Showing 6001 words to 9000 words out of 25074 words
ma yafi wannna dan yanda take gaya mashi batason kishiya, ta
tsani kishiya.
Zee Elkasee
Mmn Khady
[10/16, 7:55 PM] +234 816 616 9254: [02/08 5:24 pm] .:
*AUTAR HAJIYA*
®NWA
_ZEE MMN KHADY_
_Page_ 51-55
✍ "wannan zancen banza ne zancen Wofi, abinda baze ta6a yiyuwa bane,
Wato Zainabu kinaso ki maidamu 'kananan mutane ko? ko kinaso ki haramta abinda Allah ya
hallata, duk namiji Allah ya halatta mashi Auren mace daga d'aya har zuwa hud'u, saboda haka
ke baki isa ki haramta Abinda Allah ya halatta ba.
Mahaifin Auta ne keta faman fad'a tinda suka shigo asibitin shida mahaifin khaleed, Hajiya
tabasu labarin abinda ya faru tsakanin Auta da khaleed.
Cigaba yayi da fad'a ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba,
Auta kuma banda aikin kuka ba abinda takeyi, kwance take kan gadon asibitin ta juya
fuskarta dan bazata iya had'a ido da khaleed ba, dan ita kanta sai daga baya tayi danasanin
abinda tayi mashi, cikin zuciyarta kuwa cewa take.
_Allah kasa kada Abinda na aikata yazama silar fasa Aurena da khaleed inason khaleed son da
bazan ta6ayima wani namij iirinsaba_....
Wani sabon kuka ta fashe dashi lokacin data tsinkayo muryar daddyn khaleed yana cewa, "A'a
Alhj baza'ayi hakaba kada fa atakurama yarinya, yakamata atambayeta aji ra'ayinta, tinda ada
lokacin data Amince da aurensa ba'ayi da ita ze fara auren wata kafin itaba....
"Haba Alhj ka daina wannan mqganar" Baban Auta yafada' "yaushe zamu zauna yarinya
'karama kamar Zainab tana juyamu, "to kisani cewa aurenki da khaleed ba fashi, ke barima kiji
in sanar dake, an sassauto da lokacin bikin yadawo lokaci daya da wanda za'a d'aura mashi
nan da sati ukku, inshaAllah lokaci guda za'a kaima khaleed mata biyu, Alabashi kinga idan aka
kaiki saiki kashe kanki saboda tsabar kishi, shashasha kawai wacce bata San ciwon kanta ba.
Cikin fushi yafita daga d'akin, daddyn khaleed yabi bayansa, Hajiya ma binsu tayi,
Harabar asibitin suka tsaya daddyn khaleed yana cigaba da ba d'an'uwansa hakuri " yana cew
"Kabi kome a sannu Zainab d'in duka nawa take dazaka ri'ka yimata fad'a kamar kanayi da wata
babbar mace, duka bana fa take cika shekara sha takwas, kaga kuwa akwai 'kuruciya tattare da
ita.
Hajiya dake tsaye tana saurarensu, tace " haba Alhj ai halin Zainab dole sai da haka, idan ba'a
tsawata mata haka zata ri'ka mana yawo da hankali, ni kaina naji dad'in haka, kuma 'kara da
aka sassauto da bikin ayi a huta.
Daddy khaleed yace "Allah sa haka shine mafi Alkhairi, suduka suka Amsa da "Ameen.
Cikin d'akin kuwa khaleed na ganin fitar iayensu yafara rarrashin auta, yana nuna mata irin
sonda yakemata,
Amma ko kallo be ishetaba,
Ahankali ya matso ya dur'kusa kusa da gadon datake kwance, ya marairaice, cikin sigar rarrashi
yake magana.
"Haba Zainab ki yarda dani, ki yarda da son danike maki, duk duniya ba macen danikeso kamar
ke,....
A fusace ta d'ago ta kalleshi cikin tsiwa tace "Akwai khaleed, na tabbata kafi son Fadila a kaina,
khaleed ka ha'inceni, ban ta6a tinanin ko a mafarki zakayi mani haka ba.
Ya salam...ki fahimceni Zainab, Fadila fa bani nace ina sontaba, had'in iyaye ne,kuma ke....
"Dakata khaleed, bakada kalaman dazasuyi tasiri akaina, ka adana kalamanka, wata kila
suyima amfani nan gaba....
_(Hmm zainabu kenan halinki sai ke)_
*Zee Elkaseem*
*Mnn Khady*
[02/08 6:26 pm] .:
*AUTAR HAJIYA*
®NWA
_ZEE MMN KHADY_
_Page_ 56-60
✍ Kwanan Autar Hajiya biyu aka sallamota daga asibiti, duk ta wani rame ta kod'e hancinnan
ya'kara tsayi, ga wani haske data 'kara, idan ka ganta sai kayi tinanin tayi ciwon wata biyu ne,
dan ba 'karamar rama tayiba, duk tsabar kishine kawai.
Ranar sukayi waya da 'kawarta sadiyya, tace dan Allah tazo yau tana son ganinta, sadiyya tace
"lafiya dai? Auta tace "lafiya lao kizo mana akwai labari 'kawata wallahi ina cikin tsananin
damuwa da ba'kin ciki, cikin rud'ewa sadiyya tace "Damuwa 'kawata?, wace irin damuwa kuma?
Auta tace "kedai sai kinzo kome kenan kinji.
•••••••••••••••••••••••••••••••••
Sanye take cikin doguwar riga ta atamfa kalar sararin samaniya, wacce tasha d'inkin zamani,
dinkin ya matu'kar kar6ar jikinta, dan ba karamin kyau yayi mataba, bata d'aura d'an kwaliba,
sai wani karamin gyale me sharara ta yafa akanta, amma hakan baze hana ka hango
madaidaicin gashinta ba Wanda yasha 'kuna, tayi parking dinsa tsakiyar kanta.
Wankan tarwad'a ce, amma dayake tana amfani da cream da lotion masu tsadar gaske masu
matu'kar gyara fata,hakan ya 'kara fito da hasken fatarta, tanada idanu madai-daita, da dogon
hanci, Wanda yayi dai-dai da matsakaicin bakinta, Wanda yasha romantic red colour,
kallo d'aya zakayi mata ka tabbatar da boko ya zauna jikinta, da kwalwarta, *Fadila kenan*.
Da sallama ta shiga falon da akayi Mashi masauki, tafiya take cikin yanga da karairaya,
Lokacin khaleed ya d'ago ya kalleta tare da amsa sallamarta,
Yanda take tafiya baya birgesa ko Alama, dan tanada 'yar'kiba shiyasa tafiyar bata mata kyau,
ga Allah ya hore mata manyan nonuwa kamar me shayarwa.
Sannu da zuwa angona, tafad'a tare da zama kan kujerar dake kusa dashi, hannu tasa ta d'auki
sauran lemun dayasha cikin cup d'in glass ta kur6a sannan ta ajiye, ta maida kallonta gareshi,
tare da tambayarshi, "ya hidima? Yace "Alhamdulillah,
My dear lefe yayi kyau amma ka manta, da sarkar gold d'in dana fad'ama ba irin wacce ka sako
bace, inaso dan Allah ko zaka musanyo mani ne?.......
"Ke Fadila, cikin d'aga murya yafad'a, idan bazaki iya amfani da abinda kika gani acikiba, to
ba'ayimaki dole ba, nidai namaki iya 'kok'arina.........
Daga mashi hannu tayi, cikin d'aga murya take magana, "Dakata khaleed, bazakaje wata ta
6ata maka raiba kazo ka huce kaina, ko kana tinanin banida labarin abinda ke faruwa,
tsakaninka da wannna yarinyar, Auta take ko miye.....
A fusace ya mike tsaye, yace ni zan wuce, ba wannan ya kawoniba, zowa nayi inji idan kina
bu'katar wani abu, kuma naji bakida bu'katar kome sai anjima,
Ya fita Daga falon yanufi harabr gidan inda ya ajiye motarsa, yana niyyar Shiga yaga mamar
Fadila, direba ya sauketa, ta dawo daga Unguwa, nan ya gaisheta, ta tambayeshi momynsa,
yace tana lafiya, sannan ya shiga motarsa ya wuce.
Zee Elkaseem
Mmn khady
[10/16, 7:55 PM] +234 816 616 9254: [03/08 10:20 am] .:
*AUTAR HAJIYA*
®NWA
_ZEE MMN KHADY_
_Page_ 61-65
*_Bayan sati biyu_*•
✍ Yau sauran sati d'aya bikin khaleed da Autar Hajiya da kuma Fadila, duka 6angarorin guda
ukku shirye-shirye suke, ko'ina ka gani suna cikin farin ciki.
Amarya Fadila ansha gyara anyi fresh, dan tin ana saura sati biyu bikin take faman gyara kanta,
duk wani Abu datasan yana da amfani a jikin mace tana amfani dashi, tin Daga kayan gyaran
jiki zuwa kayan tsumi ba Wanda batayi.
6angaren Autar Hajiya kuwa kullum ba abinda take sai tinani, duk tabi ta rame ta kod'e tayi wani
irin fari, idanunta sun kara fitowa, a haka dai aketa shirin biki, 6angaren Hajiya kuwa ba irin
rarrashin da batayima Auta ba, haka babanta tin yana mata fad'a har ya dawo yana rarrashinta
yana mata nasiha, da haka dai aka samu tad'an saki jikinta, aka cigaba da hidima.
A 6angaren khaleed kuwa shima hidima yake sosai shida abokaninsa, zuciyarshi fal da farin
ciki, dan jiya yaje gurin Autar Hajiya ta saki jiki sunyi magana ta fahimta, wacce rabon daya
samu haka tin ranar da tasan ze auri Fadila.
Ana saura kwana biyu d'aurin aure sadiyya tazo gidan su Auta, da sallama ta shigo, gidan cike
yake da 'yan'uwa da abokan arzi'ki, bayan ta gaisheda mutanen dake tsakar gidan, sannan ta
wuce kitchen inda ta hango Hajiya tana faman had'a wasu kaya, tace "Hajiya ina wuni, Hajiya ta
amsa da "lafiya lao sadiyya, ya mamarki, tace "lafiya lao tace a gaiaheki, kuma tace abaki
hakuri bazata samu zuwa yau ba sai zuwa gobe, saboda tayi ba'ki, cikin fara'a Hajiya tace "ba
kome wallahi Allah kaimu goben, sadiyya ta amsa da Ameen, sannan ta tambaya, "ina Autar
take? Tana d'aki ki isa, tana ciki.
Kwance take kan godo ta juya fuskarta ta kalli bango, tayi lamo kamar me bacci, muryar
sadiyya taji tana cewa "Amarya bakya laifi koda kin kashe d'an masu gida......
Auta tayi kamar bata jita ba, dan ko motsi batayiba, daga inda take kwance, sadiyya ta matso
kusa da ita ta zauna gefen gadon, takara magana karo na biyu, "Amarya......., nan ma shiru
Auta tayi mata, sadiyya ta'kara magana karo na ukku cikin jin haushi ta kaimata duka, tare da
fad'in Auta banison rainin wayo, ya inata maki magana zaki wani sahareni......
Da sauri Auta ta tashi zaune tana Sosa inda sadiyya ta doketa, tana murmushi, tace "ina jinki
wallahi, abinne naki yabani haushi da kika kirani amarya, aini nafi 'karfin amarya sai uwar gida,
sadiyya tayi dariya tace to ai kinsan dai Fadila ta girmeki saboda haka itace babba, kuma itace
uwar gida kekuma amarya, Auta tace "tab wallahi bazan yardaba, badai ance d'akin wacce
yafara kwana ba itace uwar gida, to wallahi d'akina ze fara kwana.
Sadiyya ta kyalkyale da dariya, dan ita yanzu rigimar Auta dariya take bata,tace "to yanzu ba
wannan ba kitashi muje gurin gyaran jiki, Auta tace "ke nifa na gayamaki ba wani gyaran da
zanyi, a kaini haka yanda nake, wallahi sadiyya konayi niyyar yin wani Abu da natuna ba
nikad'ai za'a kai gidan khaleed a matsayin matar saba sai inji duk na sire,
Sadiyya tayi murmushi, tace "Hmm auta kenan, to ay yanzu yakamata ki gyara, dan na tabbata
ita waccan bazata zauna hakaba, kema dagewa zakiyi, ki gyara kanki yanda koda kin jera da
waccan aga kamar sarauniya da baiwarta.
Suduka suka kwashe da dariya, haka sadiyya ta rarrashi 'kawarta harta yadda sukaje gurin
saloon, Daga nan suka wuce gurin 'kunshi,
Basu dawo gida ba sai gab da magrib, suna dawowa, sadiyya tayo Alwala ta kabbara sallah, ita
kuma sadiyya wanka tashiga, bayan tafito Daga wankan ta haye gado tayi kwanciyarta,
kasancewar tana fashin sallah, bayan sadiyya ta idar da sallar ne suka cigaba, da tattauna
yanda party da za'ayi gobe ze kasance, dan kuwa partyn Baki d'aya za'a yishi da fadila da Auta,
kuma kowace da 'kawayenta.
Zee Elkaseem
Mmn khady
[03/08 11:57 am] .:
*AUTAR HAJIYA*
®NWA
_ZEE MMN KHADY_
_*Page*_ 66-70
✍washe gari ana gobe d'aurin aure, yau ne aka shirya wani 'kawataccen party Wanda Za'ayi a
liyafa parlance dake cikin garin katsina, duka a 6angarori guda ukku, kowane yana cikin shiri,
khaleed da abokaninsa da 'yan'uwansa, Autar Hajiya ma da 'yan'uwanta da 'kawayenta, haka
ma Fadila, tana cikin shiri itada 'kawayenta da 'yan'uwanta.
Da misalin karfe hud'u za'a fara aiwatar da partyn, sabida haka kafin lokacin Fadila ta gama
shiryawa, wani tsadadden material ne red colour tasanya dinkin riga da siket, kayan sun
matseta sosai, abinka game jiki, kirjinnan kamar ze fasa rigar, kanta kuma golden gwagwaro ta
d'ora takalmanta masu masifar tsini, wanda suka taimaka gurin 'kara mata tsawo, suma golden
colour, sai wata 'karamar jaka dake hannunta itama kalar golden, kallo d'aya zakama Fadila
kasan amarya ce, fuskar nan tasha make-up, dan me kwalliya ta d'auko ta musamman ta gyara
mata fuskarta, ta biyata kud'i me yawa.
A 6angaren Autar Hajiya kuwa zaune take itada 'kawayenta, anata labari anata shewa, ko
kad'an Auta batada niyyar yin wanka barantana ta shirya, sadiyya ce ta duba agogon wayarta
sannan ta kalli Auta tace, Auta kinsan kau 'karfe nawa yanzu? amma ko niyyar shiryawa
bakiyiba, kafin tayi wata magana, taji 'karar wayarta, tana dubawa taga sunan Ahmad, wani
abokin khaleed ne, hannu tasa ta d'auki wayar sannan ta dannan OK ta kara a kunne tare
dayimashi sallama, a d'ayan 6angaren Ahmad yace Ku fito gamu kofar gida muna jiranku,
Tayi saurin tashi tsaye tare da dafe 'kirji tace kuna waje fa kace, yace "eh tace "gashi kuma
bangama shiri ba, yace owk bari muje gidan su Fadila, idan kingama mundawo, bejira abunda
zata fad'aba ya tsinke wayar.
Da sauri tashiga toilet tayi wanka, tana fitowa ta d'auko wani lotion me dad'in 'kamshi ta shafe
jikinta dashi, sadiyya ce ta 6ata lokaci gurin yima Auta make-up, tin nan Auta tafara yin kyau,
fuskar nan kamar wata balarabiya, ga kunshinta Wanda yayi masifar kyau, manyan Flowers ne
yayi bakikirin sai Jan ranin daya 'kara 'kawata kunshin.
Wani tsadadden farin Swiss less ne, Wanda yasha ado da flowers silver colour ta sanya dinkin
doguwar riga, rigar ta kar6i jikinta dan ba 'karamin kyau tayimata ba, sannan ta sanya, takalmi
silver colour, sai yar post d'in hannunta itama silver colour,kanta kuwa gwahgwaro me ta d'ora
shima kalar silver, tayi masifar kyau, sannan ta d'auko turarurruka masu dadin 'kamshi ta feshe
jikinta dasu.
Sadiyya ta kalleta tace Amarya kinsha 'kamshi, Auta ta harareta, cikin wasa tace "kin manta,
sadiyya tayi dariya tace "oh sorry tuba nike Amarya uwar gida, Auta tayi dariya tace "ki karani
kirani Uwar gidana
Kawai,
Sadiyya tace "to uwar gida sarautar gida, suduka suka kyalkyale da dariya.
Suna cikin wannan sukaji tsayuwar motoci, Ahmad, yakirasu yace su fito gasu a waje, nan aka
fafa d'ibar 'kawayen amarya ana kaisu.
Daga karshe kuma aka d'auki Auta da wasu sauran 'kawayenta dasuka rage.
Zee Elkaseem
Mmn khady
[10/16, 7:55 PM] +234 816 616 9254: [03/08 9:43 pm] Zee Elkaseem:
*AUTAR HAJIYA*
®NWA
_ZEE MMN KHADY_
*_Page_* 71-75
✍ Hall d'in cike yake ma'kil da 'yan'uwa da abokan arziki, tun daga kan 'yan'uwan khaleed da
abokaninsa, har zuwa 'yan'uwan Autar Hajiya da kuma 'kawayen Fadila da kuma 'yan'uwanta,
Kowa yayima kansa mazauni, ana jiran shigowar ango da Amarensa, Autar Hajiya da Fadila.
Bayan hall din yayi shiru, sakamakon Mr DJ daya fara magana cikin speaker's dinshi, Kowa ya
maida hankali ga yanda yake jawabi.
Can na hango Ango khaleed da Amarensa sun jero, tsakiya suka sanyashi, Auta na gefen
damarsa yayinda Fadila ke gefen hagu, suna tafiya ahankali cikin nutsuwa, kallo d'aya
zakayima Auta ka fahimci tana cikin wani yanayi, dan yanda taga Fadila ta wani shishshigema
khaleed ta kama hannunshi ta ri'ke abin ba 'karamin takaici yayi mata ba, tin nan tafara tinanin
me zatayi ta ba'kantama fad'ila rai, kamar yanda ta ba'kanta mata.
Sun Isa high table inda nan ne yazama masaukin Ango da Amarenshi, tsayawa khaleed yayi
yayima fad'ila nuni akan ta wuce tafara zama kujerar can, yayinda shi tashi kujerar take tsakiya,
Bayan Fadila ta wuce ta zauna kan kujerar ta, khaleed na niyyar zama kan tashi kujerar kawai
sai ganin Auta yayi kan kujerar, yana shirin yimata magana ne yaji, ta kamo hannunsa, ta wani
kashe Mashi manyan idanunta, tace "ka zauna mana my dear, tare da nuna mashi kujerar da
itace zata kasance gurin zamanta, ba yanda zeyi haka ya zauna, sai tsarin zaman ya canja, ya kasance Autar Hajiya itace tsakiya,
yayinda Fadila ta koma gefe, cikin 'kawayenta.
Wani 'kululun ba'kin ciki ya tsayama Fadila a wuya, ta rin'ka cika tana batsewa, fuskar nan tata
ba annuri ko kad'an duk 'ko'karin datayi na taga ta share da abin ta nuna be dameta ba kasawa
tayi,
Itako Auta sai fara'a take, ta dan du'ko da Fuskarta saitin fuskar khaleed har sunaiya juyo
numfashin junansu, Labari tari'ka bashi shikuma dama abinda, yake nema, sabkda haka ya biye
mata, dan tin lokacin da Auta tasamu labarin ze auri Fadila maganr ta minti goma bata 'kara
had'asuba, Shiyasa ya biye mata sukayita labari suna sakarma junansu wani 'kawataccen
murmushi.
Can zuciya ta 'kule Fadila, batasan lokacin data tashi, cikin tsananin masifa, da bala'i ta fito
daga ida take zaune, ta tsaya gaban tebur d'inda aka cika da kayan ciye-ciye da lemuka
kala-kala, tasa hannu tafara watsi da kayan, 'karar fashewar kofunan glass d'in gurinne ya
maido da hankalin duk illahirin mutanen dake gurin.
Cikin tsananin mamaki Auta ta nufi Fadila, wacce idanunta suka rufe saboda tsabar masifa, ta
ri'ke hannunta tana fad'in "Haba Fadila lafiya, ya muna taron arziki zakizo ki 6ata mana, cikin
tsananin fushi Fadila ta bankad'e Auta, abinka ga marar jiki ta tafi taga-taga zata fad'i dai-dai
lokacin khaleed ya iso gurin yayi saurin tarbeta, ta kuwa fad'a jikinsa tana kukan shagwa6a,
tana fad'in "my dear menayi mata zata tureni? 'Kara rungumeata yayi jikinsa yana rarrashinta,
ita kuwa sai wani 'kara narkewa take.
A fusace Fadila ta nufi hanyar Barin hall din tana zubar da hawayen ba'kin ciki, Ahmad ne
yabita yana cewa, "Fadila ki tsaya mana a gyara, ai bekamata kiyi hakaba, wallahi muna cikin
maganar zamuyima khaleed magana agayara tsarin zaman kawai sai gani mukayi kin tashi kina
wannan d'anyen ayki, cikin dusashshiyar murya tace " Ahmad ka taimakeni ka maidani gida kada zuciyata ta buga bazan iya ba.
Bayanda Ahmad beyiba akan tayi