Showing 6001 words to 9000 words out of 28768 words

Chapter 3 - ASP Zahra Book 2 Complete By Jasmine


soyayya tamkar zasu haɗiye juna, yau kwanansu goma kenan da aure amma kullum a haka
suke wuni tare batare da M.J yayi tunanin bada haƙƙin addini akan wanda yayi sabon aure ba
ko da yake bata zaton hakan daga gareshi domin ko da take ita kaɗai ma baya bata haƙƙinta
daya rataya a wuyansa. Tunaninda takeyi ne ya katse sakamakon muryar Hajara da ta daki
cikin dodon kunnenta tana faɗin
"Hubby haka kenan gidanka zai cigaba da kasancewa mafakar fasiƙai alhalin da ranka da
lafiyarka.?" mikewa yayi daga kwancen ya zauna sannan ya dubi Zarah dake ƙoƙarin shigewa
part ɗinta ya ce
"Ina fatan kin wanke janabar da kika ɗebo tun a waje baki shigomin dashi cikin tsabtaceccen
gidana ba.?"
Kaɗa kai kawai tayi sannan ta shige ɗakinta cike da takaici domin ya ci ace ta saba da irin cin
kashin da mijinta da kishiyarta ke mata a duk kwanan duniya.

*1:45am*

A daidai wannan lokacin ko wani halitta na ɗan adam yana tsaka da bacci in ka ɗauke ɗaiɗaiku
da wani uzurin ya hana su bacci, cikin waɗanda basu yi bacci ba a wannan lokacin harda Zarah
dake zaune gaban na'urarta tana gabatar da wani aiki gefenta kuwa wani ƙaramin kofi ne da
shayi a ciki sai tururi yake yi, tana sanye da riga da wando na bacci mai santsi kalar sararin
samaniya ta ɗaura wata hula mai gashi a kanta, gabaɗaya hankalinta ta maida akan aikin da
take gabatarwa.
A hankali ta miƙe ta nufi window ɗin ɗakin saboda jin alamun kamar hayaniya na tasowa daga
farfajiyar gidan, labulen ta ja kaɗan tare da leƙa tsakar gidan ga mamakinta sai taga kamar
gilmawar mutum, ganin dare ne yasa bata wanj damu ba ta koma inda take zaune da ta cigaba
da aikinta. Zamanta ke da wuya ta ji an hayaniya da kururuwar Hajara a babban falon tare da sallallami da
M.J ke yi, take ta gane cewa wasu sun shigo cikin gidan, da sauri ta miƙe ta ɗauki jacket ɗinta
ta saka sannan ta zari ƙaramar bindigarta ta nufi falon. Ai kuwa kamar yadda ta zata mutane ne
a falon su tara kowanne da shiga mai kyau fuska a rufe, uku daga cikinsu ne kawai maza amma
duk sauran mata ne, ganin fitowarta ne yasa wasu mata su huɗu suka nufeta da nufin rikota,
wani wawan naushi ta kaiwa waɗanda ke da nufin riƙe mata hannu da duka hannuwanta biyu
sannan ta sunkuya ta kaiwa wacce take gabanta naushi a ciki take ta durƙushe saboda zafin da
taji. Sai dai kafin ta kuma wani yunƙuri wasu suka tura ta ta faɗi ta gaba kafin ta ɗago suka yi
nasarar ɗaure mata hannaye. Ɗaya daga cikinsu ne yayi maganar su ƙyale Zarah haka sannan
ya juya ya kalli M.J ya ce

"Ran matan ka ko kuma dukiya.?"
Cikin kauda kai M.J dake riƙe a hannun ƙarti biyu da mace ɗaya yace
"Malam ni matata ɗaya ce kuma gata nan" ya nuna Hajara sannan ya cigaba da cewa" Ku kama
wacce ta muku laifi ku rabu da mu."

Dariya yayi sannan yace
"Ya za'ayi mu yarda da hakan bayan a mun shaida ɗaurin auren ku."

Shiru yayi na wasu mintuna sannan yace
"Idan kuna so ma zaku iya shaida warwarewarsa."
Cike da dariya mugunta ya kuma cewa
"Mai zai hana kuwa."

Cike da takaici Zarah tace
"Yaya Jawwad kada kayi abinda zaka zo kana da na sani, ina da rauni sosai sannan ni
marainiyace. Kada ka lalatamin rayuwa ta hanyar maida ni ƙaramar bazawara."
Bai kula da maganganunta ba ya ce
"Na sake ki saki ɗaya Zarah."
Tabbas mutuwar aure babu daɗi ko da babu soyayya wannan dalilin ne yasa Zarah taji
zuciyarta tayi mata zafi sosai lokacin da ɗan'uwanta ya furta kalmar saki a gareta.

"Kinsan abinda ya kawo mu dan haka ki bamu salin alin saboda yau zamu yi ta mukare tsakanin
mu da ke." Mutumin ya kuma faɗa batare da ya kula da halin da take ciki ba, kauda kai tayi gefe
tana addu'ar Allah ya bata nasarar kunce kanta duk da suna da yawa tasan zata iya musu
mugun lahani ba tare da makami ba ma. Saura ƙiris ta fasa ƙara saboda wani gigitaccen zafi
daya ziyarce ta a gefen cinyarta, kallonta ta maida gurin taga ashe ɗaya daga cikin matan nan
ne ta yi mata muguwar yanka a cinyarta take kuwa jini ya ce dama hanya nake nema nan ya
fara zuba tamkar kwararo shi ake yi, raɗaɗi take ji sosai amma hakan bai sa ta amsa tambayar
da ya kuma mata ba, ya ce
"Ba zakiyi magana ba ke wace iriyar yarinyace mai taurin kai ne, mtsssw ku shiga ku bincika
min ko ina a cikin gidan nan."
Dukkansu suka nufi hanyar da suka ga Zarah ta fito mutum uku kaɗai suka bari biyu na tsare da
M.J da Hajara sun saka musu bindiga akai sai babban dake gefen inda Zarah ke ɗaure yana
wasa da wuƙar hannunshi yayinda ɗaya hannu ke rike da bindiga. Kusan mintuna arba'in suna
dube-dube a cikin gidan amma basu ko ga wata alamar da zata nuna musu cewa Diamonds ɗin
suna cikin gidan ba, cike da rashin kwarin gwiwa suka dawo suka sanar da shi, bai ce komai ba
ya zaro waya ya daddanna sannan ya kara a kunnenshi jim kaɗan ya fara magana yace
"Yallaɓai jiya i yau fa, taurin kan yarinyar yayi yawa ta tushe kowace hanya bata bamu damar
sanin komai ba."
Huci ya furzar mai zafi kana yace
"Wannan karon inaso ku taɓa Zarah, ina so taji a lafiyarta cewa ba'a gardama dani, ina so taji
lallai cewa bazata iya cigaba da ajiyar Diamonds ɗin nan ba, lallai ku yi mata mummunan lahani
kamar yadda zuwa yanzu na tabbatar idan Raliya tana raye to tana cikin mawuyacin hali."

"Angama ranka ya daɗe." daga haka ya katse wayar ya kalli matan dake tsaye ya ce
"Ku cika aiki" tamkar suna jira haka suka ruftu su biyar akan Zarah kowa da irin dukan da yake
kai mata amma duk da haka ko tari bata yi ba bare ayi tunanin zatayi kuka.
Karo na farko Hajara taji mugun tausayi da dana sani sun baibayeta, ciwon ƴa mace na ƴa
mace ne, sosai taji da na sanin haɗa kai da ita da akayi tun farko har zuwa yau da suka shigo
cikin gidan nasu. Shikuwa M.J ba yadda za'ayi ka gane yanayin da yake ciki domin fuskarsa
tana nan yadda take. Cikin mintuna ƙalilan farin tiles ɗin dake falon ya fara rinewa yana yin ja saboda jinin dake
gangarowa daka jikin Zarah sakamakon bugu da yanka da suke jikinta, ganin kamar ta daina
numfashi ne yasa ya dakatar da su sannan suka fice a gidan.
Da hanzari Hajara ta rarrafa ta isa kanta hawaye na biyowa a idanunta ta juya ta kalli M.J ta ce
"Hubby ɗauki key da sauri mu kaita asibiti."

"Ni? Asibiti? Babu inda zan fita da daren nan, ita ta jawo wa kanta."

"Ka dubi halin da take ciki mana dan Allah ka taimaka."

"Yaya Jawwad dan Allah ka kiramin Daddy ko da bazaka kai ni asibitin ba." Zarah ta faɗa a
galabaice, numfashinta na fita ɗaiɗai.
Bai kula ta ba ya zo yaja hannun Hajara suka nufi ƙofar part ɗin shi, tsayawa yayi cak! Sannan
ya dawo ya tsugunna a gabanta yana ƙare mata kallo shi kansa yasan tana buƙatar taimako na
gaggawa amma yana jin zafinta sosai a ƙasan zuciyarsa, gyaran murya yayi sannan yace
"Kinsan yanzu babu igiyar aure tsakanina dake, dan haka zan taimaka miki ne kaɗai a matsayin
karuwar da nakeso ta tuba ga Allah kafin ta mutu, wannan ne kaɗai gatan da zan miki, kin
amince na taimaka miki.?"

"Zan fi ƙaunar na mutu a haka matukar da wannan ƙudurin zaka taimake ni, na tsane ka, baka
da tausayi ko kaɗan, kai mara imani ne."

Kafaɗa ya kaɗa ya mike sannan yace
"Duk yadda kika gani sai ki kira wanda kike jin shi zai iya taimakonki ko a cikin abokan
watsewarki ne." daga haka yaja matarsa suka shige suka barta a nan kwance.
Cikin dakiya da juriya ta miƙe zaune tana jan jiki harta isa ƙofar da zata sada ta da farfajiyar
gidan cikin tsananin azaba da ciwo.



A firgice ta miƙe daga baccin da take yi, juyawa tayi ta kalli agogo 2:05am kallonta ta maida kan
Saleem dake sharar baccinsa hankali kwance, a hankali ta fara bubbuga bayansa har ya farka
ya buɗe idanunsa ganinta a zaune ne yasa shima ya zauna yana miƙa ya kalleta yace
"Lafiya kuwa me ya same ki.?"

"Sa-Jid nayi mafarki Zarah na ta kirana tana faɗin na taimaka mata, zuciyata da jikina sun amsa
bana jin daɗi sam ina da tabbacin cewa akwai abinda ke faruwa da ita."

"Me zai faru da ita da wannan daren haba dan Allah mafarki fa ba gaskiya bane."

"Na sani amma dai wannan yayi kama da gaskiya, miƙomin wayar can na kirata."

Hannu yasa ya ɗauko wayar dake kan bedside drawer ya bata, cikin hanzari ta fara danna
lambar Zarah tana kira amma kusan kira 30 babu amsa. Zuwa lokacin ta gama ruɗewa, kuka ta
sakawa Saleem akan lallai sai ya kaita gidan Zarah a daren duk yadda yaso ta haƙura amma
taƙi, sanin da yayi cewa idan damuwa zata iya jawowa ƙaramin cikin dake jikinta matsala ne
yasa dole ya miƙe ya zura jallabiya ya ɗauki key ɗin motar suka fice a gidan, har zuwa lokacin
kuma bata daina kuka da sambatu ba...✍


*BY*
*JASMINE*

*ASP ZARAH*

*BOOK 2*

*Page 5*

... Su uku ne zaune a cikin wani ƙayataccen falo da yaji kayan alatu tamkar na shugaban ƙasa
Sadiq, Rahma da kuma Zarah, kallo ɗaya zaka musu ka gane suna cikin tsantsar farin ciki da
suka daɗe basu samu ba duba da yanayin yadda fuskokinsu suka kasa ɓoye farin cikin da suke
ciki. Rahma ce ta ajiye cup ɗin dake hannunta a center table ɗin dake gabanta sannan ta juyo
ta dubi Sadiq dake nunawa Zarah abu a waya suna ƙyalƙyala dariya ta ce
"Bazan iya tuna ranar ƙarshe da naga dariyarku haka ba musamman Zarah."

"Ba mu da wata sauran damuwa ne shiyasa ki ka ganmu haka, ke ba abin farin ciki bane a
gareki ace yau wanda yayi sanadin da iyayenmu suka bar duniya shima ya mutu ta dalilinmu,
baya ga haka ƴar'uwar mu wacce muke tunanin ta zauce yau ta samu lafiya ingantacciya, kinga
kuwa dole mu yi farin ciki." Sadiq ne yayi wannan sharhin bayan ya maida hankalinsa kanta.
Gyaɗa kai tayi ciki da gamsuwa tace
"Haka ne amma naku ne kawai ke fitowa fili, nawa na barshi a zuci."
Zarah waccw tun da aka fara maganar bata tanka ba ta ɗago tace
"Meye zai hana ki fito dashi fili mu haɗu mu yi murnar tare."
Cike da zolaya Rahma tace
"Yau kam naci girma na bar muku."
Ɗaya daga cikin ƙananun pillows ɗin dake kan kujerar Sadiq ya ɗauka ya jefeta da shi cikin

harara yace

"Ke banson raini fa"

Itama cikin zolaya tace
"Kwanaki ƙalilan a ne tsakaninmu fa."

"Duk da haka dai ya riga ki shaƙar iskar duniya." Cewar Zarah.

"Haka ne toh na baka girman ka, yanzu daga nan ina zaku wuce."
Shiru sukayi na wani lokaci kafin Sadiq yace
"Daga nan Malasia zamu wuce, Little zata fara karatun masters ɗinta acan, ni kuma na cigaba
da aikina."
Fuska ta sauya kamar zatayi hawaye tace
"Za mu ƙara yin nisa da juna.?"

"Ki shirya mu tafi tare." fadin Zarah.

Hararar wasa ta mata sannan ta kuma cewa
"Na gaji da kawaici fa, tun ɗazu inaso ku ɗauko min hirar abubuwan da suka faru amma kun
share."
Dariya suka yi duka sannan Sadiq yace
"Tun ɗazu na lura dake kawai na yi miki shiru ki furta da bakinki."

"Na tambaya yanzu a gayamin meya faru."

"Labari ne mai tsawo fa ki nemo biro da takarda" Inji Zarah.

"A'a bani wannan baiwar sai dai na kira Sis Jasmine ta mana aikin rubutun."

"Tom shikenan haka za'ayi."

"Ke nake sauraro."



Ina cikin tsananin azaba a wannan rana da yaran Alpha suka shigo har gida sukamin rauni
amma Yaya Jawwad yaƙi ko kula da lamarina bare yayi tunanin kaini asibiti duk da a lokacin
babu dangantakar aure a tsakaninmu amma nayi tunanin zai taimakeni a matsayi na na
ƴar'uwarsa sai dai hakan bai kai ga ci ba. Ganin sun bare yashe a falo cikin jini ne yasa nayi
ƙoƙarin nafara jan jiki domin zuwa na saka Baba Mai gadi ya kiramin Daddy ko Sa-Jid saboda a
halin da nake ciki a wannan lokacin nasan komai zai iya faruwa dani sakamakon jinin da ke
zuba daga jikina, da jan jiki na fita har farfajiyar gidanmu zuwa ɗakin Mai gadi sai dai nayi rashin

sa'a domin shima sun yi mishi duka bai san inda kansa yake ba. A lokacin nafara ficewa daga
hayyacina saboda tsananin azaba da zafin raunukan dake jikina, ina cikin wannan halin ne naji
ana horn a ƙofar get ta waje amma bani da kuzarin da zan iya xuwa na buɗe, an daɗe anayin
horn ɗin daga baya kuma akazo jikin ƙofar ana bugawa, ganin gate ɗin a buɗe ne yasa su
shigowa ba kowa bane illa Sa-Jid.
Ko da suka shigo da ni suka fara yin arba a kwance cikin jini ai kuwa hankalinsu ya tashi sosai
domin saida Jiddah ta suma dakyar ya samu ta nutsu kaɗan sannan ta taimaka mai suka shigar
da ni cikin motar ba su ko kula da mai gadi ba bare su ɗauke shi mu tafi asibitin a tare saboda
tsananin firgici da suke ciki. A guje Saleem ya ja motar muka bar cikin anguwar muka nufi
hanyar asibiti, gudu yake yi tamkar zai tashi sama saboda azalzala da Jiddah ke yi masa, ni dai
a lokacin sama-sama nake iya jiyo maganganunsu saboda zafin raunukan dake jikina da kuma
jinin da har a lokacin bai daina zuba ba. Cak! Motar ta tsaya taƙi yin gaba ko baya duk yadda
Saleem yayi ƙoƙarin ta motsa amma taƙi hakan ne yasa ya fito daga cikin motar cikin tsananin
mamaki domin yasan motarsa lafiya lau take sannan akwai mai sosai a ciki, buɗe-buɗe ya fara
yi yana dubawa ko zai ga ta inda matsalar take amma bai fahimci komai ba, ganin haka yasa
itama Jiddah ta fito a motar tana taya shi dubawa ko zasu gano matsalar motar. Kamar wanda
aka umarta haka ya sunkuya ƙasa tare da leƙa ƙasan motar, abinda ya gani a gurin ne ya
matuƙar bashi mamaki, bakomai ne ya hana motar tafiya ba illa wani littafi ƙaramin dake ƙasan
tayar gaba na hagu, cikin al'ajabi ya sa hannu ya zaro littafin da ƙarfi, cikin zarewar idanu ya
nunawa Jiddah littafin wanda a bango cikakken sunana ne a rubuce cikin rubutu mai matuƙar
kyau. A wannan lokacin bana tsayawa wasu maganganu bane saboda halin da nake ciki hakan
yasa Saleem ya ajiye littafin a gaban motarsa zuwa lokacin da zan samu kaina. Bansan abinda
ya faru ba domin a lokacin juriyata ta ƙare tuni na sume, a haka muka isa asibitin cikin
gaggawa, ba mu sha wahalar samun likita ba domin a wannan asibitin Jiddah ke aiki sannan ita
ke dubani lokuta da dama idan kalar hakan ta faru, a wasu lokutan ma bama zuwa asibiti idan
zamana a asibiti na da hatsari.
Emergency room aka shigar dani, nan da nan Jiddah da wasu likitoci biyu tare da nurses suka
duƙufa domin ceto rayuwata, sai bayan da aka idar da sallar asuba'i kafin numfashina ya
daidaita bayan sun gyaramin raunukan dake jikina sannan nasha ɗinkuna a waɗanda ke
buƙatar ɗinki. Daga haka aka yimin alurar bacci sannan Jiddah da kanta ta turani ɗakin hutu.
Sai a lokacin ta samu sukunin kiran Daddy ta shaida mishi abinda ke faruwa, ba'ayi mintuna
ashirin ba kuwa sai gasu a cikin asibitin gabaɗayan su harda Baaba, ganin yanayina kuwa ta
matuƙar ta da musu da hankali nan suka tambayi abinda ya faru, Saleem ne kaɗai ya iya buɗe
baki ya musu bayani tun daga kan farkawar Jiddah daga bacci har zuwa lokacin da nake
kwance bansan me ke gudana ba.

Sun shiga damuwa sosai musamman Baaba da a lokacin take tunanin na mutu ne ake ɓoyewa,
shi kuwa sarkin zuciya Sadiq ya kasa furta ko kalma ɗaya amma kallo zaka yi masa ka gane
yana cikin tsananin damuwa da ɓacin rai duba da yadda idanunsa suka sauya kala zuwa jajaye
sannan kyakkyawar farar fuskarsa ta rine tana nuna alamun ɓacin rai. Haka suka zauna shiru
har ƙarfe goma na safiya amma ban farka ba wannan dalilin ne yasa Momi da Daddy suka nemj
komawa gida domin taho da abinda ba'a rasa ba na buƙatar majinyaci domin ita kam Jiddah ta
ce babu inda zata motsa sai taga farkawa ta, tana gefen Baaba a zaune acan wata kwanar

ɗakin suna sharar kwalla lokaci lokaci.
Duk cikinsu babu wanda yayi tuna M.J bare ayi tunanin abinda ya hanasa zuwa a matsayinshi
na mijinta, Sadiq ne kawai ya farga ga haka tun lokacin da yazo baiga M.J a wajen ba yasan
akwai wata manaƙisar a ƙasa saidai ya share saboda jiran farfaɗowata amma cikin ranshi ya
ɗau alwashin cin zarafin M.J matuƙar ya bincika ya samo da sa hannunshi a cikin abinda ya
faru dani.
Wani abu da nafara manta wanzowarsa a cikin shafin rayuwata shi ya sameni a lokacin da nake
tsaka da baccin dole da likitoci suka sani yi sakamakon allurar baccin da akamin, duk da
daɗewar shekaru amma ko a ina naga wannan fuskar zan ganeta, kinsan wacece?"

Rahama dake sharar kwallar tausayin ƴar'uwar tata ce ta girgiza kai alamun a'a domin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login