Showing 15001 words to 18000 words out of 28768 words

Chapter 6 - ASP Zahra Book 2 Complete By Jasmine

ya isa shiga makaranta
Mai Martaba ya ɗauke shi zuwa saudiyya inda wata ƙanwarsa ta ke aure, anan ya yi karatunsa
daga na boko har zuwa addini hutu ne kawai ke maida shi Nigeria, sanda ya isa shiga jami'a ne
ya koma London ya haɗa degree ɗinsa na farko daga nan ya koma Malasia yayi Masters ganin
ƙoƙarinsa da sanin kan aiki ne yasa bayan ya gama karatun ƙasar ta riƙeshi zai yi mata aiki na
tsawo shekaru biyu, ɗan uwansa Mahmud kuwa tunda ya gama karatu mai martaba ya sashi ya
kuma Najeriya inda ya buɗe mishi wani babban company tun da dama karatunshi akan
kasuwanci yayi, saboda kasancewarsa magaji shiyasa mai martaba bai yarda ya zauna a waje
don yin aiki ba, a yanzu haka yana da shekaru 35 kuma har zuwa wannan lokacin bai yi aure ba
duk takurar da iyayensa ke masa an haɗashi da ƴaƴan manya sosai sai dai duk cikinsu ya kasa
zaɓar ko guda ɗaya._
_Farkon ganinta da Safwan washe garin ranar da suka zo Malasia ne, gidansu da nashi na
fuskantar juna ƙaramin titi ne kawai ya rabasu, a ranar Sadiq ke gayamata cewa ya shaida
Safwan ɗin don sun taba haɗuwa sau biyu a saudiyya sanda ya je Umrah, anan ne ma ta ke jin
tarihinsa da inda ya fito shiyasa wani lokacin bata ganin laifinsa idan yana girman kai bata ganin
laifinsa don ya fito ne daga gidan sarauta_

Ta na iya jiyo hirar da suke yi daga inda ta ke, tana mamakin yadda ya ke hira haka harda
dariya amma idan ka ganshi a wani wajen kamar mala'ikan mutuwa.

"Zuwa wani sati zanje Egypt." Cewar Sadiq

"Haba dai yaushe ka dawo daga Egypt din da har zaka koma, me Ammi ta ke baka hakane ko
kuma akwai wacce ka ajiye acan ne shiyasa kake zuwa ganinta." Safwan ya faɗa cike da
zolaya.

"A'a ka bari dai ai yanzu Yola zanje na zaɓo santaleliyar mata jinin Fulani, zanje na taho da
Rahama ne kasan har yanzu ba wata isasshiyar lafiya gareta ba."

Hararar wasa ya aika masa sannan ya ce

"Kana shagwaɓa yaran nan dayawa fa, yanzu duk wayar da kuke yi da video calls bai ishe ku
ba har sai ka aje aiki kaje ka ɗauko ta."

"No bawai haka bane wallahi, next week little zata ƙara shekara shiyasa nake so tazo mu yi
murnar tare."

"La'ilah party zaka koya musu."

Dariya yayi mai isarsa sannan ya ce

"Ba wai party bane, Abbah ya rigada ya saba mana ne duk ranar zagayowar haihuwar wani
daga cikin mu sai an haɗu an taya shi murna hatta ni da bana ƙasar ma, har inda nake ake
zuwa a same ni ayi komai tare dani. Kuma kaga ita little bata taɓa ƙarin shekara cikin nutsuwa
ba aikin nan nata baya barinta ta yi abubuwa cikin lumana ko bata gari anyi ta kiranta a waya
kenan har sai ta gaji ta koma."

Dariya ce ta so kwacewa Zarah jin irin sharhin da ɗan uwan nata ya yi, shidai Sadiq akwai
surutu idan ba haka ba yanzu me ya haɗa Safwan da wannan dogon zance na family, ko da ya
ke Sadiq ɗin ba shi da wasu abokai sai turawa shi yasa idan ya haɗu da bahaushe ya ke zuba
kamar ruwan sama.
Gyaɗa kai Safwan ya yi cikin gamsuwa ya ce
"Hakane gaskiya bai kamata ace don Abban baya raye ba kuma a daina musu hakan zasuji
kewa ta damesu. Allah ya jiƙansu Abbah ya gafartamusu."

"Ameen" Sadiq ya faɗa sannan ya kalli inda Zarah ke zaune, ganin hankalint baya kansu ne
yasa shi cewa

"Ka faɗa a hankali karka tada min rigima dan idan little ta birkice ta fi tsohuwar mota."
Dariya suka yi duka harda tafawa.

Miƙewa ta yi bayan gama cin abincin ta fara tattara kwanukan tana kaiwa kitchen, harta gama ta
shige ciki ta barsu suna hira batasan lokacin da Safwan din ya tafi ba don a Malasia dare baya
yiwa mutane sai dai idan mutum ne ya gaji da zirga-zirga ya je ya kwanta.



Kwanaki uku tsakani Sadiq ya wuce Egypt, kwananshi ɗaya acan suka dawo tare da Rahama.
Ranar kusan kwana suka yi suna hira irin ta ƴan uwa.

Washe gari da safe dukkansu ukun suka shiga kitchen dan haɗa breakfast, sosai Sadiq ke
zaƙewa wajen baiwa ƙannen nashi kulawa.
Bayan sun gama breakfast ne kuma suka hau aikin gyaran cikin gida har zuwa farfajeyar gidan,
gabaɗaya Zarah da Rahama sun yi kaca-kaca da ruwa sun jika ko ina wai suna baiwa fulawoyi
ruwa har abun ya koma suna watsawa juna.

Yana daga ɗakinshi ya ke hangosu ta window, sosai ƙaunar da suke wa juna take matuƙar
burgeshi musamman yadda yaga dukkansu suna baiwa alawar zuciyarsa kulawa, murmushi
yayi mai sauti saboda wani abu da ya tuna. Safwan kenan.

Wuni suka yi ranar cikin nishaɗi da kulawa da juna, yadda suke nuna ƙaunar juna kowa ya
gansu sai sun bashi sha'awa.

Kamar wacce aka yiwa baki tunda Zarah ta kwanta bacci bata tashi ba, kasancewar tana fashin
sallah shiyasa Rahama bata tasheta ba lokacin sallar asuba.
Sai wajen ƙarfe goma na safiya ta farka, da wasu haɗaɗɗun greeting cards ta fara yin tozali, da
hanzari ta miƙe saboda tunawa da ta yi yau ranar zagayowar haihuwarta, cards ɗin ta janyo
guda uku ta fara karantawa cikin jindaɗi sai dai guda ɗaya ya matukar tafiya da ita kuma ga
alama ya fi duka kyau da tsada, duba suna ta yi taga an rubuta SMH bata gane ko na wanene
ba tunda na Sadiq da Rahama duk sun saka sunansu bata wani damu ba ta miƙe ta nufin zuwa
toilet, idonta ya sauka akan dressing mirro wani kwali ta gani dan haka ta yi saurin isa ta buɗe
shi, wata haɗaɗɗiyar arabian gown ne a ciki kalar pink mai matuƙar kyau dai wani takalmi
golden.
Da hanzari ta shiga bayan gida ta watsa ruwa ta fito dan tasan ƴan uwanta na jiranta.
Simple makeup ta yi a fuskarta sannan ta saka doguwar rigar wacce ta mata kyau matuƙa, veil
ɗin rigar ta naɗa akanta sannan ta nufi falo.

Da alamun mamaki a fuskarta ganin falon gabadaya duhu mamaye shi, bata gama mamakin ba
kuma haske ya gauraye falo ta re da suwar happy birthday to you, ido ta waro tana kallon
mutanen falon cikin mamaki harda maƙotansu da matayensu, tuni ta ƙara rudewa ganin Jiddah
da Saleem a gefe ɗaya, hawayen da ake kira na farin ciki ne ya sauko a fuskarta. Da sauri
Rahama ta zo ta ja ta zuwa gaban tebur din da aka aje ƙaton cake kalar pink da fari, hannun ta
kai da nufin yankawa Rahama ta yi saurin riƙe hannun, kallonta ta yi da alamun tambaya bata
amsa mata ba sai ma zura hannayenta da tayi ta rufe mata idanu, kusan sakan goma sannan ta
buɗe mata, sai da ta razana saboda abinda ta ga ni ta kuma ji, Safwan ne a durƙushe gabanta
riƙe da ɗan ƙaramin akwati na zobe yana faɗin
"Will you marry me (Shin zaki iya aurena)"

Sam ta rasa a wata duniyar ta ke ciki, tana fata idan mafarkine ta yi gaggawar farkawa, kallon
gefe da Jiddah ke tsaye ta yi, gira ta ɗaga mata tare da kashe ido ɗaya sannan ta rungumo
Saleem a jikinta. Abin yaso baiwa Zarah dariya matuƙa yadda Jiddan ke yi kamar za'a kwace
Saleem din.
Bata san ya akayi ta gyaɗa kai ba sai ji tayi kawai an zura mata zobe a hannu.
Tafi suka yi gabaɗaya sannan ne ta yanka cake ɗin.
Ƙaramin shagali suka yi sannan kowa ya watse sai su Jiddah da zasu wuce Dubai da daddare
ita da Saleem zasu je siyayyar haihuwa.

Cikin ƙanƙani lokaci soyayya mai ƙarfi ta ƙullu tsakanin Safwan da Zarah, har wani lokacin suna
mamakin junansu ta yadda basa iya ɗaukan awanni ba ta re da sun ji muryar juna ba, idan suka
zauna hira kuwa da ƙyar Sadiq ke lallaɓa Safwan ya tafi gida ya kwanta idan dare ya yi, da ya
shiga gida kuma zai kirata su ɗaura daga inda suka tsaya. Harta su Daddy sai da suka san da batun soyayyar nan domin Safwan dai ya yi wa Abbansa
maganar Zarah inda shi kuma ya aika Waziri da wasu wakilansa har garin Gombe su ka
tambayowa Safwan auren Zarah tare da bada kuɗin nagani inaso da goron tambaya kamar
yadda ya ke a al'ada ya tanadar.
Yau ma kamar kowani lokaci a ƙarshen mako sukan wuni tare ne harta ayyukan gidan tare suke
yi, su na yi wani lokacin Sadiq na tsokanar Safwan mijin Hajiya, don shi Sadiq ba shi da wani
girman kai irin na Yayu akan ƙannansu musamman idan su na soyayya da abokansu, ya na
zama su yi hira sosai wani lokacin idan su ka yi faɗan masoya ma shi ya ke sasanta tsakaninsu
idan bayanan kuma sai a kira Rahama ta video ta shirya tsakaninsu.

Yana zaune saman durowar kitchen ita kuma tana gaban fanfo tana wanke-wanke, hirarsu su
ke yi cikin nishaɗi kamar waɗanda suka ɗauki tsawon shekaru su na soyayya. Tufa ɗin da ke
hannunshi ya gutsira sannan ya ce

"Mrs. Safwan kinsan me ya sa ban takura anyi auren nan da wuri ba.?"

Ba ta re da ta juyo ba ta ce

"Sai ka fada"

"Saboda inaso ki gama ƙarasa wannan karatun don idan na aure ki nasan ba zaki nutsu ki yi
karatun nan ba saboda yadda zan ruɗa ki da salon soyayyata sai kin daina fahimatar kowani
zance idan ba nawa bane."

Dariya ta yi sannan ta juyo ta naɗe hannayenta a ƙirji tana kallon shi ta ce

"Saboda ina da ƙaramar kwakwalwa koh.?"

"A'a saboda soyayyar da zan nuna miki ta musamman ce kina buƙatar cikakkiyar nutsuwa don
fahimtarta."

"Toh Allah ya kaimu lokacin yasa kada ka canza abinda ka fada."

"Bazan canja ba saboda ina miki ƙaunar da bana yiwa kowa irinta a duniyar nan."

"Uhmm" ta ce cikin murmushi sannan ta juya ta cigaba da wanke-wanke suna hira har ta gama
ta gyara gurin.
Sai a lokacin ya sauko daga inda ya ke zaune ganin ta fara hada-hadar ɗaura abincin rana,

kamar ko da yaushe idan yana nan yakan taya ta da ƙananun aiyuka kamar su yanka albasa,
fera dankali, bare maggi da sauransu a haka har su gama girkin.

A haka Sadiq ya zo ya tarar da su a kitchen ɗin ya kalli Safwan ya ce

"Mijin Hajiya zo ka min wani aiki a falo."

"Haba babban Yaya baka ga ina taya ta aiki bane." cewar Safwan.

"Little ba shi umarni kinji abu zai min mai mahimmanci."

Dariya Zarah ta yi ta ce

"Ba ni na riƙe shi ba fa, jeka ta ya shi aikin mana"
Hannunshi Sadiq ɗin ya kama su ka fice ta re suna dariya.

Haka kullum suke kasancewa cikin farin ciki yayinda soyayyarsu ke da ɗa ƙaruwa.

Kwanci tashi asarar mai rai a haka kwanaki ke shuɗewa har suka zama watanni.


NIGERIA

A watannin da suka biyo baya duk wanda ya kalli M.J zai gane hankalinshi ba'a kwance ya ke
ba gabaɗaya ya rame ya yi baƙi, abubuwan da Hajara ta ke masa ya ƙaro musamman yanzu da
take ɗauke da juna biyu babu kalar fitsarar da bata yi mishi idan ya nemi ya tanka sai ta yi
iƙirarin zata zubda ciki, gashi Allah ya ɗora mishi son cikin sosai musamman da su Daddy su ka
sassauta mishi tunda suka ji labarin Hajaran na ɗauke da juna biyu, a gefe guda kuma tunanin
Zarah da ke addabar zuciyarsa duk yadda ya so dainawa amma ya kasa nan ya fahimci cewa
sonta ne ya mishi mugun kamu sai dai yana ƙoƙarin ɓoye hakan don har a wannan lokacin bai
daina zargin cewa tana bin maza ba musamman idan yayi la'akari da yadda ya ganta a hotel ta
re da wanda ba muharraminta ba.

Yana zaune a office ɗinshi cikin tunanin da ya saba ya ji ana kwankwasa kofar shigowa, umarni
ya bada aka shigo sakatariyarsa ce riƙe da takarda a hannunta ta ce

"Yallaɓai wannan saƙo ne aka kawo ance a baka."

"Daga wanene saƙon?"

"Bai fada ba yallaɓai ya ce dai a baka ne yana sauri zaku yi waya."

Kan tebur ɗin ya nuna mata ta ajiye daga haka ta fice, hannun ya zura ya janyo takardar ya

buɗe, wata irin zabura ya yi tare da miƙewa tsaye daga zaunen da ya ke.

Zufa ce ta karyo masa lokaci guda wasu hawaye masu ɗumi suka sauko daga idonshi, sambatu
ya fara yana kiran sunan Hajara. A haka Abdallah ya turo ƙofar ofishin ya shigo ya same shi
cikin wannan yanayi, a kiɗime ya ke tambayarsa abinda ya faru. Bai iya magana ba illa takardar
da ya miƙa mishi cikin zubda hawaye.
"Innalillahi wa inna ilahi raji'un." shi ne abinda Abdallah ke maimaitawa bayan ya karanta abinda
ke cikin takardar...✍


*BY*
*JASMINE*

*ASP ZARAH*‍✈️

*BOOK 2*

*Page 10*


Fuska ba walwala ya ɗaga ido yana kallon M.J dake dube-dube a kan tebur ya ce

"Me kake nema ne haka.?"

"Abdallah gidan zanje naji ba'asi wallahi yau kome za'ayi sai na ci mutuncin Hajara a garin nan."

Duk da suna cikin wani hali amma hakan bai hana Abdallah dariya ba ganin yadda gabaɗaya
M.J ya birkice yana neman key ɗin mota bayan ga key din nan a gefen tebur amma tashin
hankali bai barshi ya gani ba, kai ya kaɗa sannan ya ce
"Muje na sauke ka a yadda kake din nan bai kamata kayi tuƙi ba."

"Muje muje Abdallah."

Fita suka yi M.J a gaba tamkar zai tashi sama, a haka suka shiga motar Abdallah ya tada suka
ɗauki hanyar zuwa gidan M.J din, Abdallah ne ya kalleshi ya ce

"M.J ya akayi haka ta faru har yake ƙoƙarin maka ka a kotu.?"

"Bansani ba Abdallah, innalillahi wa inna ilaihi raji'un, a gidana ace har matata na ɗauke da cikin
wani amma bansani ba. Wallahi sai yanzu na tuna sam bai kamata ace cikina bane don yanzu
ne cikin ya shiga wata uku kuma rabona da ita na jima sai lokacin da aka ce tana da cikin nan
sam zumuɗi bai barni nayi lissafi ba." M.J ya fada idonshi na zubar da kwalla.

"Ishara ce Allah ya nuna maka Jawwad shiyasa ake so mutum ya dinga kyautata zato akan ɗan
uwansa."

"Me kake nufi ne.?"

"Abubuwan da kake zargin Zarah da su ne Allah ya tabbatar maka akan matarka."

"Ba zarginta nake ba tabbatarwa nayi."

Murmushi Abdallah ya yi wanda iyakarsa baki sannan ya ce
"Rana na tafe, sai dai kamar yadda nayi alƙawari duk randa ka gane gaskiya kada ka neme ni
don taimaka maka. Yanzu ya za'ayi da batun Hajara.?"

"Abdallah zanje na tuhumeta sai ta faɗa gaskiya matuƙar da aurena ta ke bin wasu mazan
wallahi sai na rabu da ita bayan na wulaƙanta ta, har ni za'a turowa takardar sammaci zuwa
kotu akan bana kula da cikin da wani ƙato yayi har ana ikirarin idan wani abu ya same shi sai
anyi shari'a da ni."
"Uhmm" kawai Abdallah ya ce daidai lokacin da yayi horn a gaban gidan M.J mai gadi ya buɗe
masa ya shiga da motar, ko parking bai gama tsaidawa ba M.J ya fita a sukwane yana faɗin
"Jirani ina zuwa."

Rai ɓace ya shiga falon ganin bata nan ne yasa ya nufi hanyar ɗakinta, a fusace ya banka ƙofar
ɗakin.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ya shiga maimaitawa, tashin hankali da ba'a saka masa rana,
Hajara ce da wata babbar mata a kwance kan gado haihuwar uwarsu suna aikata masha'a.
Sulalewa yayi a ƙasa ya rasa ma abinda zaiyi, sai lokacin suka farga dashi da hanzari suka
miƙe matar ta rarumi kayanta zata gudu aikowa ya miƙe ya rufe ƙofar ɗakin sannan ya koma ya
zauna, sun ɗau mintuna a haka lokacin duk sun maida suturunsu miƙewa yayi ya kwance belt
ɗin da ke jikinshi ya shiga dukansu ba ji ba gani tun suna ihu da neman taimako har muryarsu
ta daina fita, sai da ya tabbatar sun galabaita sannan ya tsagaita cikin fushi ya ce

''Kinci amanata Hajara wallahi yau bazan barki ba sai kin gayamin abinda na miki har kika nemi
ƙuntata min haka, dama badan Allah kika aureni ba. Bayan zina har ƴan uwanki mata kike bi, ke
kuma ki tashi ki ficemin daga gida tun kafin na halaka ki."

Da mugun sauri ta miƙe ta bude ƙofar ta fita, karo suka yi da Abdallah wanda tun sanda suka
fara ihu ya jiyo su shine ya shigo dan ganin abinda ke faruwa, sai yanzu da M.J ya yi magana
ya fahimci dalilin dukan na su. Kaɗa kai ya yi cike da takaici ya shiga ɗakin don fito da M.J kar
ya yiwa Hajara wani illah. Da ke Hajara matsoraciya ce gashi kuma ta ji jiki a hannun M.J tuni ta fara sakin zancen da
batasan tana furtawa ba, tiryan-tiryan ta labarta mishi dalilin da ya sa ta aureshi har zuwa ranar

da aka zo har gida aka duki Zarah, ashe da ita aka haɗa baki ta buɗe musu ƙofar falon dan ta
kasance automatic ne ba da key ake buɗewa ba. Cikin kuka ta cigaba da cewa

"Ni bansan me ta yi musu ba, kawai sun same mu ne suka faɗa mana cewa ta yaudari wani da
ke musu aiki har tayi sanadin da aka kamashi a garin bauchi shiyasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login