yasa kwata-kwata basu haÉ—u da M.J ba.
í ½í²•í ½í²•í ½í²•í ½í²•í ½í²•í ½í²•í ½í²•í ½í²•í ½í²•í ½í²•
A ɓangaren M.J da Hajara kuwa soyayya da shaƙuwa mai ƙarfi ne ya shiga tsakaninsu, basa
iya É—aukar dogon lokaci batare da sunji muryoyin juna ba. Da fari Hajara tanason auran M.J ne
saboda kuÉ—inshi saidai daga baya ta gane shine irin mijin da take so kuma gashi ta samu dan
haka ne ma tayi alwashin cewa idan akayi aurensu ta gama aikin da zata yiwa Alpha zata
cigaba da zama da mijinta domin ta samu kalarta. Shima a nashi ɓangaren yana mamakin
yadda cikin ƙanƙanin lokaci ya kamu da matsananciyar soyayyarta.
Takurawar da Malam Surajo ke mishi akan idan yanason Æ´arsa ya turo magabata ne yasa yau
yasha alwashin bayan ya tashi a aiki zai biya ta gidan ya sanar musu komai zai faru ya faru.
Ƙarfe shida ya tashi a office kai tsaye kuma gidansu ya nufa, saida ya tsaya yayi sallar magriba
a masallacin dake unguwar kafin ya ƙarasa zuwa cikin gidan nasu.
A harabar gidan ya ga motar Zarah hakan ya tabbatar masa cewa tana cikin gidan, ba ƙaramin
daÉ—i yaji ba kuwa domin yana son duk abun da za'ayi ayi a gabanta. A babban falo ya tarar da
su duka suna ƙoƙarin yin dinner Daddy, Momi, Sadiq da kuma Zarah, dan haka shima kai tsaye
teburin ya nufa da suci abincin tare. Gaishe da iyayensa yayi kana ya baiwa Sadiq hannu suka
gaisa fuska babu yabo ba fallasa ko da Zarah ta gaidashi sharewa yayi batare da ya amsa ba
wanda duk su Daddy sun lura da hakan amma babu wanda ya tanka haka suka fara cin abincin
cikin nutsuwa kowa da abinda ke ransa.
Bayan gama cin abincin kuwa cikin falon suka koma suna hira har kaÉ—an kaÉ—an, cikin dakiya da
dauriya tare da fargaba M.J ya buÉ—i baki yace
"Ehhmm Daddy dama nazo muyi magana ne."
Tun farkon shigowar shi Momi ta fahimci akwai abinda ke tafe dashi amma sai ta basar batayi
magana har yanzu da ya furta da kanshu, murmushin manya Daddy yayi kana yace
"Ina jin ka."
Shiru ya kuma yi har sai da Daddy yace
"Ko maganar na buƙatar sirri ne."
Cikin hanzari yace.
"A'a ba wata magana ba ce, dama ehmm dama iyayen yarinyar da nake nema ne suka ce na
turo magabata na ayi magana, a taÆ™aice dai aure nakeson Æ™arawa."...âœ�í ¼í¿»
_BY_
_JASMINE_.í ¼í¼¸í ¼í¼¸
*ASP ZARAH*í ½í±©â€�✈ï¸�
*BOOK 2*
*Page 4*
Wata irin zabura Momi da ke kan kujera tayi har saida ta sauko ƙasa ta dira a gaban M.J tana
ƙura mishi ido, shikuwa Sadiq wayarsa ƙirar IphoneRx dake hannunshi ne ta saɓule ta faɗi ƙasa
ji kake tasss ta fashe akan tiles, murmushin da akewa laƙabi da na ciwo shi Daddy yayi sannan
ya kalle Momi da Sadiq yace "Mene ne haka kamar kun riski saƙon mutuwar wani na jikinku.?"
Jan jiki Momi tayi ta jingina da kujerar da Zarah ke zaune,wacce tun faÉ—ar maganar M.J
zuciyarta taki nutsuwa a ƙirjinta sai barazanar fitowa take yi. Daddy ne ya kuma magana yace
"Muhammad Jawwad kace aure zaka ƙara koh.?"
Cikin fargaba da tsoro jin Daddy ya kira asalin sunanshi abinda bai taɓa ji daga bakin uban
nasa ba tun yarinta,ya gyaÉ—a kai yace
"Ehh Daddy."
"Ƙarya kake yi wallahi ba isa ka jamin zagi a gari ba Jawwad, bazai taɓa yiwuwa ba wani kallo
kakeso a dinga min idan na shiga cikin mutane." Momi ce ta faÉ—i haka cikin hargowa tana mai
fashewa da kuka.
KaÉ—a kai kawai Daddy yayi cikin takaici ya kuma maida hankalin shi ga M.J yace
"Shin zan iya sanin dalilin ƙarin auren ko akwai wani abu da Zarah take maka ne wanda bakajin
daÉ—insa."
"Babu komai Daddy dama muna soyayya da yarinyar ne yanzu kuma mahaifinta ya ce yana
bukatar aurar da ita." ya fada kai a sunkuye.
"Kaji ka amince cewa kanason yarinyar kuma zaka aureta ." Daddy ya kuma tambaya.
"Ehh Daddy." ya amsa a taƙaice.
"Shikenan tunda dai kai kazo da zancen bazan hanaka raya sunnah ba , na yarje maka kaje
kayi aurenka amma bawai dan hakan zai min daÉ—i a raina ba, kaje ka fara shiri sannan ka
turomin adireshin gidansu yarinyar nan da sati biyu masu zuwa in sha Allah za'a É—aura maka
aure da ita kamar yadda kake so. Sai dai inaso ka shaida wallahi duk wani abu da ya biyo baya
karka tunkareni da shi. Tashi kayi tafiyarka."
"Nagode Daddy." ya faÉ—i haka da hanzari ya mike ya fice daga falon gudun kar Momi ta kuma
yin magana
Baki sake kamar mutum-mutumi Momi ke kallon Daddy kamar wacce taga wani abin al'ajabi
mai girma, shikuwa Sadiq sarkin zuciya har ya mike ya finciki hannu Zarah da nufin su fice a
falon Daddy ya dakatar dashi, cak! Ya tsaya ita kuwa Zarah tuni ta fara sana'ar tata na kuka.
"Indai ka É—auke ni a matsayin uba ka dawo ka zauna."
Babu musu suka juyo suka zauna zuciya sam babu daÉ—i, mintuna suka shuÉ—e babu wanda ya
tanka kafin daga bisani Daddy ya ce
"Ku yi haƙuri da kalan hukuncin da na yanke, akwai wani abu da na hanga ne da sannu zaku ga
abinda zai biyo baya domin jikina baya bani akwai alkhairi a ciki. Kiyi haƙuri Zarah faruwar
komai jarrabawa ce daga Allah watarana sai labari., labarin ma watarana va za'a samu masu
bada shi ba. Kiyi hakuri kinji, Allah ya jiɓanci lamuranki, kai Sadiq tashi ka rakata gida." Babu musu ya miƙe ita kuma ta yi musu sallama suka wuce, a hanya babu mai magana a
cikinsu har lokacin da suka isa har cikin harabar gidan M.J kafin Sadiq ya riƙo hannunta ya ce
"Ki dinga yawan tunawa da nasihar da Abba yake mana a ko yaushe, hakuri shine ribar zaman
duniya, nima inaso na dinga kwatanta hakan sai dai zuciyata bata iya jure ganin É—ayan ku cikin
ƙunci. Da sannu ni da kai na zanzo har cikin gidan nan na ɗauke ki na kaiki inda zaki samu farin
ciki na har abada." Murmushi kawai tayi mishi kana ta fita a motar ta shige gida, shi kuma ya juya kan motar ya fice
a harabar gidan.
Kamar yadda suka tsara cikin sati Raliya ta zana musu fiskar matar kamar yadda ta dage wajen
koyan abinda ake koyar da ita. Sai dai batun tafiyar ta su a katse sakamakon tasuwar bikin mijin
Zarah.
A wannan lokacin kuwa tuni batun auran M.J ya kankama domin an bada sadaki sannan ankai
kayan aure ranar kawai ake jira tazo a É—aura auran, sai dai mutane da dama basuyi farin ciki da
wannan auran ba amma babu yadda aka iya da hukuncin Allah.
Rana dai aka ce bata ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, kamar yadda ya kasance ranar juma'a
bayan zagayowar sati aka É—aura auran Muhammad Jawwad Sulaiman da Hajara Suraj, bikin
daya kasance tamkar na bazawara saboda rashin jama'a.
Haka amarya dai ta tare a gidan mijinta cike da buri a ranta na abubuwan da ta shigo cikin
gidan da niyyar aikatawa.
Hausawa kan ce _Rawar da aka fara ta da tsalle ƙarshenta baya kyau_, kamar haka ce ta faru
a gidan M.J wanda tun farkon kawo amaryarsa ya nuna mata cewa Zarah bata da wani matsayi
a gurinshi face na Æ´ar uwa domin baya mata kallon matarsa, wannan dalilin ne ya saka sam
Hajara bata ganin girmanta bare ayi tunanin zasuyi zaman amana, a wasu lokutan a gaban
Hajara M.J ke yiwa Zarah cin kashi tare da cigaba da yi mata ƙazafin zina batare da lura da illar
hakan da zai haifar masa anan gaba ba.
Yau ma kamar kullum Zarah ta dawo daga aiki a gajiye liƙis, ta shigo babban falon ɗauke da
sallama a bakinta, kamar ko da yaushe suna kwance a dogowar kujera manne da juna suna