Showing 24001 words to 25074 words out of 25074 words

Chapter 9 - Autar Hajiya Book Compelet By Zeey Maman khady

20 Jul 2026

77


Auta yaci sunan Baban khaleed, Ana kiransa shaheed, sai kuma babyn Fadila wacce yanzu
haka tana hannun Auta ta had'a da yaronta tana shayar dasu, ita kuma sunan Mahaifiyarta aka
maida mata *_Fadila_* mashaAllah anyi suna lafiya lau, duk da ba wani taro akayiba, amma
'yan'uwa da abokan arzi'ki sunzo, Auta tasha kyaututtuka ita da baby's daga gurin danginta da
dangin khaleed, 'yan'uwan Fadila kuwa sha tara na arzi'ki suka had'oma Auta, abinda yakara
d'aga hankalinta tari'ka sharar 'kwalla tana tuna sister d'inta Fadila.

momyn khaleed ce tasamo wata dattijuwar mata wacce zata zauna da Auta dan ta tayata rainon
yan biyunta.

***************************

Bayan kwana arba'in su Auta sun gama wanka, suduka suna cikin 'koshin lafiya itada yaranta,
sunyi 6ul-6ul dasu yarinayar Fadila kya'kyawa kamarsu d'aya da mamarta, sai dai ta d'auko
farin babanta.

shaheed kuwa babansa ya biyo, fari tas dashi, kamar d'an larabawa.

Haka yaran suka taso cikin kulawar iyayensu, dan khaleed kullum idan yataso ayki be'kara fita
zama yake suna raino tare.

*_BAYAN SHEKARA BAKWAI_*

Wasu kyawawan yara na hango a harabar gidan khaleed suna wasa da ball, cike da nishad'i.
Can kuma sai suka kama rigima bansan kome ya had'asuba, macen ce ta rugo da gudu,
tashigo gida, namijin na biye da ita, jikin Auta tafad'a tana cewa "Ammi kice kada ya
dakeni,suanan dasuke Kiran Auta dashi kenan _*Ammi*_ Auta ta'kara rungumeta, tace"kai
shaheed kada ka doketa, miye ya had'aku? "Ammi wai dan munyi ball naci 3 itakuma taci 1 dan
nayi dariya shine ta dokeni ta rugo.
Auta ta rungumoshi jikinta tace yi ha'kuri kaji shaheed d'ina bazata 'karaba.

Ya kalli Fadila wacce ta'kara narkewa jikin Auta yace "kuma yarinya idan kika 'kara saina
doddokeki.

Ta kalli Auta tace "ai dai Ammi bazaki bari ya dokeniba ko? Auta tace Bazan bariba mana, aiko
Fadila najin haka sai ta kyalkyale da dariya tayima shaheed gwalo, Aiko yabiyota da gudu ze
doketa ta ruga tana kiran Ammi... Ammi kice kada ya dokeni, Auta ta tashi tana 'ko'akrin raba
rigimar ne khaleed ya shigo da sallama, aiko da gudu suka ruga suka rungumeshi suna fad'in
_welcome my daddy_ 'daga Fadila yayi sama yana dariya yace welcome my baby, sannan ya
ajiyeta ya d'aga shaheed yace "welcome my dady, sannan suka wuce ciki, nan suka zauna
yana tambayarsu karatun dasuke a school suna bashi amsa, dan yaran badai 'ko'kariba,
Auta ce tagabatar masu da abinci, suka zauna sukaci sunata nishad'i, bayan sun gama khaleed
yace su shirya zasu fita Unguwa, aiko nan suka kama tsalle suna murna,

Sun fito cikin shiri, sunyi shar dasu gwanin ban sha'awa Fadila sanye cikin wata had'ad'diyar
doguwar riga, milk me zanen Flowers pink, sai takalminta masu tudu suma pink colour, kanta
kuwa yasha gyara, kamar na yan indiya, yazubo har bisa 'kafad'unta, shaheed kuwa fararen
jacket ya Sanya, sai farin takalmi cover yayi kyau abinsa, haka suka shiga mota gidan Momyn
khaleed suka fara zuwa, cike da murna ta tarbesu, tanata ji da yan jikokinta, har daddyn
khaleed yadawo suka gaisa sannan suka wuce,...

Gidan su fadila suka sauka, da sallama suka shiga gidan, da gudu shaheed ya Fad'a jikin
Momyn fadila yana Fad'in momyna gani nazo, cike da fara'a tace "a'a yau megidanne da kansa,
to sannu da zuwa, nan suka shigo suka gaggaisa, sunjima anan kafin daga nan su wuce gidan
Hajiya.
A gidan Hajiya suka 'karasa wuninsu, sai bayan ishsha'i suka tafi, yaran sunata kewar Hajiya,
da Fadila da kyar ta yarda aka tafi da ita wai ita a dole nan zata kwana, saida akayima wayo
akan gobe za'a kawota tare da kayanta duka, sannan fa ta yarda aka tafi da ita tanata murna
gobe za'a maidota gurin hajiyarta,
Shaheed ya harareta yace, yarinya nima idan aka kaiki nima sai an kaini gurin Hajiyata (Momyn
Fadila)
Khaleed yace duka gobe zan kaiku, aiko suka shiga murna.


*_Anan inso inyi amfani da wannan damar inyi kira ga 'yan mata masu kafewa akan su bazasu
auri me mataba, shin bakusan tin kafin kazo duniya Allah yariga ya tsara yanda yakeso
rayuwarku yakeso ta kasanceba_

*Kawai ku ro'ki Allah yaza6a maku mafi Alkhairi*

```Alhmdulillahi anan nakawo 'karshen littafina me suna Autar Hajiya,
Ina mi'ka dumbin gaisuwa ga masoyana a duk inda kuke Allah bar 'kauna, nagode```


*Sadaukarwa*
Na sadaukar da wannan littafi ga 'kawata, kuma 'kanwata, kuma takwarata *Zainab*
```(AUTAR HAJIYA)```
Allah bar mu tare


Kyakyawar gaisuwa gareku group member's d'in

*CIWON YA MACE*
*ZEE MMN KHADY FAN'S*
Allah 'kara hada kawunanamu.

Daga marubuciyar
*siyasa ko soyayaya*
*Duniya juyi*
*Halin girma*
*Autar Hajiya*

Sai kunjini a buk dina na gaba

```ALHINI```

Kya'ky'kyawar gaisuwa ga All writer's ✍

Lokaci baze isa in lissafo kuba, amma kuna raina akoda yaushe.



Love u All
[16/08 3:35 pm] .:
*_ALHINI_*



®```NWA```


_written by_
*_Zee Mmn khady_*

```Fatima shine asalin sunanta, amma ana kiranata da balaraba,

Balaraba yarinyace yar kimanin shekara 14,yarinya me farin jini da kwarjini a fad'in karakararsu
duk wani namaiji me ji da kanshi a 'kauyen yana so Balaraba tazama mallakinsa, samari suna
gasa akanta, kowa yanaso yazama mijinta,

Amma matsala da Balaraba ta fuskanta itace duk wanda ta tsaida matsayin mijinta, da lokacin
biki yagabato sai ya mutu,

Hakan yasa Balaraba tashiga cikin matsanancin tashin hankali.


Suakuma muatnen 'Kauyen gain haka yasa suka fara gudunta.

Har abin yakai duk Inda doshi mutane sai kaaga suna gudu, 'kawayenta kuwa duka gudunta
suke```

Shin waye ze Auri balaraba, da wannan matsalar ? Kuma miye matsalar ta wadda duk Wanda
yanemi aurentayake mutuwa?
*shin me ya jawo ma fatima (Balaraba) wannan?*

_Amsar wannan tambaya tana cikin littafin *ZEE MMNK HADY* me zuwa kada kubari abaku
labari ALHIHI labari mai ban tausayi ban Al'ajabi da kuma ban mamaki da tsan-tsan
soyayya gami da nishad'antarwa da ilmantarwa, kudai kubiyoni dan jin yanda zaya kasance_


```COMING SOON
COMING SOON
COMING SOON```


Zee Elkaseem
Mmn khady

7
8
9

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login