Showing 9001 words to 12000 words out of 25074 words

Chapter 4 - Autar Hajiya Book Compelet By Zeey Maman khady

20 Jul 2026

73

ha'kuri ta koma ta 'kiya, dole tasa ya d'auketa a motarsa dan
kada yabarta tatafi yanda ranta yake 6ace wani Abu yaje yafaru da ita a hanya.

Haka aka tashi partyn Kowa na jimamin abinda ya faru, wasu na ganin laifin Fadila, wash na
ganin laifin khaleed,wad'anda kuma suka fahimci yanda abun yake laifin Autar Hajiya suke gani.





Mmn khady
[03/08 10:51 pm] Zee Elkaseem:

*AUTAR HAJIYA*



®NWA



_ZEE MMN KHADY_


*_Page_* 76-80




✍ washe Gari da misalin karfe biyu na rana, dubban mutane suka sheda d'aurin Auren khaleed
da Amarensa, Zainab _(AUTAR HAJIYA)_da Fadila.

Da misalin 'karfe hud'u na yamma aka fito da Auta dan kaita gidan mijinta, bayan an kaita d'akin
mahifinta yayi mata nasiha me ratsa jiki, da kuma yimata nuni da tayi ha'kuri, dan duk Wanda
yayi ha'kuri duniya baze ta6a ta6ewa ba.

Bayan an fito da ita daga d'akin mahaifinta aka wuce da ita d'akin Hajiya, itama Hajiya tayi mata
nasiha me ratsa jiki, 'karfe hud'u da rabi aka fito da Auta aka sakata mota, ba abinda take sai
kuka, da kyar aka rabata da hajiya,

A unguwar lay out dake cikin garin katsina, misalin 'karfe biyar suka isa gidan, can suka iske
'yan'uwan khaleed dana Fadila dan ita tin 'karfe hud'u aka kawota.

Bayan sallar magrib ne aka fara gabatar da walimar da 'yan'uwan khaleed suka shirya, wanda
aka gayyato shahararriyar malama wacce zata gabatar da wa'azi kan zaman aure da kuma
nasiha ga Amare, wato malama *AMINA ALIYU MOHM'D (BINTUSH~SHEIKH)*

Bayan malama ta bud'e taro da Addu'a, tayi wa'azi akan ha'kuri sanna tafara nasiha ga Amare
kamar haka: "Alhamdulillahi Allah Kaine abin godiya, daka azurtamu da rai da lafiya, bayan
wa'azi da nayi akan ha'kuri yanzu kuma inaso inyima Amare nasiha akan zaman Aure, Wanda
shima dai ha'kurin akeyi, yaku wad'annan Amare ina ro'konku da kada kuyi kishi irinna jahilai,
kada kuyi kishi irinna wad'anda basu san ciwon kansuba.

Kuyi kishi irinna matan Annabi Muhammad _(S.A.W.)_ Kada kuyi kishin da ze tada hankalin
mijinku, kuyi kishi Wanda kullum burinku Ku kyautatama mijinku, kunsan shi rai yana son me
kyauatata mashi, sannan daga 'karshe na horeku da tsafta, Ku zamto masu tsafta kada ku
yarda mijinki yaga wata 'kazanta ajikinki ko ya sha'ki wani abu a jikinki sa6anin daddad'an
kamshi.

Haka dai malama tayi nasiha me ratsa jiki, daga 'karshe aka rufe taro da addu'a Kowa ya tafi
gida, bayan an raba sadakar Qur'an Kowa izif sittin,
Ana Allah shima malama Albarka, Akan wannan wa'azi datayi.

Da misalin 'karfe takwas na dare, gida yarage daga Auta sai 'kawayenta guda biyu sadiyya da
Zahra'u sune suka tsaya suka gyagayara mata kome suka share ko'ina suka kunna turaren
wuta, ko'ina na sashen ya bige da 'kamshi sannan sukayi bankwana suka tafi.

Itama Fadila 'kawayenta ne suka tsaya sukayimata 'yan gyare-gyaren daya dace, sai misalin
karfe tara da rabi suka bar gidan,

*TO FAH MASU KARATU GIDA YA RAGE DAGA AUTAR JAJIYA SAI FADILA• SAI
ALLAH YA KAIMU GOBE MUJI WACE IRIN WAINA ZASU TOYA*





Mmn khady
[10/16, 7:55 PM] +234 816 616 9254: [04/08 8:00 am] .:

*AUTAR HAJIYA*




®NWA



_ZEE MMN KHADY_


_*Page*_ 81-85





✍Da misalin karfe goma da minti arba'in da biyar basuji shigowar ango ba, dama kowace na
d'akinta, kasancewar gidan irin plate house ne, farko idan ka shigo get d'in ka wuce harabar
gidan akwai 'kofa waccce zata sadaka da general falo na gidan, cikin falonne 6arin dama d'akin

Autar Hajiya yake, Wanda ya kasance cikinsa akwai falo d'aya sai bedroom guda biyu, a
6angaren hagu kuma d'akin fad'ila ne, itama kamar yanda na Auta yake, sai d'akin me gida
khaleed da yake tsakiyar nasu d'akunan shikuma falo ne da bedroom d'aya, kowane da toilet
cikin bedroom d'insa, daga side din kowace kuma kitchen d'inta yake.
Fadaila ce ta kalli agogon dake manne jikin bangon d'akinta, 'karfe sha d'aya saura minti biyar
amma bataji shigowar ango ba, saboda haka toilet ta shiga ta she'ka wanka, bayan tafito ta
d'auko wani tsadadden less ta sa, bata tsaya d'aura d'ankwaliba, bayan ta tsara make-up yafa
d'ankwalin kawai tayi a kai, sannan ta fito general falo ta zauna jiran shigowar angonta.
Auta kuwa itama tana d'akinta ta gaji da jiran shigowar ango, saboda haka, itama wanka
tashiga, bayan ta she'ka wanka, ta fito, ta tsaya gaban dressing mirror tana tinanin me ma
zatayi, yanzu dai kam batada lokacin yin make-up da wannan daren, lotion kawai tashafa me
d'adin kamshi, sannan ta feshe jikinta da turarruka masu kyau, tanufi wadrope ta d'auko rigar
baccinta, ta Sanya, tsayawa tayi tana kallon kanta, yanda rigar tayi mata, sharara tamkar
batasa kome ba, dan duk illahirin surar jikinta bayyane take, tayi niyyar canja riga saboda tana
kunyar khaleed yashigo ya ganta haka, amma kuma tana jin zafi-zafin da ake a garin, saboda
haka tace bari ta d'an sha iska, idan taji shigowarsa sai ta caja, gado ta haye,ta kwanta lamo,
zuciyarta cike da tinani kala-kala, daga nan bacci yayi awon gaba da ita.

Karfe sha d'aya da rabi khaleed yayi horn Bakin get d'in gidan me gadi ya bud'e mashi yashiga,.

Fadila na zaune Falo saboda haka, da sauri tanufi d'akinta ta 'kara shafa humra, me dad'in
'kamshi sannan ta dawo falon ta zauna.
Da sallama ya shigo falon, cikin kashe murya Fadila ta amsa salamar, tare da mi'kewa ta
rugomeshi tayi Mashi sannu da Zuwa sannan ta kar6i ledar daya shigo da ita ta ajiye gefe.

d'akinsa ya nufa tabishi, acan ta had'a mashi ruwan wanka, sannan ta taimaka Mashi ya cire
kayan jikinsa ya shiga wanka, bayan ya fito daga wanka, wasu 'kananan kaya ya sanya masu
sakai-sakai, sannan ya umarci Fadila da ta tashi suje falo.

Bayan sundawo falo sun zauna, khaleed ya umarci Fadila data d'auko ledar daya shigo da ita,
ta tashi tana wani yanga tana karairaya, ta d'auko ta ajiye, sannan ya umarceta ta d'auko plate
da cup's, kitchen tanufa ta d'auko duk wani Abu datasan zasu bu'kata.

Tana fitowa daga kitchen d'in taga ba khaleed, bata kawo kome a ranta ba, tana tinanin yana
d'a'kinsa, saboda haka zama tayi tana jiran fitowarsa, amma har kusan minti talatin be fitoba,
saboda haka d'akinsa tanufa, da sallam ta Shiga d'akin amma saitaga ba Kowa ciki, sai tayi
tinanain koyana toilet ne, Bakin 'kofar toilet d'in ta kanga kunnenta bataji alamar mutum aciki ba, Ahankli ta tura 'kofar
toilet d'in nan ta'kara tabbatar da baya ciki.

Take zuciyarta ta ayyana mata inda khaleed yake, a fili ta furta *~Wallahi bazan yarda ba~*

Zee Elkaseem
Mmn Khady
[04/08 11:19 am] .:

*AUTAR HAJIYA*




®NWA



_ZEE MMN KHADY_


*_page_* 86-90





✍ khaleed kuwa a lokacin daya umarci Fadila data d'auko plate kitchen, tana shiga kitchen d'in
da sauri yanufi d'akin Auta , dan tunda yashigo hankalinsa na gun d'akinta ko zata fito amma
shiru bata fitoba.

Ahankali ya tura 'kofar d'akin kwance ya hangota kan katafaren gadonta wanda yasha shimfid'a
da wani 'katon bedsheet, da manyan filo da 'kanana.

Baccinta take cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, ahankali ya isa Bakin gadon ya tsaya yana
k'are mata kallo, kaf surar jikinta bayyane take, ga fitila d'akin kunne haske fayau ko'ina, lokaci
guda yaji jikinsa yafara kyarma, besan lokacin daya hau kan gadon ba ya rungumota jikinsa
baki d'aya yafara shafata, yakai hannunsa kan kirjinta yafara wasa da dukiyara fulaninta.
Cikin bacci tajita jikin mutum, gashi kuma anata romancing d'inta, cikin firgici ta bud'e idonta

khaleed tagani ya 'kura mata ido baya ko 'kiftawa, ta bud'e baki tana shirin yin magana, ya had'e
bakinsa danashi yacigaba da kissing d'inta, lokaci guda ya tsinci kanshi cikin wani irin yanayi,
itako auta 'kara narkewa tayi jikinsa, tana mashi shagwa6a shikuma sai kara matseta yake
jikinsa kamar wani ze kwace mashi ita,
Ji yayi anturo 'kofar da 'karfi, a firgice yakai dubansa ga 'kofar, Fadila yagani tsaye tana cika
tana batsewa, shi kwata-kwata yama manta da ita, wani irin haushinta yaji dan ta yankemashi
jin dad'insa, cikin d'aga murya yace, "Fadila meya shigo dake nan? Bata bashi amsa ba kuma
bata motsa daga inda takeba, cike da jin haushin abinda tayimashi yace "get out, ki fita nace
maki ganinan zuwa.

Ita kuwa Auta ganin Fadila yasa ta'kara narkewa jikin khaleed, ta dauki hannuwanta duka biyu
ta sa'kalosu a wuyanshi, tana mashi wani shu'umin kallo wanda ya'kara rikitar dashi, tace "haba
my dear, meyasa ka shigo baka sallameta ba, kamata yayi ka sallameta kuyi sallama kafin ka
shigo, kaga yanzu tazo muna cikin jin dad'in rayuwarmu ta mana cikas.
Da gudu Fadila ta juya tabar d'akin dan jin hawaye na niyyar zubo mata saboda tsabar takaici,
falo ta zauna tana share hawayen ba'kin ciki, a zuciyarta tana cewa

*_Lallai yarinyar nan ni zata gwadama duniyanci, to wallahi sai nayi maganinta cikin gidannan
saina nuna mata nafita iya duniyanci_*

Nan suka isketa zaune suma suka zauna, Auta yanda take haka tafito, bako d'an kwali kanta,
gashin kanta ya zubo kan kafad'unta, saboda haka hankalin khaleed yana kanta duk wani motsi
nata sai ya had'iyi yawu,
Da kanshi ya d'auko ledar ya d'auko plate ya juye dankwala-dankwalan kajine guda hudu,
sai fresh milk daya ajiye masu gefe, da ruwan roba na swan.

Nan ya Uamrcesu dasu zo su ci, Auta dama ta kwanta da 'yar guntuwar yunwarta saboda haka
matsowa tayi taci me isarta, sannan ta kora da fresh milk tasha ruwa, shima khaleed yaci sosai,
sannan yasha ruwa, Fadila kuwa kasa cin kome tayi saboda zuciyarta cunkushe take da ba'kin
ciki.
Bayan sun kammala ne khaleed yayi masu basiha akn zaman tare, sannan daga 'karshe, ya
sanar dasu abubuwan dayake so da wanda bayso, dan su kiyaye.

Sannan ya kallesu yace idan akwai me magana zata iyayi, Fadila tace "babu,
Auta tace ni maganata kawai itace duk abinda kakeso shi nakeso wanda bakaso kuma shine
baniso kaga ra'ayimu yazo d'aya kenan.

Nan suka cigaba da fira sam-sama, yawancin firar ma tsakanin Auta ne da khaleed, Fadila duk
takaici yahanata magana.

Saida suka kai 'karfe sha biyu da rabi suna falo, lokacin khaleed yafara jin bacci dan dama
akwai gajiya tattatare dashi, saboda haka yace to yakamata mu kwanta hakanan dan dare yayi
saosai, Fadila tace "Eh gaskiya nima baccin nakeji, kazo mutafi dan nima gajiyarce a jikina,
Fadila ta tashi tanufi d'aki tana lumshe ido alamar bacci, ganin Auta bata tankaba yasa khaleed
ya tashi yabi bayan Fadila, Auta tayi saurin shan gabanshi tace "Ai d'akina zamuje ko, Fadila
najin haka ta juyo tace "kamar ya d'akinki, amma kinsan ay na girmeki, kuma niyakamata ace
anba girmana, Auta tayi murmushi tace "ay nan gidan aure ne ba maganar girma, saboda haka
kazo muje kawai,
nan rigima ta kaure tsakaninsu, wannan tace d'akinta za'a fara kwana wannan tace nata za'a
fara kwana, khaleed yarasa yanda zeyi dasu kawai sai ya koma falon ya zauna kan kujera three
seater ya zauna, suma suka biyoshi suka zauna, kowace da abinda take sa'kawa a zuciyarta.

Shikuwa khaleed daya gaji da zama kwantawa yayi kan kujerar, tin yana kallonsu yana
mamakin halinsu, har bacci yayi awon gaba dashi.

Kiraye-kirayen sallar asuba ne ya tasheshi daga baccin dayake, zaune yagansu, suduka sunyi
shiru, da Alama ba wacce ta runtsa cikinsu, tashi yayi yanufi d'akinsa yashiga toilet yayi wanka
sannan yayo Alwala ya kabbara sallah.

Sai lokacin sukuma kowace tanufi dakinta dan gabatar da tata sallar.






Zee Elkaseem
Mmn khady.
[10/16, 7:55 PM] +234 816 616 9254: [04/08 6:34 pm] .:

*AUTAR HAJIYA*




®NWA



_ZEE MMN KHADY_


*_Page_* 91-95

✍ Haka rayuwa tacigaba da kasancewa a gidan khaleed, yau kimanin kwana ukku kenan
kullum kwanan zaune sukeyi a falo, dan Auta ta kafe ita a dole sai anfara kwana d'akinta, ita
kuma Fadila tace Sam bata yardaba, hakan ke sawa khaleed yayi kwanciyarshi kamar yanda ya
saba, wato falo kan kujera three siter sukuma haka zasu zauna su tasashi gaba sunata hararar
junansu.

Yauma kamar kullum, zaune suke babban falon gidan, da musalin 'karfe biyu da rabi na dare,
shikuma khaleed yana kwance yanata sharar baccinsa hankalinsa kwance, yau ma atakaice
haka sukayi kwanan zaune, asubah nayi ya wuce d'akinsa dan gabatar da sallah suma kowace
tanufi d'akinta.
Khaleed abin na damunsa yarasa yanda ze 6ulloma Al'amarin, saboda haka bayan yayi break
fast ya shirya cikin 'kananan kaya, wandon jeans ba'ki da jar T-shirt yayi matu'kar yin kyau.

'Dakin Auta yashiga, zaune ya isketa tsakiyar falonta, kan carpet hannunta ri'ke da waya tana
game, da sallama ya shiga d'akin bayan ta amsa ya'karso inda take ya zauna kusa da ita, ta
d'ago da manyan idanunta ta kalleshi tace "barka da kwana, yace "ku zanyima barka kuda ke
kwanan zaune, Kafin tayi magana yaci gaba da cewa, yanzu Zainab rayuwar da kuka za6ar mana
agidannan kuna ganin ya dace, ace ku duka ba wacce zatayima 'yar'uwarta hakuri,
Amma Auta kinga kece 'karama yakamata kiyi hakuri nafara kwana d'akin fad'ila duka fa
kwana biyu ne zan dawo d'akinki, haba Auta bakison kwanciyar hankalina ne?
Wani irin kuka ta fashe dashi, cike da mamaki khaleed ke kallonta, cikin maganar dayayima
Auta miye abin kuka.

Kuka tacigaba dayi tana cewa "shikenan khaleed ka nunamin kafi son Fadila akaina, kaje ka
kwana d'akinta d'in wallahi nikuma idan har ka kwana d'akinta ranar zan bar gidannan, kuma
idan natafi kada kayi tinanin gidanmu zanje, a'a zan tafi inda ba'a sanniba inda bansan kowaba,
incigaba da rayuwata acan.
"Idan abin gaskiyane it's kace ta hakura ta barmin mana.

Haka khaleed yayi rarrashin duniyar nan amma Auta ta kafe akan sai dai ya fara kwana
d'akinta, haka khaleed yabar d'akin Auta yana mamakin rigima irin tata.

A d'akin Fadila ma haka yasha daga da ita yana rarrashinta akan ta ha'kura ya fara kwana
d'akin Auta, amma tace sam ita bata San wannan ba, aiko abin ya 6ata ransa nan ya balbaleta
da fad'a ta inda yake shiga ba nan yake fitaba, yace "shikenan kuyi duk abinda kuka iya, yanzu

ke Fadila bazakiyi hankali ki ri'ke girmankiba ki kawo 'karshen wannan kwanan zaunen da
kukeyi,

Cikin masifa itama take magana "Wallahi bazan yardaba, yanda ita bakace ta hakura ta barmin
ba nima wallahi bazan barmataba, ai ba fina sonka tayiba.

Cikin fushi khaleed yafita, a harabar gidan yanufi gurin ajiye motoci ya hau motarsa ya kunna,
me gadi ya bud'e mashi get yadau hanya,
Gidan abokinshi ya wuce Ahmad, a ranar can ya wuni be baro gidan ba sai bayan magrib,
daga nan kuma gidansu ya wuce be dawo gidaba sai 'karfe tara da rabi na dare.






Zee Elkaseem
Mmn khady
[04/08 8:04 pm] .:

*AUTAR HAJIYA*




®NWA



_ZEE MMN KHADY_


_*Page*_ 96-100




✍ Da sallama ya shigo falon, Abin mamaki yau bega kowa a falon ba kamar yanda yasaba
kullum nan yake iske matan gidan zaune suna jiran dawowarsa,

A hankali take tafiya dan bayaso suji karar dawowarsa, su fito su sashi kwanan falon nan,
d'akinsa yanufa toilet ya shiga ya she'ka wanka sannan ya saka jallabiya marar nauyi, a
hankali ya fito daga d'akin yanufi d'akin Fadila, kwance ya isketa kan katafaren gadonta tayi

dai-dai tana sharar bacci.

Dalilin baccinta kuwa shine, bayan fad'an da khaleed yayimata yana fita ta fashe da kuka, a
zuciyarta tana cewa

_(Shikenan ni dama nasan khaleed ba sona yakeba, hakanan su Momy suka ma'kale akan sai
ya aureni, kuma nima ina masifar sonshi, sai yanzu na tabbatar da son maso wani nakeyi, dan
kuwa kome Auta zatayi khaleed baya ganin laifinta, dama hausawa sunce so hana ganin laifi)_

Haka tasha kukanta ta gaji,
Nan take kuwa kanta yafara ciwo, dama ga rashin bacci na kwana ukku, bayan magrib taji
ciwon kan yayi tsanani tasamu magani tasha, da misalin karfe takwas na dare tad'an kwanta
aikuwa bacci yayi awon gaba da ita.

Nan khaleed ya 'kare mata kallo, yayi murmushi, sannan ya fito daga dakin, cikin hankali
yakeyin kome dan kada 'yar rigimar tajiyoshi, aiko yana fitowa daga d'akin Fadila ita kuma tana
fitowa daga d'akinta.

Da sauri ya 'karaso inda take ya had'a jikinsa da nata yayi mata ky'k'kyawar runguma, ita kuwa
ganin ya fito daga d'akin Fadila yasata jin wani irin ba'kin ciki, ta bud'e baki zatayi magana yayi
saurin had'e bakinshi da nata, hot kiss yake mata, yana romancing d'inta lokaci guda ta mance
duniyar datake ciki.
'Daukarta yayi kamar wata jaririya, bezame ko'ina da'itaba sai bedroom d'inta ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login