Showing 15001 words to 18000 words out of 25074 words

Chapter 6 - Autar Hajiya Book Compelet By Zeey Maman khady

20 Jul 2026

77

yayi awon gaba da ita.

Zee Elkaseem
Mmn khady
[10/16, 7:55 PM] +234 816 616 9254: [10/08 11:29 pm] .:

*AUTAR HAJIYA*




®NWA



_ZEE MMN KHADY_



```Page```121-125






✍ Haka Auta tacika kwanakinta biyu kullum zata tsaya ta kwantar da hankalinta ta tsara girki
tun kafin ta kai kan dining saita d'and'ana taji testing d'insa saita tabbatar da lafiya lao sannan
take ajiyewa, amma abin mamaki sai sun zauna cin abincin suji gishiri za'ka'ka, Abin yana
matukar damun Auta amma ba yanda zatayi, dan batada hujjar kare kanta akan cewa ba ita ta
zuba gishiri haka ba,
ba abinda ya kara d'aure mata kai sai lokacin da tayi girki ranar ko gishiri bata zuba ba dan
gudun kada yayi yawa, amma babban abin mamaki shine suna fara ci sukaji gishiri zau' abin ba
dad'in ji.


****************************
Fadila ce cikin shigar 'kananan kaya riga da wando sun matseta sosai, wasu had'ad'un kuloli ne
take d'aukowa daga kitchen tana jerawa kan dining, gefe kuma lemun ```5alive``` ne sai ruwan
swan, abin gwanin ban sha'awa.

Da misalin 'karfe biyu da rabi khaleed ya dawo gida, Fadila ta tarbeshi cike da murna, Auta
kuwa tana zaune gefe, cikin sanyin jiki tace "Sannu da zuwa, ciki-ciki ya amsa, sannan ya wuce
d'akinsa,

Dan yanzu Auta tariga tagama sure mashi, kwata-kwata tagama 6ata ranshi, ace kullum
mutum baze iya tsayawa yayi Abu cikin tsariba, sai ace yau ayi girki acika gishiri, kuma gobe
ma haka za'ayishi,
babban abin takaici sai kaji gishiri cikin zo6o ko kunun aya, wnnan ay rainin wayo ne.

Wani 'karamin tsaki yaja "mtsw, sannan ya wuce d'akinsa, Fadila ta bishi tana wani karairaya,
koda takai bakin 'kofar d'akin saita juyo ta kalli Auta dake zaune kan kujera abin duniya duk ya
dameta, tayi wani shu'umin murmushi sannan tashige d'akin tare da canja salon tafiya tana wani
juya mazaunai.
Fadilar ce ta taimaka mashi ya cire kayan jikinsa yayi wanka, da kanta taje cikin kayanshi ta
dauko mashi kaya marassa nauyi ya Sanya, sannan suka fito falo, dining suka sauna dan cin
abinci Auta kuwa ba'kin ciki ya gama cika mata zuciya, bayan shigewarsu d'akinta tanufa tafad'a
kan gado ta rushe da wani irin kuka, sai da tayi me isarta sannan tafad'a toilet ta she'ka wanka,
bayan tafito ta shafe jikinta da cream me dadin kamshi da gyara jiki sannan ta shafa powder ta
dauko man le6e ta shafa,
wadrope tanufa ta d'auko wata doguwar riga ba'ka me adon fararen duwatsu daga gabanta ta
Sanya, sannan tasa d'an 'karamin gyalen rigar ta rufe kanta dashi, lokaci guda ta fito balarabiya
Sak, dan ba 'karamin kyau Auta tayiba.

Kan dining ta iske Fadila da khaleed suna jiran fitowarta, guri ta samu ta zauna duk da zuciyarta
na cunkushe da ba'kin ciki da kuma jin haushin Fadila amma ko kad'an bata yadda khaleed da
fadilar suka fahimci halin datake ciki ba.
Bayan Fadila ta zuba abincin ta ajiyema Kowa nashi gabanshi, jalouf d'in taliyace wacce
taji kifi, cike da fargaba Auta ta ebi taliyar takai bakinta, ```Ya salam```...... Auta ta fad'a tare
dayin hanyar toilet da gudu ta rina'ka kwara amai, saida ta amayo duk abinda ke cikinta,
khaleed kuwa binta yayi daga baya yana mata sannu, bayan ta gama ta wanke bakinta khaleed
yakamo hannunta suka dawo falon, kan kujera ya zaunar da ita yanamata sannu, ita kuma sai
wani langwa6ewa take, tana lumshe ido, Fadila ta kalleta cike da jin haushi, amma sai ta daure
dan bataso a d'ago da ita, tace "sannu dama bakida lafiya ne? Auta tace lafiyata lau, kifin da
akasa agirki ne 'karninsa yayi yawa shine ya tayarmin da zuciya,
Fadila ta ta6e baki ta samu gu ta zauna, a zuciyarta tana cewa

```lallaima yarinyar nan nizakima duniyanci kice wai bakison kifi sau nawa ke kikeyin girki da
kifin akwai dai inda kika dosa```.

Auta kuwa 'kara narkewa take tana wani shagwa6ewa, 'karshe ta kwanta kan kujerar datake
tayi filo da cinyar khaleed,
Shikuwa sai wani rarrashinta yake yana tarairayarta, "sorry my dear ki daure kici abincin
bekamata dan kinyi amai ki zauna da yunwa ba.
Cikin shagwa6a Auta tace " nidai banison wannan ka siyomin wani, tunda yanzu ba time d'in
da zan girka wani, yace "fad'i mi kikeso in sayo maki, cikin shgwa6a tace ka siyomin kome kaga
ze Sani farin ciki, yace "kada ki damu my only ina zuwa, makullin motarshi ya d'auka yafita, be

kobi takan Fadila ba wacce tacika tayi fam saboda takaici.






Zee Elkaseem
Mmn khady
[11/08 11:44 am] .: [11/08 10:19 am] .:

*AUTAR HAJIYA*




®NWA



_ZEE MMN KHADY_


```Page``` 126-130




*_BAYAN KWANA BIYU_*
✍ Auta ana kitchen anata faman girki, yau tasha Alwashin tsayawa tsayin daka tayima mijinta
abinci wanda ze faranta ranshi, wanda zesa ya manta duk wani 6acin rai na baya, kuma ya
dawo da tsananin so da 'kauna da kulawar dayake mata.

Sakwara tayi niyyar dafa mashi da miyar agushi, saboda haka doyarta me kyau ta fere ta d'ora
kan wuta, sannan ta dora miya kan wani stove kusa da doyar, bayan ta kammala sakwarar ta
maida hankalinta kaf gurin miyar, cikin 'kan'kanin lokaci ta kammala miyar ta juye kome cikin
wasu kuloli masu Khan gaske, fridge tanufa da niyyar ta d'auko abarba domin yau *(pineapple
juice)*lemun abaraba tayi niyyar had'a musu, tana bud'e pridge din kuwa cikin rashin sa'a
saitaga ashe batada sauran abarba, sai lokacin ta tuna aahe fa ta kare tin bayan kwana biyu
datayi lemun da ita.

'Dakinta tanufa ta dauko karamar hijab ta sanya sannan tanufi harabar gidan da niyyar taba me
gadi ya siyo mata Abarba,

Zaune ta iskeshi kan benci yana ri'ke da yar rediyonshi yana sauraren labaran duniya, cike
da ladabi ta gaidashi sannan ta bashi sa'kon ba musu ya kar6a yafita ya siyo mata, dayake
kusa da su akwai wurin da ake saida kayan fruit.

Data tashi dawowa sai bata biyo ta babbar kofar falon ba, ta baya ta biyo hanyar da zata sadata
da kitchen d'inta kai tsaye,
tazo dai-dai window kitchen dinta kamar ance tayi duba gurin,
Wani irin mummunan fad'uwar gaba taji dan ganin abinda ke faruwa a kitchen d'inta.
Fadila tagani da kullin gishiri cikin leda ta bud'e had'ad'd'iyar miyar agushinta wacce keta
zuba 'kamshi ga nama zud'u-zud'u aciki tsoka zallah tayi amfani da ita gurin yin miyar.

Aiko da sauri Auta takoma baya ta la6e dan taga ikon Allah,
Gani tayi Fadila tasa cokali ta ebo gishiri ta zuba cikin miyar ta 'karo wani cike da cokali ta juye,
saida ta zuba cokali biyar ciakakke sannan tasa cokali ta motse,
Ta kulle ledar gishirinta ta kakka6e hannunta tayi saurin barin kitchen d'in.

Cike da mamaki Auta ta shigo kitchen d'in, ta bud'e miyar tasa cokali ta motsa lokacin gishirin
yagama narkewa cikin miyar, saboda haka zubar da miyar tayi ta ta d'ora wata cikin 'kan'kanin
lokaci tagama had'a wata sabuwar miyar ta gama kome ta had'a lemun abarba, tasaka pridge
sannan ta gyara ko'ina na kitchen d'in, 'Daki ta wuce ta fad'a toilet ta she'ka wanka, bayan tafito simple kwalliya tayi sannan ta
d'auko riga da siket na atamafa ta sanya ta dauko turare ta feshe jikinta dashi, tafito falo sai
'kamshi take bugawa, sannan ta d'auki makullin kitchen d'inta tafita zuwa kitchen d'in, dan tin
lokacin dataga abinda Fadila tayimata data gama girkin ta kulle kitchen d'in ta tafi da makullin
d'akinta.

Bayan tagama jera kome kan dining, lokacinne kuma khaleed yashigo gidan, cikin murna dajin
dad'i Auta ta tarbeshi tayi Mashi sannu da zuwa, ciki-ciki ya amsa, sannan ta kar6i jakar
hannunsa tayi gaba zuwa d'akinsa shikuma yabi bayanta, bayan ya rage kayan jikinsa suka fito
zuwa falo Sun zauna kan dining Auta ta zuba ma Kowa ta ajiye gabanshi, lokaci guda 'kamshin girkin ya
mamaye falon,
Fadila tasa hannu ta d'ebi loma guda zata kai bakinta, sai kuma ta tsaya ta kalli khaleed tace
"my man , ya juyo ya kalleta, tace "nifa wallahi fargabar saka abincinnan nake a bakina, saboda
kasan gishiri yana iya yima mutum lahani, kasan fa da mutum ya d'ibgama cikinsa gishiri 'kara
yaci ba dad'i.
Auta tayi murmushi tace "Fadila kici mana kiji, idan kikaji gishirin yayi yawa ai baza'ayi maki
dole akan sai kinci ba, sannan ta kalli khaleed tace "my dear kaci abincinnan hankalinka
kwance, nayima Alkawarin daga yanzu kagama jin wani aybu cikin abincina, wancan lokacinma
matsala ce aka samu amma yanzu kome yakoma normal inshaAllah.
Khaleed bece kome ba, sai dai ya ebi abincin ya kai bakinshi cike da fargabar irin testing d'in

dazeji,
Cike da mamaki khakeed ya ida saka abincin bakinsa, dan wani irin dad'i yaji yartsa kwanyarsa.

Besan lokacin daya sakarma Auta wani tattausan murmushiba, yace *Weldon* my wife, amma
nayi matu'kar farin ciki dajin wannan gyara naki, gaskiya yau kin matu'kar faranta raina Allah
maki Albarka ya saka miki da Aljannah, cike da jin dad'in yabata da kuma addu'ar da mijinta
yayimata, tayi dariya har dimple d'inta ya lo6a tace Ameen mijina, Allah kara dan'kon soyayya
tsakaninmu, yace "Ameen my wife.

Cike da mamaki Fadila ta kai abincin bakinta, take dad'in abincin ya ratsa mata kwanya,
batasan lokacin data cigaba da cin abincinba, dan dama su duka akwai tsohuwar yunwa tattare
dasu dan tin lokacin da Fadila tafara 6ata ma Auta abinci da gishiri suka daina cin abinci su
'koshi, Domin dai ita Fadila kotayi ba sosai suke iya Ciba, saboda ba dad'in yau bare na gobe

Ranar dai haka suka ci abinci cike da farin ciki da annushuwa,
Sa6anin Fadila wacce ba'kin ciki yagama cika zuciyarta.

```Auta dai tagano Fadila ce me 6ata mata abinci, amma kuma bata tanka mataba kuma bata
nuna 6acin ranta ba```

*_Kome take nufi da hakan kubiyo zee mman khady dan jin yanda za'a kwashe tsakanin Auta
da Fadila_*



Zee Elkaseem
Mmn khady
[10/16, 7:55 PM] +234 816 616 9254: [12/08 3:00 pm] .:

*AUTAR HAJIYA*




®NWA



_ZEE MMN KHADY_


```Page``` 131-135

✍ "Haba 'kawata aini wallahi bayi fushi dake, ace tunda aka kawoni gidannan sai yau kika tuna
dani,
Sadiya tace "Ayimin afuwa wallahi kinsan hidimomi idan sukayima mutum yawa sai ahankali,
Auta ta harareta cikin wasa tace "kinjiki ko, ke har wata hidima ke gareki kamar wata me iyali,
Sadiya tace "ay iyalin ake niyyar yi shiyasa hidimomin suka fara tun yanzu,
"Hakane fa yau saura 3 week's koh? Sadiya tace "au tambayata ma kike, duka yaushe mukayi
waya dake na gaya maki.

Haka sukacigaba da firar yaushe gamo, nan Auta ke tamabyar ta "waini ina uwar gidanki?
Tunda nazo ban gantaba, "Auta ta harereta tare da kaimata duka cikin wasa tace "Uwar gida fa
kikace, kodai amarya' ay nice uwar gidan kamar yanda nad'au Alwashi, nan auta tabata labarin
yanda sukayi ranar da aka kawosu da kuma kwanakin da suka kwashe suna kwanan zaune.
Sadiya tayi dariya sosai sannan ta kalli Auta tace "kai Auta bakida dama gsky rigimarki tafiki
'karfi, khaleed d'in kuka samu shiyasa kuke yanda kukaga dama, idan nice shi wallahi sai in za6i
d'akin danikeso kawai inyi kwanciyata kuma dole wacce ban za6a ba ta hakura.

Auta tayi dariya tace" Ay koda hakan yayi nasan d'akina ze za6a dan na dad'e da fahimtar irin
tsananin son da khaleed kemani, shiyasa bani yarda inyi abinda zai 6ata ransa,
Sadiya tace Yauwa 'kawata haka yakamata kiri'kayimasa shine zesa ya'kara jin sonki da
'kaunarki, kuma kada ki yadda koda wasa kiyi fad'a da abiyar zamanki wanda ze d'aga
hankalinsa randa duk haka ta kasance sai son dayake maki ya ragu a cikin zuciyarsa.

Auta tace "ina ay bazan yarda haka ta faru ba, dan nayi al'kawarin babu ranar daza'ayi
kace-nace dani a gidannan, amma kuma naga take-rakenta tana Neman ta ragemun son da
mijina yakemin ta haryar 6atamin duk wani Abu dana girka dan na faranta ransa.
Nan Auta ta kwashe labarin yanda Fadila tari'ka zabga mata gishiri cikin abinci, Wanda
sanadin haka khaleed yafara juya mata baya,
Sadiya tace "tab ammafa yarinyar nan makira ce, wato ita nata ba dad'i shine ta 6ata maki,
tsabar ba'kin ciki kawai, amma kin kyauta da kika kyaleta, kawai ki ri'ka kaffa-kaffa da duk wani
Abu wanda kikasan zata iya 6ata maki.
"Tab wallahi bazan 'kyaletaba, Auta ta fad'a cikin d'aga murya, Sadiya tayi saurin sa hannunta ta
rufema Auta baki, tare da cewa "ki rufamin asiri kada kiyi wani Abu ace nice nazo na sakaki,
kuma kinsan fa yanzu haka tana jinmu,
Sai lokacin Auta tayi 'kasa da murya tace "wallahi bazan 'kayletaba dole sai na rama abinda
tayimin, sadiya tashiga bata hakuri akan ta hakura ta 'kyaleta ai dai tasan tafita, Auta tace
"Hmm Sadiya inaga kin fara manta ni, sadiya tayi murmushi tace "ina zan manta da rigimarki
Auta, amma ai yanzu yakamta ki rage wasu abubuwan saboda yanzu gidan aure kike ba gidan

iyayenki ba.

Auta tasan halin Sadiya idan ta biyemata tsaf zata sage mata gwuyawu taji bazata iya aiwatar
da kome akan ramuwar abinda Fadila tayimata ba,
Yawarta ta d'auka dake ajiye kan bedsite ta duba, sannan ta kalli Sadiya tace "kinga rana tayi
har karfe sha d'aya da yan mitoci, bari nashiga kitchen na samo maki abinda zakici, nasan
bazaki iya cin abincin waccan matar ba,
Sadiya tayi murmushi tace "wallahi da kin barshima dan tafiya zanyi yanzu, Auta tace wallahi
bazaki tafiba sai kinci abinci, kinsan me zan dafa maki, bata jira abinda zata fad'a ba tace taliya
da manja da yaji zan dafa, nasan ke mayyar tace, suduka suka sa dariya.

Tare suka shiga kitchen d'in, cikin minti talatin suka gama girka taliyar suka zuba a flate, sauka
zabgo uban yaji, amma duk da haka saida Auta ta taho da wani Yajin cikin wani 'karamin vowel
wai zata 'kara gabanta.

Sai gurin karfe sha biyu da rabi Sadiya tayi haramar tafiya gida, tare suka fito daga d'akin a
babban falo suka had'e da Fadila ta fito daga d'akinta zata shiga kitchen, nan suka gaisa da
Sadiya kowanensu ba yabo ba fallasa, sannan suka wuce, har kusan get Auta ta rakata sukayi
bankwana, tare da mi'ka mata wata yar 'karamar leda wacce ta had'amata kayan make-up aciki.
Auta na komawa d'akinta, toilet ta fad'a ta she'ka wanka, bayan tafito ta zauna gaban mirror ta
d'and'asa kwalliya, sannan ta d'auko wasu 'kananan kaya riga da wando ta sanya,
Rigar ta d'an sauko dan ta rufe mata rabin cinyarta, amma ta matseta sosai, sai wando pencil,
sannan ta dauko wani karamin gyale tayi rolling, lokaci guda ta tashi daga jinsin Hausa zuwa na
larabawa, dan idan ba magana tayiba sai kace bata ta6a jin yaren hausa ba.

Fadila kuwa itama lokacin tagama tsara kome na abinci kan dining, sannan takoma d'aki ta
she'ka wanka shigar doguwar riga tayi ta atamfa, itama tayi kyau gwargwadon nata.

Da misalin 'karfe biyu da minti arba'in khaleed yadawo gidan, suduka falo ya iskesu, sukayi
mashi sannu da zuwa, hankalinshi duka nakan Auta, kallonta kawai yake yanajin wani feeling
tattare dashi,
Saida Fadila ta lura da irin kallon dayakema Auta sannan tayi dabarar zuwa kusa dashi tace,
"muje ka watsa ruwa ko, ga kuma abinci yana jiranka.

Beyi mata musu ba suka wuce d'akinsa, amma cikin ransa jiyake inama Auta ce suke tare da ba
abinda ze hana su kashe arna kafin su futo.




Zee Elkaseem
Mmn khady

[12/08 4:14 pm] .:

*AUTAR HAJIYA*




®NWA



_ZEE MMN KHADY_


```Page``` 136-140




✍ Zaune suke kan dining sunyi shirin cin abinci, kamar yanda suka saba duk wacce ke girki ita
ke zuba ma kowa ta ajiye masa gabansa, yauma Fadila ce ta zuba masu ta ajiye masu, lokaci
guda Auta ta ebi abincin takai bakinta,
Dadai lokacin shima khaleed ya ebo abincin yakai bakinsa,
Wani irin zafi yaji ya ziyarci 'kwalwarsa, ya mamaye duk illahirin Kansa, har cikin kunnuwansa
yakejin bala'in yajin da aka zambad'a cikin abincin,
Wani mugun attaruhu aka zabga irin me yajin nan,
Kalmar innalillahi kawai yashiga furtawa, dan shi mutum ne wanda be shiri da yaji ko kad'an,
Robar ruwan dake gabanshi yayi saurin jawowa, ya tsiyaya ruwan cikin cup ya shanye, ya kara
cika cup d'in ya shanye ko zeji sau'kin rad'ad'in yajin dayakeji amma abanza dan ko alamar
zebar jin zafin beyiba.

Dai-dai lokacin kuma yaji Auta ta fashe da wani irin kuka, yanda kasan wata 'karamar yarinya
ta tashi tsaye, duk ta wani gigice tanata yarfa hannu, ta bud'e baki tana sha'kar iska tana fad'in
yaji, lokaci guda fuskarta tayi jawur, abinka ga farar mace, ga hawaye share-share.

```{Niko zee da nike tsaye ina kallon ikon Allah ri'ke baki nayi ina mamakin Auta dake kukan yaji,
kamar ba ita bace tagama cin abinci da 'kawarta suka zabga yaji amma ita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login