Showing 1 words to 3000 words out of 25074 words
[10/16, 7:54 PM] +234 816 616 9254: [29/07 3:49 am] .:
*AUTAR HAJIYA*
®NWA
_ZEE MMN KHADY_
_Page_ 1-5
_Amincin Allah ya tabbata ga duk wanda ze karanta wannan littafi nawa, duka da ma wanda
besamu damar karantawaba_.
✍ Kwance take kan d'an madai-daicin gadon mahaifiyarta, hannunta ri'ke da waya, kirar tecno
H³ wani game take me matukar sanyata nishad'i, Ta tattara hankalinta duka ya koma kan wayar.
Muryar Hajiya ta tsinkayo tana kwalla mata kira, da sauri tasanya pause a game d'in domin
zuwa kiran mahaifiyar ta.
"Hajiya gani, tafad'a bayan ta d'an rissina gabanta, Alamar girmamawa, matar da takira da
Ahjiya ta d'ago ta kalleta, tace "ki shirya inaso in ayke ki yanzu, tace "ina? Tace "kije ki shirya
mana koma inane ay zakiji.
'Daki tanufa ta cire kayan jikinta, tayi d'aurin kirji, sannan, tafito ta cika bokiti da ruwa ta nufi
toilet.
Bayan ta she'ka wanka, tafito tanufi d'akin dai daya kasance nan ne na mahaifiyarta Wanda da
Alama itama nan take, kwandon kayan shafarta ta d'auko ta ajiye gabanta, Wanda babu abinda
babu aciki, tafara d'and'asa kwalliya, takai kimanin awa d'aya tana kwalliya, bayan tagama ne ta
tashi' tanufi wadrope ta dauko wata green d'in atamfa, me zanen ganye golden, nd yellow,
wacce akayima ado da yellow Codeless d'inkin zamani riga da zani pieces.
Bayan tasaka kayan, sun kuma kar6i jikinta, dan ba 'karamin kyau saukayimata ba, sun fiddo da
duk wata kya'k'kyawar halitta da Allah yabata.
Fara ce, Amma ba irin tass d'innan ba, farinta dai-dai misali, tanada manyan idanu Wanda
akoda yaushe idan ta kalleka, sai kayi tinanin kashe maka su takeyi, amma ba haka bane haka
yanayin kallonta yake, ga dogon hanci Wanda ya 'kara fito da anaifin 'kyawunta, bakinta d'an
karami, hakoranta farare tas, sai wushiryar data 'kara fito da kyawun su, gefen kumatunta ko
magana take yana lotsawa, barantana kuma idan tayi dariya, wannan dimple ba karamin 'kara
fiddo da 'kyawunta yake ba.
Bayan tagama shirinta tsaf, ta dauko hijab d'inta, kalar golden, ta Sanya tiare ta dauko ta feshe
jikinta dashi, sannan ta d'auko plat shoes shima kalar golden, ta Sanya, tanada tsayi shiyasa
bata damu da takalmi me tudu ba.
Fitowa tayi tsakar gida, inda mahaifiyarta ke jiranta, tace "gani Hajiya.
Hajiya tace "yauwa dama gidan Maman Ummi zakije, kicemata ya maganar adashi, yanaji shiru,
ko har yanzu, ba'a gama had'a kud'in ba?.
Kuma kice ina gaisheta, sannan ta d'auko naira Hamsin tabata, Anshi ki hau napep, ta kar6a
sannan tafice Daga gidan, Hajiya namata fatan zuwa lafiya da kuma dawowa lafiya.
Taje gidan ayken harta, Isar da sa'kon takuwa yi sa'a dan angama had'a kudin saboda haka aka
bata, dama kwasar adashine na Hajiya.
Kasancewar hajiyar kud'in zuwa kawai tabata, can kuma gidan dataje, Mmn Ummi tabata, kud'in
napep d'in Amma ta'ki kar6a, saboda haka a 'kafa ta tafi, tana tafiya tana zancen zuci, tayi
matu'kar danasanin tahowa a 'kafa domin yanda ta lura da duk Inda ta gifta maza ke binta da
ido.
Azuciyarta tace "Allah ya taimakeni hijab na Sanya, da nabani.
✍Zee Elkasem
Mmn khady.
[29/07 4:33 am] .:
*AUTAR HAJIYA*
®NWA
_ZEE MMN KHADY_
_Page_ 6-10
✍ Da sallama tashigo gidan, kitchen ta iske Hajiya, tana faman dafa masu abincin rana, Hajiya
tafito Daga kitchen d'in tana mata sannu da dawowa.
Ta fiddo da kud'in ta mi'ka mata tace "gashi kuma Mmn Ummi tace tana gaisheki, kuma tace
"dan Allah kiyi hakuri wallahi mutanen ne sai Ahankali,
Hajiya ta kar6i kud'in cikin farin ciki, ta kirga su dubu tamanin dai-dai, sannan ta kalli Autar
Hajiya tace, "to Auta ga kud'in adashi sun samu yanzu ki gaya mani dami-dami kike bu'kata,
kinga gobe idan nafita gurin ayki sai in sawo maki.
Autar Hajiya tayi murmushi, taji dad'i har cikin ranta, game da yanda iyayenta suke nuna
tsantsar so da Kauna da kuma kulawa a gareta, dan ita iya saninta tinda ta taso gidan, bata
ta6a neman wani Abu tarasa ba, duk da iyayenta ba masu kud'i bane Amma sunada rufin asiri,
domin mahifinta yana ayki, mahifiyarta ma tana ayki.
Da misalin 'karfe hud'u na yamma, Hajiya suna zaune tsakar gida itada autarta suna shan iska,
kasancewar yau Alhamis ba'a zuwa islamiyya.
wani yaro yayi sallama, bayan an amsa Mashi, ya gaida Hajiya, sannan yace "wai ance ana
sallama da Zainab a waje, Hajiya tace je kace waye, yaron yaje ya tambayo sannan ya dawo
yace, "wai yace ba'ko ne, dan Allah ta taimaka tafito, Hajiya tace jeka kace tana zuwa.
Tayi saurin tashi daga kwancen datake, tace dan Allah Hajiya kice baninan, ni wallahi banison
wannan kiran, nifa ban ma San ko wayeba, Hajiya tace "to kifita mana sai kiga kowaye, haba
zainabu na wulkanci bashida kyau, kifita ko gaisawa kuyi sai ki dawo ba sai kin dad'e ba.
Hijab dinta ta Zara, ta Sanya, wacce tsawonta ya kai mata iya gwiwa, sannan ta fita.
Jingine yake jikin motarsa, baki ne amma ba kirin ba, yanda 'kya'k'kyawar fuska, yanada saje
Wanda ya'ara fito da kyawunsa, gajere ne dan baza'a ta6a sashi sahun masu tsayi ba, zai kai
kimanin shekara talatin da takwas a duniya.
Tinda ta fito ya zuba mata, idanu yana kallonta, harta 'karaso, ta gaidashi, ya amsa cikin fara'a,
Daga nan bata 'kara magana ba, sai shi yacigaba da magana.
"Wato Zainab, hausawa sunce maso tsuntsu shike binsa da jifa, a gaskiya tinda naganki naji kin
kwanta min arai, kuma ba kome ya'kara karkatar da Hankalina garekiba illah kamun kanki, da
kuma kaywun surar da Allah yayi maki, nidai tafe nake da 'ko'kon barata, idan kin Amice aurenki
zanyi dan ba maganar wasa ta kawoni anan ba.
"Au sorry nacikaki da saurutu ban ko fad'a maki sunana ba, sunana "Adam kuma ni d'an nan
cikin garin katsina ne, ina zaune a Unguwar Al'kali da iyalina, inada mata d'aya da yara ukku, da
fatan zaki kar6i soyayya ta.
Kafin tayi wata magana ta hango babanta tafe kan mashin d'insa saboda haka bata tsaya bashi
amsaba ta shige gida.
Nan Baban nata ya Tarar da Adam kofar gida, bayan sun gaisa, yayi Mashi yan tambayoyi.
Zee Elkaseem
Mmn khady.
[29/07 9:30 am] .:
*AUTAR HAJIYA*
®NWA
_ZEE MMN KHADY_
_Page_ 11-15
✍ Koda ta shigo gidan d'aki ta wuce, ta d'auki wayarta tacigaba da danne-danne, azahiri idan
ka ganta wayar take dannawa, Amma zuciyarta cunkushe take da tinani barkatai.
Itako a tsarinta babu Auren me mata, saboda ita mace ce me tsananin kishi, yaushe zata yarda
ta auri namiji me aure, Amma wannan mutumin yama raina mata yawo, to wallahi, da matar shi
hada 'ya'ya ukku kuma sannan yace yana so ya aureta, ya Allah tsareta da aurensa, wani irin
mugun hauhinsa taji ya rufeta, itako da beda mata da zata iya daurewa ta Auresa, kidan
saboda yanda babanta ya matsa akan yanaso tayi aure.
Da sallama mahaifin nata ya shigo, Hajiya dake zaune tsakar gida ce ta Amsa sallamar, sannan
tayima me gidan nata sannu da zuwa, bayan ya amsa da "yauwa" d'akinsa ya wuce, Hajiya
tanufi gurin ajiye ruwa tacika boket da ruwa takai toilet, sannan ta iske me gidan nata d'akinsa
tace "Alhj ga ruwan wanka can na kai ma kewaye, yace "to bari inje inyi wankan, "Amma kafin
in Shiga inaso in tabayeki, tace "to Alhj inaji, yace "Wannan yaron dana gani 'kofar gida yazo
gurin Zainab tin yaushe yake zuwa, Hajiya tace "yau ne farkon zuwanshi, da Autar ma tace
bazata fitaba dan bata sanshiba, nice nace tafita taji me ke tafe dashi,
Alhj yace "kin riga kinsan banison inga yarinya tana tsayawa da samari barkatai, saboda haka ki
gaya ma ita Zainab d'in idan har tana son wannan yaron to tasanar dashi yaturo da
magabatanshi, kafin yacigaba da zuwa gurinta.
Hajiya tayi murmushi tace, "Haba Alhj Daga zuwa d'aya sai ace yaturo kamar muna Neman
maraba da d'iyar, ay dole dai su samu su fahimci juna kafin a kai ga maganar iyaye, yace " kidai
gaya mata idan tana sonshi ya turo magabantashi, idan kuma bata sonshi kada in'kara ganinsa
'kofar gidannan, "kuma da kikace ba Neman maraba ake da itaba, so kike mu tasa ta gaba
muyita kallonta, tinda tagama makaranata, kuma islamiyya sunyi sauka ai Alhamduliilah, Aure
kawai yarage muyi mata hankalinmu ya kwanta, haka suka gama tattaunawa sannan ya fito
yanufi kewaye, dan yin wanka, ita kuma tanufi d'aki inda Autar Hajiya take tana ta tinane-tinane
kala-kala.
Da sallama ta shigo d'akin, ta isketa kwance, kamar me bacci, amma ba baccin takeba' tinani
ne kala-kala acikin zuciyarta, nan Hajiya ta bayyana mata yanda sukayi da babanta, na maganr
ba'kon datayi yau.
Cikin tsananin firgici, ta dafe 'kirji tace "wallahi Hajiya bani sonshi, ni banma sanshiba, yau ne fa
kawai nafara ganinsa, "Dan Allah ki gaya ma baba abar wannna maganar, murya saukaji kamar
Daga sama yana cewa, "ba saita gaya maniba inaji, waike zainabu yaushe zakiyi hankali, ki
nutsu ki fitar da miji kiyi aure, yaufa shekara biyu kenan da gama makarantarki, Amma ko
kad'an bakiso ayi maki maganar aure, to kisani bazan sanya maki ido ba kina zaune, muddin
idan nagaji da zamanki zan za6a makin duk Wanda naga ya kwanta min arai.
Wasu hawaye masu zafi suka zubo, kan kumatunta, tace dan Allah Hajiya ki gayama baba
wallahi banison miji me mata, wallahi zan iya auren Kowa amma banda me mata, Hajiya
tacigaba da rarrashunta tana cewa, haba auta, saboda me bakison me mata, mace nawa ta
Auri me mata ukku ma itace cikon ra hud'u kuma ta xauna lafiya.
Wani kululun ba'kin ciki taji ya tokare mata zuciya.
Azuciyarta tace _Ni in auri me mata ukku ay 'kila kafin a kaini zuciya ta buga namace saboda
tsananin kishi_
_kome mata d'aya bazan iya aureba_
Wani sabon kuka ta faahe dashi.
Zee Elkaseem
Mmn khady
[10/16, 7:54 PM] +234 816 616 9254: [29/07 7:16 pm] .:
*AUTAR HAJIYA*
®NWA
_ZEE MMN KHADY_
_Page_ 16-20
✍ washe gari haka Autar Hajiya ta tashi jikinta sukuku, a zuciyarta tana ma Adam Allah ya
Isah, yanzu gashi sanadin zuwanshi, yajawo mata babanta ya tado da maganar tayi aure,
Wanda a da ya lafa da maganar, kuma shi gashi yanada mata barantana ta auresa, itako yanda
babanta ya matsa mata akan tafito da miji wallahi da Adam bayada mata data auresa, saboda
Adam beda makusa, Amma kuma ya cuceta daya furta mata kalmar "So" Alhalin yanada mata,
_Allah ya isah tsakanina da kai Adam_ ta Furta afili tare da zubar da wasu guntayen hawaye.
Ranar haka ta kasance ita d'aya cikin gida, tinani kala-kala ya addabi zuciyarta, kasancewar
yau litinin Hajiya tana gurin ayki, tana aykine a general hospital katsina, yayinda babanta yake
ayki, ma'aikatar agric, fannin dabbobi.
Da sallama wani yaro ya shigo, ta amsa masa sallamar, sannan yace auta ana sallama dake
waje, tanajin haka bata tsaya tamabayar waye me sallamar ba tace kace ina zuwa, ko ba
tamabaya tasan be wuce Adam, takoyi matu'kar farin cikin zuwansa dai-dai wannan lokacin,
yanzu ko zata fita ta bige masa warning.
Hijab ta Sanya, sannan ta zari silifas d'inta na wanka tanufi kofar gida.
Shine kuwa, Wanda take tsammanin, jingene yake jikin motarsa, yauma yayi shiga ta
musamman, yayi masifar kyau, cikin gadara da tsiwa ta isa gabanshi, yau ko gaisuwa be samu
arzi'kinta ba, ta tsaya gabansa tare da d'aure fuska kamar bata ta6a dariya ba.
Cikin fara'a yake magana, "sannu da fitowa gimbiyar mata, ina fatan dai ban takura maki ba
danazo dai-dai wannan lokacin, wallahi nakasa daurewa ne da rashin ganinki.......
Hannu ta d'aga mashi, tare da yimashi magana cikin d'aga murya, "dakata! Adam kake ko
waye, inaso in gaya maka ka fita hanyata, dan wallahi tallahi kaji rantsuwar musulmi wacce
daga ita babu wata, to ko duniya zata rage daga ni sai kai bazan aure kaba.
Cikin tsananin tashin hankali, da mamakin jin kalamanta, Wanda koda wasa beyi, tinanin jin
wannan daga gareta ba, a yanda ya d'auketa yarinya, me hankali, da nutsuwa ga kuma uwa
uba ilimi, na addini dana zamani.
Cikin sanyin jiki Adam yafara magana, yace "Zainab saboda me kika yanke wannan
tsatstsauran hukuncin a kaina,? Ko kinyi bincike ne kingano wani aybu da nike dashi?.
"Ko d'aya tafad'a, illah dalili d'aya shine bazan iya auren me mata ba, "idan kuwa ka nace akan
saika aureni to wallahi saidai akai gawata gidanka, dan zan iya shan guba in kashe kaina, na
tsani kishiya, hakan ne yasa duk Wanda ze zomin da maganar aure bamu dai-daitawa, saboda
mafi yawancin masu zuwa Neman aurena masu auren sunfi samarin yawa.
Bata jira abinda ze fad'aba tashige gida,zuciyarta cunkushe da abubuwa da dama.
Wani kululun ba'kin ciki ya tsaya ma Adam azuciya, yama kasa matsawa daga Inda yake, yakai
kimanin minti talatin tsaye a gurin sannan Daga bisani ya shiga motarsa ya tafi, jikinsa ba laka
ko kad'an.
Tana shiga gida, ta wuce d'aki kan gado ta fad'a ta fashe da wani irin kukan takaici, kuka take
baji ba gani.
Daga waje kuma anata sallama, amma batajiba, saboda kukan yinsa take tsakaninta da Allah.
Jitayi ba'ada niyyar amsa sallamar data dad'e tanayi, saboda haka kutsa kai tayi cikin d'akin,
dan tanada tabbacin Hajiya bata nan.
Autar Hajiya datayi nisa cikin kuka, sai ji tayi an dafata, da sauri ta d'ago da manyan idanunta
da suka canja zuwa ja saboda tsananin kuka, sadiyya tagani wacce batasan lokacin data shigo
gidan ba.
Cikin tsananin damuwa sadiyya, ke magana, "kawata, meya faru? Naganki cikin wannna
yanayin.
Bata tanka mataba, illah cigaba datayi da kukanta.
Zee Elkaseem
Mmn khady
[30/07 7:37 pm] .:
*AUTAR HAJIYA*
®NWA
_ZEE MMN KHADY_
_Page_ 21-25
✍ Sai da tayi kuka me isarta sannan ta d'ago ta kalli sadiyya, wacce ta kasance 'kawa ce
gareta, tin suna yara kuma bata da wata aminiya data wuce ta.
Nan tabata labarin duk abinda yafaru, tin zuwan Adam dakuma Abinda babanta ya fad'a na
cewa idan bata fito da miji ba ze za6a mata duk wanda yaga yayi masa.
Sadiyya ta numfasa, sannan tace "wallahi Autar Hajiya kinada problem, ni narasa gane kanki,
kwata-kwata tinda nake ban ta6a gani ko jin me irin wannan tsatstsauran ra'ayin ba irin naki, be
kamata ace kin kartake akan ke bazaki auri me mata ba, ki duba kiga kwanaki yanda kukayi
soyayya da Bashir kamar bazaku ta6a rabuwa ba, ba irin tsantsar soyayyar dabaki nuna masa
ba, Amma lokaci d'aya kika bad'e ido toka kikace baki sonshi, dan kingano yata6a Aure kuma
ya rabu da matar, wai kina gudun kada wata rana yace ze maida ita.
Auta ta numfasa sannan tayi wani guntun murmushi Wanda yafi kuka ciwo, tace "hum sadiyya
bazaki ta6a ganewa ba wallahi duk lokacin da wani namiji yace yana sona daya furta min
yanada aure jinake kamar in kashe kaina, dan na kwammace na mutu dana auri me mata.
Sadiyya tace "to Allah kyauta, Allah rage maki wannan zafin kishin naki, tace Ameen ni kaina
ina yawan yin wannan addu'ar dan wallahi wani lokaci abin har tsoro yake bani.
"Wai ina khaleed ne? shiru naji kin daina zancensa, ko shima yanada matar ne?.
Auta tayi murmushi, wanda yasa har kumatunta suka lo6a, tace "Hmm khaleed mutanen Sudan,
ay yana can karatu, kawai yasa gaba, ni inaga kila yanzu ya manta dani, shekara hud'u fa
kenan rabon da muga juna, kuma tinda yatafi ko waya bamu ta6a yi dashi ba, Amma kuma ni
nasan har in mutu bazan ta6a son wani d'a namiji kamar yanda nake sonshi ba.
Sadiyya tayi murmushi, tace tabbas kunyi tsantsar soyayya da khaleed, kuma bani tinanin
shima ze iya mantawa dake, kuma naji ajikina khaleed shine mijin dazaki aura.
Wani farin ciki ya rufe Autar Hajiya, dan tinda take duniya bata ta6a son wani namiji ba, irin son
datakema khaleed, Cikin jin dad'in maganar sadiyya tace "Allah ya tabbatar min da hakan, Allah
sa khaleed yazama mallakina ni kad'ai batare daya had'ani da wata jaka ba.
Sadiyya tayi dariya, cikin tsokana tace au amaryar taki kike kira jaka, Auta ta kaimata duka
cikin wasa tace "bani son iskanci, ki dainamin wannan wasan khaleed nawa ne ni d'aya Kedai
kawai ki tayani addu'a Allah sa be manta daniba, sadiyya tace "to Allah sa be manta dakeba
kuma Allah sa yana dawowa musha biki, su duka suka sa dariya, haka suka sha firarsu, sam
Auta ta manta da wani ba'kin ciki datake tattare dashi, jitake kamr har khaleed d'inma yadawo
an d'aura masu aure saboda tsabar farin ciki.
Sai gab da Hajiya zata dawo sannan sadiyya tayi haramar tafiya, Auta tayimata rakiya, tare
dayimata Al'kawarin zuwa gidansu ranar Friday.
Zee Elkaseem
Mmn khady
[10/16, 7:54 PM] +234 816 616 9254: [31/07 10:47 am] :